Showing 12001 words to 15000 words out of 63190 words
*SHEIK*
Suna tunanin samun nutsuwa amma abin ya ci tura!. Abin da yake faruwa shi Sheik ga
tsoron kunnen da ya gani a banɗaki ga kuma tunanin yadda ya hango su Mai Gari a sukwane,
shi bashi da nutsuwar da za tambaye su ba'asin gudunsu tun da har ya ga suna tseren shiga
ɗaki da masu garin to tabbas ya san wataƙila cikin garin yana can a rikice kamar filin yaƙi, kuma
ya san kowa shi zai jira, shi ma kuma ga a halin da ya kwana ga kuma a halin da ya falka ko
sallah bai yi ba, kenan lamarin garin Ƙundu ba ƙaramin lamari bane in dai a ce aljannu da ranar
gari ma sai sun addabi jama'a to lallai akwai sake.
Kowa gabansa faɗuwa yake, shi Malam Liman sai yanzu yake jin da na sani da sun juya baya
sun koma cikin gari, amma gashi sun shigo wannan gida mai ruɗani bayan sun san cewa
wannan gidan shi ne kan gaba wajen matattarar aljannu amma kuma ƙarfin gwiwar tasu shi ne
Sheik to shi ma babu yadda yake, sun lura a ruɗe yake ruɗun ma iya ruɗewa, bayan shi suke
ganin zai kawo musu ɗauki amma sho ma kamar dai yana neman ɗaukin ne.
Mai Gari kasancewar shi kaɗai ne a cikin yankin bargon da ya shiga, duk da a katifa ɗaya suke
amma sai yake jin tsoro yana ƙara baibaye shi, ya so a ce bargo ɗaya suke da malam balarabe
mai jar fata kuma babban malami wataƙila aljannun sa yi sassauci a lamarin. Samarin nan guda
biyu sai numfashi suke ƙasa-ƙasa kwata- kwata a ruɗe suke.
Ya Sheik shi idan ya tuna da kunnen da aka jefo masa a banɗaki sai ya ji cikinsa ya murɗa
alamar gudawa, yanzu haka yana ta fafutuka wajen danne wata guntuwar tusa da take son ta
fito masa wacce yake da tabbacin matsawar ta fito kashi zai iya kuɓuce masa. Wannan dalilin
ne ya sa yake ta mutsu-mutsun dannewa, don ya san matsawar ya saki tusar to su Mai Gari za
su ji wari kuma hakan kamar zubar da kimarsa ne a matsayinsa na bababan malami, shi ba ma
wannn ne matsalar ba yadda suka biyo shi suka cika masa ɗaki, ya san cewa yanzu kowa shi
yake son ya kawowa ɗauki bayan shi kansa ta kansa yake. A daidai wannan lokacin kuma ɗaya
daga cikin samarin nan ne ya ji ɗayan ya janye masa inda ya rufu don haka ɗan jijjiɓin yaƙi ya
kaure a tsakanin su biyun, shi ɗayan so yake ya rufe har ƙafafunsa, shi kuma ɗayan an janye
masa don kansa ma yanzu a tantagayyar waje yake, wannan ya sa yake ganin va zai yarda ya
ɗauki dala ba gammo ba. Hakan ya sanya suke ta jaye-jaye da rigar Malam Liman wamda
fitsari ya cika masa mara, duk fusgar rigarsa ɗaya da suke barazana ne ga mararsa da take
cike da fitsari, hakan ya sa ya damƙe baki, a zuciyarsa yana faɗin
'Lahaula wala ƙuwwata, kar ku mini haka ƴan samari, ina zan kai wanann abin kunyar a ce
limamin gari guda amma ya yi fitsari a wando, ku taimake ni kar ku kunyata ni' Ya faɗa a
zuciyarsa yana wani damƙe idanu tare da haɗe ƙafafunsa waje guda yake fafutukar matse su.
Ɗayan ne ya fisge rigar da ƙarfi ya zungura kansa wanda kan nasa yake a saitin mazaunan
Malam Liman, Malam liman ana zungurar mazaunansa ya ji guntun fitsari kaɗan ya kufce masa
da sauri ya sake haɗe ƙafafun don ya lura in bai yi da gaske ba sai an saka shi ya saki fitsarin
nan duka.
