Showing 48001 words to 51000 words out of 63190 words
Chapter 17 - MALAMIN BOGI COMPLET BOOK by Ameera Adam.pdf
gabansa yana tsananta bugu.
Mai Gari ya ce
"Ai wataran aljannunta sun tashi sai aka ɗauke ta zuwa wajen mai magani, to mai maganin ne
ya shiga dukanta da dorina, ashe dai aljannun sun ji haushi shi ne suka cirewa mai maganin
mafitsara ita kuma suka cire mata ido ɗaya.
Dadammm gabansa ya yi wani irin bugu musamman da ya ji an yi batun mafitsara, tun da ya
san dole in ya aure ta a yi sunna to kuwa ina zai yarda ya tuɓe a gabanta ya je a masa mai
kankat wato a guntule shi kamar yadda aka bashi labarin an guntule wani malamin mai magani,
lallai yana cikin jalala amma dai hakan ba zai sa ya nuna karayarsa ba, a matsayinsa na wanda
ake girmamawa.
Haka suka yi ta saka masa albarka a ƙarshe suka ce gobe za a ɗaura auren tun da gudun kar
aljannun su fara aika-aika a garin.
Duk da Sheik yana da son mata amma yana ji yana gani, wannan macen ba ya ɗokinta.
Bayan tafiyarsu haka Sheik ya kwana da zulumi bai runtsa ba, saboda ga damuwar aurensa
da mai ido ɗaya, ga kuma yadda aka kwana ana taɓa jikin langa-langan da aka binne mai
ƙusumbi a gidan.
Washe gari aka ɗaura auren Sheik da mai ido ɗaya, kowa sai kiransa ango yake, amma Sheik
ransa ƙuna ma yake da aka ce an ɗaura auren. A ranar ne aka ce za ta tare gudun shaiɗacin
aljannun kar su yi abin da suka ce za su yi a garin.
Ranar kaji biyu aka dafawa Sheik saboda sun zama su biyu, kuma dai a gidan da yake za su
zauna shi tunaninsa ma buhun kuɗinsa da yake taro, da kuma ya zai yi in zai je wajen Malam
karɓar magani, shi dai kawai gani yake wata maƙarƙashiya aka shirya masa don a tona masa
asiri. Bayan magriba yana zaune a ɗaki yana tunanin yadda zai ke yi da hular gashin kansa kar
amarya ta harbo jirginsa.
Turowar ƙofar gidan da kuma shigowar Mai Gari da mahaifiyar amaryar ta Sheik dukansu a
kiɗime suna rafka sallama, shi ya sanya hantar cikin Sheik ɗin kaɗawa ya fito daga ɗakin a
ransa yana ambaton Allah sa ma aljannun ne suka ɗauke ta da ya huta.
Mai Gari a rikice ya ce
"Sheik akwai matsala fa, aljannun nan dai sai ka tashi tsaye a kansu, suna son yin fito na fito da
kai a gurin amaryarka, yanzun nan muna jiran fitowarka mu yi sallar isha'i sai ga sirikarka a
kiɗime wai amarya tana shirin da za a kawo ta gidan miji, tun da ka ce ba sai an kawo ta da
komai ba katifar ɗakin ma ta isa, abinku ku malamai mai sauƙi ne kar a yi wahala, to shi ne fa
amarya ta kurma ihu mahaifiyar tana zuwa ɗakin ta ga amarya kwance amma abin mamaki
abubuwan nan guda biyu sun ɓace ɓat babu su"
Gabansa faɗuwa yake duk sun ruɗa shi, ya kasa ma gane inda maganar ta dosa, uwar
amaryar ce ta karɓi maganar da faɗin
"Wallahi sun ɗauke mata mashayar shayar da yara duka biyun(Breast) Babu ko ɗaya wajen ya
shafe shafal kamar ƙirjin babe, ko in ce kamar bayan silba"
*MUNA DAB DA GAMA BOOK 1 WANDA PAGES KAƊAN SUKA RAGE MANA, KAMAR
KULLUM KUN SANI INA BAKU BOOK 1 FREE BOOK 2 PAID, WANNAN KARON MA ZA A
BIYA 500 KACAL DON KARANTA LABARIN HAR ƘARSHE, AKWAI CAKWAKIYA KUN SAN
DAI YADDA AKE CAKWAKIYA TO NAN MA BA ZA A BAYAR DA KUNYA BA IN SHA ALLAH.*
*MAI BUƘATA ZAI IYA TURA KUƊIN KARATUNSA TUN YANZU DON WASU TUNI MA SUKA
BIYA, ZA A TURA ZUWA FAIZA ABAUBAKAR 9030283375 OPAY SHAIDAR BIYA TA
09025576222 IDAN AKA KAMMALA CMPLT DOCMENT 800.*
MAMAN AFRAH
09025576222
[7/15, 8:21 PM] Mom mashkur & Afrah: ♂️ *MALAMIN BOGI*♂️
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.
