Showing 54001 words to 57000 words out of 63190 words

Chapter 19 - MALAMIN BOGI COMPLET BOOK by Ameera Adam.pdf

18 Jul 2025

5277

ya buga da mugun ƙarfi kasancewar bai ma
taɓa kawo cewar Mummy ba ce, gabaɗaya sai ya razana, fitilar wayarta ta kunna a takw haske
ya gauraye É—akin, sai a lokacin idanunsa suka yi tozali da ita, duk da ya tsorata da kama shi É—in
da ta yi, kuma ya ga fuskarta ma babu yabo babu fallasa amma kuma sai ya maje ya É—an saita
kansa.

Mummy ita dai haushin inda ya fita da tunanin amsar da zai bata take, amma kuma bata taɓa
kawo cewar wai aure ya yi kai bata ma yi tunanin har zai iya fita daga gidan ba.

Cike da tuhuma ta ce

"Alhaji daga ina haka?" Ta tambaya tana kafe shi da idanu don gani ta harbo jirginsa
musamman da ta ji wani ƙamshin turare da ba nashi ba, yanayin ƙamshin mai sanyin ya sa ta ji
tamkar ma turaren na mata ne, sai dai ba za ta yanke hukunci ba, kai zuciyarta ma ba za ta bari
ta zargi Alhajin ta ba, saboda ta bashi yarda, ba ma wannan ne abin yin ba, sai alƙawarin da ta
sanya ya É—auka na dole, a kan cewa ba zai mata kishiya ba.

Cike da iya sarrafa harshe ya ce

"Ni ke ce ma kika bani tsoro kawai sai ki zo cikin duhu ki zauna? " Sai ta ji gabaÉ—aya ma ranta
ya ɓaci kasancewar tana tambayarsa yana tambayar ta.

Rai ta haÉ—e ta ce

"Kai É—in ma ai a cikin duhun ka fita, da ka dawo ma a duhun ka dawo"

Gabansa ne ya bada rass jin furucin ta, tunaninsa ko dai shuka ya yi a idon makwarwa wato
Mummyn ya ga tafiyarsa ko kuma dai Rahma dama ta gan shi ƙyale shi ta yi ita ce ta faɗa mata,
wani gumi ne ya karyo masa, ya san in her Rahma ta ganshi amma ta nuna bata ganshi ba sai
da ya fita ta bi sawunsa to tabbas babu abin da za ta ɓoye wa Hajiya. Jarumta ya ara ya ce
"Haba Hajiyata ai ni na fita a duhu ne saboda kar in kunna haske ki hango daga É—akin ki, ki ce
na bar miki idanuna basu runtsa ba wato ban yi bacci ba, kuma da na dawo ma wannan dalikin
ne ya sa ban kunna hasken ba" Ya faÉ—a zuciyarsa cike da zulumin Allah tarkonsa ya kama
tsuntsu.
Wani daÉ—i ne ya baibaye Hajiya don yanzu kam na gane komai ma saboda soyayyarta ya yi,
wani farrrr ta yi da idanunta ta ce

"To yanzu dai ina ka je?"

Hannu ya kai ya shafo gashin kanta da babu hula ya ce

"Kawai fa ina kwance na falka nake jin motsi a ƙasa shi ne na sauka na duba, ashe ma dai
kunena ne don ban ga komai ba"

Murmushi ta yi tana cewa

"Kai kam baka son abin da zai taɓa iyalinka"

Murmushin jin daɗin samun nasara a kanta ya yi, don ya san tabbas matuƙar ta gano shi to
akwai gagarumar matsala ko da kuwa ganin budurwarsa ne bare kuma a ce matar aure, auren
ma kuma a ɓoye ba tare da sanin ta ba duk da cewa ya san ita ce ta ja koma mene ne, a ce
mace ta ce ita ba za a mata kishiya ba, wannan son zuciya ne da dannewa namijin haƙƙinsa tun
da Allah ya halatta masa.



Washe gari tun da sanyin safiya Hajiya take famar a je a sallami Ma'aruf da kuÉ—in kota ya
kama hanyar ƙauye, Daddy kuwa da ya gama shirin fita ya ɗauki Ma'aruf ɗin suka fita tare, bai
zame da shi ko ina ba sai gidan Zee a nan ne yake gabatar da Zee a wajen Ma'aruf tun da ita
dama ta san shi a bakin Daddy.
Daddy ya ce ya zauna a ɗakin baƙi kafin ya gama sama masa admission a wata ƙasar inda
yake ganin zai dace da cigaba da karatun sa. Ma'aruf ya yi mamakin jin cewa Daddy yana da
wata matar bayan ya san babu wanda ya sani kuma ya san akwai matsala ko dai ya ce tashin
hankali duk ranar da ƙwan ya fashe za a yi ɗan jijjiɓin yaƙi.

