Showing 24001 words to 27000 words out of 63190 words
tana dosar zauren tana ɗan ɗar-ɗar.
. Tunde yana tsaye ya ga Inna ta fito riƙe da gatari, a tsorace ya fara ja da baya yana faɗin
"Ba tashin hankali bane ya kawo ni" Ganinsa sai Inna ta sauke gatarin da ta ɗaga saman, ta
shiga kallonsa da mamaki ta ce
"Bayerabe mai kuma ya kawo ka gidan nan?" Kallonta ya yi ya ce
"Dama Ibra ne ya ci bashi a wajena... Tun bai ƙarasa ba Inna ta fara sababi tana faɗin
"Allah sa uban bashi ya ci ba bashi ba, ni ina ruwana ko na san lokacin da kuka yi, ko ka taɓa
gani ko siyen ashena na je shagonka, saboda ba na son arne ya ƙaru da ni, in sha fafutukar
neman halal ɗina ta hanyar siyar da kayan miya amma in je in yi wa arne ciniki, on bar musulmi
to na san ciwon kaina ehe" Ta faɗa tana muzurai
Cike da jin haushin ta cw za ta yi wa musulmi ciniki ya ce
"To in ma liman za ki yi wa ciniki ni babu ruwana, yanzu ki shiga ki fita ki biyani kuɗin da nake
bin jikan ki tun da lika biya kuɗin saniya ma...
Tana masifa ta ce
"Wato ga Tasallar mahaukata, sai aka ce ni gabaɗaya rayuwata a biyan bashi za ta ƙare, ni ba
zan yi abin kaina ba sai dai in yi ta biyawa Ibra rigimar da ya ɗakko, tun yana ƙarami nake
faman asarar kuɗi a kansa, kuma wanda ya ce na biya kuɗin saniya ƙarya ya shirga maka, don
ni wallahi Jummai ko kuɗin igiyar ɗaurin saniya ban bata ba bare kuma kuɗin wata saniya"
Ransa a ɓace ya ce
"Ko baki biyata ba ni dai dole ki bani, mayukan bilicin ɗin da ya karɓa kaɗai ma ba na ƙananan
kuɗi ya karɓa ba idan baki bani ba sai na je birni na ɗakko ɗan sanda...
Kamar za ta kai masa duka ta ce
"Gwafar uban ɗan sandan, idan ka yi asarar kuɗin motar zuwa birnin ka ce ɗan sandan na ce
ba sanda ba ko ƙota ce na bi ta kanta da gudu aikin banza da wofi, wani shegen ya ce ka bashi
bashin man bilitin(Bilicin) Gabaɗaya ka sauyawa yaro kamanni da man turawa ka mayar da shi
fata kamar ƙullin ƙosan da ya sha jan tattasai, fuska tana masa tabbare-tabbare, ni ba don na yi
wa Ibra farin sani ba wallahi tsabar wannan shafe -shafen da yake ba zan gane shi ba, duk ya
sauya halitta da jikinsa da baƙin bayan tukunya bambancin kaɗan ne wajen baƙi, amma yanzu
gabaɗaya jikinsa babu baƙi, ban da ma Ibra ya girma yanzu na tabbata ko mazaunansa aka
kwataye aka buɗe sai an samu sun yi fari ina dalili" Ta faɗa tana hararar Tunde da yake jin ba
don kar a kore shi daga garin ba, ko kuma a yi shari'a da shi da tuni ya make Inna ta faɗi
sumammiya saboda takaici.
Ganin bashi da niyyar tafiya ta yi wurgi da gatarin tana faɗin
"Yanzu zan yi maganin ka, ka bari in shiga in fito, kai ba kai kaɗai ba duk wanda ya ƙara zuwa
neman bashi wajena, bayan ba ni na ci ba aradu sai ya gwammace kiɗa da karatu" Ta faɗa a fili
a zuciyarta kuma ta shiga cikin gidan tana faɗin
'Anya Ibra zai ga annabi kuwa, a ce ka gudu da saniyar mutane, jiya ma da tsakar rana sai da
me wainar rogo ta zo karɓar jaka biyu da rabi (500) Yo in ba fashi da makami nake yi ba ina zan
samu wannan maƙudan kuɗi in biya ta in na biya kuɗin bashin Ibra sai na daina siyar da kalwa
da kuka wallahi' Murfin wata ƙatuwar tukunya irin ta girkin gidan biki ta ɗakko, tana ɗauka ya
fara rinjayarta kasancewar yana da nauyi, amma a haka ta nufi zauren da ɗan saurin ta, Tunde
yana ganin Inna ya fita a guje don takardar ma a zauren ya barta, yana gudu yana masifa cikin
yarbanci.