Daga marubuciyar:
Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*
BOOK1️⃣
PAGE 13
IMZEEDVENTURE
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha!
Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko
gonjo mai kama da sabo?
To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE!
Za ki sha mamaki! Muna da:
✅ Adashe na kayan kitchen
✅ Kayan yara sabbi da gonjo
✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau
Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253
DM: WhatsApp
IG/Tiktok: @imzeed_venture
*INNA TASALLAH*
Har aka ɗaura auren Jummai tana sume bata falka ba, Lami tana gefe mamaki ya kashe
mata jiki, ta rasa ma ina za ta sanya wannan lamari shin waye mai laifi Jummai da ta kawo a
karɓa mata haƙƙinta ko kuwa ita ma da aka cinye mata kuɗin adashe, ko dai Mai Gari ne mai
laifi wajen rashin aiwatar da komai bisa adalci.
Inna ta sanya mayafinta ta kare fuskarta sai wani murmushi take dokawa, bayan an shafa
fatiha sai Mai Gari ya yi gyaran murya ya ce
"Sule ga amaryarka nan aure dai sunan ce ta ma'aikin Allah S.A.W ka riƙe ta da amana kar ka
ga ta fika shekaru ka ce za ka mata abu na rashin kyautawa ko dai ka bari matanka su mata, ba
zan lamunta ba, tun da dai ka ga ta yi hakan ne saboda ta sadaukar da kanta a matsayin kawo
masalaha ga wannan tashin tashina da ake yi, ta yi biyan bashi da kanta ka ga hatta ni ta sama
mini lafiya a kan wannan shari'a da ban san ranar ƙarewarta ba" Sulen yana wani murmushi sai
washe haƙora yake ya ce
"Ai kar ka damu Mai Gari babu abin da zai faru kuma ai amarya ko ta buzuzu ce dole za a so ta
a yi ɗokinta" Inna jin wanann lafazin sai ta ƙara jin wani daɗi a ranta.
Abin da basu fahimta ba shi ne Inna ta jefi tsuntsu biyu ne da dutse ɗaya, ma'ana ta auri mijin
Jummai saboda kawo maslaha sannan kuma saboda take samun abinci tun da yanzu ta ga dai
idan aka kafa mata ƙahon zuƙa a kan biyan bashin nan hatta abinci ma sai ya gagare ta amma
yanzu in ta yi auren dole dai a ciyar da ita, tun da ta lura abincin ta yana dab da ƙarewa kuma
yanzu tun da da biyan bashi ba za ta samu sararin siyan abubuwa ba.
Cikin jin kunya ta ce
"Mai Gari a samo ruwa a yayyfawa ƴar uwata ta tashi mana" Kowa sai da ya jinjina lamarin wani
ne daga cikin mutane wajen ya ce
"Kai Inna amma dai bakya ma kishi da Jummai"
Inna ta ce
"Haba ina ni ina kishi da ita" A daidai nan aka miƙo ruwa Lami da take cike da al'jabi da jin
kunya ganin an ɗaurawa kakar mijinta aure a wajen ta karɓi ruwan ta yayyfawa Jummai, sai ga
Jummai wuruf ta tashi tana waiwaye ganin jama'ar wajen da kuma Inna da take kakkare fuska
da mayafi hakan ya tabbatar mata da cewa ba mafarki take ba a zahiri ne.
Tana tashi tsaye ta kalli Mai Gari ta ce
"Ni ba ni aka yi wa amarya ba tun da ni ce mai bin bashi ni za a biya kuɗina tun da Sule ne ya
auri mace"
Mai Gari ya ce
"Jummai Tasallah fa ta ce bata kishi da ke, kin fa zaman nan da za ta yi na ɗan lokaci ne, daga
Ibra ya dawo za a bata takardar saki ta bar muku gida... Sule ne ya ce
"Aure ai ba abin wasa ba ne tun da har aka ɗauka babu batun saki, a bar Tasleey ta ƙarasa
rayuwarta a gidana" Sunan Tasleey da Sule ya kira a maimakon Tasallah shi ne abin da ya ƙara
fusata Jummai, sannan shi ne abin da ya faranta ran Inna ta ji ta dawo tamkar ƙaramar yarinya.