Ya ji daɗin cewa Daddy za fitar da shi ƙasar waje karatu, wannan ya nuna cewa Daddy har
yanzu yana riƙe da zumunci kuma, zugar Hajiya da Rahma bata yi tasiri ba kuma dama
bashushe ya ce hassada ga mai rabo taki ce.


Zee ta karɓe shi hannu biyu shi kuma yana girmama ta duk da cewa ya girme ta amma kuma,
tun da dai matar Daddy ce babu wani batun girmansa tun da idan ana dara fitar da uwa ake.

Daddy ya kammala masa komai na tafiya, inda zai tafi China nan da kwana uku, murna
kamar zai yi mai, ashe da rabon ya shiga jirgi. Ana jibi zai tafi ya je Ƙundu ya musu sallama, duk
da a tsaitsaye ya yi saboda bai gama shiri ba, har ya je ya dawo basu haÉ—u da Sheik ba.

Ranar laraba misalin ƙarfe biyu jirgin su ya tashi, Zee da Daddy ne suka raka shi airport yana
ta farinciki saboda shi yana son karatu.
*(A page 15 buk 1 zai ƙare mai buƙatar book 2 zai biya ɗari biyar*

Haka rayuwa ta cigana da tafiya, Rahma tana fantamawar ta, sai samari take yi kala-kala
ƴaƴan masu faɗa a ji, don ita ta ƙi jinin masu ƙaramin ƙarfi ƴaƴan malam shehu. A ɓangaren
Daddy kuwa har yanzu yana ta cin karensa babu babbakaa, domin babu ranar da za ta zo ta
faɗa bai kwana a gidan amarya ba, ita kuma Mummy da yake hotiho ce bata taɓa lura ba,
saboda idan ta je ta hangame baki sai bacci bata taɓa sanin abin yake wakana ba.

Sannan basu da masaniya a kan tafiyar Ma'aruf karatu su duk tunanin su yana can ƙauye,
don Mummy takan ce Ma'aruf ana can ƙauye an kama sana'ar sayar da rake.


Ranar wata juma'a ne Mummy tana kwance bayan ta dawo daga fitsari, bacci bai É—auke ta ba,
sai ta ji kamar alamar hayowa saman benen, shiru ta yi tana son gano cewa ko dai kunnen ta
ne amma sai sai bata kawo komai ba tana dai kasa kunne tana jiran ta bambance, kamar daga
sama haka ta ji, ƙaran buɗewar ƙofar ɗakin Daddy mamaki ne ya yi masauki a kwanyarta,
zaune ta tashi, amma yau kawai sai ta ji tana son sanin mai ya saukar da shi ƙasa, don
zuciyarta ma ta fara wasi-wasi wato shaiɗan ya fara mata biyar ko dai ɓangaren masu aiki yake
zuwa, ba komai ya sa wanann zargin ya ɗarsu a zuciyarta ba sai furucin wata ƙawarta da ta ce
mata ba a gane gaban namiji bare bayansa, haka ta faÉ—a mata bayan ta bata labarin cewa ba
zai msta kishiya ba kuma shi mata ma basu ishe sa kallo ba.

Da sanÉ—a ta sakko duk da tana masa zato mai kyau amma kuma dai tana son idan ta yi abin
da za ta yi É—in ta tarar da shi a kan gaskiya. Abin da ma ya sa ta fara wannan tunanin sai
tunawa da ta yi da wannan ranar ma da kamar wannan lokacin ne ya dawo inda ya ce mata
ƙasa ya sauka ya ji motsi, a nata ganin ai ba kunnen maciji ne da shi ba da za a ce wani
ƙaramin motsi ya je kunnensa.

Jinginuwa ta yi a window tana É—an É—aga labule a zuciyarta tana cewa.

'Idan ka ji ana cewa raka no in yi kashi to tabbas kashin ba gudawa ba ne'

A daidai lokacin da ta É—aga labule Daddy yana dab da shiga É—akinsa, abin da ya É—aure mata
kai kuma shi ne yadda yake wani sanÉ—a yana waige-waige, alamomin rashin gaskiya dai sun
bayyana ƙarara a yanayinsa.

Gabanta ne yake faÉ—uwa, amma haka ta daure tana kallonsa har ya shige É—akin, kuma a duhu
bai kunna fitilar waya ba ko kuma fitilar É—akin. To in har ba babu gaskiya a tare da shi ba mai ya
sa zai yi hakan.

Sai da ta bari ya ɗan jima da shiga sai ta buɗe tata ƙofar ta fito, Daddy da ya shagala da yin
waya da Zee bai ma san Hajiya ta buɗe ƙofa ba don ba ya cikin nutsuwar da zai ji ƙaran ƙofar.
Sai da ta zo za ta buɗe ƙofar ta ji dirin maganarsa sai dai bata ji mai yake cewa ba, mamaki
take da wa za su yi waya a doshin asubar nan.