Inna har ƙofar gida ta fito riƙe da murfin tana huci saboda nauyin da ya mata....
*A yi haƙuri da wannan yau ko malam bamu leƙo ba, in sha Allah sai a next page*
MAMAN AFRAH
09025576222
[7/7, 7:36 PM] Mom mashkr & Afrah: *MALAMIN BOGI*
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.
Daga marubuciyar:
Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*
BOOK1️⃣
PAGE 7
IMZEEDVENTURE https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha.
Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada
ko gonjo mai kama da sabo?
To shiga group ɗin
IMZEEDVENTURE
join Here.
Za ki sha mamaki!
Muna da
✅Adashe na kayan kitchen
✅ Kayan yara sabbi da gonjo
✅Kayan gyaran gida masu kyau
Tuntubi mu:+2347077532253
DM ;Whatsapp
IG/Tiktoc:@imzeed-venture
*SHEIK*
Gabaɗaya sai hankalinsa ya tashi ganin mutane da ya zo wajen don ya taimaka musu suna
gudunsa, wato wasa tare amma ci bamban. Duk mutane an koma can nesa da kukar ana
kalllon ikon Allah, Sheik kuwa gabaɗaya ya yi saranda ya san tabbas abin kunya yana dab da
bayyanuwa, don bai san yadda zai kuɓuta daga wannan tarkon ba.
Kan ƙwarangwal ɗin nan ya fara yawo a saman kukar da yake mutane babu wanda yake
ganin kan sai Sheik abu ɗaya dai suka sani shi ne in ba aljannu ba babu wanda zai ɗaga Sheik
ya kai shi saman kuka.
Kan ne ya nufo kusa da fuskar Sheij, yana ji yana gani kan yake nema kaiwa bsminsa
sumbata, Sheik ya shiga kawar da kai gefe, don ya san tabbas akwai gagarumar matsala a ce ,
amma kan kamar an ce dole ne ya sumbaci Sheik, duk ya ruɗe amma har lokacin saboda ƙarfin
hali fantekar kuɗinsa tana ƙanƙame a hannunsa. Gashi yana son ya ɗakko robar ruwan
maganin nan ta cikin fantekar ya watsawa kan amma kuma tsoro da fargaba ba zai bari ya yi
hakan ba, ba ma a nan gizo yake saƙar ba so yake ya maje, ya jajirce kar ya bari rauninsa ya
bayyana ga ƴan gari don idan ya bari suka gane yana tsoro to kuwa akwai babbar matsala,
kuɗin da yake saka ran ci daga gare su ma zai zama ya masa wahala saboda za suke masa
kallon kamar dai ba malamin bane.
Lura da ya yi basa ganin kan wannan ya san hakan ba ƙaramar matsala ba ce amma da
hakan yake ƙoƙarin saita kansa. Baki ya buɗe zai yi magana kan ya karkata ya saka masa
kunne a baki, ma'ana ƙwarangwal ɗin ya saka kunnesa a bakin Sheik.
Sheik a zuciyarsa ya ce
'Mai Gari a kawo taimako saboda aljannu sun fara mini ɗaurin goro' A fili kuma ya shiga ciccira
idanu, amma saboda ƙarfin hali yana so ya ɓoye halin da yake ciki, duk da abin yana neman cin
tura.
Mai Gari a zuciyarsa ya ce 'Shikenan ma in suka ɗauke ka, uban kuɗin nan da ka tara ai sai na
maye gurbinsa, kafin Allah ya sa ka kuɓuto' Ya faɗa idanunsa a kan fantekar kuɗin saboda gani
yale matsayinsa na Mai Gari da a ce mutanen gari haka suk tara masa kuɗaɗe da yanzu ya yi
ban kwana da talauci.
Sheik da wani irin sauti ya ji wannn kan yana masa magana yana cewa
"Ibra, ka baro garinku ka zo wannan gari baka san matsalolin da suke ciki ba, to ka kawo kanka
cilin gagarumar matsala, ko dai ka haɗa kayanka ka koma inda ka fito ko kuma mu shiga
fafatawa da kai" Tsuru Sheik ya yi yana jin maganar kamar tana amsa kuwwa amma ya lura shi
kaɗai yake ji, idanu ya sauke a kan uban kuɗin da aka saka a cikin fantekar nan masu uban
yawa, duk da yawanci ƙananun kuɗi ne amma ya lura akwai ƴan dubu-dubu. Ganin kuɗin nan
sai ya ji babu gudu babu ja da baya tun da gani yake babu mai ja da cikar burinsa, wani yawu
ya haɗiye yana muzurai, kai ya ƙara cewa
"Ka amince za ka bar garin Ƙundu a yau?" Wannan tambaya ta sanya ya ji wani takaici saboda
ga shi dai a kwana ɗaya ya haɗa wannan uban kuɗi babu aikin fari bare na baƙi, to ina ga ya yi
watanni, duk da shi a ransa yana ganin in har ya samu dama a shekara goma ma ba zai bar
garin Ƙundu ba, tun da ya ga wannan hanyar arziƙinsa. Shiru da ya yi sai kan ya ce
"Shirunka ya nuna ba za ka tafi ba to mu zuba mu da kai" Ana gama faɗa masa haka sai ya ga
kuɗaɗen cikin fantekar sun fara ɓacewa, idanu ya shiga zarewa yana son yin ihun kuka amma
babu dama, ba ya so ya bayar da kansa a wajen Mai Gari da mutanen gari.
