Showing 33001 words to 36000 words out of 63190 words

Chapter 12 - MALAMIN BOGI COMPLET BOOK by Ameera Adam.pdf

18 Jul 2025

5275

ni ina zan gane wannan yaren naki, Mai Gari za ki yi wa bayani" Banza ta yi da Lami ta
wanke hannunta, ɗaki ta shiga ta haɗo kan kuɗin kayan miyan da ta sayar, akwatin ƙarfen ta ta
buɗe tana zaune a gaban akwatin ta fito da atamfofi guda uku ɗinkakku, wanda a wanke suke
tas sun sha linki takaicin ɗakko atamfofin take ji a ranta amma haka ta zuba a ledar Viva ta fito
ta ɗakko wata samira irin ta ƴan da mai hawa huɗu duk sun yi lamba a jiki, ta ce Lami ta riƙe
mata, ita kuma ta yafa gyalenta ta ɗauki ledar atamfofin ta rufe gidan suka kama hanya a ranta
tana cewa

'Ba saniya ba ko giwa ce Ibra ya gudu da ita in na bada kayan nan ba zan ƙara komai ba' Ta
faɗa tana kallon setin samirarta da yake kan Lami...


MAMAN AFRAH
09025576222




[7/9, 3:38 PM] Mom mashkr & Afrah:
https://chat.whatsapp.com/BcJ4LIJJQlfHRgfiJUnBJo?mode=r_c


‍♂️ *MALAMIN BOGI*‍♂️


NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.�

Daga marubuciyar:

Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*



BOOK1️⃣
PAGE 9


*SHEIK*

Jin kamar dai babu alamun wani da zai taho daga ƙofar gidan ya kawo masa ɗauki, wato ya
tabbatar muryarsa bata isa waje ba, don haka yanzu kam matar ta cim masa ba zai iya ma bari
ta cigaba da azabtar da shi ba, dakyar ya ƙwace kansa ta shiga binsa da gudu suna tsere a
ɗakin bai ankara ba sai ya ji ya kama rigarsa daga baya a haka yake gudun tana jansa tana
rinjayarsa kasancewarta ƙatuwa ta fishi ƙiba, sai ya zamana dakyar yake iya gudun kasancewar
rigarsa jallabiya ce a zuciyarsa ya ce

'Ina ganin ikon Allah, in ban da maluntar nan da na ɗakko ta larabawa ina dalili mutum zai kafa
fama kullum da doguwar jallabiya kana tafiya tana taɗe ka' Ya faɗa a daidai lokacin sun zo saitin
ruwan da ya ajiye, wanda yake kwalfa yana ba mutane, ruwan ne suka ture ya zube, tsautsayi
ya sa suka shiga ciki gabaɗaya Sheik ya yi gaba ya yi baya ji kake tim santsi ya kwashe shi ya
faɗi, ya yi zaman ƴan bori a cikin ruwan ita ma tana ɗora ƙafarta sai ta zame ta tiƙu da ƙasa.

A reran ta je ƙasa, ganin haka Sheik ya yi ta maza ya daure ya matso don ba ƙaramin buguwa
mazaunansa suka yi da ledar ba, qulhuwallahu ahad ya shiga karanta mata yana tofa mata sai
dai wannan karon ba tofi ƙarami yake yi ba tsabar bala'in da yake ganinsa a ciki, yawu kawai
yake tofa mata ba kaɗan ba.
Karkarwa ya ga jikinta yana yi kuma ya fahimci kamar jikinta ya yi sanyi alamar aljannun za

su sake ta, da hanzari ya janyo hularsa ganin ta ɗan leƙo daga bireziyar da ta saka ta a ciki, bai
sake bi ta kanta ba sai ya shiga suturta kansa wato ya saka hularsa da gemun, mukullin ya gani
a inda ya faɗi daga hannunta ya ɗauka ya buɗe ƙofar yana mayar da numfashin wuya, jin
maganar wani mutum yana rafka sallama sai Sheik ya ɗauki wata ƙatuwar bulala da take ajiye
ya ɗaga ya tsulawa matar nan da ƙarfi ta ce

"Zan fita" Gabansa ne ya faɗi sai yanzu ya fahimci ashe aljannun basu saka ta ba, sai ya ji
mutumin nan na waje yana cewa

"Ah ashe dai ruƙiyya ake yi wa matar nan, shi ya sa ta daɗe ta bar mutane a layi ana jiran
fitowarta, bari in fita in faɗawa jama'a halin da ake ciki" Ta haka Sheik ya fahimci cewa mutumin
da ya shigo ya zo ne ya ga dalilin daɗewar matar.