Ƙofar ta murɗa, Daddy da yake waya ya danne wayar da sauri ta ɗauke, idanu ya rufe
kamar mai baccin ƙarya. Fitilar ta kunna abin mamaki har da munshari yake saki, wanann ne
dalilin da ya sa ya fara jefa masa ayar tambaya a ranta, tana tunanin wane irin sake ne wannan
ta yi a cikin gidanta, sai yanzu ne ma take mamakin yadda Alhajin ba ya ƙulafucin ta zo ɗakin
nasa wanda a da can baya ba sa É—aukan wannan tsawon lokacin ba tare da sun kusanci juna
ba, amma sai yanzu ta lura da ita da babu ma duk É—aya, bata san cewa sabuwar fulawa ya
samu yake ban ruwa ba.

Yadda ya mata bariki ita ma barikin ta masa, gaban gadon ta ƙarasa ta ɗan buga ƙafarsa
tana kiran sunansa, idanu ya buɗe dakyar yana wani ƙanƙance su irin na mai bacci, sai ta ji
wani haushin sa ma tun da ta ga zai munafurce ta.

ÆŠan washe fuska ta yi tana masa murmushi take cewa ya tashi lokacin sallah ya yi, ko kunya
haka ya tashi yana wani murtsuka idanu, duk da ta san ba a ma fara kiran sallar ba, amma dai
dama ta zo ne don ta tababtar da baccin makaho, da a ce yana da gaskiya Daddy da ba zai yi
baccin ƙarya ba, sai dai ta ci alwashin sai ta gano abin da yake sauka yi a ƙasa.
Ɗakin ta ta juya ta koma shi kuma ya shiga banɗaki, yana suuke ajiyar zuciyar kuɓuta don shi
a nashi tunanin ko ta ji yana waya ne, don bai taɓa kawo cewa ta ga shigowarsa ba, bare har ya
yi tunanin ta ji yana waya ya san ma ba zai yiwu ta yi shiru ba.


Bata sauya masa ba ko a fuska bata nuna masa ba, sai dai a ɗauki alƙawarin sai ta ƙurewa
motarsa gudu. Sai da dare ya yi ta hau ƙawar ya kwana a ɗakinta amma firrr ya ƙi yana cewa
shi katifar É—akin ce ba ya so, da ta nuna cewa ko É—akinsa za su je, sai ta ga ya É—an basa da

zancen, ita kuwa bata wani nuna masa ta damu ba ko kuma ta damu, sai kawai ta kwanta a
nata ɗakin ya mata sallama ya fita ya rufo ƙofar. Yadda ta ga rana haka ta ga dare, tana jiran ta
ga abin da zai faru. Har ta fara ganin lafin kanta da kanta cewa ta zargi mijinta kamar daga
sama ta ji an buɗe ƙofar ɗakinsa, bizigir ta miƙw zaune daga kwanciyar da take ba tare da ta
shiryawa hakan ba.

A hankali ta lallaɓo ta zo window sai gashi ya fita, tana nan tsaye ta ji ya buɗe ƙofar falon
ƙasa, shi ma don idanun ta biyu shi ya sa ta ji kuma saboda ta kasa kunne. Gabanta ne ya
tsananta bugu tana jin faÉ—uwar gaba don zuwa yanzu ta tabbatar da cewa wajen Æ´an aiki yake
zuwa, tun da dai babu abin da zai fitar da shi da dare, windown da ake hango harabar gidan ta
zo ta leƙo sai kawai ta hangi Daddy ta cikin hasken farin wata yana ta sauri, kallonsa take
hawaye cike a fuskarta don a halin da take yanzu gani take ko rantsuwa za ta yi cewa biyan
buƙatarsa ce ta wajen ƴan aiki ta fita da shi.

Sai dai akalar tunaninta ya sauya ne a lokacin da ta ga ya nufi ƙofar fita daga gidan ta baya, a
sannan ne ƙirjint a ya shiga bugu da mugun ƙarfi,, ji ta yi hankalinta ya tashi, da sauri ta bar jikin
labulen bayan ta ga fitarsa, a kiÉ—ime ta juyo ta kunna fitilar É—akin, haske ya gauraye ko ina,
ƙaramar lokar jikin madubi ta janyo inda take ajiye mukullai, dakyar ta samu mukullin ƙofar fita
daga bayan gidan, jikinta yana ta ƙyarma, saboda jikinta ya bata akwai wani gagarumin abin da
yake faruwa.

