Showing 9001 words to 12000 words out of 63190 words

Chapter 4 - MALAMIN BOGI COMPLET BOOK by Ameera Adam.pdf

18 Jul 2025

5280

tana cewa

"Oyoyo Daddy nah" Yana nuna farin cikinsa ya raba ta da jikinsa yana riƙe da hannunta yake
cewa

"Oyoyo baby fatan kin ci abinci" Ɗan tura baki ta yi ta ce

"Ban son cin abinci yau Daddy fruit nake ci" Murmushi ya yi yana riƙe da ita suka ƙarasa
tsakiyar falon.

Yaya Ma'aruf cike da girmamawa ya shiga gaishe da Hajiya, amma ta amsa kamar bata so,
don ita har yanzu kallon wanda bai waye ba take masa, kallon baƙauye, ita dama ba don dai
ɗan gidan ƙanin mijinta bane kuma mijinta yana jin maganar Yayansa da tuni ta kore shi daga
gidan.
Ganin Rahma ta tashi tsaye tana wani buga ƙafa alamar ɓaci, wai Daddy ne zai cigaba da
bata fruit, da sauri Yaya Ma'aruf ya ɗauke kai, ganin kayan sun kama mata jiki, kuma ya san shi
ba muharraminta bane. Sallama ya musu yana shirin juyawa ya ji Rahma tana cewa

"Daddy ka ce Yaya Ma'aruf ya miƙo fruit ɗin ka cigaba da bani" Ta faɗa lokacin da Daddy ya
zaunar da ita kusa da shi yana lallashin ta yana faɗin zai bata har sai ta ƙoshi.

Idanu Yaya Ma'aruf ya runtse jin rainin wayon wannan, ba don yana son ilimi ba, kuma yana
da burin ya je garinsu ya kawo musu cigaba daga jahilcin da suke ciki da tuni ya bar gidan nan
ya koma ƙauye. Maganar Daddy ce ta katse mata tunani.

"Ma'aruf miƙo fruit ɗin can na ƙanwarka" Daddy ya faɗa hankalinsa yana kan Rahma da take ta
zuba masa shagwaɓa, yana mugun son ƴar tasa. Haƙori Yaya Ma'aruf ya sanya ya danne
leɓensa na ƙasa yana jin takaicin wanann aiken, amma babu yadda zai yi, kasancewarsa mai
biyayya, cike da ladabi ya je gaban Hajiya ya ɗauki tiren, Hajiya tana aika masa wani kallo
saboda ita kawai bata ƙaunarsa.

Sai da ya je zai ajiye amma Rahma ta miƙo hannu ta ce ya bata plate ɗin, ya mayar da tiren
kicin. Daddy bai ji daɗin abin da ta yj ba amma babu yadda zai yi don ba ya son abinda zai

mata ran Rahma. Haka Yaya Ma'aruf ya danne zuciyarsa ya ɗauki plate ɗin fruit ya miƙa mata
ashe dai bata riƙe ba, ai kuwa plate ɗin ya kuɓuce gabaɗaya kayan marmari suka yi masauki a
jikin fararen kayan Rahma, duk ruwan kankana ya fito jawur a jiki, tana kallon jikinta ta fashe da
wani kukan ɓaci, da sauri Hajiya ta tashi har tana neman yin tuntuɓe, tana zuwa vata yi
wata-wata ba ta ɗaga hannu ta saukewa Yaya Ma'aruf yatsunta biyar a kumatunsa, kuncin ya
safe cike da mamaki ya ɗago idanu yana kallonta Daddy kuma ya miƙe tsaye, duk da ya ji zafin
abin da Ma'aruf ya yi na zubaw Rahma kayan marmarin a jiki amma kuma ya ji haushin marin
da Hajiyar ta wanke Yaya Ma'aruf da shi a ganinsa abin da ya yi bai kai a mare shi ba, hakan ya
sa Daddy ya ce

"Hajiya...