Gabaɗaya cikin fantekar sai robar maganin kaɗai ta rage sai wata tsohuwar naira biyar. Takaici
ne ya kama shi yana ji a ransa da a ce shi malamin gaske ne ba MALAMIN BOGI ba da sai ya
yi addu'ar da zai ƙona aljannun garin gabaɗaya, tun da gashi yanzu ya ga samu ya ga rashi.
Kafin ya gama wannan mamakin sai ya ji an fara tura shi daga baya kamar dai idan mutum ya
hau lilo ake tura shi yana yin gaba yana dawowa baya, to haka ya ji, idanu ya runtse tun da shi
banda fantekar wannan da ya riƙe babu wani reshe da ya riƙe, illa wuyan rigarsa ne kawai
yanzu a maƙale da bishiyar kukar.
Turashin da aka fara sai ya fara ganin kamar zai hantsila ƙasa, suratul nasi ce kaɗai ya samu
nasarar wartowa a bakinsa ya shiga karantowa babu sautin yana fita a hankali sai shi kaɗai
yake ji, su Malam Liman da suke ƙasa da mutanen gari suna kallon yadda ake shilla Sheik
bakinsa kuma sai kaiwa da komowa yake alamar yana magana sai dai kasancewar a can sama
yake basa iya jin furucin nasa. Ya daɗe a haka har ya fara fidda rai da rayuwa, hawaye suna
safa da marwa a saman fuskarsa. Dakyar ya samu ya daina hangen ƙwarangwal ɗin kan
wannan don ya ɓace ɓat, sannan an daina cilla shi yana lilo.
Ganin haka sai ya fara tunanin mafitar da zai wanke kansa ba tare da mutanen gari sun gano
ainihin abin da yake faruwa ba. Hannusa ɗaya ya cire daga jikin fantekar ya kaiwa jikin reshen
kukar wani uban naushi, har sai da bayan hannun ya fashe alamar ƙumewar da ya yi, ya buɗe
murya yana faɗin
"Allahu akbar!" Sai da ya kaiwa reshen nan naushi sau biyar yana ambaton kabbara, duk da
azabar da take ziyartar hannun nasa.
Ji ya yi an finciko rigar tashi daga inda take a maƙale, idanu ya waro ganin ya nufi ƙasa
gabaɗaya mutane aka dare daga wajen, Sheik fatansa da addu'arsa Allah ya sa ya faɗa a kan
Liman ko Mai Gari, sai dai saboda ƙarfin hali yana dab da faɗowa ya buɗe murya yana faɗin
"In sha Allahu balaraben malami ne da nasara a kan ku, garin Ƙundu ya fi ƙarfin ku aljannu" Da
wanann kalaman ya faɗo sai gashi wancakar a tsakiyar wajen, ƙatuwar fantekar wannan ta kife
kansa, gabaɗaya jama'a aka yi kansa, faɗuwar da ya yi ya ji hular gashin sa tana neman
cirewa.
Ga faɗowar da ya yi ƙugunsa kamar zai cire amma dai saboda wannan ce hanyar cutar jama'a
da zai yi wajen samun kuɗinsa dole ya daure. Mai Gari ne ya miƙa hannu saman kan Sheik ya
cire fantekar yana ta faman jera masa sannu.
Duk da ya jigata kuma idanunsa a rufe amma a haka yake jero kabbara. Jin hular gashin
kansa tana nema zamewa ya yi azama ya dafe kansa da hannu, mutane duk an kewaye shi ga
hawayen nan da ya yi ga bayan hannunsa ɗaya a dauje, da kaɗan-kaɗan ya shiga buɗe idanun
kowa ya zuba masa na mujiya ana jiran a ji ta bakinsa.