Can kusa da katifar ya koma yana raɓe, har sai da ya ga matar rana sakin atishawa wata
ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke ganin yana sha n wahala a maluntar nan ta BOGI amma ƙarfin
hali da sa kai wanda ya fi wauta ciwo ya hana shi barin maluntar bogin.

Duk da ya san yana amfani da maluntar yana damfarar jama'a bayan ya san shi jahili ne babu
abin da ya sani, ko surorin qur'ani da yake karantawa izun ƙasa ne, tun lokacin yana zuwa
makaranta kafin ya kangare da ya kangare kuwa ai makarantar ma ba ya zuwa. Ko karatun
bokon ma ko secondary bai gama ba.
Zaune ta tashi tana kalle -kalle ta ce

"Waye ya kawo ni nan" Sheik ya ce

"Magani aka miki maza tashi ki je gida, kike shan sauran ruwan alwalar la'asar da magriba,
sauran aljannun kan naki za su kama gabansu" Shiru ta yi ba don ta gama fahimta ba, ta
muskuta ta tashi tana ganin yadda duk ta jiƙe, fita ta yi Sheik a fili ya ce

"Gwara in faɗa miki bogi ki tafi yo ina na ga nutsuwar baki magani ma ki je ki ƙara shaƙo ni, ni
na rasa mai hular gashin nan nawa ta yi wa aljannu da mutane, duk abin jikina ba a kaiwa
komai farmaki sai hula ta" Ya faɗa yana gyara zaman hular, yana tuno artabun da ya sha da
aljannu suka ɗauke masa ranar nan.

Dakatar sa masu shigowa ya yi, ya sauya jiƙaƙƙiyar rigarsa ya goge ruwan, a haka ya cigaba
da karɓar mutane suna bashi kuɗin yana tarawa ransa fari ƙal yake ji idan ya kalli kuɗin nan
yana zaune yake samu.

Sai da ya gama da jama'a ya ce sai kuma gobe za a cigaba da karɓar mutane.

Tun daga wannan rana Sheik ya zama limamin garin Ƙundu, shi yake jan sallah, sai dai
waɗannan ƙananun surori na ƙasa su ne kullum yake jan sallar da su, idan yana jan sallah ya
ƙara maƙe murya ya lanƙwasa sai ka ɗauka cewa a masallacin makka ne ake jan sallar amma
dai a wajen mutanen Ƙundu, saboda su ne basu gama tantance asalin karatun balaraben
mutum da kuma Sheik baƙar fata wanda mayuka da sabulai suka wanke masa fata. Idan za a yi
sallah mutanen ƙauyen kafin Sheik ya zo masallaci sai masu manyan wayoyi adroid su zo su
kunna recording su ajiye wayoyin, daga an yi sallah an idar, sai ka ga idan sun fita daga
masallacin suna samun wuri su kunna, suke ji sai ka zo wucewa ka ga mutum ya duƙufa da
earpiece a kunna sai dai ka ji yana faɗin

"Allahu akbar, uhmmm, ma sha Allahi, Allah ƙara lafiya babban malamin ƙasar larabawa"

Sai ya zamana hatta mata masu waya sai su ba mazajen su, wayar in za su je masallaci su
ɗakko musu sallar Sheik.

Wanann dalilin ne ya sa Mai Gari ya ce Sheik ya musu karatun qur'ani wanda za suke saurara
a waya, na izu sittin irin wanda ake turawa na su Ahmad Sulaiman da yake Mai Gari yana da
irin su a waya. A nan ne fa gizo yake saƙa, don Sheik ya san dai bai sauke qur'ani ba hakan ya
sa ya ƙaƙalo ƙarya kamar yadda ya saba ya ce
"Ai an fi so mutum yake sauraren abin da ya iya, wato tun da basu sauke qur'ani ba ba za suke
saurara, na fi so kuke sauraren izufin ƙasa saboda kuke biyawa yadda za ku ƙara ƙwarewa a
hadda" Ya faɗi haka don ganin ya tsira daga tarkon wannan, hakan sai ya sa Mai Gari ya
gamsu Sheik ya musu rukodin ɗin iya surorin ƙasa da ya iya, suke saurare.
Batun magani kuwa duk waɗan da Sheik ya ba magani sai suka zo suke godiya da saka
albarka a cewarsu magani ya musu amfani, saboda Sheik yana zama ya yi wa'azi a kan cewa
ba a ƙaryata malami ko a tuhume sa, hakan ya sa ko da mutum bai ga amfanin magani ba sai
yaja bakinsa ya yi shiru, sannan ma dama duk abin da aka baka a matsayin magani in dai ka
yarda cewa zai yi to ko ba maganin bane yana maka magani.

