Showing 18001 words to 21000 words out of 63190 words
kema kin san alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba, in ba tada zaune tsaye ba, ni yanzu
a kan kuɗin ƙafar kaza ma sai a harbe ni, bare wata saniya, ni ban ci nanin ai nanin bata ci ni ba
ko?" Ƙirji Jummai ta buga tana hayayyaƙowa Inna kamar ta kai mata duka ta ce
"Ai dama ɗan kuka shi yake jawa uwarsa jifa, nima dai kayan marayu ne, don Inna ko kan ki za
ki kai kasuwa a yi cinikin ki masu yankan kai su saye ki yasin sai kin siyar kin biyani kuɗin
saniya" Da wani kuka mai jiniya Inna ta fashe jin ana batun ta sayarwa ƴan yankan kai kanta ta
biya kuɗin saniya, Mai Gari ne a fusace ya ce
"Wai shin ni zan yi hukunci ko kuwa ku za ku yi, idan har ku za ku yi babu amfanin zuwanku,
kuma nima babu amfanin zumana a wajen nan" Mutanen fadar Mai Gari suka haɗa baki wajen
faɗin
"Wannan gaskiya ne ranka ya daɗe, Allah ja zamaninka mai gudumar dukan talauci" Wani zama
ya gyara yana gyara babbar rigarsa, don maganar da ya yi ba iya su Inna ya katsewa hanzari
be har da Lami da ta ƙunso nata maganganun amma sai ta ja bakinta ta ƙunshe.
Mai Gari ne ya shiga faɗin
"Tasallah yanzu magana tana hannunki amma dai kafin nan sai na fara da Jummai, ke Jummai
me ya sa kika cinyewa Lami kuɗi har dubu ɗari biyu?" Ƙeya Jummai ta sosa irin ta mararsa
gaskiya sai ta ce
"Tsautsayi zagin mahaifi" Wani kallo ya mata ya ce
"To in har cinye kuɗinta tsautsayu ne to ke ɗin ma ɗaukan saniyarki tsautsayi ne" Ɗagowa ta yi
tana kallonsa da sakakken baki, sai kuma ta kalli Lami da take aika mata harara kamar idanunta
za su faɗo.
Bai jira cewarta ba ya ce
"Kowa a cikin ku yana da laifi, ke Lami bai kamata ki taka har gidan Jummai ki since saniya a
turke, ki ba mijinki ya kai kasuwa ba, mene ne amfanina a wannan garin, da kin kawo ƙaranta ai
da na san abin yi" Kai Lami ta sunkuyar tana jin haushin Mai Gari ganin zai ɗora mata jakar
tsaba kaji su bita.
Bai ba kowa damar magana ba ya ce
"Yanzu Tasallah kina da kuɗin da za ki biya wanann cakwakiya?" Inna kamar jira take ta sakin
wani kuka mai ɗan sauti tana jin ciwo kayan miyarta da za ta bayar ta ce
"Ya na iya da abin da ya fi ƙarfina, ai dama faɗan da ya fi ƙarfinka wasa kake mayar da shi, ni
nan bani da komai amma ga kayan miyar nan da wannan naira ɗarin da na yi ciniki, su kaɗai ne
na mallaka, ta karɓi jingina har zuwa ranar da Ibra zai bayyana, idan ya bata kuɗin saniyarta sai
ta bani kayan miyata, amma da sharaɗi ko kalwata ko kuka suka yi ciwon kai ba zan yarda ba
yadda zan bata kayan miyar nan salin alin ta ajiye kar ta sake ta taɓa" Ta faɗa tana ɗaga robar
ta juye kayan miyar a kan tabarma a gaban Mai Gari.
