Showing 45001 words to 48000 words out of 63190 words
shi shiknn"
Jummai ta ce
"Tsofai tsofai da ke sai ki auri jikan cikin ki?"
Inna ta ce
"Yo haramun ne kuma da kike wannan maganar sai ki ga ni tsohuwar na fiki kataɓus a gidan
auren... Cike da haushi ta katse Inna da cewa
"Yo Sale mai zai yi da ke"
Inna ta ce
"A'a Jummai tsakani da Allah kar ki ari bakinsa ki ci masa albasa ai sai ki bari ya bada amsa da
kansa" Jummai tana nuna Inna da yatsa kamar za ta tsone mata ido ta ce
"Yo wannan abu ai a bayyyane yake gwara tun muna shaida juna ki biya bashi in ba haka ba
birni zan je in ɗakko miki ɗan sanda"
Inna ta ce
"Kulki za ki ɗakko mini, ke ko ƙarewa ki ɗakko soja" Sale ya ce
"Haba Jummai ya ana neman masahala kina ƙin karɓa ko kin gwammace ake abu ɗaya wato
faɗa" Juyaw Jummai ta yi bakinta sake tana son tabbatar da manufar mijin nata, saboda a
yanayin maganarsa sai ta ji kamar dai yana goyon bayan Innar ne.
Ya cigaba da faɗin
"Tun da har ta amince ai babu komai in har hakan zai zama masalaha" Inna wani murmushi ta
yi saboda ita dai ta san wannan ce mafita babu inda za ta samo kuɗin saniya.
Jummai ta ce
"Babu wani masalaha munfurci dai irin naka in ba haka ba, ta yaya za ka amince da auren
tsohuwa" ,Mai Gari ya dakatar da su ya ce
"Haba Jummai wai ni ku mata wani lokacin me ya sa bakwa son gaskiya, duk wani abu in dai
aka ce warwarar matsala ne shikenan kuma mutum ba ya fita a wajenku"
Zuwa wannan lokacin Jummai ta kai linta a ɓacin rai, ji take tamkar ta yi da dukan Sule, Inna
da kuma Mai Gari, tsabar haushi.
Lami ta ce
"Inna wai da kike maganar aure da mijin Jummai da wasa kike? Idan ba da wasa kike ba ni
kuma ya za a yi da nawa kuɗin"
Inna ta ce
Lami kin san dai ni guda ɗaya ce ba biyu ba, kuma dai jikana kike aure bare ke ɗin ma in ce
zan aure mijinki a fanshe kuɗin, sannan tun da ba wani shegen ya aike ki basho sanoysr ba sai
ki jira ya dawo ya biya ki"
Mai Gari ne ya katse da cewa
"Ni kaina na gaji da shari'ar nan kuma shi wanda ya cinye saniya ba a san inda yake ba ma,
yanzu tun da Tasallah ta amince da auren Sale za a ɗaura auren... Jummai ce ta koma ta yi
zaman ƴan bori ta ce
"Yanzu Mai Gari wanann ne adalci? Ya za a yi a dakeni a hanani kuka, a cinye min saniya kuma
a aure mini miji"
Mai Gari ya ce
"Idan har kin amince kin haƙura har ranar da Ibra zai dawo to, amma da sharaɗin kar in ƙara
ganin ƙafarki a fadar nan"
Jummai ta fitittike ta ce bata yarda da jiran Ibra ba kuma ba za a auri Inna ba. Sale ya ce ai ko
an fasa shari'ar nan to fa shi dai aure da Inna babu fashi, a cewarsa ma zai biya Jummai kuɗin
saniyar idan ya yi noma da damina" Kafin ya gama rufe baki Jumma ta je tsakiyarsa inda yake
zaune tana ruwan bala'i, a ƙarshe dai Inna ta ce
"Jummai ki kwantar da hankalinki auren nn na wuce gadi ne, idan na aure shi duk inda Ibra ya
dawo to takardar sakina za a bani in bar muku gida, in ba larura ba ma ina ni ina aure a wannan
shekarun nawa"
Mai Gari bai jira komai ba ya fara gabatar da shawara a wajen jama'ar fada kowa ya ce
wannan ce mafita, Sule ya kyallara idanu yana kallon Inna da wani murmushi Inna ta rufe fuska
irin na jin kunyar nan.
Har za a fara gabatar da ɗaurin auren Inna ta ce
",Mai Gari a ja kunnen Jummai fa kar a zo bayan aure take ce mini ƴar sadaka, ko take kiran
aurena da auren biyan bashin saniya"
Mai Gari ya ce
"Ai sai dai in bana garin nan na Mai Mangwaro"
Sule ya ce
"Daga na bata kuɗin ta in na yi noma ai kin zama mallakina ma" Wani farrrr da idanu Inna ta yi.
