Showing 36001 words to 39000 words out of 63190 words

Chapter 13 - MALAMIN BOGI COMPLET BOOK by Ameera Adam.pdf

18 Jul 2025

5278

kawai ja yake
babu ƙaƙƙautawa, sai da ya ji zuciyarsa ta daina bugun da in ya yi magana za a harbo jirginsa
na tsoro ya yi ta maza ya ce

"Subhanallahi, subhanallahi, subhanallahi, wannan aikin aljannun garin ne yanzu abin har ya kai
a tono gawa a kabari kai abin ya girmama, yanzu ya za a yi?"

Ya tambaya har lokacin tamker ana fisgo maganganun daga bakinsa. Ɗaya daga cikin
mutanen ne ya ce

"Ya Sheik yanzu dai ka yi gaggawar zuwa maƙabartar nan ka rufe kaburburan da aka tone,
gudun kar a yi bori da sanyin jiki su cigaba da tone sauran kaburburan maƙabar nan, tun da
hatta yaron nan da ya mutu yana nan ajiye a makara ba a binne shi ba, an bar sabuwar gawa
ajiye a maƙabarta" Nannnauyar ajiyar zuciya ya sauke wacce ta kasa ɓoyuwa a ɗakin ya ce
"Tabbas wannan iblisan aljannu ne, da ifiritai" Mai Gari ne ya zaro ido duk da yana ganin za a
magance matsalar garin amma jin wannan sunaye na aljannu ya ƙara rikita shi ya ce

"Yanzu waɗanann aljannu ya za ka yi ka fitar da su daga garin nan, bayan ƙauyen ya yi lafiya
amma kuma yanzu za su dawo mana da hannun agogo baya"

Sheik ya ce

"Kar ku damu, na taho daga ƙasarmu ne don in kawo ɗauki ga mutane masu neman taimako
babu gudu babu ja da baya" Ya faɗa yana miƙewa tsaye, ganin haka sai suka fita suka bar shi,
gabaɗaya ji yake kamar ya rufe ido ya gan shi a garinsu MAI MANGWARO ji yake kamar dai ya
bi wata hanyar ya bar garin ba tare da sanin kowa ba, sai dai wata zuciyar tana tuna masa irin
badaƙalar da ya baro a garinsu, da basussukan da ake binsa kuma dai bai akiye ba bai bayar
ba ajiya, ya san tabbas in ya koma zaman banza ne zai cigaba da yi, amma tun da ya samu
sana'a a nan dole ya jajirce.

Ruɗin da yake ciki ya sa bai rataya hiramin a wuyansa ba kamar yadda yake saƙalawa, yau
sai ya masa naɗin gwaggwaro, daga gaban goshin ma naɗin ya ɗan zamo ya karkace sai ya yi
tamkar tsohuwa, ya ya ɗauki zumuƙeƙen carbinsa, ya ɗauki littafinsa na ƙamus, sai wani ruwan
magani da ya karɓo cikin magungunan da ya siyoa wajen malaminsa, shi tsabar ruɗani ma ya
manta ko ruwan maganin mene ne.

Yana fitowa ƙofar ɗaki ya ga saka takalminsa ya ga su Mai Gari tsaye suna jiransa, fitowarsa
ke da wuya duk da ruɗun da suke ciki sai suka fara magana cikin girmamawa.

"Allah ya taimaki balaraben Malamin, Allah ƙara ilimi, haƙiƙa mun samu jajirracce da yau sai dai
kowa ya yi hijira daga garin nan don ba za mu iya da wanann aljannun ba" Sheik a zuciyarsa ya
ce

'Kwa mini kirari mana tun da kun haɗani da aikin tsohuwar gawa da sabuwa, yau ai sai ta Allah'
Ya faɗa yana yin yaƙe tare da ƙara ƙanƙame littafinsa a ƙirjinsa yana jan carbin haka suka fito
daga gidan bayan ya kulle ƙofar.

Abin da basu sani ba shi ne, Sheik ya fi su shiga ruɗani da tashin hankali.

Tun da suka fito tsakiyar garin maza suka fara tururuwa don sai lokacin, suka ji ƙarfin gwiwar
fitowa tun da Sheik ya fito gani suke aljannu ba za su fafata da Sheik ba ko su ja da shi.

