Showing 1 words to 3000 words out of 65850 words

Chapter 1 - KALUBALENAH (complete) Writing By Chuchujay.pdf

Advertisement

02 Aug 2025

2662

KALUBALENAH

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

1
A zabure ta miƙe sakamakon sassanyan ruwan da taji saukarsa a jikinta ,
Salati tasaka tana kallan wadda ta jikata da ruwan tace "amma dai salima kina ganin  yanayin
sanyin garinnan kika zo kika watsa mun ruwan nan mai shegen sanyi da asubar farin nan maye
laipi idan kikazo kikace deenah ki tashi asuba tayi?
Jifa da kofin ruwan salima tayi jin muryar mahaifiyarta tace cikin ƙaraji da mamaki"yanzu
deenatu fitsarin kwance kikayi wa ladi akan katifa ,
Ince saida tamiki gargaɗi jiya da dare?
Ladi shigo kiga kaniyar da deenatu ta maki,
Kamar guguwa haka ladi ta shigo tana fadin "kan ta balain nan fitsari fa?
"Aradu zo ki duba shine dai ta miki gandar gandar da ita"

Kasa magana deenah tayi sakamakon dukan da ladi ta rufeta dashi tana zazzaginta ta uwa ta
uba,
Sai da tayi mata lis lis kafun ta jata ki ta watsar a kofar dakin mahaifiyarta tana mai fadin"
Fito fito zainaba,fito kiga abunda shegiyar yarinyar da kike ikirari taki tamun ,to wallahi daga yau
ta daina kwana dakin su salima sai dai kuyi mata guri tsakaninku keda kabiru tana kwana
tsakiyarku,
Zainaba mahaifiyar deenah itace ta fara fitowa jin kwarajin ladi kafun mijinta da already dama ya
tashi yana shirin fita masallaci ya mara mata baya kafaɗarsa dauke da sallaya,
Kallan banza basu ishe shi ba ya raɓa ta gefen su ya wuce ,
Tsaye zainaba tayi zuciyarta na kuna ganin yarda deenah ke kuka a tsugunne a kasa ,
Bata dai cewa ladi komai ba har ta gama balain ta har tana ce mata barauniyar miji ,
Barinta gurin keda wuya zainaba ta kalli deena tace sai ki tashi ai ko ki shiga ki sake kaya kizo
ki yi sallah kiyi shirin makaranta kuma,
Wani kukan mai cin rai deenah ta sake fashewa da tace "wallahi tallahi mami banyi fitsari ba
salima ce fa kawai ina bacci tazo ta sheka mun ruwan sanyi a jikina shine tana jin muryar baba
ladi fa tace wai fitsari na mata ,
Rabiatu dake labe kanwar salima ce ta fito tace wallahi hakane mamin deenah batayi fitsari ba
jiƙata ne wallahi ya salima tayi ,
Dan murmushi mamin deenah tayi tace "toh ai ba komai duk wanda yayi nagari dan kansa ,

Kamo deenah tayi wadda har lokacin bata daina kuka ba tace tashi muje kisake wadannan
jiƙaƙƙun kayan kizo kiyi alwala.
Kullum haka rayuwar gidan take kasancewa ,babu wanda ake chima kashi aka kamar deenah
da zainaba ,ba daga mutanen gidan ba har ma da me gidan nata ,
Gidansu deenah gidane na zuria mai yawa irin gidannanne da mutane ke ma laƙabi da gidan
gargajiya .
Duk fadin unguwar mai suna "kan tudu dake cikin garin nasarawa babu lungun da ba'asan

gidan Marna ba kasan cewar gidane irin na gado wanda anyisa ne tun kaka da kakanni.