Tsabar takaici Jummai bata yi magana ba, ƴan fadar ne suka shiga danne dariyarsu, Mai Gari
cike da takaici ya ce
"Haba Tasallah a gabana kike mayar da babbar magana ƙarama, ana batun saniya kina batun
kalwa da kuka da barkono?" Ɗan karkata kai Inna ta yi ta ce
"To ai kowa da abin hannunsa yake ado, guntun gatarinka ya fi sari ka bani, ita saniya gare ta ni
kuma kayan miya ne Allah ya bani"
Mai Gari bai sake bi ta kan Inna ba, ya shimfiɗa sharaɗin za a jira daga nan zuwa kwana uku,
a ga ta inda Ibra zai dawo, in ya so sai a san abin yi. Haka ya kashe rigimar ba don ta mutu ba,
ya ce idan Ibra ya dawo da saniya ko kuɗin saniya sai Jummai ta karɓi kayanta, sannan ta biya
Lami kuɗinta.
Inna wani irin washe baki ta yi, tamkar ba ita ce wacce take wannan kukan ba, dama kukan
takaicin za a raba ta da kayan miyarta ne. Haka ta kwashe ta saka a robar tana jerawa Mia Gari
godiya, ta tafi gida a ranta tana Allah wadai da halin Ibra mutum kusan shekara arba'in amma
bai san abin da ya kamata ba sai tunani irin na yara.
Lami da Jummau kowa a ƙufule da ɗan uwansa ya bar fadar Mai Gari.
Lami tana komawa gida ta samu kishiyarta Sa'a a tsakar gida tana riƙe da ƙugu, shigowar
Lami ko zaunawa bata yi ba Sa'a ta ce
"Sannu Lami wato ke kin iya ɗauki ɗam baki ajoye ba ko? A kan me za ki ɗaukar mini gayan
tuwo?" Lami wacce take cike da ɓacin ran rashin dubu ɗari biyun ta, da kuma yaudarar da Ibra
ya mata a tsawa ce ta ce
"Sa'a hawainiyarki ta kiyayi rama ta, saboda rainin wayo ni da nake da dubu ɗari biyu kuɗin
adashe uban me zan yi da gayan tuwo, to Allah tsari gatari da saran shuka"
Sa'a hannuwa ta tafa ta ce
"Da ba a san asalin barbela ba sai ta ce daga madina take, kuɗin adashen da ko naira biyar
bata zo hannunki ba, kika ɗauki saniyar mutane kika ba wanann marar imanin ya tafi to ai kin yi
saki na dafe.
Sa'a ta ci gaba da cewa
"Shi ne za ki ɗauke mini gayan tuwona ki fice da shi, na san a gyalenki kika duƙunƙu ne tuwon
kika je maƙota kika yi kwaɗo da mai da yaji kika cinye" Galala Lami take kallonta sai dai takaicin
da yake cikin ranta ya fi wannan wanda Sa'a take takalarta faɗa da shi don ta san ita da Sa'a
basa jituwo ko kaɗan, haka ta tashi ta shige ɗakinta tana jinta tana jera mata Allah ya isa amma
bata ji za ta iya biya ta su yi ba, don ita a halin da take ciki ko yunwa bata ji bare har ta saci
gayan tuwo ta san kawai neman masifa ne irin na Sa'a.
*WASHE GARI*
Sa'a ce a tsakar gida tana shanya kayan wanki, Lami tana bakin ƙofar ɗakinta tana zaune ta
kifa uban tagumi, bata da buri illa ta ga Ibra ya dawo da kuɗin wannan ko saniya amma shiru
malam ya ci shirwa.
Wata uwar sallama ake rafkawa a zauren gidan, da murya wacce hausa bata gama ratsa ta
ba, alamar yare ne yake maganar. Wani takaici ne ya turnuƙe Lami ta taso rai a ɓace ta zo
bakin zauren ta tsaya ta ce
"Tunde sai aka yi yaya kuma? Ya za ka zo da safen nan ka ishi mutane da rafka sallama"
(Tunde inyamuri ne da ya zo daga Lagos yana zaune a garin Mai Mangwaro yana da gidansa
da matarsa ɗaya da ɗansa, sai kuma shagonsa da yake a ƙofar gidansa nasa).