Sheik ne a gaba mutane gari suna take masa baya, sai wani bada faɗi yake shi ala dole
masanin qur'ani da addu'o'i, ana cikin tafiya, sai lokacin ya kalli ƙafarsa, idanu ya zaro ganin
takalman ƙafarsa gamin bauta ne, wato takalmin ƙafar dama takalminsa ne sandal amma kuma
na ƙafar hagun ne ba wai na ƙafar dama bane, don haka a juye yake, shi kuma takalmin ƙafar
hagun ɗin silifas ne na wankansa, amma kuma ƙafar dama ne a hagun ɗin wato dai shi ma a
juye yake a zuciyarsa ya ce

'Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, mutanen garin nan kun saka ni a masifa, da tashin hankali tun

da uwata ta haife ni ban taɓa wannan gamin bautar takalmin ba, amma yau saboda kun jefani a
ruɗani gashi nan, takalmin kwalliya da na wanka na saka, su ɗin ma kowanne ba ƙafar ba ce'

MAMAN AFRAH
09025576222
[7/10, 4:03 PM] Mom mashkr & Afrah:
https://chat.whatsapp.com/BcJ4LIJJQlfHRgfiJUnBJo?mode=r_c


‍♂️ *MALAMIN BOGI*‍♂️


NA

MAMAN AFRAH


First Class Writer's Asso.�

Daga marubuciyar:

Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*


BOOK1️⃣
PAGE 10



*MAƘABARTA*

Tun da Sheik ya lura da takalminsa sai ya wayince ya je kusa da Mai Gari ya masa raɗa
cewar garin saurin ya zo ya ceci gari ya sako takalmi ba iri ɗaya ba, Mai Gari ya ce

"Allahu akbar! Tabbas Sheik kana ƙaunar garin nan" Nan ya nuna masa babu komai ruɗun da
jama'a suke ciki ma ba zai bari su lura da takalmin ba, kuma ko sun lura ma sai a musu bayani.
Wannan bayanin ne ya sa Sheik ya ji daɗi tun da ya lura yanzu dai ba za a zargi cewa tsabar
ruɗani ne ya sa ya sako takalmi gamin bauta ba daidai ba.
Tun da suka zo dab da maƙabarta Sheik gabansa ya fi na kowa faɗuwa, amma a haka ya
daure yake jan carbi, da yake maƙabartar ƙauyen ba a kewaye take ba, sai dai akwai bishiyoyi
da suka mata ƙawanya, sannan akwai hanyar da aka ware don ake shiga ta wajen.


Gabaɗaya jama'ar sai suka yi turus kowanne yana tsoron shiga, Sheik ne a kan gaba
sannan suka mara masa baya. Suna shiga jikinsa yana karkarwa amma sai ya maje ya nuna ba
karkarwa jikin nasa yake ba, mutane gabaɗaya suka tsaya suna jiran su ba abin da zai faruwa,
kowa yana gefe.
Ƙarasawa ya yi gaban kabarin guda biyu gabansa yana faɗuwa, kallon ɗaya da aka tono ya
yi, wani yawu ya haɗiye muƙut ya juya ya kalli Mai Gari ya duk kamar a ce asss su zura da
gudu, ɗan wayincewa ya yi ya ce

"Babu tsoron Allah a wannan lamari, a ce a tone gawa tsohuwa da sabuwa, kai Allahumma
ajirni min wannan mummunan aiki, ya subhanallah," Ya faɗa yana girgiza kai irin na malamin da
ya ga an yi wani aiki marar kyau.
Wani ne daga cikin tawagar mutanen ya ce

"Ni fa a hanya na haɗu da masu binne yaron can, na ji suna cewa wai ji suka yi yaron ya saki
kuka shi ne aka rasa mai tsayawa a cikin su...

Kafin saurayin ya gama magana Sheik ya kai hannunsa mai carbi ya sharce gumi, ya ce

"Alkazibu, ƙarya haramun, babu gawar da za ta yi kuka" Duka wurin babu wanda ya tona don
shi Sheik sani ne bai yi ba kafin ya zo garin wataran tsakiyar dare ake jin ƙaran turmi ana daka
a cikin maƙabartar ko dai a ji ƙaran injin markaɗe, abubuwa dai barkatai.

Mai Gari ya kalli Sheik ya ce

"Ya Sheik ko da matsala ne?" Sheik ya ce

"Ah haba matsala da kanta ƙarya take ta doshi balaraben Malami daga Yemen" Wani sanyi ne
ya ratsa zukatan mutanen wajen.

Sheik ya matsa gaban gawar guda ɗaya, ya buɗe littafin hannunsa, ya shiga dubawa kamar
mai duba qur'ani ki littafin addu',oi ya ji ya kasa komai so yake ya karanta wata addu'a ko sura

amma bakinsa ya ƙi basa haɗin kai, ganin haka ya juya ya kalli jama'a ya ce

"A karanto" Suka kalle shi da rashin fahimta.