Bare kuma Sheik da yawanci matan dama kissa ce yake faɗa musu, da kyautatawa mijin
kuma ko wanda ya ce mata suna gudunsa saboda muninsa da ya je ya yi abin da Malam ya ce
na bayar da kuɗi ga budurwa sai gashi ya samu mai son sa har an ɗaura aure, hakan ya sa
kowa ya ƙara yarda da maganin Malam. Sanann masu aljannu yana cewa suke karanta nas da
falaƙi kullum wanann ya sa suke samun kariya tun da sun yi amfani da ayar qur'ani, idan kuma
aljannun wanda ya fitarwa suka aara tashi, sai ya ce dama ciwo na ɗaya rana ne sauƙi sai a
hankali.


Duniya ta yi wa Sheik daɗi yana cin karensa babu babbaka, gabaɗaya ya ƙara ƙiba saboda
cin kayan daɗin da yake, duk da cewa yanzu Mai Gari yana sanyawa a masallaci ana haɗa
sadaka to da su yake amfani wani lokacin ana ciyar da Sheik, sannan wasu ma suna kawo

gudunmuwar kaji, wasu zabbi wasu ma dama idan daga rugar da suke maƙotaka da Ƙundun za
su zo magani da kaji da nono suke zuwa a matsayin abin sadaka.


Wata rana ana zaune Sheik yana faɗakarwa, Liman sai muzurai yake don shi yanzu bashi da
maƙiyi sama da Sheik, tun da an ƙwace masa Limancinsa wanda tun yana saurayi yake yi. Duk
da a ganin Liman ɗin Sheik ya fishi ilimi kuma yana karatu irin nasu na larabawa amma dai duk
da haka yana jin haushi.
Wani ne ya ɗaya hannu ya ce

"Ya Sheik ni ina so a fassara min Assalamu alaikum, kuma a fassara mini karatun cikin suratul
fatiha wacce ake karantawa a kowacce sallah, ina so in san me yasa a kowace sallah sai an
karanta ta?" Ƙululuuuu cikin Sheik ya bada wani sauti a hankali ba tare da kowa ya ji ba.

A zuciyarsa ya ce

'Na shiga uku yau an ƙure ni?' A fili kuma sai ya ce

"Ma sha Allah, su'alun mai kyau" Ya faɗa yana ɗan lashe baki.

Gabaɗaya waje ya kaure da cewa

"Yawwa ni ma ina so in sani" Kowa sai ya ce yana son ya sani har Mai Gari. Da gangan Shei ya
tsiri wani tari yake yi ba ƙaƙƙautawa daga tarin ya lafa sai ya ce

"Ma sha Allah ya ikwan... Sai kuma ya sake fara tarin alamar tarin ba zai bar shi ya yi magana
ba, nan aka shiga masa sannu aka kawo masa ruwa amma ya ƙi dainawa saboda dama da
gangan yake tarin saboda bai san amsar da zai bayar ba.

Ganin haka sai Mai Gari ya ce Sheik ya je gida ya huta, daga haka maganar fassarar ta sha
ruwa.

Wata rana da daddare Sheik ya fita daga gida ya saci hanya, gidan wani matashi da yake
babu nisa da inda aka sauke shi ya je, ƙogar gidan ko kara ta ba a yi ba kasancewar sairayin
yana shaye-shaye idan ya dawo daga yawonsa a buge sai ya shiga ya kwanta. Can Sheik ya
shiga ya ga sausayin kwance a tsakar gida a ƙasa yana bacci. Machine ɗin saurayin ya ɗauka
ya fito daga gidan, sai da ya ɗan tura machine ɗin ya wuce gidan saurayin, ya tada mashin ɗin
dama ko mukulli ba a sakawa mashin ɗin a hakanake tashin sa.

Hawa ya yi ya tafi ƙauyen da malamin wanda Sheik yake karɓar maganin da yake ba
mutane, ya same shi ya bashi kuɗi mai yawa daga kuɗin da yake samu, nan malamin ya bashi
magungunan amma Sheik ya ce maganin matsalolin mata ya fi yawa saboda sun fi zuwa da

matsaloli. Ya bashi kuɗin mayukansa da sabulai da turaren oud da sunayen su a rubuce ya ce
zai dawo ya karɓa, dama malamin yana zuwa birmi. Bayan ya karɓo ya dawo gidan saurayin ya
akiye mashin, ya tafi gidansa.

Yau ta kama laraba misalin ƙarfe goma Sheik yana zaune a ɗakinsa yana karantar ƙamus mai
larabci da hausa, yana ta haddar kalmomin larabci don ya haddace saboda sakowa a magana,
duk da cewa ya san ko kwaɓa larabcin ma ya yi ba ganewa suke yi ba, Allah ma da ya taimake
shi rubutun larabcin akwai inda aka yi fassarar hausar larabci.
Shigowar mutane ya ji zaure gidan suna rafka sallama kamar dai ma a kiɗime suke, da sauri
ya mayar da littafin ya tashi ya hau sallaya, jin suna ta cigaba da sallamar sai ya shiga jan
gyaran murya alamar baya rabuwa da bauta da ibadad kowane lokaci.