Hannu ya miƙa ya sakarwar kan wannan saurayin wanda yake kusa da mazaunansa, ya sakar
masa ranƙwashi a zuciyarsa yana faɗin
'Shegun yara, kamar da ubanku muka haɗa kuɗi muka sayi rigar, sai ja kuke kamar kun samu
guga a rijiya' Ya faɗa a zuciyarsa yana jin da a lafiya ƙalaw ake ko iyayensu ba za su yarda su
shiga rigarsa ba saboda yadda yake da kima ana girmama shi, a matsayinsa na Limamin garin.
Saurayin nan da Liman ya kaiwa ranƙwashi, zafin ranƙwashin ya saka shi ƙara cukuikuye rigar
Liman da gangan, dama shi ne wannan me ƙarfin da aka taho da shi zai buɗe ƙofar gidan, wato
ƙaƙƙarfan. Jan rigar da ya yi shi ma ɗaya saurayin yana ta ƙoƙarin ja ya rufe kansa, sai ya
zamana gabaɗaya an shaƙewa Liman wuyansa, jin shaƙe wuyan yana barazana ga
maƙogwaronsa sai ya lanƙwasa kansa da sauri ya zame kansa daga cikin babbar rigar, hakan
ya sa garin ya zame rigar sai kansa ya fita daga cikin bargon da suke tare da Sheik, shi kuma
Sheik sai ya ja bargon ya ƙara duƙunƙune kansa, don yana a goho ne duk da yana jin kashin.
Samarin nan jin Liman ya sakat musu rigar sai suka cure waje guda suka rufa, tun da yanzu ta
ishe su sun rufa tare dama saboda tana jikin Liman ta musu kaɗan.
Malam Liman kasancewar a firgice yake kuma a tsorace kansa yana fitowa daga rufar da
yake sai idanunsa suka masa gizo da ganin Kakan Mai Gari wanann marigayin da aka binne a
gidan, ya tsago jikin ƙofa yana tahowa sanye da likkafaninsa, ya ɗan duƙa kasancewar yana da
ƙusumbi.
A kiɗime Liman ya nayar sa kansa ya cusa a katifa haɗe da cewa
"Wallahi marigayi kakan Mai Gari wato mai ƙusunbi ya tatso ta jikin ƙofa ya shigo ɗakin nan"
Ya faɗa yana miƙa hannu a niyyarsa ya samo bargon da ya fito ya shiga, sai ya cafko towel ɗin
jikin Sheik, Sheik kuwa jin furucin Liman na cewa Kakan Mai Gari ya shigo ɗaki, hakan ya tuna
masa da jawabin da Audu ya masa a daren jiya na cewa Kakan Mai Gari ƙasa ta ƙi karɓarsa da
ya mutu, saboda saɓon da yake yi, sai gida aka dawo aka masa kabari aka binne. Kenan
wanda ake zuwa maƙabarta ana samun sa yana gefe kabarin da aka saka shi ma a gefe, to ba
abin mamaki bane in aja ce yanzu ya taso da ƙafafunsa, wataƙila fatalwa ya yi. Tsabar ruɗanin
da Sheik ya shiga yana jin an iska ta fara shiga jikin mazaunansa alamar mazaunan nasa a
buɗe suke tantagarya, amma tsoro ba zai bari ya suturta su ba, don shi tunaninsa towel ɗin
zamewa ya yi.