Marigayi othman ali mahaifi ne ga deenah wanda harkata neman kudi ta fita dashi cikin garin
nasarawa inda a nan ne ya hadu da wata diyar attajirin mai kudi a lokacin da ta kawo masa
saka iskan taya wanda dama sana'ar sa kenan,
wasa ta maida gurin wajen zuwanta dan othman ya shiga ranta.
Ita ta fara nuna tana sansa ,tun yana zizzillewa ganin tafisa ta ko ina har yazo ya mika wuya
dan babu ma yarda za'ayi mace kamar MAIMUNA ta kawo maka tayin soyayyarta Kayi watsi da
ita.
Lokacin da mahaifinta ya nemesa da yazo ya gansa ya razana sosai musamman da ya fara
shiga tamfatsetsen gurin da suke kira gida ,
Yanayin yarda iyayenta suka Karbesa shine abunda ya kara darsa masa soyayyarta dan sun
karbesa ne hannu biyu biyu babu ƙyara babu Nuna shi din kaskantacce ne a gabansu,
Jagora suka nema da yayi musu zuwa ga iyayensa ,
Bai musu ba duk da yasan mahaifinsa malam Ali marna mutum ne mai mugun zafin rai da
kafiyar tsiya ,
Lokacin da magabatan maimuna sukaje ma malam ali da yan uwansa na gidan marna da
maganar auren ba karamu tirja akayi ba dan su a cewarsu sun riga da sun masa mata zainaba
wanda yar uwarsa ce kuma marainiyar Allah dan haka bazasu yi naam da wannan auren ba,
Da ƙyar dai da sudin goshi suma suka nace kasancewar yarsu ta nuna tana sansa kuma babu
abunda take nema agurin iyayenta ta rasa dan haka baza a fara akan othman ba,

Sharadai iyayen othman suka kafa masu inda sukace lallai sai dai a daura masa aure da ita
maimunan da kuma zainaba a rana daya kuma nan gidan a nan maimuna zata zauna tare dasu
basu yarda ya fita da ita ba,
Da fari iyayenta basu yarda ba amma ganin yarda maimuna ta kafe yasa mahaifinta yace yaji ta
aminta amma sai ya gyara mata inda zata zauna,
Basu musa ba sukayi na'am inda aka gyara bangaren da sukace nan ne na othman din,basu
ware ba har inda zainaba zata zauna,

An Daura auren zainaba ,maimuna da othman wanda suke zama irin na aminci dan ko kadan
maimuna bata nunawa zainaba wani abu a matsayinta na uwar gidansa ,itama zainaba din
ganin alherin maimuna yasa ta kwantar da hankalinta duk da kuwa yarda take kishin othman
wanda daidai gwargwado yana kwatanta adalci duk da kuwa maimuna ce mafi soyuwa a
gareshi.

Kasancewar maimuna yar hutu wadda bata saba wahala ba yasa take balain shan wahalar
rayuwar gidan,
Da gayya kishiyoyin surukuwarta wadda bata raye da matan yan uwan othman su ladi ke bata
kashin wahala musamman gurin surfe da chasa dawa da gero,
Wahala babu irin wadda maimuna bata sha ba hannunsu ,duk lokacin da othman yakai
maganar gaban manyansu sai su haushi da faɗa akan yana nuna banbanci tsakanin matan
nasa biyu ,

Meye laipi idan ana nuna wa lalatacciyar matarsa da batasan zaman gidan aure ba aikin da ya
wajabta "acewarsu "

sau sa dama zainaba kan fito dan shigar mata amma sai su haye mata akan bata da zuciya
dama ai"
Kasancewarta mace mara hayaniya sai dai kawai tayi shiru ta kama ma maimuna tana mai bata
hakuri,.

A shekara da ta zagayo da aurensu maimuna ta haifo yarinyarta mai kyau mace wadda Allah ne
kawai ya rayata dan da cikinta ma bakaramun wahalar su ladi tasha ba dan akwai lokacin da
har tabarya ladi ta buga mata akan ciki dan kawai tasata aiki tace mata bazata iya ba dan tayi
nauyi sosai, A washe garin ranar da ta haihu suka nemeta suka rasa ,
Neman duniya othman yayi mata ,tashin hankali sun shiga sosai amma babu maimuna babu
alamunta ,
Mahaifinta yayi kuka yayi kuka na rashin maimunatu dan da ace kudi zasu dawo da ita to da
tuni ta dade da dawowa amma shiru ko da mai labarinta bai samu ba.

