Showing 15001 words to 18000 words out of 63190 words
ba, hannu ya kai ya fisge towel ɗinsa na wajen Liman, Liman da dama bai riƙe towel
ba kasancewae hannuwansa suna matse a matse matsinsa, sai ji ya yi an buɗe masa kansa,
hakan ya sa ya ƙara runtse ido haɗe da bada ƙaimi wajen ƙara danna hannuwansa don ganin
ba a yi kaciyar nan da shi ba, har lokacin yana faɗin
"Attakabir" Da sauri Sheik ya ɗaura towel ɗin ya ɗan muskuta ya koma kan sallayar da take
shimfiɗe, tare da miƙa hannu ya ɗakko hirami a jakarsa yana gyra zaman hularsa da gemunsa,
sai da ya zauna yana kallon gabas , ya rufa hiramin yana ta cigaba da a'uxiyya.
Dakyar ya samu nasarar warto suratul fatiha a bakinsa, ya shiga karantowa, sai da ya yi sau
uku, sannan yana zaunen ba tare da ya juyo ba ya ce
"Alhamdulillahi, na samu nasarar korar fatalwa, komai ya dawo daidai" Ya faɗa cikin muryarsa
ta balarabe. A hankali suka fara tashi zaune kowa yana ɗan ƙyallara ido, ganin babu fatalwa a
ɗaki, sannan Sheik yana kan sallaya ya rufa hirami sai suka fara hamdala Mai Gari faɗi yake
"Allah mun gode maka da ka kawo mana babban malamin larabawa da yau ya za mu yi?" Ya
faɗa yana kallon gwiwar ƙafarsa, da ta jiƙe, shi kuma Sheik bai ma san inda gudawarsa ta yi ba
domin yanzu ba ya ma ji.
Malam Lima cewa yake
"Ai ba ƙaramar sa'a muka yi ba" Ya faɗa yana ɗan satar kallon wandonsa da ya jiƙe ya ce
"Wannan yara an yi yaran banza, yanzu a cikin ku aka samu wani marar imanin ya zage wando
ya mini fitsari a jikina?" Ya faɗa yana kallon samarin nan da suke sharkaf da gumi. Ɗaya ya
buɗe baki zai yi magana Mai Gari ya yi saurin cewa
"Kai ba a son wani tone-tone ku bashi haƙuri" Haka suka bashi haƙuri ba don son so ba, sai don
ba yadda za su yi kuma dai ga wandonsa ya fi nasu jiƙewa tun da shi ya yi fitsarin su dai kawai
sun shiga lemar ne.
Liman daɗi ya ji a ransa ganin girmansa bai zube ba. Nan suka kalli Sheik da ya juyo daga
kallon gabas yana gyara zaman towel ɗin da hiraminsa, gumin da yake yi tamkar ya dawo daga
filin tsere.
Mai Gari yana kallonsa ya ce
"Sannu Ya Sheik lallai ka yi artabu" Sheik a zuciyarsa ya ce
'Artabun yau ka gani, da ka ga na jiya da na sha da ina ga wano zancen ake ba wannan ba'
Amma a fili sai ya ce
"Kai wannan ai ƙaramin abu ne, ai ina tabbatar muku kuna zuwa cikin gari za ku ga aljannu sun
lafa komai ya daidaita" Da mamaki suke kallonsa jin yana batun cikin gari, Malam Liman ne ya
ce
"Cikin gari babu lafiya ne dama?" Shiru Sheik ya yi yana tambayar kansa a zuciyarsa cewa
'To da uban me ya taho da ku da gudu idan ba tashin hankali kuka baro a cikin garin ba?' A fili
ya ce
"Dama cikin garin lafiya, na ɗauka ai babu lafiya da na ga kun shigo gidan nan a kuɗime" Mai
Gari ya ce
"A'a gari lafiya ƙalaw dama zuwa muka yi, mu ga ko lafiya mun zo da asuba kiranka a yi sallah
amma aka gaji da bugawa shiru, to shi ne muka samo samarin nan muka ce su ɓalle ƙofar a
duba lafiyarka, da aka tura ƙofa kuma sai muka hango ka taho a guje da takalmi ɗaya a ƙafa jiki
duk kumfa, wannan dalilin ne ya sa mu ma muka ga tun da har kana gudu to akwai gagarumar
matsala gwara mu bika mu tsira ka ji dalili amma gari kowa yama sabgar gabansa lafiya" Wata
ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, yana jin wani mugun haushin su, da suka firgita shi, shi a
nashi tunanin garin ne a ruɗe suka taho ashe dai shi ya ruɗa su.