Samarin nan jin furucin Liman sai suka rungume juna kamar sa zama mutum ɗaya, haka
kowanne yake jin bugun zuciyar ɗan uwansa alamar dai ana cikin fargaba da tashin hankali,
Malam Liman da ya samu towel ɗin Sheik ya rufe yana ta ƙoƙarin son ya ga ya samu ko da
addu'a ɗaya ce cikin wanda ya iya don yake karantawa ko a zuciyarsa ce amma ji ya yi
gabaɗaya ya manta komai a halin da yake ciki yanzu gani yake sunansa ne kaɗai zai iya
tunawa. Yana wannnn halin ne ya ji saukar hannun Mai Gari a bayansa, wanda hakan ya sa ya
ɗauka hannun marigayi mai ƙusumbi ne wanda ya masa gizo, duk tunaninsa a zahiri ya gan shi,
hakan ya sa gumi ya shiga zarya a gabaɗaya ilahirin jikinsa tare da kufcewar wannan fitsari da
yake ta dannewa, saboda yanzu an zo wajen da ba ta girma da martabarsa ta Liman ake yi ba,
ana magana ne ta ceton rai tun da har yana ganin gawa ta taɓa shi, gawar ma ta marigayi mai
ƙusumbi.
Liman a zuciyarsa yake faɗin
'Allahu akbar! Tamu ta zo (Yana nufin mutuwa) Allah ka bamu ikon amsa tambayar kabari, Allah
ni nake jan sallah a garin ƙundu ka bani cikawa da imani' Wannan yake ta maimaitawa a
zuciyarsa.
Mai Gari kuwa hannun da ya miƙa shi lalumen bargon Sheik yake yi, so yake ya koma cikin
bargon Sheik ko ya samu salama a ransa, tun da yana ganin bargon Sheik za a samu tsari
kasancewar malamin balarabe ba za a ce ruɗani ya hana shi addu'a ba.
Jin ya sauke hannun nasa a jikin riga, kuma ya san dai Sheik bashi da riga suka shigo ɗakin,
tun da idanun Mai Garin a rufe suke ba ya so ya buɗe bare ya ga fatalwar kakansa mai
ƙusumbi, son ya fara tunanin ma kar dai mai ƙusumbin ya ce ya zo ya tafi da shi ne. Hannun da
ya fara matsarwa a jikin Liman kasancewar rigar Liman ta shadda ce ta ci uban duniyar ta da
tsinke, domin daga baya a yage take kasancewar ya ɗora babbar riga shi ya sa ba a ganin
yagar, yanzu kuma da samarin nan suka sa ya cire babar rigar sai yagar ta bayyana a bayansa.
Hannun Mai Gari ne ya shige cikin bayan Liman ta wanann yagar, hakan ya sa ya shafo bayan
fatar jikin Liman.
Liman mutuwar kwance ya yi don zuwa yanzu ma kawai bakinsa ne yake karkarwa kamar
wanda zazzaɓi ya yi wa mugun kamu, haƙoransa suna haɗuwa da juna, saboda ya gama
saddaƙarwa cewa fatalwar mai ƙusunbi ce ta dama masa baya take shafa fatarsa, ya san yau
babu makawa da shi za ta koma lahira
Mai Gari da sauri ya ɗauke hannunsa, saboda fatar da ya taɓa ya ji wani karsansan, alamar
fatarsu ce irin ta baƙaƙen fata, ya san ta Sheik tana da laushi da santsi irin na larabawa, shi zai
tabbatar da haka tun da jiya ya kama hannun Sheik mai laushi kamar na jarirai, bai san cewa
tsabar amfani da allurai da magunguna da kuma sabulai na garan fata ne ya sa take duk a
yanayin da ya ji fatar.
Yana ɗauke hannun ya miƙa wani wajen tun da gabaɗayan su a kan katifar suke, duk sun
cushe, tun da su biyar a kan katifa ɗaya, yana ƙara miƙa hannun ya sauke a kan ƙafafun
samarin nan shafawa ya yi sai ya ji wani gautsin fata, don har ya shafo kaushi da faso a ransa
ya ce
'Kai jama'a har yanzu dai ina ta dawurwuri a jikin ƴan ƙasar nigeri'a Allah ka kaini a kan daidai
wato in taɓo fatar balarabe' Ya faɗa yana jin tausayin kansa.
Samarin nan kuwa jin an taɓo musu ƙafafu, kowanne sai numfashinsa ya tsaya cak! Tunanin
su fatalwar da Liman ya gani ce za ta yi awon gaba da su. Juna suka ƙara ƙanƙamewa
kowanne yana ta ƙoƙarin warto addu'a a zuciyarsa domin ya kuɓuta, sai dai a cikinsu babu
wanda ya yi nasarar ambatar kowacce addu'a don ruɗanin ya kai ruɗu.
