Showing 51001 words to 54000 words out of 63190 words
aka banko
ƙofar ɗakin, a tare suka ɗago suna kallon wanda ya banko ƙofar a tare suka zaro ido ganin
Jummai sanye da wani tafkeken gajeran wando da wata riga mai ƙaramin hannu, sai wata adda
sabuwa dal a hannunta, ƙofar ta mayar ta rufe har da saka sakata, su duka sun tsorata sun fara
tunanin ko dai kashe su za ta yi.
Inna bata san lokacin da ta saki naman hannun ta ba, shi kuma ango ya ajiye ruwan
hannunsa a take ruwan ya fara malala a tsakar ɗakin.
Jummai tana zare ido ta kalli Sule cike da kakkausar murya ta ce
"Sule saniyar da ake shari'a taka ce?" Cike da tsoro yana kallon yadda sabuwar addar take
ƙyalli ya shiga girgiza kai alamar a'a
Ta ce
"To wannan ba amaryarka ba ce tawa ce, don haka dole ta bini ɗakina muke kwana, in ha haka
ba sai dare ya tsala kun sakankanci da cin amarci, zan shigo in datse maka mafitsara" Idanu ya
zaro yana saka hannu biyu ya dafe mararsa, don ya san kaɗan daga aikin Jummai.
Ta ɗora da faɗin
"Ita kuma na sare mata mazaunai" Inna da sauri ta kai hannu biyu ta dafe mazaunan ta tana
zare ido gabanta yana faɗuwa domin kuwa ta ga samu ta ga rashi.
Tana nuna su da yatsa ta ce
"Shawara ta ragewa mai shiga rijiya"
*SHEIK*
Yana zaro idanu amma bakinsa ya kasa furta ko uffan sakamakon yadda zuciyarsa take zilli
tamkar za ta huda ƙirjinsa ta fito.
Tunani yake wace irin baƙar ƙaddara ce a shegen neman kuɗinsa a ce za a ɗaura masa aure
da mace mai aljannu, mai aljannun ma wacce aljannu suka raba ta da ido ɗaya, sannan yana ji
aka ce an cirewa mai maganin mafitsara amma kuma sai a ɗora masa jakar tsaba gashi nan
yanzu kaji suna bin sa.
Managar Mai Gari ta katse masa tunani da faɗin
",Ai yarinyar nan Allah ya taimake ta ba ƙaramin sa'a ta yi ba da ta auri Sheik amma in ba Sheik
ba wa zai iya auren ta?"
Sirikar Sheik ta karɓe da faɗin
"Yo ai dama riƙon mahaukaci sai sarki" Numfashin sa ya samu daidaitawa ya ɗan saka harshen
sa ya laso bushashshen leɓansa da ya bushe ya ce
"Kai amma wannan dai sun takurawa rayuwarta, dama ana yi a ce an ɓatar da mashayar jikin
mace?" Ya tambaya cike da tsoro don shi yanzu ya kasa bambance komai ma, duk tsoro ya
hana shi sakat musamman idan ya tuna cewa yau da ita za su kwana a gida ɗaya kuma a ɗaki
ɗaya.
Cike da alhini mahaifiyarta ta ce
"Kayya malam yo aljannu mene ne basa yi, yarinyar nan wataran fa ko rashi ta yi za ta yi fitsari
sai ka ji ta ce babu wajen sun toshe mata, sai ranar da suka bushi iska suke buɗewa ai tana
wata rayuwa, yanzu dai Allah ya kawo mata ƙarshen wahala, in ma ba malamai irin ku magada
annabawa ba waye zai yarda a ce mace an cire mata mashayar ɗa(Breast) Kuma ya yarda bai
sake ta ba, kai wani mai aljanun ma ba zai yarda ya aura ba, kai ɗin ma jahadi ne ka yi"
A fili Sheik ya ce
"Yo ai dama kura ma ta san gidan mai babbar sanda, amma su sani rana dubu ta ɓarawo rana
ɗaya ta mai kaya"
A zuciyarsa kuma ya ce
"Za ku yi sake reshe kama ganye, wannan dai wayon a ci ne an kori kare daga bakin ɗinya, in
ba haka ba kawai kuje fakewa da malami kuna turo mini mutuwa yo mutuwa mana wannan da
aljannu suka zama danginta jinin jikinta za a kawo min ita, baku san ni ɗin ma ƙarfin hali ne
ɓarawo da sallama ba, babu wani malam kawai MALAMIN BOGI ne'
Cike da murnar kalamansa Mai Gari ya ce
"Ai sai mu je ko? Dama mutane sun kewaye ta in ji mahaifiyar amma kowa cewa yake ai matar
babban malamin larabawa ce daga ya zo komai ya ƙare"
Baki Mai Gari ya washe ya ce
"Shi ya sa nake alfahri da shi a garin nan Allah ya tarfawa garinmu nono"
Sheik a ransa ya ce
Ai dama ba wahalalle sai kwaɗayayye, haka kawai garin neman gira in je in rasa ido, ni ban
amfani kuɗin da na tara ba in rasa abin da kuɗi ba zai saya ba, amma ya na iya haka zan ringa
tarar aradu da ka, in ta yi ruwa rijiya in bata yi ba masai'
A fili ya ce
"Ai kar ka damu mai gari, mu ko a ƙasashen larabawa bamu san tsoro ba, zan yi ta ba mutanen
garin nan magani mata na basu na gyaran aure kai kowa sai ya samu abin da yake nema"
Sirikar da Mai Gari suka yi kabbarar jin furucin ta, tana murna ƴarta ta samu mijin nunawa sa'a.