Ko ƙofar ɗakin bata rufe ba, haka ta fito fitilar wayarta a kunne, da matakala bibiyu take sauka
daga saman benen, ƙofar falon ma a buɗe ta bari ko takalmi babu a ƙafarta, ita fatan ta ɗaya shi
ne Allah sa dai ba wai fira yake da wata macen ba, shi ne ba ya zuwa sai dare ya tsala saboda
gudun ɓacin ranta, amma wace mace ce za a ce tana fitowa daga gidansu a wannan daren, sai
dai in mutuniyar banza ce, haka take ta saƙawa har ta zo wajen ƙofar, ganin ƙofar a kulle ,
zargin ta ya zama gaskiya, mukullin ta saka ta buɗe ƙofar sai dai bata da nutsuwar rufe ƙofar,
amma sai ta laɓe ta leƙo, daga can ta hange shi tsaye da alama wani yake jira, tana hango shi
tana jin tsanarsa a ranta, wato su iyalansa suna nan suna bacci shi kuma lokacin ne safiyarsa
ta waye.

Wani machine ne ya tsayar ya hau, suna fara tafiya sai ga wata mata a mota, nan Hajiya ta
tsayar da ita ko tsoro ma bata ji, matar kasancewar ta likita kuma sama da gidan su Mummy
take, ta fito ne za ta je karɓar haihuwar wata mata, haka ta ɗauki Mummy ganin kamar ba a
hayyacinta take ba machine É—in ta nuna mata a kan cewa ta bi bayansu, ganin sai kuka take
tana mata bayanin abin da ya sa ta biyo bayan mijin nata.

Ta tausayawa Mummyn, sun ɗan tsaya daga ɗan nesa ganin machine ɗin ya tsaya a ƙofar
wani gida, Mummy ta mata godiya bayan an buÉ—ewa Daddy ya shige ta fita daga motar ta
ƙarasa a ƙafa. Ganin katangar bata da wani tsayi a ranta ta ce

'In ka ji kana ba za ka iya ba to bai same ka ba ne, ai ni yau sai na ga ƙwal uwar daka' Ta faɗa a
zuciyarta tana komawa daga can bayan gidan ta kama katanga ta É—are, haka ta ti dabara ta dira

amma fargabar abin da za da tarar sai ya sanya bata ji buguwar da mazaunanta suka yi ba.


Tashi ta yi ta yi saurin laɓewa ganin ana hasko fitila, sai da ta dakata mai gadin ne ya zo ya yi
É—an haske haske ya juya bai ganta ba, da alama bai fuskanci cewa gidan aka diro ba.


Ƙofar falon ta lallaɓa ta tura a hankali jin ba a saka mukulli ba zuciyarta tana ta ayyana
mata cewa

"Namiji ba É—an goyo ba ne, tun da ta yarda da mijinta ashe dai saka reshe kama ganye ta yi, sai
dai ta ɗaukarwa kanta alƙawarin za a yi kan mai uwa da wabi, domin ta lura tsugunne bata ƙare
ba amma sai ta nuna musu tun kafin a haifi uwar mai sabulu barbela take da farinta, tun shi
Alhaji ganin hadarin nesa zai sa shi yin wanka da kashi, don ta lura wadatar biki ne tsarki da
romo, tun da har ya iya zuwa wajen wata mace za ta nunawa matar cewa abincin wani gubar
wani ne, don abin nasu aikin banza ne shafa lalle a É—uwawu'

ÆŠan hasken da ka bari a falon wanda yake kawowa yana É—aukewa hasken mai kalar blue,
ganin falon shiru hakan ya bata tabbacin suna sama, saman ta hau tana jin cewa yau duk sai
sun baƙunci lahira, a ɗaki na farko ta fara jin magana ƙasa -ƙasa muryar Zee ta ji tana cewa

"Haba kai kuwa gaskiya yau ka makara baka fito da wuri ba, ka san dai ai bana iya bacci sai da
kai, sai ka je ka tare a gidanka ni ka barni da kewa" Mummy ji ta yi kamar ta fasa ihu, Daddy ta
ji ya ce

"Haba Æ´ar lele ai komai nake hankalina yana kanki, kin sha gaban duk matan duniya ke kaÉ—ai
idanuna yake iya gani da kuma hange, haba amarya mai capacity, amarya kin fi quality, mu
kwanta...

Banko ƙofar da Mummy ta yi shi ya ankarar da su juyo, zumɓur Zee ta miƙe daga cinyar
Daddy, a take idanun Mummy suka sauka a kan cikin wata huÉ—u na Zee wanda ya yi kufkuf a
jikinta kamar ƙaramar ƙwarya...


*BOOK 1 free shiga grp na BOOK 2 500, cmplt doc 800*
*Acc no faiza abubakar 9030283375 opya shaidar biya 09025576222 gobe za mu gama book
1*

*Yau ba samu leƙo inna amarya ba da kuma ango Sheik mai breast*
😂😂😂😂😂😂

*Sai gobe in muna raye*

MAMAN AFRAH

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login