Zainaba ce ta cigaba da rainon yarinyar da ta ci suna Deenah dan tunda ta auri othman ko ɓari
bata tabayi ba,
Har ranta take jin soyayyar deenah kamar ɗiyar da ta haifa a cikinta,

Wasa wasa Othman ya Fara jinya wadda aka kasa gane gabanta da bayanta ,
Anyi maganin anyi amma abu yaki ci yaki cinyewa ,babu abunda yake ambata sai maimuna
diyarsa da matarsa zainaba,a kullum ka zauna dashi,
Jadadawa ɗan uwansa amanarsu yake yana faɗin kabiru idan bani ka rike mun amanar iyalina,
Jinyar wata biyu yayi Allah yayi masa cikawa.
Haka zainaba ta cigaba da rainon deenah duk da batajin daɗin yarda ake kyararta akan yar
amma haka ta danne ta kudiri niyyar babu ruwa ko iskan da zaisa ta bar deenah ta wulakanta .
Lokaci guda zainaba na zaune cikin gidan kabiru ya fito akan yana san aurenta tunda dama shi
kanin sa ya bawa amanarta ,
Na'am iyayensu sukayi da abun duk da bata so amma kasan cewarta mace mai kawaici sai ta
amince,
Balai gurin matansa ladi da talatu ba'a sa masa rana kar ma ace ladi wadda itane uwar gidansa,
Wahala babu wadda bata sha ba gurin su ita da deenah ,ko ina babu dadi baga kakannin ba
baga matan kabiru ba baga shi kansa kabirun ba dan bata taba sanin mugun mutumin banza
bane sai da ta auresa.

Zaman gidan take amma zama kawai na hakuri shima saboda deenah ,
Gaba daya dukiyar othman sunyi bankan bankan akai ga wata tsana da suke wa deena wadda
ta faro asaline daga mahaifiyarta .

iyayen maimuna sunsha bin didigi akan ɗiyar maimuna amma karshe malam ali yace musu ai

Wannan ƴa babu ita kuma ya ja kunnen kowa akan baya san kuma yaji wata magana daban
musamman daga bakin zainaba wadda itama tsoro ya hanata magana ,
daga bisani ta tsinci labarin barinsu garin dan an shaida wa mahaifin maimuna an ganta a
jalingo wanda hakan yasa sukayi balaguro da sa ran ganinta a garin.

CHUCHUJAY
KALUBALENAH

2
SADAUKARWA GA MARYAM SHEHU GANA.

Tunda deenah take rayuwarta shekara goma sha biyu kenan bata taba sanin ba zainaba ce ta
haifeta ba duk da kuwa yarda mutanen gidan kan zageta da hakan amma bata daukan hakan
da komai amma bangaren kabiru kuwa ta san bashine mahaifinta ba tunda ko a makaranta ba
sunansu iri ɗaya da su salima ba sannan sau da dama yakan zageta da othman yabar masa
gadonta na tsiya amma bayan ita babu tsiyar da ya barmasa duk da kuwa da wadataccen
dukiyar da ya barwa iyalansa suka danne.
Tsugunne deenah take tana shan dan kokon da aka kawo musu da gari yawaye bayan sun
dawo daga makarantar asuba ,zainaba ce ta fito daga ɗakinta falan ɗaya da yanzu ta dawo
bayan aurenta da kabiru ɗan yanzu bangarensu na da ya zama na hutawarsa.
Kallanta zainaba ta tsaya yi cikeda tausayinta ,
Tanasan bawa deenah rayuwa mai kyau amma itama bata da wani gata kuma bata da karfi ,
Mahaifinta da mahaifan su othman yayan mace da na namijine,
Gaba ɗaya rayuwarta gidanta tashi sabida ita ko iyayenta bata riska da rai ba,
Sauda dama idan tayi kokarin daukar deenah su gudu a gidan sai tafara tunanin idan ta
dauketa sun gudu ɗin ina zasu?
Zama tayi kusa da ita tace deenahn mami maisa kike shan abu a tsugunne bayan nasha faɗa
maki hakan bashi da kyau,
zama Deenah tayi tace "wallahi mami sauri nake ne na tafi makarantar gidan gona kar yauma
malam ilu ya mun bulalar latti,
Wallahi yana bani haushi mami ni bansan mai yasa kowa baya sona ba ,duk gidan nan ke kadai
ne kike sona haka makaranta ma bani da kawaye fa dukkansu kawayen salima ne ,idan wata ta
kulani sai su salima su hadu a lungun tsalha su maka duka ,
Haka Malam Ilu ɗinnan wai saurayin salima ne shine take sawa ya zaneni shima ya tsaneni,
Mami kijifa yar salima ɗinnan da duka wata biyar ne ta bani ,
Kallanta zainaba tayi tana mai ɗan murmishi tace ,"deenah na kina wannan zubar ai zakiyi wani
lattin da shi malam ilu ɗin zai zaneki sannan dama ai ba kawaye kikaje makaranta ba karatu
kikaje ,ko bakiga kinfi ita salima ɗin kokari ba ai saboda ke ba kawaye kikaje makaranta ba dan
haka ba ruwanki da wasu kawaye , Sannan duk wanda kika ga dama baya kulaki Allah bai tsarasa cikin rayuwarki ba kuma bashida
amfani,
Sannan kar na kuma jin kince kowa baya sanki ,ni maminki ina sanki kuma sona ya ɗara na
kowa a duniya indai kina da soyayyar mahifiyarki to ta kowa banza ce.