*SHEIK*

Yana cikin wannan halin wandonsa jargaf da fitsari, ya fara ganin wasu ƙananan yara kamar
jarirai amma tsaye suke a kan ƙafafunsu suna doso shi, kusan su goma, da alama daga cikin
garin suke, abin da ya tsorashi ma babu wani mai sutura a jikinsa su duka tsirara, bai gama
tunanin jinsin mutane ne ko na aljannu ba sai ya ji budurwar nan ta ƙofar gidan da take kiranshi
ta ce

" Sheik waɗannan ƴaƴanmu ne ni da kai, wanda na haifa maka su daren yau, gasu nan zuwa
kowanne ka masa kuɗuba ka raɗa masa suna" Galala yake kallonta, ganin jariran suna dab da
zuwa suna faɗin

"Baba Sheik" Kawai Sheik ya yanke shawarar ya tsira da rai da lafiyarsa, don da alama wanann
yaran suka rafke shi wato suka ɗane jikinsa kowa fisgar inda ya samu zai yi ba lallai su bar shi
da fatar jikinsa bama, fakar idanun budurwar yayi kawai sai ya zura da uban gudu, ganin wata
kwana sai kawai ya sha kwanar, amma kamar almara sai ya ji ƙarab takun gudu a bayansa,
haka ya tabbatar masa da biyo bayansa ake yi, ganin wata bishiya ya yanke shawarar hawa
kanta, a nashi tunanin idan ya hau bishiyar in wanda suka biyo shi sun zo sun wuce sai ya
sakko in ya so ya gwammace ko gadin gidan wasu ya je ya yi da ya zauna a wannan bala'i da
tashin hankali, da shegen kaɗayi da son abin duniyarsa ya kawo shi ciki.

Yana hawa bishiyar yana jin wani santsi dakyar ya samu ya haye sai da ya hau can sama, ya
samu waje ya zauna, sai ganin jariran nan ya yj sun tasho suna gudu suna kiransa, haɗe da
wanann budurwar mai fitila, suka zo suka wuce bishiyar, wata dariya Sheik ya fashe da ita
marar sauti a zuciyarsa ya ce.
'Ashe aljannu ma ana iya guje musu, ka ga sakarkaru wato ni ina saman bishiya ku kun wuce
kuna kirana, wannan shi ake kira hotiho!'

Yana kallonsu har suka yi nisa kifta idanun da zai yi sai ya neme su ya rasa a fili ya ce

"Ai indau zan samu cikar burina to da in fallasa kaina a gane MALAMIN BOGI ne gwara kullum
in ke kwana a saman bishiya, a to don na ga wajen zama ni sai in ke kwantawa ma a kan
bishiyar in kr baro musu gi...

Jin an zungure shi daga bayansa shi ne abin da ya dakatar da shi daga maganar da yake, cike
da faɗuwar gaba ya ɗan waiwaya, jariran nan ya gani su duka suna kan bishiyar da yake
muryar ɗaya mai amo a cikin su ita ta katse shi da faɗin

"Baba Sheik muna ta nemanka ashe dai ka zo gidanmu" Jin an ambaci gidansu sai lokacin
hankalinsa ya kai ga kallon bishiyar da yake kai a nan ya ga bishiyar kuka ce wato matattarar
aljannu" Hawaye ne suka taru a idanunsa, ya tashi dakyar jikinsa yana karkarwa, rigar wuyansa
ya ɗakko ya ɗaure tsantsa, bai jira komai ba a fili ya ce
"Innal hamda, wal ni'imata laka wal mulk, la sharikala, Allahu akbar! " Yana gama faɗar haka ya
yi tsalle ya diro daga saman bishiyar nufinsa sai dai su tsera, da aljannun yaran, amma abin
mamaki maimakon ya ji shi a ƙasa sai ya ji shi ya dira a kan hannaye, yana dubawa ya ga
wannan jariran ne su duka suka masa ɗaukan makarar mamaci.
Babu damar guduwa ya zubawa sarautar Allah ido, don shi kansa ya san riƙon ma ba na jarirai
bae, tamkar wanda aka tara ƙattan maza.