Kallon Lami ya yi ya ce
"Ba wajenki na zo ba wajen mijinki na zo" Ya faɗa cikin hausar sa da bata gama kama bakinsa
ba. Ambaton mijinta da ya yi ya ƙara sosa mata mikin takaicin Ibra da ta kwana da shi, cikin
takaici ta ce
"Baya nan ya ɓata, hijira ya yi da saniyar mutane ba a san duniyar da yake ba" Idanu ya zaro ya
saka hannu a lajihu ya fito da takarda wacce rubutu ne rututu a jiki ya ce
"In na yarda shegiya nake, kalli basukan da mijinki ya ci" Ya faɗa yana nuna mata takardar.
Kallon sheƙeƙe ta wa takardar ta ce
"To ai ka yi ta banzar ni da ba boko na yi ba ina zan san me aka rubuta" Yana zaro idanu ya ce
"Idan ma ɓoye mijinki kika yi ki fito da shi, don yau ba zan bar nan ba sai da kuɗina, shinkafa
kwano uku wake rabin kwano, sabulun bilicin da ya sha karɓa, da mayukan bilin har allurai da
nake masa na sanya fari bai biya ni ba wallahi ko a ni ko a shi jiya ya ce zai dawo daga kasuwa
ya biyani yanzu ki ce wai ya yi hijira"
*SHEIK*
Kukan zuci ya shiga yi wanda ya fi na fili ciwo, ya san tabbas yau watan tonuwar asirinsa ne
ya kama in ba haka ba hular da ita ce kaɗai rufin asirinsa kuma ita ce take fito da asalin
kamarsa da larabawa a ce babu ita. Shiru ya yi yana nazarin yadda zai kuɓuta amma iya
tunaninsa bai tuno komai ba, don babu mafita, kansa gabaɗaya ya kulle. Ga abin da ya fi ɗaga
masa hankali ma shi ne yadda samarin sukemta azalzalarsa a kan ya fito ana jiransa.
Cikin ɗaga murya ya ce
"Afwan ya shabbab, gani nan ina zuwa, ina yin shirin ko ta kwana ne, saboda aljannu dubu
saba'in ne a kan matar nan mai farfaɗiya" Ya faɗa yana ta safa da marwa a ɗakin ya haɗa uban
gumi yana ganin yau dai ƙarya nema take ta ƙarewa ɗan kada, saboda ya lura yana cikin tsaka
mai wuya.
Kamar zai yi kuka a hankali ya ce
"Allah ka taimake ni, Allah kar ka bari in kunyata" Ya faɗa yana ciccira ido a ɗakin, fani yake
kamar zai ga hular amma babu niyya wai ango ya kwana da wando.
Wata dabara ce ta faɗo masa ya buɗe baki ya ce
"Gabaɗaya ku fita daga gidan nan, gani nan fitowa saboda maganin aljannun da zan fito da shi
yana da ƙarfi, wataƙika idan na fito guguwa ta taso ta haɗe gidan da ƙura... Tun bai kai ƙarshen
maganar ba, samarin nan kowa ya yj ta kansa, sai lokacin ya ɗan ji sawaba, kamar ƙiftawar ido
da fitar su Sheik ya fara ganin labulen windown ya fara kaɗawa da ƙarfi kamar dai ana iska mai
ƙarfi ne,
Idanu ya zaro cikin taku biyu ya koma jikin bango ta raɓe, bakinsa yana karkarwa ya fara
addu'a, kawai sai ganin hular gashin nasa ya yi tana reto a saman ɗakin, kai ya ɗaga yana ta
kallonta, a ransa yana jin daɗi da ya ganta sai dai ba a nan gizo yake saƙar ba yanzu tunaninsa
ɗaya ya za a yi ta zo hannunsa. Bai ankara ba ya ga an wurgo dogom gemun jikin fuskarsa sai
kuma sauran sajen da hular gashin suka ɓace, kamar zai yi kuka ya hau faɗin
"Ku taimaka mini, ya zan yi da gemu shi kaɗai, damuwata gashin kan nan nawa da babu yadda
yake salsal su kuwa sun san Sheik da gashi laɓaɓa na larabawa." Yana rufe bakinsa sai ga
sauran ma sun fito sai kuma suka faɗo, duk da yana tsoro haka ya lallaɓa ya je ya ɗauka yana
godewa Allah a ransa yana jin daɗin cewa ashe dai da sauran shan ruwansa a garin Ƙundu tun
da gashi dai asirinsa bai tonu ba lallai akwai damfara.