Mai Gari ya ce
" A yi wa annabi salati"
Jama'a suka ce S.A.W"
Yaraf Jummai ta yanke jiki ta faɗi sumammiya.
*MA'ARUF*
Da sauri Ma'aruf ya ɗago kansa yana kallonta, Rahma kuwa sai ƙwafa take a ranta tana cewa
Allah ya ƙara maganin mai shishshigi da shiga abin da babu ruwansa.
Daddy jikinsa ne ya yi sanyi jin furucin Hajiya tabbas yana son Rahma amma ba zai kori
Ma'aruf daga gidansa ba saboda ya san Mai Gari yayansa shi ne sanadiyyar dawowarsa garin
abuja da zama sannan a taƙaice ma shi ne silar arziƙinsa, yanzu yana jin nauyinsa ya kora
masa ɗa gida saboda wanann maganar sannan ba zai iya yi wa su Hajiya musu ba hakan ya sa
ya ce
"To shikenan Ma'aruf ke ɗauki kayanka mu je in sauke ka a tasha sai ka je gida, idan ka je ka
haɗani da Mai Gari in masa bayani" Cike da takaici da kuma da na sani Ma'aruf ya ɗago kai ya
sauke a kan ɗan uwan mahaifin nasa, amma abin mamaki sai ya ga Daddy ya faki idanun su
Hajiya ya ƙifta masa idanu, duk dabya kasa ganewa cewa gizo idanunsa suke masa ko kuwa
dai ya ga Daddyn ya masa wata alama.
Daddy ya ce
"Amma yanzu tun da dare ya yi da safe sai ka tafi" Haka ya buɗe baki zai yi magana Daddy ya
dakatar da shi, akwatin ya kinkima Hajiya tana murmushin nasara, na ganin sun jefar da
ƙwallon mangwaro sun huta da ƙuda, Rahma har da cewa Allah raka taki gona.
Da daddare bayan kowa na gidan ya yi bacci, Hajiya da ta gama ƙwawar Alhaji ya kwana a
ɗakinta ya ce shi ba ya jin daɗin katifar ɗakinta saboda bata da laushi ya fi so ya kwana a
ɗakinsa, ta rasa mai ya sa yanzu ya fi son kwana a ɗakinsa, ita kuma kawai bata son gadon
ɗakinsa saboda irin ƙaramin nan ne bashi da wasaci sosai, wannan dalilin ya sa sai ta yi
kwanciyarta. Yau ma kamar kullum hakan ce ta faru, Alhaji da tun da ya shiga ɗakinsa ya rufe
ƙofa ya hangi wayarsa da take kan bed side drower tana kawo haske wani murmushin gefen
baki ya saki yana shafa haɓarsa, wajen wayar ya nufa kamar yadda ya yi zato kuwa hakan ce
ta kasance sunata ya gani kamar yadda ya yi saving my zee bakin gadon ya koma ya zauna ya
ɗaga wayar cikin muryarta mai ɗauki da sinadarin shagwaɓa ta ce
"Haba baby ka barni sai tsoron nake ji ina dakon jiran dawowarka" Ta faɗa tana sakin kukan
kissa. Wata ajiyar zuciya ya sauke tana jin ta har cikin kunnenta cikin ƙasa da murya ya ce
"Haba amarya ke kin san sai dai in wani abu ne zai riƙe ni amma ina nan zuwa gare ki, kin san
dai daga kasuwa ma a nan na yada zango, to yanzu ma ina so ta yi nisan zango a bacci in
lallaɓo in taho" Daɗi ne ya rufe Zee ta ce
"Sai ka ƙaraso" Amsa mata ya yi yana lunshe ido tonowa da ya yi da cewa yanzu idan ya je
tana nan sanye da kayan baccin nan nata masu taushi da kama jiki.
Sai da ya ɗauki kamar minti talatin ya fito ya nufi ɗakin Mummy yana zuwa ya tura ƙofar ɗakin,
tun kafin ya shiga ɗakin kunnuwansa suka yi arba da munsharin da take sakin tamkar an
shaƙewa raƙumi wuya, kasancewar tana da nauyin bacci har ya ɗan tsaya amma ko motsi bata
yi ba ta yi shame -shame.
Ƙofar ya jawo mata a hankali, ya rufo, ɗakinsa ya koma ransa fari ƙal, yana zuwa ya ɗauki
wayarsa da kuma mukullin ƙofar baya wacce yake bi ya yi ɓadda kama ya tafi gidan Zee.