Gwiwarsa ya ja bargonsa yana ƙamale a kafaɗarsa idanunsa a rufe, ya miƙa hannunsa bai
masa masauki a ko ina ba sai a kan mazaunan Ya Sheik, laushi luɓus ya ji, hakan ya sa ya
miƙa ɗaya hannun ma ya zamana hannayensa biyu a kan mazaunan don yana son tabbatar da
cewa tabbas a kan fatar Ya Sheik ya sauke hannunsa, amma fa duk abin nan da yake bai san
cewa a kan mazaunan Sheik ya sauke hannu ba. Sheik kuwa jin an taɓa masa mazaunai a
lokacin ya ƙara gane mazaunansa a tantagarya yake babu rufi ba ma wannan ba lalumen da
Mai Gari yake yi nema yake ya wuce gona da iri a wajen Sheik domin kuwa hannunsa yana
neman taɓo mafitsarar Sheik, Sheik wanda tunaninsa ya fara bashi cewa fatalwa ce take
lalumen jikinsa sai ya ƙara tsorata ya shiga ruɗu, da tunanin kar dai fatalwar mai ƙusunbin tana
so ta tsinke masa mafitsarar ne gabaɗaya ma, wani sashen na zuciyarsa yana bashi cewa ko
dai shayi ake son a masa(Kaciya,sallatu) Idanu ya zaro bai san lokacin da ya buɗe baki ba
gabaɗaya ya manta sa ƙalƙalar sa yake yi ta larabci wajen yin magana, wato yadda ko hausa
yake sai ka ɗauka ɗan koyo ne.
Wanann karo da hausa sak irin yadda bahaushe yake magana babu gargada ya ce
"Wallahi na rantse da Allah an mini kaciya, don Allah kar a cire mini mafitsara" Ya faɗa a fili
ɗakin har yana ɗaukan amsa kuwwa. Don ya fara tunanin kar a je ko dai a tsinke masa
mafitsarar ko dai a je garin masa kaciyar a yanke fiye da rabin mafitsarar a bar masa ƴar
guntuwa. Yana faɗa wani hawayen tausayin kansa ya cigaba da zubo masa domin ya fara tuno
matansa su Lami da ya baro a ƙauyansu ya san duk inda fatalwar kakan Mai Gari ya gabce
masa rabin mafitsara, ko ta cire masa gabaɗaya to in har ma bai mutu ba kenan, ya san
shikenan sai dai kowacce ta ce ya bata takardar saki, tuno da wannan kuma ya san yana son
matansa sai ya ƙara ware murya duk da yana cike da tsoro ya ce
"Wallahi ina son matana, ba zan sake su ba wani ya aura" Mai Gari tun maganar da Sheik ya yi
ta farko wato inda ya ji Sheik yana batun kaciya da cire mafitsara, bai san lokacin da ya ɗauke
hannuwansa salin alin da sauri ya koma wajensa da ya taso ya kifa kansa yana ambaton
'Lahaula wala ƙuwwata ' A zuciyarsa, don shi ya san dai ya ji an yi magana amma ko za a saka
masa wuƙa a maƙoshi ba zai gane ga wanda ya yi maganar ba, sannan ruɗanin da yake ciki bai
bari ya gane cewa Sheik ne ya yi maganar hausa sak ba, babu ƴar ƙalƙalar larabcin.
Malam Liman jin ana ambaton kaciya sai ya fara tunanin ko dai fatalwar ta yanke shawarar
yayyanke musu mafitsara ne hakan ya sa ya saki towel ɗin da ya rufe kansa da shi, ya mayar
wajan matse matsin ƙafafunsa a nufinsa ya yi shirin ko ta kwana, saboda kar a masa sakiyar da
ba ruwa.
Gabaɗaya kowa da zaman jiran tsammanin da yake, Sheik ya yi ƙarfin halin jan bargon ya
rufe mazaunansa, yana jin da na sanin zuwa garin ma baki ɗaya, sai dai shegen kwaɗayi da
son abin duniya ba za su bari ya bar garin ba, ya yi wa kansa alƙawarin zama daram sai ya ga
abin da ya turewa buzu naɗi.