Cike da ƙarfin gwiwa ya sheƙo wata sheƙeƙiyar ƙarya don kar a ga gazawarsa ya ce
"Ai nake faɗa musu ina cikin banɗaki ina wanka, nan na ga wani aljani mai ƙaho bakwai ya
tsaga bango ya fito, yana fitowa ta sheƙe da dariya yana cewa, wai yanzun nan za su saki
manyan aljannun da za su rikita gari, kai har cewa ya yi mai gari ma ɗauke shi, za su yi,
wannan dalilin ne ya sa ina nuna shi da yatsa wani hayaƙi ya tashi da shi sama, ya bi iska ya
ɓace, to ni kuma tuno halin da garin zai kasance shi ne na fito hankali a tashe domin na kai
muku ɗauki cikin gari, ganinku a guje kun shigo ya ƙara sanya hankalina ya tashi, saboda bana
son jama'a su shiga damuwa, sai yanzu bayan na gama addu'ar nan na gano ashe dai aljanin
nan ne ya shiga jikina ya haifar da tsuma da ruɗu da tsoro, don kar in taimaka muku, shi ne fa
muke rige-rige tsakanin ni da ku wajen samun maɓoya" Ya faɗa yana dafe goshi alamar
damuwa.
Mai Gari har da ƙwallar farin ciki ganin ba ƙaramar ƙauna Sheik yake yi wa garin nasu na
Ƙundu ba, sannan ba ƙaramin taimakon su yake yi ba, bai san cewa Sheik kasuwanci ya zo yi a
garin nasu ba, don ba a aikin banza a ko ina.
Cike da girmamawa ya ce
"Allah saka da alkairi Malam ashe kana ta fafutuka ne a kan garinmu, silar haka har aljani ya
shiga jikinka ya saka muke tsere, bawan Allah dama na yi mamakin ganin muna ta neman
mafaka tare da kai ashe dai ba da kai muke nema ba, da aljani ne" Ya faɗa yana kallon Sheik.
Liman ya ce "Ai ni na yi mamaki dama, malamai ai magada annabawa ne" Sheik ya ce
"Ina ai ƙaryar aljani in ji tsoronsa, su kansu sun sanni" Ya faɗa amma yana ɗan rage murya
saboda tuno kunnen jaririn da aka jefo a banɗaki.
Liman ya ce
"Allah mai baiwa, ku dai Allah ya baku" Sheik aka wani gyara zama gudun kar towel ya kunce
ya ce
"Ai aljanin ya yi niyyar hanani yin addu'a ma lokacin da fatalwa ma ta shigo hatta bakina sai da
suka so riƙe mini, yanzu ma sai da na sha fama na hau sallayar nan, so suka yi kar in yi addu'a"
Gabaɗaya suka ce
"Allah ya fi su"
Nan dai aka sa samarin nan su fita da katifa su gyara ɗakin, a nan ne ma Mai Gari ya ƙarewa
Sheik kallo ganin idanunsa luhu-luhu alamar ko dai kuka ko rashin bacci ya ce
"Ya Sheik ka ga idanunka kuwa, hatta fuskarka a kumbure take" Sheik tuno artabun da suka
sha jiya da jarirai da aljannu har ya hau bishiyar kuka, sai ya ɗan yi gyaran murya ya ce
"Haba Mai Gari wanann tambayar ma ai ɓata baki ake yi, ni da na zo taimako ina ni ina bacci, ai
ni nan da na gama cin abinci kawai alwala na yi na hau sallaya, nake salloli ina addu'a ban tashi
ba sai da aka fara kiran assalatu, shi ne na sake alwala na yi shirin fita masallaci, sai kuma na
tuna ku ne za ku zo mu tafi tare, to dai ni ban ji zuwanku da asubar bama don ni nan na yi
sallah da nafiloli, wataƙila aljannu sun saka mini auduga ne a kunne shi ya sa ban ji bugun naku
ba" Ya faɗa yana kai hannu ya share zufa a goshin sa.
Sosai suka jinjina masa, daga nan suka ce za su je a kawo masa abin kari, nan ya ce wainar
ƙwai da dafaffan ƙwai sai a biredi da shayi me kauri. Mai Gari sai da gabansa ya faɗi, jin
abubuwan da ya zana, sai dai har da wasu sunayen abubuwan larabci da shi kansa Sheik bai
san mene ne ba, ya zayyana sai da Mai Garin ya ce vasu san abubuwan ba sannan Sheik ya
ce a barsu dama abincin su ne na ƙasar larabawa.
Bayan samarin sun gama gyaran suka tafi da su Mai Gari. Lokacin ya saka jallabiya, ya ce zai
yi wanka, suna tafiya ya gabansa yana faɗuwa, amma haka ya je ya garƙama sakata ya ɗauki
ruwa ya tuɓi ya yi wanka a tsakar gidan, don ba zai iya komawa banɗakin a lokacin ba. Yana
gamawa ya buɗe ƙofar gidan saboda masu kawo abincin don an ce masa mutane za su fara
zuwa neman magani yanzu gidan zai cika maƙil in ya gama cin abinci.