Suna tafiya suna faɗin

"Mama mun ɗakko miki Babanmu" Sheik kuwa sai ruwan ido yake tamkar an buɗe famfo. Suna
zuwa ƙofar gidan suka samu wannan dai budurwar, shi bai san wane irin tunani zai yi ba ma.

Tana ta musu sannu da kawo Babansu ta matsa gefe suka shige da Sheik yana ji yana gani,
suna gama shiga, ta rufe ƙofar gidan ta saka sakata.

Ɗakin da Sheik ba a can ya sauka ba can aka nufa da shi, suna shiga suka zaune da shi yana
ta kallon ikon Allah, da suka ajiye shi suka fara kama jikinsa kowa yana mamula, guda biyu sun
kama breast ɗinsa suna sha wasu kuma jikin fatarsa da babu riga, a zuciyarsa ya ce

'Wai ni Ibra yau ni ɗiyan aljannu suke mamular fatar jikina da bakinsu marar haƙori, har da masu
sha mini mama, na ga ta kaina duk tsorona amma yau an ƙure mini gudu' Ya faɗa a zuciyarsa
hawaye suna zuba shaaaaa.

Yana nan zaune suna ta faman tsotsarsa, idanunsa a rufe don ya lura duk idanunsu babu
ƙwayar ido a ciki. Idanun a rufe ya ji kamar daga saman matar nan ta ce

"Ka raɗa musu suna ka zo mu kwanta dare ya yi" Cike da faɗuwar gaba ya buɗe, ya ganta
zaune a bakin wani gado mai kyau. Haka ya ringa kai bakinsa wajen kunne jariran yana musu
gwalan gwalantun larabcin da bai san mai yake faɗa ba bare ya san addu'a ce ko mene ne. Abu
ɗaya ya sani duk wanda ya gamawa gwalan gwalantun sai dai ka ji daga ƙarshe ya ce,
Mamuda, Lawwali, Amiru a haka ya gama raɗawa kowa suna. Yana gamawa suka tashi suna
masa bye-bye suna cewa sai sun dawo, haka budurwar nan ta miƙo masa hannu, wannan
karon a zuciyarsa ya ce zai gwada sa'arsa don yadda ya ga za su kaɗaice a gado da aljanna
yana tsoron wani abu ya wakana a tsakaninsu ma'ana ta je ta masa cikin gaske, tun da yanzu
ma gashi tana cewa ƴaƴan can nasa ne.

Ganin ta fara wani abu kamar mai shirin yin dambe sbai san lokacin da zuruf ya tashi tsaye ba,
sai kawai ya ga ta fara sawaya ta koma tsohuwa tukuf, a guje ya fito daga ɗakin, ɗakinsa ya
shige, yana haki yana shiga ya banke ƙofa ya saka sakata, kan katifa ya faɗa ya ja wani tsohon
bargo da ya gani a kan katifar, da gari lafiya ƙalau ne ya san, sai dai ya cewa ƴan garin
larabawa basa shiga tsohon bargo, amma yanzu da yake neman mafaka yake gani yake ko
cikin kashi aka ce ya shiga babu musu zai shiga kashin in da hali har wanka sai ya yi da
kashin..


Tun da ya rufa da bargon nan yake ta faman gumi amma bakinsa sai warto addu'a yake wacce
bai san wace iri ba ce shi dai fatansa ya tsira dafa halin wannan, sai ya ji a ransa zai bar garin
Ƙundu a gobe amma in ya tuna irin kaji da shayi mai kauri da zai je sha to tabbas sai ya ji zai
jure komai.