Washe hakora deenah tayi tace "wallahi mami ina sanki sosai ,Allah ya bani kudi,so nake nayi
karatu sosai nazama likita na siya miki katon gida na dauke ki daga gidan marna,
Dadine yacika zainaba dan a kullum idan deenah na fadan irin haka sai ta tsinci kanta cikin jin
dadi da wata soyayyarta da take ratsata dan ita har mantawa take ba ita tayi nakudar deenah
ba,
Rabiatu ce ta karaso gurin da sarsarfa tana faɗin ya deenah kizo mutafi gidan gona mun kusa
lattifa,
Jakarta ta dauka tana mai aje kofin kokon tana cewa"mami sai na dawo".

Kamar yarda deenah ta guda suna zuwa kofar shiga makaranta gwamnatin dake cikin garin na
kan tudu malam ilu yana kwafe a bakin gate din shiga hannunsa da doguwar bulalar bedi,
Suna zuwa bakin gate din yace "uwar yan latti anzo kenan maza zo ki dage mun wandanki na
zane wadannan kafafun masu kama da tsinsiya,
Kuka ta fara tun kan ya fara dukanta amma duk da haka ko kadan bai ji tausanta ba ya zane
kafafunta inda rabiatu ke gefe tana ta challara kuka kamar ita yake duka ,saida ya zane mata
kafafu tas kafun yace su shige.
Haka ranar ta gama jinyar kafafu wanda salima da kawayenta sukayi ta tsokanarta a
makaranta.

Suna zaune kan tabarma zainaba na shafa mata man zafi a inda take fadin yana mata ciwo
kabiru ya shigo ,
Fancham fancham ya karaso gurin yayi fatali da kwanon da zainaba ta aje mata dan waken da
ta siyo mata kafun ta dawo daga makaranta,
A tare suka tashi sakamakon ɓata sun da yayi,
Zainaba ce tayi karfin hali wajen faɗin Alhaji lapia kuwa,?
Kamar jira yake ya fara kumfar baki yana faɗin"ban sani ba ,ban sani ba nace miki zainaba ,ko
zaki dake ni ne eye?
To wallahi ni nagaji da daukar nauyin wannan shegiyar yarinyar ,ko ku fito da miji ayi mata aure
ko kuma na kaita gidan marayu ,
Ina dalili yarinya kullum a cikin neman mun magana take ,nan nan yanzu ladi ke kawo mun
kararta akan tana zuwa lungun gidan almajirai ɗakin samarin nan to wallahi da ta dauko mun
abun magana gwanda nayi maganin abu''
Cikin kuka deenah tace"wallahi baba karya ake mun wallahi tallahi ni layin lungun almajirai ma
bana bi ko aikena akayi kuma nasan salimace zata faɗawa baba ladi haka walllahi na rantse da
Allah baba karya take ,
Kamar jira yake yayi kanta yana cewa au matar tawa kike cewa tana karya dan uwarki gayyar
tsiya ?
To Bari na fasa maki baki sai uwarki da ta gudu ta barki tasa babanta mai kudi ya ɗaureni
shegiya gayyar tsiya,
Gabansa zainaba ta shiga ranta a mutukar bace tace wallahi baka isa ka daketa ba yau kabiru
sai dai kabi ta kaina idan har zaka daketa,

Tsaye yayi yana mai kama kugu yace kabiru?