Cikin harzuƙa Jummai ta ce
"Mu zuba mu gani sai na zame muku ciwon ido a gidan nan" Tana faɗar hakan ta juya fuuuu ta
bar fadar kamar za ta hantsila.
Mai Gari ya ce ya sallami kowa, ya kalli Inn yana dariyar wasa ya ce.
"Ka ga amarya ran gida, amarya bakya laifi Tasallah amaryar Sule" Wani daɗi Inna ta ji, ta
kunce ƙullin hannun zaninta da ta yi ta ɗauko kuɗin kayan miyarta haka ta zaro ɗari biyar ta ce
"Mai Gari ga jaka biyu da rabi (500) Ka ci goro" Sosai ya ji daɗi yana washe baki ya ce
"Yaushe za ki tare?" Ta ce
"Yo tun da aure ya ɗauru ni kuwa tariyar mai zan jira ai a yau ba sai gobe ba"
Sule ya ce
"Dama akwai ɗakina kawai sai ta zauna a ciki".
Lami tsaye ta miƙe ta ce
"Mai Gari ni ina nawa zancen ya kwana tun da ita Jummai an samu mafita?" Kallon sheƙeƙe ya
mata ya ce
"Ana batun giwa wa yake maganar ɗan tsako, amma dai ai kin san wanda ya zai je sama ya
taka leda ya ci ƙarfin tafiya ko?" ,Takaici ya sa bata sake cewa komai ba, juyawa ta yi sai Inna ta
ce
"Yanzu Lami maimakon ki tsaya ki ɗauka mini samirar nan da ledar kayana, ki raka ni gidan in
kintsa, amma kya tafi ki barni ai an yi ba a yi ba rufin ƙofa da ɓarawo"
Cike da jin haushi Lami ta ce
"Haba Inna tun yanzu ai a tunanina duk gaggawar asara ta jirayi samu" A faɗa ce Inna ta ce
"Ke kika sani ƴar baƙinciki wato kina jin babu daɗi na samu jirgina ya ɗaga na yi aure bayan a
gari ga yan mata nan galla-galla da zawarawa masu jini a jika amma ni na tashi na barsu, to ai
dama abin rabo ne auren mace da ciki"
Takaicin ta ta danne ta ce
"Haba Inna ai ba batun baƙin ciki ba ne, ai ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, ni ma ba zan so ki
ƙarasa rayuwarki babu aure ba, gwara ki yi ko a sama mana ƴan ƙanne"
Kallon kallo aka shiga yi a fadar Lami ta sunkuya ba don ta so ba ta ɗauki samira da ledar Inna
ta yi gaba, ita kuma Inna ta tashi tana ta jin kunyar jama'ar wajen Mai Gari ya ce
"Tasallah babu batun kunya ba a aure kuma ai jahadi kika yi" Ya faɗa yana saka ɗari biyar ɗin
da ta bashi a aljihu.
Inna ta ce
"Haka ne ai da rashin tayi ake barin araha, kuma da rashin kira karen bebe ya ɓata"
Gabaɗaya ƴan fadar aka amsa mata ana mata jinjina, har ta yi gaba Sule ya tashi yana washe
baki ya ɗan bi ta suka keɓe ya ce
"Amarya bakya laifi, yaushe za ki zo"
"Ta ce ahaf dag an yi sallar isha'i mana za a rako ni, kar in je in zauna Jummai ta zo ta min tijara
a kan kuɗin saniyar da na fansa da aurenka"
Haka ya tafi yana wani waiwayen Inna, wasu daga fadar suna masa kallon sha-sha-sha.
Tafe suke a hanya Lami tana barin Inna a baya har Inna ta gaji ta ce
"Lami sai wani cin magani kike, wai ke baki san mata tsoffi ƴan da basa tsufa ba, mu fa nan mu
ake yi wa laƙabi da mace daki bari" Cike ta haushi Lami ta ce
"Daki bari kamar wata atamfa?" Inn ta ce
"Yo ai atamfa wataran tana yagewa ko ta mutu a jefar da ita, amma mutane da ƙarko garemu
kuma shi namiji ba ya ganin tsufan mace waɗannan matan nasa sai ki ga na je na fiye masa su
sau miliyan, duk wannan hayagagar da Jummai take wiyarta in tare ai duk wanda ya daka rawar
wani zai rasa turmin daka tasa rawar, dama alƙawarin Malam na ɗauka na ce ba zan yi aure ba
amma yanzu na fasa aurena zan zauna yo malam ɗin ma da shi ne ba lallai ya bari a mini
arba'in ɗin mutuwa ba zai gallo wani auren, ita ma Jumman kallon raini take min bata san cewa
idan makaho ya ce a yi wasan jifa to tabbas ya take dutse ne, amma dai zan nuna mata gani ya
kori ji"
Banza Lami ta mata, har ta fara tunanin ma dama duk rawar kan Ibra da rashin jin nasa wajen
Inna ya yi gado.