Shirinsa ya yi tsaf ya ɗauko wani baƙin takalmi sabo a jakarsa ya saka, ya ɗakko turaruka ya
shafa ya saka hular gashin ya manna gemun ya saita sajen da yake wani abu ne a jiki da ake
ɗayewa mai danƙo daga ya ɗaga wajen sai ya manne kamar a fuskarsa a ka halicce su.
Ɗakinsa ya kulle ya fito yana riƙe da wata roba mai ɗauke da ruwa da wani garin magani da aka
jiƙa a ciki ya fito daga gidan gabansa yana faɗuwa, yana tunanin yadda za a ƙare da wannan
lamari, shi ya sa ko wayarsa bai ɗauko ba gudun masu aljannu su warce ko ma a fasa masa ita.
Tun da ya fito yake hangar mutane jefi -jefi suna yin wata hanya sannan kuma sai wani
girmama shi ake ana bashi hanya, wanann ya ƙara masa jin kansa ya ƙara girma, duk da yana
cikin yanayin tsoro haɗe da fargaba.
Sheik haka ya doshi cikin garin ya yi inda mutane suke yi da alama nan ne wajen da su Liman
ɗin suke.Duk da idanunsa sun kumbura saboda fargaba da rashin baccin da bai samu jiya ba,
kai har da kukan da ya yi ma.
Tun kan ya ƙaraso yake jin ana ta yin salati, yana kusa ƙarasowa ya ji ana faɗin
"Shikenan ma ga Sheik nan, ga ƙare kukan ka nan, balaraben malami yanzu komai zai zo
ƙarshe.
Mutanen gari sun taru suna jiran ya fitar da maganin da zai kori aljannu kuma ya kuɓutar da su
Liman. Amma Sheik yana cikin firgici har yanzu saboda abin da ya faru da dare. Yana ganin
taron mutane sai ya fara rawar baki da hannun yana murza carbi, yana faɗar kalmomin larabci
marasa ma'ana, don shi kansa bai san abin da yake faɗa ba yayin da yake karanta addu'a sai
wani ƙaramin yaro ya faɗi a gabansa ya fara rawa ɗari tamkar yana shi ma mai farfaɗiyar ne,
mutane suka shiga faɗin suna cewa
"Aljannu yanzu za ku gane shayi ruwa ne" Shi kuwa Sheik ganin yaro ya zube a ƙasa idanunsa
sun kakkafe sai ya sha jinin jikinsa gabansa yana tsanata faɗuwa, ya yi shiru don bai san me ya
faru ba, amma ya ci gaba da murza carbi yana ambaton maganganu. Jama'a suka fara mamaki
da tsoron Sheik suna ganin tsabar maluntarsa ce ta sa yaron ya zube a ƙasa.
Bai bi ta kan yaron ba ya ɗaga kansa sama, mutane uku ne a kan bishiyar kukar da mutane
gari suke kira da kukar bulukiya saboda tarin aljannun da suke kanta
Hannu ya saka ya kama yaron nan da ya faɗi ya ɗaga shi, ƙirjinsa ya dukan uku-uku ya shiga
karanta fatiha da ƙarfin halinsa yana tofawa yaron a fuska, wani gurnani yaron yake, Sheik
kuwa ji yake kamar ya sheƙa da gudu amma babu hali. Ɗan ranƙwafowa ya yi yana cigaba da
tofa masa karatun idanun yaron a kakkafe ya miƙa hannu bai masa masauki a ko ina ba sai a
gemun Sheik.