Ɗaki ya shiga ya ɗauko magani ya ɗakko dogon carbinsa ya fito, Sirikar Sheik ta ce
"Ai Allah ya kawo mana ƙarshe wahala, yo wahala mana da asubar fari idan aljannunta suka
tashi kowa na gidan nan sai jikinsa ya faɗa masa, haka za ka ji saukar doka da dorina"
Gabaɗaya sai ya ƙara kiɗimewa zuwa yanzu ya gama tabbatarwa cewa matsala ya aura wato
har tana duka. Tsabar ba ya hayyacin sa sai ya bi bayan su a haka.
Mai Gari da ya waiwayo ya ce
"Subhanallahi Ya Sheik kana lafiya kuwa, baka saka takalmi ba" Cike da wayincewa ya ce
"Ashsha duk saurin zuwa nemowa amarya lafiya ne"
A ransa ya ce
'Lallai akwai lauje cikin naɗi, yau dai na yarda cewa dalili ne kaɗai yake sa a leƙa gaban sirika'
Takalmin ya ɗakko, lokacin da suka doshi gidan, sai haɗuwa da jama'a suke a hanya ana
girmama Sheik basu san cewa ba ya gane abin da suke faɗa ma, shi hankalinsa ba ya jikin sa
musamman da suka kusa shiga gidan suka ringa jin wani kururuwa da iface-iface.
A zaure suka tsaya, Sheik zuwa yanzu ko magana ba ya iya yi ta fito sosai sai jan carbi da
yake ta faman yi yana addu'a a ransa cewa, Allah ya ɗora shi a kan aljannun nan, shi yanzu so
yake ya cigaba da bayar da magunguna amma batun aljannun nan ba so yake yi ba.
Sai tashin hanyaniya da suke ji ta mata a cikin gidan, jim kaɗan sai ga sirikar Sheik ɗin ta
dawo tana cewa
"Bismillanku ai gata can ma jikin ya matsa, amma abin mamaki sunan Sheik take ta faman faɗa"
Sheik da ya ji faɗuwar gaba an ce ana kiran sunansa sai ya yi zaton ko dai sunan sa na asali ta
faɗa wato Ibra tun da ya san su aljannu babu abin da basu sani ba.
Da ɗan diriricewa ya ce
"Ya subhanallahi wane sunan daga ciki?"
Ta ce
"Sheik kawai take cewa, amma idanunta a rufe"
Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, ta shiga gaba suna biye da ita, duk mata ne da alama ƴan
taron bikin ne da kuma kai amarya.
Ɗakin da take karaɗin ihun ne wanda sai da aka rufe daga window ake leƙen ta.
Mai Gari ne ya ja ya tsaya yana mai cewa
"To Ya Sheik a fito lafiya" Ɗiff Sheik ya yi yana jin faɗuwar gaba tana ratsa dukkanin gaɓoɓin
jikinsa da zuciyarsa, amma haja ya daure ya gyaɗa masa kai yana mai faɗin
"In sha Allah"
Haka sirikar tasa ta buɗe masa ƙofa ya shige, har da rufo ƙofar.
Tana kwance reran sai wani gurnani take tana surutai da ihu.