"Mai za a karanto?" Mai Gari ya tambaye shi

Sheik ya ce

"Kowa ya karanta karatun da ya iya" Ya faɗa don shi ya kasa saamun kowacce sura ma bare ya
karanta, haka kowa ya buɗe baki yana karatu a nan Sheik ya fisge wata surar ya fara, kowa
yana kaiwa ƙarshe sai aka yi ɗif, matsawa ya yi ya ɗauki shebir ya fara kwashe ƙasar kabarin,
saboda gabaɗaya ƙasar ta koma ta rufe inda za a mayar da mutumin yana cikin kwasowa ya ga
cinyar mutum a ciki, gabansa yana faɗuwa ya juyo zai sanar da mutane tun da su suna can
baya sun bashi wuƙa da nama.

Kafin ya furta komai sai ji ya yi gawar wajen ta saka ƙafa ta tura shi sai ga Sheik ya kusa ya
faɗa ciki, dakyar ya yi nasarar komawa gefe yana haki lokacin mutane duk sun ƙara ja baya,
littafinsa da ya ajiye ya ɗauka tare da maganin nan da ya ɗakko na wajen Malam yana nufo
mutane gabansa yana faɗuwa don ya tabbatar gawar nan ta tura shi gashi tsohuwar gawa.
Yana zuwa ya ce

"Kar ku damu wannan ba wani abu bane, akwai siddabarun aljannu a lamarin, kuma wannan
mayar da gawar kabari ba na mutum ɗaya bane ku matso mu taru mu yi aiki tare" Kowa ya fara
zare ido Sheik ya ga suna masa kallon tuhuma.

Da sauri ya nuna musu robar maganin hannunsa ya ce

"Wannan magani ne daga ƙasar Yemen na taho da shi idan aka yayyafa a bakin kabari aljannu
suna guduwa cikin daƙiƙu" Si ya ga kowa ya ɗan saki jiki.

Bai nuna musu ya ga cinya a cikin ɗaya kabarin ba haka suka mayar da gawarwarkin don sun
yarda da maganin da Sheik ya barbaɗa basu san cewa shi kansa Sheik ɗin bai san maganin
mene ne ba wataƙila ma yana cikin magungunan mallakar da za a ba mata.

Kabarin yaro nan ne kawai ya rage, Sheik ya ce tun da ba gawar garin ba ce a nemo ƴan garin
su zo su binne, don tun da ya ji saurayin nan ya ce an ce gawar ta yi kuka sai ya tsorata dama
gabaɗaya ma ƙarfin hali yake yi.

Mai Gari ya ce ai kawai su binne tun da yana cikin tawagar mutane ai su ma garin namu
ƙarƙashin mulkinsa yake. Kai Sheik ya gyaɗa tana wayincewa, sun kewaye kabarin mutane
damƙam, Sheik tun da shi ne balarabe shi ne yake jagorantar komai.

Hannu ya miƙa zai ɗauki yaron , da ya miƙa hannu ta wajen kan yaron sai ya ga kamar ba shi
ya ɗago kan yaron ba, kamar dai gawar ce ta ɗago da kanta, da sauri ya janye hannayensa ya
ɗago sai ya ga ba a lura da abin da ya gani ba, kamar gawar ta san mai yake tunani kawai sai
ya ga ta fara ɗagowa sai ga yaro a zaune dakaka duk da yana sanye da likkafani, Sheik da ya
tashi a firgice ya tsallake yaron sai ƙafarsa ta maƙale da likkafanin da aka ƙulle ƙafar yaron
yana fisga ya yi tsalle da yake yana ɗaya gefen ne Mai Gari kuma suna ɗaya gefen, sai lokacin
kowa ya lura da abin da yake faruwa, tun da dama gawar yaron daga can gefen kabarin take ba
a dab da kabarin ba, tsalle ɗaya Sheik ya yi ya tsallake ramin kabarin sai gashi a gaban Mai
Gari ya kama rigar Mai Gari, jama'a kowa ya fara kama gabansa da yake dama maƙabarta ba
wani a kewaye take ba sai kowa ya fara kama gabansa wasu gabas waau yamma wasu arewa,
Mai Gari da Sheik suna cikin mutanen da suka fita ta yamma.

Don Mai Gari ya warce riƙon da Sheik ya masa haka suke falla gudu kowa yana ta kai- ta kai.

Babbar rigar Mai Gari sai tashi sama take, rawanin ya kunce yana binsa yaraf, ko takalmi
babu a ƙafarsa ya sille, Sheik ƙafarsa maƙale da dogon tsumman likkafanin da aka ɗaurewa
yaron ƙafa, haka suka ratsa ta cikin gonaki suna sheƙa gudu, Sheik ya tattare jallabiyarsa
saboda gudun samun akasin faɗuwa, suna cikin gudu da yake Mai Gari ne a gaba Sheik yana
take masa baya, jama'a kuwa kowa ya yi tashi hanyar, kamar daga sama sai ganin wannan
yaron da suka baro a maƙabarta zaune a kan makara ya diro a gabansu, Sheik ya taka wani
uban birki shi ma Mai Gari haka, sai Sheik ya juya a guje ya bi wata hanyar sai tafiyar ta
kasance Sheik ne a gaba Mai Gari a baya gawar yaro tana take musu baya.