Sheik a zuciyarsa ya ce
'Shikenan asirina ya tono zai fisge min gemun a bainan nasi, kowa ya gane bogi ne' A fili kuma
sai ya fara faɗin
"Subhanallahi, ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba, hasbunallahu wa ni'imal wakil" Duk
abin nan da ake yaron ya ƙi sakawa, shi kuma Sheik hannunsa ɗaya yana riƙe da carbin da
robar maganin nan ɗayan yana riƙe da yaron, ji yake kamar ya yi kuka, bai yi wani yunƙuri ba
kawai sai yaron ya naɗe jikin malam yana cewa
"Ka kaini saudiyya" Sheik a zuciya ya ce
"Ni kaina ko filin jirgi ban taɓa zuwa ba' A zahiri ya ce
"Kai mutum huɗu su zo nan" Ya faɗa yana ƙara miƙa haɓarsa jikin yaron don ba ya so ya ja
yaron ya ciro gashin gemun. Samari da mata da magidanta da suke wajen sai aka fara darewa
jin malam yana kiran mutum huɗu
Malam ganin yaron yana miƙa hannu wajen wuyansa gudun kar ya shaƙe shi ya kashe shi a
banza, inda Sheik yake riƙe da hannunsa ya nutsawa yaron farce ya shiga tsunkonsa da ƙarfu
ba tare da kowa ya lura ba, mutane duk sun koma gefe.
Sai aka ji yaro ya fashe sa wani kuka, lokacin ne mahaifiyarsa da ta uso wajen tana kuka ta
ƙaraso, kukan da yaron ya fashe da shi sai Sheik ya shiga faɗin
"Allahu akbar! Ya dawo hayyacinsa sun fita" Ya faɗa lokacin har jikin yaron ya saki kamar mai
jin bacci yana lunshe idanu, babar yaron ce ta karɓe shi da hannu biyu, tana miƙawa Sheik 3k
ƴan dubu-dubu tana cewa
"Allah saka da alkairi, Malam ga abin sadaka" Ko fulaki bai yi ba ya karɓa yana cewa.
"Babu komai ai yi wa kai ne don ma an ce babu kyau mayar da hannun kyauta baya"
Mutane ganin Sheik ya warkar da yaro aljannu sun fita daga jikinsa sai girman Sheik ya ƙaru a
idanun su, suka shiga yin kabbara. Kuɗin nan ya saka a aljihu yana faɗi a zuciyarsa cewa.
'Allah kawo dubbanku, da a ce za a ke samun abin sadaka mai yawa haka ai da wuri zan cika
buhu da kuɗi' Gabansa yana faɗuwa ya matso daga gaban kukar da su Liman suke ka,reshen
kukar ne manya guda biyu a can saman amma ba tsililiko ba, ɗaga reshen Liman ne a maƙale
kamar ɓeran da aka tsamo daga ruwa, ɗayan kuma Mai Gari, sai wani lanƙwashashshen reshe
wannan matar mai farfaɗiya tana zaune a kan, su kuma suna maƙale da hannuwan su a kan
reshen. Sheik ya yi shiru jin wajen babu abin da yake tashi sai kabbara, matan gari an taru
wasu ma sai yanzu suke ƙarasowa wajen, a baya idan haka ta faru sai dai kowa ya yi ta kansa,
a ringa shiga gida ana kullewa, amma yau ganin balaraben malami kowa sai tsoro ya ragu daga
zuciyarsa.
Sheik ya fara tunanin Malam Manniru, wanda yake zaune a wani ƙauye a daji a can
wajensa yake bashi magungunan da ya zo don yon bogin da su, har ruƙiyar ma ya koya masa,
sai dai ya san yin magani dace ne ga shi maƙudan kuɗi malamim yake karɓa.
Baki ya buɗe ya shiga jan fatila, nasi,