Juyowar da zai yi ya yi arangama da wani ƙaton hanci yashe a tsakar gidan, amma girman
hancin ya yi kan mutum da gudu Sheik ya doshi ɗaki towel a hannu don da ya kunce gani ya yi
bashi ma da nutsuwar tsayawa ya ɗaura.
Yana shiga ɗakin ya banke ya jingina da jikin ƙofar yana mayar da numfashi, a fili ya ce
"Ko a ni ko a ku aljannun garin nan, wato kun ga ana girmamani hassada da tsana suke
damunku, yadda zan ke shan ganimar girki, da kuɗaɗen magani ana biyana yasin babu inda
zan gudu, ba hanci da kunne ba kai ko karo zan ke ci da mafitsara kuna jefowa aradu sai dai na
gudu ɗaki amma dai arziƙi sai na dagwala a garin Ƙundu" Ya faɗa yana ƙarasawa ya zauna, ya
shiga shafa mayukansa, sai da ya gama tsaf a saka kayansa ya samu turarukansa masu
ƙamshi ya shafa saboda su kashe warin mayukan bilicin yake yawan amfani da turaruka.
Yana gamawa ya kabbara sallah, sai lokacin ne ya yi sallar asuba, a lokacin kuma Audu yake
rafka sallama, gyaran murya ya yi, sai da ya sallame sanann ya amsa, amma da ya leƙo bai ga
hancin nan ba, haka ya buɗewa Audu ɗakin ya ajiye masa kayan abincin bayan ya gaishe da
shi, ya nuna masa kwanukan jiya ya ɗauka, har ya jiya zai tafi Sheik ya ce
"Mu manyan malamai ba a gutsure mana cinyar kaza ko wani sashe na jikinta, yadda aka ba
mutum saƙo ya ji tsoron Allah ya kawo daidai" Da rashin fahimta Audu ya kalle shi amma sai ya
ce
"Malam ban gane ba"
Sheik ya ce
"Jiya kazar nan da ka kawo bata da cinya ɗaya" Mamaki ne ya kashe Audu jin wai shi da aka
bashi abu har lissafawa ya yi, hakan ya sa ya ce
"Wallahi ni ban ɗauka ba, sai dai ko a gidan Mai Garin ne da aka dafa suka ɗauka suka rabawa
yara" Maganar Audu ta nunawa Sheik asalin gaskiya ya faɗa masa, don haka sai yayarda ya ce
ya tafi.
Tun da ya buɗe kwanukan ƙamshin wainar ƙwai ya cika ɗaki, ya cinye tass ya sha shayin
bayan ya saki gatsa ya ce
"Bari in yi shiri na san yanzun nan masu buƙatar magani za su fara zuwa, ni ko buhun hatsi ma
zan ce Mai Gari ya bayar a kawo min? Saboda in ke zuba kuɗin sadakar magungunan da zan
ke bayarwa" Ya faɗa a fili yana ciro hular kansa ya shiga taje ta da brush kumb ta kwanta sosai
ya ɗauko wani mai me sheƙi ya shafa a take ta shiga walwali. Ajiyewa ya yi a gefe ya buɗe inda
kuɗinsa yake ragowar kuɗin saniya, ya shiga ƙirgawa, yana cikin hakan sai ya ji tashi hayaniya
an shigo gidan, sai ya ji ana masa wani kira kamar na ƴan farauta ana cewa
"Sheik ka fito gari babu lafiya, aljannun mai farfaɗiya sun tashi, ƙartai goma aka tara suka riƙe ta
amma ta watsar da su" Gaban Sheik ne ya harba da ƙarfi wai me farfaɗiya, kuma ƙartai goma ta
watsar kenan yanzu shi kuma in zai mata maganin ya zai yi?.
Bai yi magana ba kuma dama ɗakin nasa a rufe, sai ya ji wani ya shigo yana cewa
"Innalillahi wallahi matar nan mai farfaɗiya ta ɗaga Mai Gari da hannu ɗaya hannunta na dama,
hannun hagun ɗin ta ɗaga Malam Liman, Sheik ka fito da gaggawa ,a ta hau saman kukar
bulukiya da su" Gabaɗaya idanun Sheik sun ciko da ƙwalla, hankalinsa ya tashi gabansa ya hau
dukan uku-uku. Dakyar ya yi ƙarfin halin faɗin
"Ya subhanallahi, mai farfaɗiya a yi haka kuma, ki ɗaga Mai Gari da Malam Liman, jama'a gani
nan zuwa" Ya faɗa yana zufa, sai dai abin da ya bashi mamaki wanann hular tasa wacce ita ce
rufin asirinsa, wacce ya cire ya taje gashin ya ajiye a gefe yana lissafin kuɗi, babu ita babu
dalilinta, wato hula dai mai gashi da gemo da saje ta yi ƙafa don bai ganta ba.