Da yake Sheik a wuyansa ya rataya carbinsa, littafinsa yana aljihunsa, Mai Gari ganin gawa
tana son cim masa sai ya miƙa hannu ya kamo carbin wuyan Sheik a haka suke gudu, sai da
suka zo dab da shiga gari Sheik ya ja wuyansa sai carbin ya tsinke, a nan Mai Gari ya saki
carbin, kamar an ce su waiwaya bayansu a tare suka hango gawar bagatatan tana binsu,
wanann karon yaron tsirara ya riƙe likkafaninsa a hannu hancinsa toshe da auduga, yana cewa

"Sheik, Mai Gari ku zo ku mayar da ni kabarina ku binne ni" ,Amma bahu wanda ya tsaya bare
ya saurare shi.

Tun daga gidajen farko -farko suke cin karo da gidaje a rurrufe, alama ce ta gabaɗaya
magana ta ratsa gari tun da dama a tsorace ake da maganar tone kabari bare kuma yanzu aka
ce gawar ta tashi zaune, tabbas sai inda mai ya ƙare shiga motar mahaukaci!.


Sun zo tsakiyar gari suke ganin mutane suna ɓullowa ko ta ina, wani babu takalmi wani hula
a maƙale a hamata wano ya tuɓe rigar ma yana zangaya gudunsa a haka.


Mai Gari maimakon ya yi hanyar gidansa sai kawai ya bi bayan Sheik, Sheik kuwa ganin
gawar yaron tana son cin musu sai ya tura wata ƙofar gida haka Mai Gari ya mara masa baya

suka shige, gidan wata tsohuwa ne wacce kp fita bata iya yi, ɗaki suka bankamu suka rufe suna
mayar da numfashi.

Sheik ya fito da robar magani daga aljihunsa ya buɗe yake tuttulewa a fuskarsa, Mai Gari ma
ya karɓa ya watsa a tashi fuskar sai suka ji da wata muryar yaro an ce

"Ku zo ga likkafaninku, raminku yana can na haƙa muku kabarin" Suna juyawa suka ga yaron
ya ratso ta bango, da rarrafe suka fito Mai Gari yana miƙewa sai gida ya yi, Sheik ma ya yi nasa
gidan yana shiga ya banke ya zauna ya kifa tagumi, carbinsa ɗaya ya ɗauka ya fara ja yana jin
tsoro sosai idan ya tuno wai gawa ce ta tashi da ƙafarta take bin su riƙe da likkafani.
Yana cikin wannan halin ta tuno yadda ya ji wani a maƙabarta ya ce, ya ga wani kabarin yana
motsi tunanin da ya fara kar sai gabaɗaya gawarwakin su fito su bazo gari shi bai san ma abin
da zai ce ba.


Tun da ya shige ɗaki bai fito ba, ranar haka garin ya tsaya cak baka jin motsin kowa hatta
masallaci ma ladan bai kira sallah ba, bare kuma mai gayya mai aiki wato Sheik ya fito ya ja
sallah, to shin wa zai ja sallar ma? Bayan mutanen gari kowa yana gida a ɓame ana tsoron
fitowa a yi arba da gawa.
Salloli dai Mai Gari sai a ɗaki ya samu ya yi alwala a wani kwano ya gabatar sa sallolinsa cikin
tsoro. Ranar dai babu watandar kayan daɗi yo waye zai dafa kayan daɗin.

Ɓangaren Mai Gari ma tun da ya kwasa da gudu ya yi gida, lokacin matarsa ta ji ana cewa
gawa ta bazo gari hakan ya sa ta taho za ta kulle gida, ta tura ƙofar kenan hakan ya yi daidai da
zuwan Mai Gari ya kai kansa ta banko masa ƙofar a goshi, haka suka shiga turarreniyar ƙofar
shi yana turawa yana so ta buɗe masa ya shiga, ita kuma tunaninta gawar da aka ce ta bazamo
gari ce, shi kuma tsoro ma ya hana shi furta komai, saboda ko da ya taho ma ya sha haɗuwa da
mutane kowa yana ta kansa, babu ma wanda ya lura da shi bare a girmama shi, yo shi ina zai
tsaya karɓar girman ma.

Jin yana neman ya ci ƙarfinta sai ta ƙara dagewa ta tura ƙofar, Mai Gari sai cewa ya yi

"Ke buɗe Mai Garin Ƙundu ne" Jin muryar mijinta a rikice sai ta matsa daga ƙofar ko kallonta bai
yi ba ya wuce ta ya shige cikin gida a guje, ganin haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login