Mai Gari ya jiƙe da gudmi sharkaf ga gwiwarsa ta ƙafa da ya tsunduma a fitsarin Liman, amma
dai yanzu a matsayinsa na Mai Gari gashi kuma yana tsoron mutuwa dole zai yi ƙoƙarin yin
magana don a samu mafita, tun da tana ganin duka manyan garin ne a ɗakin, idan kuwa
fatalwar mai ƙusumbi ta musu fata-fata to gari yana cikin garari.
Su kaɗai suka san gari lafiya lau yake, amma shi Sheik har yanzu tunaninsa wani gudun
famfalaƙin tsoron ne ya sa suka yi hijira daga cikin gari zuwa gidansa.
Da muryar kuka kuma muryar a shaƙe kai daga ka ji maganar ka san mai yinta ƙarfin hali yake
Mai Gari ya ce
"Ya Sheik, muna buƙatar taimako, muna buƙatar addu'a kar fa a mana ɗauki ɗai-ɗai, ka yi
addu',a mana, mu baƙaƙen fata muna cikin wani hali kaima babban malami kana...
Tun Mai Gari bai kai aya ba Sheik ya daure ya yi ƙarfin halin saita ƙalƙalar hausar larabcinsa
ya fara cewa
"A'uzubillahi minash shaiɗanir rajim, Bismillahir rahmanir rahim" Tun da ya sanu nasarar yin
a'uziyyar nan shikenan yake maimaitawa don shi ita kaɗai ya iya kamowa, don haka bai damu
da cewa yana ta maimaitawa za su ce wani abu ba. Mai Gari da yake jiran ya fara jin ana
zayyano addu'o'in larabci masu yawa bayan gama a,uziyya da bismillah sai ya ji ba a fara ba
ana ta maimaita abu ɗaya. Can ya ce
"Haba Ya Sheik ka fara addu'ar da muke ji ana karantowa a ƙasar makka mana" Ya faɗa yaba
ɗan ɗaga muryarsa da take ta zillo tana rawa, tare da saurin gyara fuskarsa daga inda ya nutsa
ta a jikin katifa jin ya danne hancinsa numfashi yana neman gagararsa shaƙa, amma fa duk
maganar nan da ya yi Sheik bai ce uffan ba kuma bai fasa faɗar abin da yake faɗa ba, saboda
shi a ganinsa ya samu makamar ceton kansa.
Liman da samarin nan jin muryar Sheik ta karaɗe ɗakin yana faɗin
"A'uzubillahi minash shaiɗanir rajim, Bismillahir rahmanir rahim" Cikin muryar larabawa tamkar
wanda wani balaraben gaske yake yi, basu san cewa Sheik sai da ya daɗe yana yi wa
muryarsa training a kan ƙalƙalar kafin ya zo garin nasu ba.
Liman da samari basa bambance abin da yake faɗa, don yadda yake maganar tamkar wata
doguwar sura ce yake karantawa sai suka shiga mishi amshi da faɗin
"Allahu akbar!" Idan ya faɗa sai Liman ya ce
"Attakabir" Sai samari su ce
"Allahu akbar!" Mai Gari ma tuni ya bi yarima yake shan kiɗa, don ya lura shi kaɗai ne muryarsa
bata fitowa a cikin ɗakin, yana tsoron abin ya zama shi kaɗai zai samu.
Sun kwashe sama da awa suna a haka, sannan ne Sheik ya ji ƴar nutsuwa, ya buɗe ido ɗaya
ya ƙyallara ya ga dai ɗakin babu kowa, wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, yana tunanin abin
da ya faɗa ne ya sanya fatalwar ta fita daga ɗakin.
Daƙyar ya ɗago daga gohon ya zauna, ganinsa babu towel ɗin nasa, sai ya ƙura ido a
mafitsararsa yana son ganin ko an masa shayin, amma sai ya ga yadda take haka take, sai dai
ta yamushe a waje guda ta tattare saboda wahala. Har lokacin bakinsa bai yi shiru da abin da
yake faɗa