Zee ƙawar Rahma ce amma ba ƙawa ta jiki sosai ba, sun yi aure da Daddy ba tare da sanin
Hajiya ba kasancewar tsananin kishin Hajiya ya saka ta sanya shi ya mata alƙawarin ba zai
mata kishiya ba, yanzu kuma da tafiya ta yi tafiya yana son ya yi auren amma babu hali. Don ba
za ta bari ba, sun haɗu da Zee ne watarana ta zo wajen Rahma, bayan ta fita shi kuma yana
ƙoƙarin shiga get ɗin gidan, hakan ya sa ya ɗauke ta a motarsa ya kaita har gida, daga nan ya
karɓi lambar wayarta.
Komai a ɓoye ya yi hatta bikin Zee Rahma bata san an yi ba, saboda lokacin ta je hoto
Kaduna gidan wata ƙawar Mummy.
Ya fito cikin dunu da yake gabaɗaya ƙwayayan gidan an kashe su, sannan shi ma ya kashe
na ɗakinsa, yana lallaɓawa zai sauka daga matakalae kasancewar a sama suke, kamar daga
sama ya ji an buɗe ƙofar ɗaki, da sauri ya ɗauke sawub takalminsa yana saurin ƙarasa sauka
daga matakalar. haske ya hango an kunna fitilar harabar wajen, jin ƙaran tafiya ya yi saurin
laɓewa, yana nan a laɓe sai ya ga Rahma ta sakko tana sanye sa doguwar rigar bacci
hannunta riƙe da waya ta kunna fitilar.
Gabansa ne ya faɗi saboda ya san matsawar ta ganshi sai ta gane shirin fita ne a jikinsa,
don bai yi kama da mai bacci ba, kuma ya san idan ta ganshi tamkar a kunnen Hajiya sai ta
faɗa mata.
Fitilar falon ta kunna ta nufi frige ta buɗe ta ɗakko ruwan roba ta rufe, fitilar ta kashe ta haura
sama, sai da ya ga duhu ya rasa saman alamar ta kashe fitilar kuma ya ji ƙaran buɗe ƙofa da
rufewa, alamun ta koma ɗakin ta.
Ƙofar falon ya buɗe ya fita ta ƙofar bayan gidan ya kulle ta, machine ya samu ya tsare ya hau
ya nufi gidan amaryarsa. Yana zuwa ya ƙwanƙwasa mai gadi ya buɗe masa ya shiga, yana
zuwa part ɗinta ya ta buɗe ƙofar ya shiga ta rufe, yana kafe ta da idanunsa sai wani bubbuga
ƙafa take wai ya ƙi zuwa tana ta jiransa, a rayuwarsa shagwaɓa da ɓacin da take masa shi yake
rikita masa lissafi.
Kimanin wata biyu da yin aure suna cin amarcin su suna cin karensu babu babbaka, yana
fitowa daga gidan Hajiya in ya ce zai tafi kasuwa gidan amarya yake zuwa, sai a shelaƙe zai je
kasuwar, sai dai yaransa ne a kasuwar, sannan da wuri yake tashi ya koma gidan amarya, a
can sai dare zai dawo gida kullum da uzurin da yake ba Hajiya, ko Ma'aruf bai sani ba, abu
ɗaya ya sani shi ne Daddyn yana sanya shi ya ajiye shi a gidan amma bai san mai Daddy yake
a gidan ba.
Sannan da dare ma sai ya lallaɓa ya je su kwashi soyayya ita Hajoya tana can kwance basho
bata san wainar da ake toyawa ba.. Don haka amarya bata san bakin uwar gida ba saboda
kullum ita ce take da miji safe rana da dare ma su kwana, sai ya yi asubanci ya koma, don a
mota mai gadi yake mayar dashi da yake a gidan akwai motar Zee ɗin.
Ido biyu suka kwana suna bankar amarci tamkar ba za su rabu ba, Daddy ji yake yanzu kaf
duniya babu abin da Zee za ta buƙata ya ƙi yi mata saboda yana samun yadda yake so daga
wajenta. Tare suka shiga suka yi wankan su, ganin ƙarfe huɗu da wani abu ya ce zai tafi gudun
samun matsala, dakyar ya samu Zee ta bar shi ya fito, mai gadi ya ɗauke shi kamar kullum a
motar ya nufi gidan da shi a ƙofar bayan ya ajiye shi, ya buɗe ya fita ya buɗe ƙofar gidan ya
shiga ua mayar ya kulle.
A can cikin gidan Daddy kuwa Mummy ce ta tashi zaune, tana murtsuka idanu, tare da sakin
doguwar hamma ta rufe bakinta, ta sakko daga gadon ta nufi bayin cikin ɗakin nata domin yin
fitsarin da ya tashe ta, da ta fito har za ta koma kan gadon sai kawai ta fasa, ji ta yi kawai tana
son jin ɗumin mai gidan nata, ita da ta ma manta rabonta da shi saboda ita a nata hankalin
yanzu sai ta shafe tsawon lokaci basu kasance tare ba, tana ganin ai sun girma, bata san cewa
shi namiji ba ya girma da buƙatar sunnar aure, haka nan namiji ba ya tsufa da haihuwa.