Jin suna ɗan surutai sai ya saurara ya ji suna cewa

"Ai shikenan kuma matsalolin Ƙundu sun fara dawowa, har muna murya an maganace ashe dai
da sauran rina a kaba" Didimmm ƙirjinsa ya buga, kafin wani yinƙuri sai ya ji muryar Mai Gari
alamar shi ma ya shigo yanzu, ya ji Mai Gari cikin karkarwar murya yana cewa

"Kabarin Hashimu da na wa hallaw?"

Sheik ya ji wani ya ce

"Da kabarin Fatsime" Gabaɗaya Mai Gari ya kwashi salati. Zufa ce ta fara ketowa Sheik jin ana
maganar kabari shi dai duk da bai fahimci kurman baƙin ba amma dai ya san shi ne a cikin
matsala tabbas.

Haka ya koma ya zauna daɓas sai da ya ji ya ɗan samu ƴar nutsuwa sannan ya buɗe baki ya
ce

"Bismillah a shigo" Ya faɗa yana janyo dogon carbinsa mai dubu ya fara ja yana mismis da baki
tsabar rikicewar da ya yi shi kansa bai san abin da yake faɗa ba.

Su duka suka ɗoro ɗakin Mai Gari ne a kan gaba sai wasu mutum huɗu a bayansa.

Mai Gari yana baza malun-malun ya zauna amma kana ganinsa ka san babu lafiya, yana
zama ya ce

"Barka dai Ya Sheik" Sheik sai da ya yi yaƙi da idanunsa wajen ganin basu bayyana taoron da
yake ciki ba tsumu-tsumu don shi a duniya in dai maganar aljannu ne da maganar mutuwa to ya
ƙi jinin maganar nan, ko kabarin mai Ƙusumbi da yake zaune a gidan da shi saboda, kar ya
bayar da kansa a ga gazawarsa, don dai ba yadda zai iya kuma yana son samun kuɗi ba ya so
ya bar garin wato ya bar cima mai daɗi da kuma samun kuɗi, shi ya sa yake wanann siyar da

rai, to in ba siyar da rai yake yi ba kake tunkarar aljannu kai tsaye, bayan shi ƙasurgumin jahili
ne ya shiga MALUNTAR BOGI.

Amsawa Sheik ya yi yana ɗan washe bakin dole, duk gumi ya wanke masa goshi, saboda lura
da ya yi da sauran mutanen nan su a tsugunne suke basu zauna ba, hakan duk yana nuni da
ana cikin ruɗu da masifa.

Mai Gari ya ce

"Ya Sheik abu ne na gaggawa, garin Ƙundu babu lafiya, wannan ƙaiyen da muke maƙotaka da
su ne maƙabartar su ta cika, to shi ne idan aka yi rasuwa sai su kawo maƙabartar garin nan su
binne, yanzu wani yaro ne ya mutu a garin sun zo ya za su binne shi aka samu gawa biyu an
tono su daga kabari, kuma an ce masu haƙar kabari da suka zo suka tona kabarin da za a
binne yaron lokacin da suka gama kabarurrukan da aka tone lafiya lau ba a tone suke ba, sai
yanzu da suka zo suka tarar da hakan, kuma sun ce ɗaya gawar da aka tone ta yi motsi bayan
ta shekara nawa a binne, yanzu dai sun bar gawar yaron a maƙabartar kowa ya gudu" Mai Gari
ya faɗa yana ɗago kai ya kalli Sheik.

Tun da Mai Gari yake bayani ƙirjin Sheik yake fat-fat-fat, ya yi wani tsumu-tsumu tamkar an
tsamo ɓera daga ruwa, dama sunkuyar da kansa ya yi idanunsa suna kallon ƙasa don kar su
fallasa asirin zuciyarsa na tsoron da ya ji ya kunyata.

Sheik ya ɗago da kansa idanunsa tamkar wanda aka tada daga baccin sa yake mafarkin tsoro,
ya yi wujiga-wujiga, ruwan da yake gefensa a kwano ya ɗauka ya kurɓa, bayan ya ce musu da
sai ruwan roba da na leda yake sha, ajiye kwanon ya yi ya ɗago carbinsa yana ja tsabar ya ruɗe
ma ba ɗaɗɗaya yake jan carbin ba, wani lokacin ƴaƴa goma wani lokacin biyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login