Suna dab da ƙofar gidan Inna Lami ta ce
"To Inna ga kayan ni zan wuce gida, Inna amarya ta ango" Ta faɗa cike da gatse.
Inna ta kalle ta ta ce
"Kin ga Lami kar ki mini fallasa auren bashi, idan ba za ki kai mini gida ba, ba sai kina mini
terere a titi ba, amma dai ki sani duk wanda ya ƙona rumbunsa ya san inda toka take tsada"
Tana karɓar kayanta ta shige gida, Lami kuwa baki ta taɓe ta yi tafiyarta.
Inna gidan ta buɗe ta shiga, tana murna ta shiga haɗa ƴan komatsanta da ta san za ta buƙata .
Kawayenta guda huɗu ta je ta gayyato suna ta mata barka sa fatan alhari don babu wacce
ta ce bata kyauta ba. Haka mata biyu suka yi gaba da yara aka je da kayan Inna ƴan samiru da
kayan sawa, sai randunanta da aka ɗauka a baro da sauran kaya, aka je dakyar aka shiga da
kayan kasancewar Jummai tana tijara, sai da Sule ya tada jijiyoyin wuya.
Bayan an kintsa ɗaki da gadon Inna na ƙarfe, sannan aka rako Inna a ƙafa ana ta rangaɗa
guɗa, haka aka shigo da ita aka zaunar da ita a bakin gado.Bayan kowa ya watse , Inna ana
zaune ana ta murmusawa ango ya shigo da ledar tsire da pure water, Jummai tana zaune a
ɗaki ta kasa ta tsare tana jiran zuwan ango, ita kishiyar tata ma cewa ta yi babu ruwanta ita ma
Jummai abin da ya sa ta damu saboda ga babu kuɗin saniya ga kishiya.
Bayan Sule ya shige ɗakin amarya dama ko ta kan su Jummai bai bi ba, ya rufe ƙofa yana
washe baki tare da mata kirarin amarya mai daɗin tuwo.
Ƙasa ta sakko suna zaune a tsakiyar ɗakin, ya saka hannu ya buɗe fuskar da ta rufe da
mayafi, Inna tana ta kare fuska tana zabga murmushi, Sule saboda ƙarfin hali har da shan
magani don abokansa sin zuga shi a kan cewa tsohuwa ma ai mace ce, kuma ita ma tana da
tata ni'imar hakan ya sa ya shawo ya yi tatul, don gabaɗaya mararsa hargitsa masa take
Inna kuwa babu abin da ta sha sai maganin zafi wato maganin rana, sai wani abu da wata
matashiyar mace maƙociyarta ta bata mai suna ƙwaƙwalwar raƙumi ta ce ta saka a gabanta,
gabaɗaya sai ta fi sauran matan ɗanɗano.
Ya fito da pure watern da takardar tsiren ƙamshin ya cika musu hanci Inna tana ganin ita
gaba ta kai ta gobarar titi don sai ta ji gwara ma da Ibra ya gudu da saniya tun da gashi ta tsinci
dami a kale, ga abinci za take samu ga kuma kayan daɗin amarci, tun da ta ga har da ruwan
leda(Pure water) Da har tana jin haushin an katse mata shan mangwaro ashe dai rabo ne yake
kiranta.
Sule ne ya ɗakko tsoka ɗaya ya nufi bakin Inna, tana ɗan kauda kai ta karɓa tana jin kunya
sai ƙarfin gwiwa yake bata a kan cewa babu kunya tsakanin miji da mata. Tana taunawa ya tulla
ruwan guda ɗaya, ya miƙa mata ta kurɓa bayan ta cinye naman, ita ma hannu ta kai ta ɗauki
ɗaya tana kare fuska ta miƙa masa, Sule kansa ya ji ya wani ƙara girma don shi har ya manta
da a bashi abinci a baki ko dai ya ci ko ya zauna da yunwa duk ɗaya a wajen matan nasa.
Baki ya wangale sai dai kash, naman bai kai ga sauka a kan harshen sa ba sai