Hannu biyu Mai Gari da Liman suka saka suna ƙoƙarin tada shi zaune, duk fa haka bai yi wasa
dafewar da ya yi wa hular gashon kansa. Mai Gari ne ya buɗe baki ya ce
"Sannu Ya Sheik, Allah ya maka alam nashra" Ya faɗa cike da tausayawa. Cike da ƙarfin hali
Sheik ya ce
"A haba kar ka damu Mai Gari ai mu Allah ya riga ya bamu, duk runtsi ba zan bari a cutar da
garin nan ba sai inda ƙarfina ya ƙare" Liman ne ya ce
"Kamar ya Sheik kai da ka sha wahala amma kake kiran sai ƙarfinka ya ƙare?" Sheik a
zuciyarsa ya ce
'Ka ji masu hana ruwa gudu, waɗannan basa mutuwar tsakar ɗakinsu, wato zani zai kuncr mini
a kasuwa' A fili kuma ya ce
"Ai ni nan na hangi wani bala'in tashin hankali, gingimeman yaƙin duniya na uku ne aljannu
suka shirya tsakanin su da mutanen garin Ƙundu, gabaɗaya so suka yi su tarwatsa ku, su yi
muki bazata, cikin ƙoƙari don ba na so ku firgita hankalinku ya tashi, shi ya sa a zuciyata na
ringa addu'a a kan iska ta kai ni saman kukar, domin daga can ne aka shiryo dakarun yaƙin, shi
ne ma kuka ga na tashi a saman iska, to a can ma ku abin da idanunku yake gani da ban abin
da yake faruwa da ban, kuna ganina a rataye amma bakwa ganin gwagwarmayar da take
faruwa, yaƙi ne ake tafkawa suna kawo sara fa suka da wuƙaƙe da adda ta aljannu a ƙarshe
duk na ƙwace makaman na ci su da yaƙi hatta wanann hannun nawa haɓar wani aljani na yi ta
naushi da shi kun ga yadda na ji ciwo, ku za kuke gani ina naushin kuka amma ni ina ganin
aljani ne mai ka bakwai, ganin dai zan musu lahani duk suka watse don duk na jinyata su,
saboda baƙin talaucin da suke ciki ma, na raba musu kuɗin da kuka tara mini, domin na ji suna
cewa za su bazo garin duk wasu kuɗaɗe su kwashe" Gabaɗaya maza da matan wajen suka yi
wata kabbara tamkar a filin sallar idi.
Suka ce "Allahu akbar" Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke jin ƙaryar da ya zabga ta kuɓutar
da shi, a take Mai Gari ya saka ƙasan babbar rigarsa yana sharewa Sheik ƙasa a bayan rigarsa
ganin faɗuwar da ya yi duk ya kwashi ƙasa.
Cike da tausayawa yana miƙa hannunsa kan hular Sheik daga ƙeya yana karkaɗe masa ƙasa,
Sheik kuwa sai ƙara danne hular yake gudun afkuwar matsala, Mai Gari ya ce
"Lallai garin Ƙundu ya yi dace mai shahada da sadaukar da kai ga mutanen garo domon ceton
rayuka, in ba haka na ta yaya za ka amince da garin nan har haka?, Ni da ya kamata a ce ni
zan yi wannan sadaukarwa" Sheik cike da lanƙwasa kuryarsa ya ce
"Ina ai in har ina garin nan babu wata matsala da za ta tunkaro ku in ƙyale ta, saboda mu can a
ƙasashen larabawa haka muke yi bare ni da na baro ƙasata don in zo in taimaka muku"
Gabaɗaya sai aka shiga jinjinawa Sheik bisa namijin ƙoƙarin da ya yi, haka ya ƙara girma a
idanun jama'a kowa yana yaba masa.
Haka aka yi yuya guda don raka Sheik gida ya huta saboda faɗa da aljannu. Amma a ransa
baƙinciki ne fal na yadda aljannun suka ɗauke masa kuɗin da ya tara, yana murna ya samu kuɗi
ashe dai da sauran rina a kaba.
Har cikin gida aka rako shi ana girmama shi, da zai shiga ɗaki Liman ya ce
"Sheik Allah gafarta malam ga robar ruwan maganinka, da naira biyar ɗin nan, ita da ka rage ta
a cikin fantekar ko maganin aljannun za a yo da ita" Ya faɗa cike da girmamawa yana miƙa
masa don an ba mai fantekar fantekar ta. Sheik kamar ya yi kuka ya ce
"Eh ai ina sane na rage ta, ka san har hawayen tausayin garin nan na yi a saman kuka na ji
tausayinku sosai" Ya faɗa yana danne takaicin da yake ji a ransa ga zafin da hannunsa yake yi.
*DA YAMMA*
Ƙofar gidan Sheik ya cika da jama'a maza da mata, masu karɓar magani, saboda ya ce ba
za a ke bada magani a titi ba