Tun da ya rufa shi ba a kwance ba, shi ba a durƙushe ba kawai dai ya yi goho ya nutsa kansa
a katifa, a haka yake ta jin ife-ife da guje-guje wani lokacin ya ji an buga ganga wani lokacin a
ƙwala masa kira, fitsari ya yi wajen kala biyar, har sai da aka fara kiran sallar asuba, sannan ya
ji komai ya lafa, can kafin shigar masallaci ya fara jin tashin muryoyi a ƙofar gidan, yana ji ana ta
bugawa, amma ya ƙi fitowa ma don shi yanzu babu wanda zai kira shi ya je, gani yake aljannu
ne, duk da yana ganin rashin fitarsa masallacin asuba barazana ne ga maluntarsa, amma dai a
halin da yake duk ya yi wurjanjan, da kuma jiki da fitsari jargaf in ya fita ya buɗe ƙofar abun
kunyar sai ya fi na ƙin zuwa masallaci.


Sai da ya ga rana ta fito tangararau ya tashi ya fito har lokacin rigarsa tana ƙugunsa a ɗaure,
ya since a zuciyarsa yana faɗin


'Wuya in ji tsula, yau malamin balarabe na ƙasar Yemen ya ga ta kansa cikin dare' Ya faɗa yana
shafo breast ɗinsa da suka sha damƙa a bakin aljannu. Dakyar yake tafiya haka ya je ya buɗe
ƙofar gidan sannan ya shiga ɗaki ya saka hularsa ta gashi da gemunda sajensa, yana gamawa
ya shiga bayi ɗaure da towel bayan ya kai ruwa, jikinsa ya shiga sallewa da daddaɗan sabulun

bulicin mai ƙamshi, ya gama saɓa jikin bai ɗaureye ba, dib ya ji wani abu ya faɗo daga sama,
yana dubawa ya ga kunnen jariri ne.


A can ƙofar gida kuwa Liman ne da Mai Gari suka zo da manyan ƙartai za a ɓalle ƙifar gidan a
shiga a ga ko lafiya sabon malamin balarabe bai fito sallar asuba ba, kuma an zo an buga masa
shiru, sun san dai malamai kamar Sheik ba ya ƙi yin sallar jam'i da gangan ba su da suke ganin
an kawowa ƙauyensu waraka daga jahilci, amma har rana ta yi ba a ganshi ba.
Ganin kunnen da Sheik ya yi, hakan ya yi daidai da saƙa ƙafa da wani ƙaƙƙarfan saurayi ya yi
ya hankaɗa ƙofar gidan, kasancewar Sheik sakatar ya cire bai buɗe ƙofar ba. Buga ƙofar da ta
daki bangon bayin shi ya ƙasa assasa tsoro da ruɗanin da Sheik yake ciki, tunaninsa ya bashi
aljannun ne suka kawo masa ziyara, don ya san yadda mutanen garin suke girmama shi, babu
yadda za a yi su banko masa ƙofa haka har ta gwaru da bango, towel ɗinsa ya fisgo a inda ya
rataye ya naɗa a ƙugunsa ko ɗaurewa bai yi ba, ya bazamo da gudu daga banɗakin takalminsa
ma ɗaya can ya barshi a bayin, sannan ga jikinsa kumfar da bai wanke ba, fitowarsa a rikice ya
nufi ɗaki ko kallon hanyar ƙofar gidan bai yi ba burinsa kawai ya shiga ɗaki ya kulle, Mai Gari da
tawagasarsa su Malam Liman ganin abin da yake faruwa sai suka tsorata, sun san duk abin da
zai sanya Ya Sheik babban malami balarabe gudu to ba ƙaramin abu bane, ganin shi da ya san
qur'ani da ayoyin Allah, da addu'o'i yana gudun ceton rai ina ga su ƙasurguman jahilai.