Gabansa yana tsananta bugu ya haɗiye wani yawu ya ce
"A'uzubillahi minsh shaiɗanir rajim" Ya faɗa da ƙarfi saurin yana karaɗe ɗakin, kamar aljannu jira
suke ya yi magana sai ta ɗifff kamar an ɗauke wuta, murmushi ya yi a ransa yana faɗin
'Ashe dai ku ɗin ma matsorata ne kamar ni, yanzu kuwa za ku faɗawa ƴan garinku don wallahi
sai na mori faɗuwar gaban da kuka sakani sai na baku wuju-wuju, mu zuba mu gani' Ya faɗa a
zuciyarsa yana ajiye maganin da ya taho da shi, carbinsa, da kuma hiraminsa ya naɗe hannun
jallabiyarsa.
A can tsakar gida kuwa jin ta yi shiru sai aka shiga ƙusƙus kowa yana murna, ana yabawa
lamami daga ƙasar larabawa.
Mahaifiyar ta ta ce
"Kai jama'a aiki ga mai ƙare ka, ashe dai duk ihu suke bayan hari ka ji dai ya fara maganin su"
.
Mai Gari ya ce
"Yo dama mai zai gagara ai da kike ji da gani ƴarki ta yi babar sa,a saboda yanzun nan za ki ji
ya fitar da su, ke hatta nonuwanta dole su dawo mata da su" Wannan maganar da suka yi a
kunnen Sheik da yake suna a ƙofar ɗakin ne.
Sheik jin haka sai ya ƙara ƙaimi, ya leƙi da window yana cewa
"A samu murɗuga-murɗugan bulali, guda biyar wannan dole sai sun ci ubansu" Ya faɗa da
muryar hausar larabcin sa.
Da sauri Mai Gari ya saka samari suka ciro a dalbejiyar ƙofar gidan, aka miƙawa Sheik, nan
da nan sai ya hau karatun suratul fatiha ita kaɗai ya karanta har lokacin dai bata ƙara ko motsi
ba ta yi ɗif kowa bata cewa komai sai dai yanzu ta buɗe idanunta sun yi faral kamar na gawa.
Ganin hakan ya hau zagarta da bulala, yana faɗin
"Za ku fita ko sai na koya muku hankali, sai na nuna muku kudu ba arewa ba ce matar malamin
ƙasar yemen za ku ɗaukewa mashaya, baƙin ciki kuke min, kar in angwance" Ya faɗa yana
tafka mata bulala. Sai da bulala uku ta karye duk ya burɗa mata jiki.
Ya ɗaga ta uku zai zabga mata sai gani ya yi ta miƙe a fusace, yanayin yadda ta iyo kansa sai
da hanjin ciknsa sa ya kaɗa, bulalar ta riƙe bai ankara ba ya ji ta warce, ja ɗaya ta yi wa bulala
sai ga Sheik ya saka yana zare ido cike da tsoro, gabansa yana bugawa, ɗagawa ta yi ta tsula
masa, tsabar yadda zafin ya shige tsalle ɗaya ya yi sai gashi a gefen gado, taku ɗaya ta yi sai
gata a tsakiyar gadon, ta ɗaga bulalar tana rama dukan da ya mata, amma saboda gudun kar a
gano lagwansa bai yi ihu ba, ko wani furuci da zai sa a gane halin sa yake ciki.
Mai Gari ne cikin laga murya ya ce.
"Aikin ka yana kyau Sheik kar ka bar su sai sun dawo mata da abubuwan nan masu
muhimmanci a jikin mace(Breast)"
Sheik dakyar ya mayar da kukan da yake ƙoƙarin ƙwace masa ya ce
"Ai sai sun maido... Bai ƙarasa faɗa ba ta buge masa baki tana zare ido yana kallon ta ya san
ba a hayyacin ta take ba.
Shammatar ta ya yi ta ya fito daga lungun gadon sai ga shi a tsakiyar ɗakin, farɗo ta ya yi yana
ɗaukan ɗaya bulalar ya zabga mata sai ta zube a kan gadon idanunsa ƙurrr a ƙirjin ta ya ga
wayam babu breast kamar ƙirjin yara.
Baki ya buɗe yana karanta qulhuwallahu ahad, yana zabga mata bulalar yana cewa
"Ku maido da nonon da kuka ɗauke, ku maido da shi aka ce... Bai rufe bakinsa ba mai zai ji?
Wani abu ya ji kamar an hura masa iska a ƙirjinsa, kafin ka ce kwabo sai ya ga tudu nan da
nan sai ga breast ɗin duka biyu a ƙirjin Shaikul yemen. Idanu ya zaro cike da fargaba a
zuciyarsa ya hau cewa
'Ƙirjin ta nake nufi fa aljannu, ƙirjinta nake nufi ku mayar ba ƙirjina ba na shiga uku ni Ibra jikan
Inna' Ya faɗa yana kai hannu cike da tashin hankali ya shafo ƙirjin, breast ne ya ji tamkar ƙirjin
mace....