Hankali a tashe ya kai hannunsa biyu saman kansa yana shafo tsakiyar kansa zuwa fuskarsa,
hankali tashe, jin ya shafo ƙwal kwabon kansa da kuma fuskarsa da babu saje babu gemu lallai
yau akwai cakwakiya, ya ake so ya yi wajen fita zuwa ruƙiyyar.
Wani ƙaramin mudubi ya ɗakko a jakarsa ya duba fuskarsa yana ganin tabbas idan ya kuskura
aka ganshi a haka ya kaɗe har ganyensa, don za a gano ba balarabe ba ne.
Wani mai ƙarfin hali ne ya takarkare ya ce
"Sheik ka fito su Liman rai a hannun Allah, tana hawa kukar nan ɓacewa za ta yi, don idan
aljannu suka ɗauke ta sai ta yi wata biyu ma ba a ganta ba" Ya faɗa a ruɗe ganin Sheik bai fito
ba.
Wannan furucin ya sake sanya shi diriricewa yana ƙara shafa sallallan kansa ya ce
"Gani nan zuwa ai ƙaryarta ta sha ƙarya"
*Mu haɗu a gaba don jin ya SHEIK zai yi wajen fitowa babu hula, shin ina hular tashi? Ko
dai aljannun ne suka saci don su ga ƙarshen ƙarya?*
Yanzu muka fara ku dai ku biyo ni don jin ya za ta kaya✍️
MAMAN AFRAH
09025576222
*Dan Allah masoya ina neman alfarmar addu,arku gareni da bakunanku masu albarka, Allah
kaɗai ya san bakin wani, ina nema domin Allah ko a zuciya ne ki mini addu'a NGD sosai ana
tare*
[7/4, 4:00 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/EBurrU2vz6OFGbE37xLhPS
♂️ *MALAMIN BOGI*♂️
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.
Daga marubuciyar:
Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*
BOOK1️⃣
PAGE 5
*ƘAUYEN MAI MANGWARO*
A fadar Mai Gari dakyar aka dakatar da Jummau daga kukan da take tana ta faɗar cewa yau
sai an biya ta saniyar marayu. Ita ma Lami tana faɗin sai Jummai ta biya ta kuɗin adashen ta,
tun da ita ma saniyar ba ita ta siyar ba don haka sai dai ta biya ta kuɗinta in ya so idan Ibra ya
kawo kuɗin sai ya bata, sai dai Mai Gari ya tsawar musu sannan suka yi shiru.
Isowar Kakar Ibra Inna Tasallah fadar Mai Garin na Mai Mangwaro tana sakin ɗan kuka tana
face hanci shi ya dakatar da kowa aka ɗago ana zuba mata na mujiya, wuri ta samu ta zauna
har lokacin tana ɗan matse hawaye ita takaicin ta ɗaya jarin kayan miyar nan idan ta bayar ina
za ta samu?
Mai Gari ne ya yi gyaran murya ya fara magana kamar haka yana mai cewa
"Tasallah shin kin san kiran da na aika aka miki?" A maimakon ta bashi amsa sai ta ƙara gudub
kukan nata, kasaƙe ya yi yana kallon ta, sai da ta ɗan tsagaita kukan ta ce
"Yo na sani mana Mai Gari, ai Idrisu da ya je ya kwashe komai ya faɗa mini, to zuwa wajenka
kuwa ai ya zame mini farillah tusa a masallaci, in da sabo na saba a kawo ni ƙara wajenka, yau
a ce Ibra ya cinyewa yarinya me tallah ƙosai, gobe a ce ya warci sandar rake a dandali, har ta
kai ya fara kame kajin mutane yana yankewa ya cinye, yau kuma saniya sukutum ya gudu da
ita wallahi albasa bata yi halin ruwa ba"Ta faɗa tana rungume robar kayab miyar ta tamkar wani
ya ce zai ƙwace.
Jummai ce ta yi tsoma baki ta ce
"Wallahi in har ya saba cin ƙasa ya kiyayi ta shuri, in har tun yana ƙarami yana wartar kayan
jama,a ana ƙyalewa kawo samartakarsa, to yau ya taɓo gidan rina don ko sama da ƙasa za su
haɗe sai kin biyani saniyata" Haɓa Inna ta dafe ta ce
"Haba Jummai