A take aka shiga ƴar tsere zuwa ɗakin Malam inda ya nufa, sai suke ganin nan ne wajen tsira,
samari guda biyu sai Malam Liman da kuma Mai Gari aka fara rige-rigen zuwa ɗakin Malam
Sheik, shi kuma Sheik sai da yana dab da shiga ɗaki ya lura da tawagar Mai Gari, ganinsu da
gudu a kiɗime sun nufo hanyar ɗakinsa alamar kamar an biyo su, sai ya yi tunanin gari ma babu
lafiya, tunaninsa su ɗin ma daga waje aka biyo su suka taho wajensa kasacewarsa malami
basu san a halin da ya kwana ba, basu san shi bacci ma tun na farkon dare bai runtsa ba haka
ya kwana tsakanin waje da cikin gida, yanzu ma yana wanka yana son bayan ya yi wanka ya yi
alwala ya yi sallah don yadda jikinsa yake sharkaf da fitsari sai ya yi wanka.


To sai kuma aka samu an jefo masa kunnen jariri a banɗakin, bayan ya fito hallaw gashi ya ci
karo da su manyan garin su ma sun zo. Da Sheik da Mai Gari aka yi karo wajen shiga ɗaki, shi
Mai Gari yana fatan kar Malam ya ƙulla musu salalan tsiya wato ya shige ya banke ƙofar ɗakin,
don su tunanin komawa baya ma su fita daga gidan hakan bai zo musu a ƙwaƙwalwar su ba,
bare ma sun san tun da aka samu matsala a masaukin malam to garjn ma yana dab da
rikicewa, don wani sa'in gabaɗaya aljannu garin suke rikitawa.


Karon da suka yi babu wanda ya lura, kowa ta kansa yake, a haka Malam Liman ma ya totsu
suka zama su uku a bakin ƙofar suna ƙoƙarin shiga, ƙofar ta musu kaɗan kuma kowanne ya
kasa dakatawa wani ya fara shiga. Samarin nan ma suna jira su ma su shige.

Malam Liman yana kai kansa suka yi gware da goshin Mai Gari, Sheik ne ya fara nasarar
shigewa ɗakin, sai dai da takalmin nan ƙafa ɗaya ya shige santsin ledar tsakar ɗaki ya kwashi
Sheik, sai gashi wancakal a gefe, yana ta yaƙi da towel ganin bai masa tsirara ba. Su kuea su
Mai Gari basu lura da wani towel ɗinsa ba bare su kawo zai yi wani tsirara, don gani suke
tamkar a filin ƙiyama inda ake cewa kows ta kai - ta kai yake.


Sheik da rarrafe ya ƙarasa saman katifa, sai Mai Gari da Malam Liman suka mara masa
baya, samarin nan ma suna shiga ɗayan ya banka ƙofar, su duka cakuɗe a kan katifar, Sheik ya
warto tsohon bargon nan, zai rufa ai kuwa Mai Gari ya ce da wa Allah ya haɗa shi in ba da
bargon hannun Sheik ba, nan ya shiga yaƙin warta don ya rufa shi ma, haka Malam Liman ma,
ya shiga jan bargon da ya gama shan duniyarsa, kasancewar bashi da ƙwari sai ya yage a biyu,
Malam Liman ya ɗauki ɓangare ɗaya, Mai Gari da Sheik suka shiga ɗayan, samarin nan suka
totsa kawunansu a babbar rigar Liman...






Na ba kaina daria yau Allah sa ju dara amma akwai cakwakiya.



Mu haɗu next page akwai gwarama, za ku ji yadda Sheik zai kare kansa saboda rainin wayo,
su kuma sai su bada kai bori ya hau.




MAMAN AFRAH

09025576222
[7/2, 4:03 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/EBurrU2vz6OFGbE37xLhPS


‍♂️ *MALAMIN BOGI*‍♂️


NA

MAMAN AFRAH


First Class Writer's Asso.�

Daga marubuciyar:

Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga

Da sauran su.
*09025576222*



BOOK1️⃣
PAGE 4

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login