*BOOK 1 free BOOK 2 500 shiga grp cmplt docment 800 za a biya ta asusun faiza abubakar
9030283375 opay. Saura page 2 a gama book 1*
*MAMAN AFRAH*
09025576222
TALLAH TALLAH
*Kamfanimu na MEERAH B HERBS muna da kayan mata masu kyau da inganci, akwai
maganin sanyi maganin gyaran breast, maganin hips, na rage ƙiba, na ƙara ƙiba, maganin rage
tunbi, da kuma maganun MAN POWER ga matan da mazajen su ba sa uin kataɓus a wajen
aikata sunna da sauransu.*
*Mai so ya tuntuɓeni a layina 09025576222*
[7/16, 6:52 PM] Mom mashkur & Afrah: ♂️ *MALAMIN BOGI*♂️
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.
Daga marubuciyar:
Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*
BOOK1️⃣
PAGE 14
IMZEEDVENTURE
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha!
Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko
gonjo mai kama da sabo?
To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE!
Za ki sha mamaki! Muna da:
✅ Adashe na kayan kitchen
✅ Kayan yara sabbi da gonjo
✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau
Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253
DM: WhatsApp
IG/Tiktok: @imzeed_venture
*MUMMY*
Shigewa ɗakin Daddy ta yi, kasancewar fitilar a kashe sai kawai ta durfafi kan gadon, cike
da shauƙin soyayya ta ɗare gadon, sai dai wani abu da ya ratsa ƙwaƙwalwar ta shi ne, jin gadon
kamar ma wayam yake babu kowa a ka, ma'ana kamar dai ita kaɗai ce da ta hau gadon yanzu
a ka, mamaki da al'ajabi suka haɗe lokaci guda a kwanyarta tambayoyi da tunani barkatai suna
safa da marwa a ƙwaƙwakwar tata.
Da yake tun tana dab da zuwa ƙofar ɗakin ta kashe fitilar wayarta, saboda ta fi so sai ta hau
gadon zai san da zuwanta, hannu ta kai ta gama zagaye kan gadon amma babu alamar mutum,
fitilar wayar ta kunna sai yanzu idanunta suka ƙara tabbatar mata cewa ba ya kan gadon a
zuciyarta ta ce
'To ko dai yana banɗaki?'
Wata zuciyar ta ce
'Kuma banɗakin ne ba zai kunna fitilar ɗakin ba, sannan kuma ita ma ta banɗaki ba zai kunna ta
ba?'
Ƙafafunta ta zaro daga kan gadon, banɗakin ta nufa, bata kunna fitilar banɗakin ba sai ta yi
amfani da fitilar wayar, amma sai ta ga babu shi babu alamar sa.
Haka ta rufo ƙofar banɗakin ta dawo ta zauna, nazari take amma kwanyarta ta ƙi bata haɗin
kan gano inda mai gidan nata yake, fitilar wayar ta kashe, tana jira ta ga ta inda zai fito.
Daddy kuwa ransa fari tas ya fara haurowa sama, fitilar wayarsa a kashe saboda kar a
samu akasin lissafi, saɗaf-saɗaf ya zo ya wuce ƙofar ɗakin Hajiya, ganin fitilar a kashe a
zuciyarsa ya ce
'Ka ga sarakan bacci ana can ana fama, ni ai da kike da nauyin baccin nan gaba ta kai ni
gobarar titi' Ya faɗa a zuciyarsa yana kama hannun ƙofar ɗakin nasa ya buɗe ƙofar, Mummy da
take zaune har sai da ta ji gabanta ya daɗi saboda bata tsammace shi ba, sannan bata kawo
cewa zai shigo a duhu bai kunna fitila ko da ta wayarsa ba ce.
Ɗif ta yi tamkar bata cikin ɗakin, Daddy kuwa yana shigowa ya yi wata miƙa yana salati, tare
da sakin doguwar hammar biyan bashin baccin da bai yi ba a daren na jiya.
Kan gadon ya nufa kasancewar ba ta wajen da Mummy take zaune ba ne, har ya hau gadon
bai san tana zaune ba, sai da ya ja filo ya tada kansa yana sakin wata hammar a karo na biyu,
hannu ta ɗan miƙa ta sauke a jikinsa, gabansa ne