Wayarta ta ɗauka ta kunna fitilar bayan ta kashe fotilar ɗakin nata da ta kunna, duk da ta san
ana kiran sallag zai ce masallaci zai tafi amma dai ta san kafin lokacin sun kashe arnan
soyayya ya haɗa alwala da wanka, tun da ta ga ƙarfe huɗu ta wuce.
Ɗakin nasa ta dufafa gadan-gadan ta kama hannun ƙofar ta murɗa tare da tura ƙofar ta
buɗe...
*SHEIK*
A kiɗime ya ɗago yana kallon Mai Gari ya ce
"Aure kuma Mai Gari ni Sheikul Yemen, balaraben malami daga ƙasar larabawa?" Ya tambaya
lokacin yana nuna kansa da yatsa.
Mai Gari ya ce
"Haba Ya Sheik kar ka manta ka sauka a garin nan don ka ceto garinmu daga halakar da shi da
aljannu suke yi kuma yanzu wata gagarumar matsala ta taso a ce kana tambaya mai kamar
tuhuma?"
Wani yawu Sheik ya haɗiye yana son nuna musu ba haka bane, cike da wayincewa ya ce
"Haba kai kuwa ina ni ina wannan babban al'amari ina so ne in san shin wa kuka samu ya mata
ruƙiyya har ya gano wanann baban al'amari na aurena a tare da ita?"
Mai Gari da bai zaci waɗannn tambayoyin ba ya ce
"Sai an mata ruƙiyya za a gane haka, ita da kullum bata cikin hayyacinta ita fa koyaushe
aljannunata suna tare da ita, ga shegen leƙen asiri da tone-tone, ai gwara ma da ta zaɓe ka to
ai kai ne maganin iskancin nasu idan suka je maka leƙen asiri su ganowa kansu maganin su"
A zuciya Sheik ya ce
"Kun kashe ni, leƙen asiri kuma? Ni da ba gaskiya gareni ba ina ɗan rurrumawa amma yanzu a
ce wai za a mini aure, auren ma da mai aljannu, in ƙi auren ku gano lagona' A fili kuma sai ya ce
"Kash aljannun nan basa kyautawa wataran" Ya faɗi hakan a ransa yana cewa sai ya , yanzu ni
ai ba zan ke garajen faɗar laifukansu ba kar in je a yi ta kife da shi.
Ɗaya daga cikin dattijan sa suka zo ya ce
"Amma Allah gafarta malam, me ya sa ka ce basa kyautawa wataran ni a nawa tunanin aljannu
ai kullum ma basa kyautawa, ka ga fa yadda yanzu suka ce idan baka auri amaryarka ba za a
tashi yaƙi a garin nan a kashe rayukan garin rabi da kwata, kenan akwai wani abu ko dai kan
tsoron su ne?" Sheik jin za a harbo jirginsa ya ce
"Ashsha Malam Wada ai ni nan aljannu ko wucewa na zo yi suna waje sai sun sara mini, ni ai
ba zan ƙi aurenta ba bare ma kun ce ido ɗaya gareta ai mu a ƙasashen larabawa jihadi ne ka
auri mace mai nakasa, kamar mai ido ɗaya ma muna kiranta mar'atul mubaraka, wato mace
mai albarka"
Gabaɗaya suka ɗauki kabbara " Allahu akbar!"
Don sun jinjina masa, shi kuma a zuci kuka yake yana jin wannan auren kamar dai wata
ƙulalliya ce aka shirya masa, tun da in akamce matarka ai dole za a ce za ta san sirrinka, shi
kuma da yake da manya sirrika, ya zai yi rayuwar aure da mai ido ɗaya kamar ɓera ya leƙa
buta, bayan nasa matan ma masu lafiyar ido ma ya bar su a can.
Haka ya ringa janyo kalmomin larabci wanda bai san ma'anarsu ba yana ta faɗa musu tare da
kwaɗaita musu cewa duk wannan larabcin ayoyi ne yake janyowa a kan falalar auren mace mai
ido ɗaya, yana yin hakan ne ko Allah zai sa ɗaya daga cikin su ya ce zai auri mai ido ɗaya
amma sai ya ga babu niyya ango ya kwana da wando.
Ya amince da buƙarar auren saboda ba ya so ya ƙi su ga gazawarsa, ba ma komai ne ya
ɗaga masa hankali ba sai da ya ji Mai Gari yana bayanin cewa asali da idanunta biyu aka haife
ta amma daga baya kuma aljannu ne suka cire mata idon guda ɗaya, buɗar bakin Sheik sai ya
ce
"Garin yaya?" Ya faɗa