Ni kike faɗawa kabiru ko zainaba ?
To ko mijinki baya cemun kabiru gatsetse sai ya sakaya,amma yau zaki gane ni ba sa'an
wasanki bane,
Kafun tace me ya fara kai mata hannu ,
Kuka deenah take a bayansa tana basa hakuri ganin yarda yake naɗar zainaba amma hakan
bai sa ya bari ba ,
Wasa wasa saida yayi mata ligif sannan yace ta tattara ta bar masa gidansa ya sake ta Saki
biyu dama ta ishesa.
Duk wannan bidirin da ake babu wanda ya fito a cikin gidan dan kawo mata dauki ko basa
hakuri duk da kuwa sunajin duk wani abu dake faruwa .
Barin gidan yayi bayan ya lillisata yace kafun ya dawo kuma ta tabbata tabar gidan,
Kallan deenah tayi wadda kukanta yaki yankewa yace "kukan kuma wai na menene haka ?
Ba komai ya wuce ba ,
Share hawayenki yanzunnan ,zan ɗaukeki muje gurin da kowa zai soki ,gurin da babu wanda ya
san mu ma bare ya tsangwamemu,
Cikin rashin fahimta tace "yanzu mami kina nufin kowa da kowa zamu bari danginmu muyi nisa
sosai da su?
Ni dai mami duk da basu sona amma kar mu gudu nan ne gidan mu idan mun gudu su baffa
baza suji dadi ba,
Kallanta zainaba tayi tana mai maida hawaye dake neman kwace mata ,
Tasani Allah ya azurta deenah da zuciya mai kyau duk da ita din yarinyane amma duk da haka
bata jin kin yan uwanta ,
Sauda dama takan mata korafi na rashin santa da basuyi amma yau gashi tana fada mata zata
dauketa su gudu amma tunanin ta na kan danginta.
Tana tsaka da wannan tunanin taji hayaniya na dosu sashen su,
Jan deenah cikin ɗakin tayi ta kulle kofa dan tasan wata tsiyar ce ke dososu ,
Kamar yarda tayi tsammani kuwa matan gidan ne da wasu daga cikin mazan dake gida ciki
kuwa harda mahaifin othman da kabiru wanda muryarsa tafi ta kowa tashi yana mai
faɗin,"wallahi baffa wannan matar ni kaina mamaki naji da na shigo wai da tsakar ranar nan ta
kawo mun kwarto shiyasa nikuma baffa na kasa dannewa na saketa sai kuma daga baya nake
tunanin ku da kuma abunda zakuce idan kukaji na saketa dan nasan kuna santa banda zabi
ne".

Maihafinsu ne da ya manyanta sosai a yanzun amma zuciyarsa na nan tsatsaura yace "ni ai
kamun daidai kabiru me ake da baragurbi?
Maza ku buga mata ta bude a yanzu yanzu ta bar gidannan dan zuri'ar marna bata da abun
kunya kuma baza mu fara akanta ba ,
Tana jinsu ta jawo jakar kayanta ta hade dana deenah dan tasan babu shakka zamanta gidan
ya kare ,har ranta taji kunar sharrin da kabirun yayi mata taji ba dadi sosai kuma bata tunani
akwai ranar yafiya tsakaninsu saboda taso ace koda zata bar garin yazamana da darajarta tafita
amma a yau kabiru ya zubar mata da wannan darajar sannan gidan marna ba gida bane da ake
sauraran mace ta yi bayani na nata bangaren.
Ajiyar kudinta da take da akwai boyayyiya ta bankado a karkashin gado dama ta boyene

saboda rana mai kamam ta yau wadda tasan zata zo koman dadewa ,
Sokesu tayi a habar zaninta sannan ta kara bankadawa ta dauko dan kunnenta na zinare
wanda othman ya siyan musu ita da maimunatu wanda babu wanda yasan da wannan kyautar,
Duk wannan abun da take deenah na tsaye tana hawaye musamman muryoyin da take jiyowa a
waje suna zagin mahaifiyarta,
Shahada kawai zainaba tayi ta bude dakin, ai kamar jira sukeyi su ka hau mata tofin Allah tsine,
Babu abunda tace illa jan hannun deenah da tayi suka fice a gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login