Showing 27001 words to 30000 words out of 72993 words

Chapter 10 - Auntyn Yara Book1 Complete Hausa Novels By Sadnas.doc

Sadnas   

06 Sep 2025

887

mamace taketa bata hak'uri.

Auntyn yara ta dubi tsohon dade rik'e da hannunta yana tab'a inda aka harb'etan da hannayensa,cikin ikon Allah sam bataji zafiba. Se alokacin da take kallon tsohonne seta tuna cewa wannan shine wannana tsoho mai farfad'iyan data tab'a taimakawa lokacin daya fad'i akan titi rananne farkon had'uwanta da *peach* shiyasa bata bance fiskanshiba sam. Murmushi tayi tace baba,yace na'an maryam kin ganeni ashe,tace sosaima kuwa meya kawoka nan bab ya jikinka? Murmushi yayi yace jiki da sauk'i maryam tun bayan rabuwana dake na taimakawa mutane hud'u yanzu kece ta biyar,tace eyyah baba Allah ya saka da alkhairi,dama a nan jihar bauchi kakene? A'a a jihar adamawa nake ca *hong* ayyah baba a hong kake dama toya akayi kazo nan? Maryam saboda ke nazo danaga kina cikin damuwa kuma dama nace kece mutum ta biyar dazan taimakawa shiyasa nazo. Har zatayi magana ya katseta da cewa maryam ki saurari abinda zan gayamiki da kyau,tace to baba ina jinka amma akwai wanda ya kamata mu had'u dashi nasan kuma sun iso yanzu gashi sun karb'e wayana nasan zaiyita nemana baba. Yaga dai ta damu sosai seyace karki damu zan kaiki har inda suke kiban hankalinki anan maryam,tace to baba ina jinka yare da kallon hannunta daya d'aure mata bayan wasu abubuwa dayayi wanda basan meneneba.

Baba ya kalli maryam yace nasan zaki gayawa mutane cewa *lubna ce* tasa akayi miki haka ko? Tace eh baba,yace to karki gayawa kowa maryam,cikin mamaki tace meyasa amma dolene in gayawa iyayena ai,baba yace harta iyayennaki kada ki gaya musu komai kuma bana so ki tabbayeni dalili indai har kin yadda dani kinsan bazan cutar dakeba to rashin gayawa kowa shine afi akhairi a gareki maryam. Mamaki sosai ya baiyana a fiskar maryam tace to baba idan ban fad'a an d'auki matakiba ai zata sake bin wata hanyan,yace bazata sakeba maryam maganar gaskya niba mutum bane kamar ke maryam ni alja....bai k'arasaba maryam ta tsorata sosai tare da mik'ewa tana komawa dabaya dukda dai tasan batasan kota inda zatabiba. Baba ya mik'e yace maryam karkiji tsorona ki d'aukeni kamar kina tare da mahaifinkine,dan Allah karki sanar da kowa cewa lubna ce ta miki haka kigayawa kowa cewa su saddam ne,sannan yanzu haka bawan Allah can yana can hannu sojojin zasu gana kece zaki iya dakatar dasu tawajen gayamusu cewa shi bayida hannu taimakonki yake da niyanyi shine suka miki rauni kinji maryam? Cikin rawan jiki dama tunda taji shiba mutum bane taketa add'ua,setace to baba dan Allah inaso in koma gida,yace ba gidaba maryam karki rud'e ki nitsu kinji,kibi wannan hanyan gabanki zaki samesu nina tafi.
Yana kaiwa nan ya b'ace,gudu maryam tasa tare da kiran sunan manosh...!
Kamar daga sama manosh yaji muryanta ta gefensu da sauri ya juya ya nufin gun da gudu yana apple, "where are you?" Can ya hangota tanata gudu tana juya bayanta har suka iso gun juna.

Kallon juna suka tsayayi yayinda take ta waige waige,manosh ya lura da cewa bata cikin hayyacinta sam. Sunanta ya kira aunt? Da sauri ta juyo se'a sannan ne ta dawo hayyacinta nan ta tsaya kallonshi cikin so da kuma tausayin yadda taga ya zama. Sunanshi ta kira tare da murmushi tace manosh,shima murmushin yayi tare da k'are mata kallo da wuri yakai hannunshi gurin hannu??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????nta da aka harbeta sannan ya juya yana kallonta cikin tuhuma. Ita kanta tasan dalilin kallon nan tace wani bawan allah na hango shine yayi saurin d'aukeni ya kuma taimakamin sosai shinema ya d'aure min hannun. Manosh yace yarone ko tsoho? Har cikin ido take kallonshi ta kuma gane me yakenufi wato yana kishi wani ya tab'a jikinta kenan. Tace tsohone manosh kamar mahaifina yake kuma wlh ba wani tab'a jikina sosai yayiba abun nashi daban al'ajabi kuma sam bana jin wani ciwo yanzu,murmushi yayi mata dan yasan sam maryam bazata mishi k'aryaba ya yadda da ita har cikin zuciyarshi.
Matsowa yayi kusa da ita gab kad'anne a tsakaninsu kunya sosai taji sannan ya mata kwarjini sosai ta yadda bazata iya had'a ido dashiba. Hannunshi ya mik'a mata mana'a tazo su tafi,amma sam tak'i bada hannunta tanata jan himar nata da d'ayan hannun. Murmushi yayi yace Alhamdulillah "i'm so happy to see you apple" kanta a sunkuye tace "me too" sannan ya d'auki wayanshi ya kira babanta yace baba mun sameta lfyanta k'alau gatanan yanzu zau taho,maryam ta karb'i wayan tana kallonshi tare dayin dariya tasa a kunnenta tace hello baba,yace alhamdulillah 'yar baba Allah ya amsa addu'armu barka 'yata,mirmushi tayi wanda yaji dad'i sosai tace baba ina mama,nan mama ta karb'i wayan tace maryam Alhamdulillah bari naje kichin na dafa miki abinci 'yar albarka,dariya tayi tace ina sonki mamat semun dawo na kuma gode sosai da addu'oinku.

Bayan ta gamane ya kira miher da mum nashi nanma suka gaisa sannan ya kira su marwan suka sakegaisawa daidai lokacin suka iso gun otansu manosh d'in.
Maryam ta hango bawan Allah yana ta zubar da jini a k'afanshi yayinda wani yake gyara mishi k'afa. Da sauri tace peach me kuka mishi haka,wlh sam bayi da laifi kokad'an dan shinema wadda yake kiran baba a waya,sannan taimakona yakeyi sam bayida hannu a ciki dan Allah ku rabu dashi,manosh yace apple pls karkisa baki a ciki,tace pls manosh ka saurareni wlh..ya isa apple,yana da hannu mana tunda ya biyosu kuma ai shima yasan da zance sacekin inhar da gaske yakeyi meyasa bai sanar da 'yan sandaba. Shiru maryam tayi dan yadda taga ran manosh ya b'aci cikin k'ank'anin lokaci da sauri tabar gun ta koma jikin motarsu tana zubda kwallah.

Manosh yabi bayanta tare da bud'e mata gaban motan yace shiga mu tafi,ba musu ta shiga ta zauna daga tsakiya tana ci gaba da kukanta wanda babu sauti hawaye awai kake hangowa yana zuba. Hankalinsa ya tashi nan ya shigo gaban shima yana zaune tagun k'ofa driver a ya shiga maryam tana tsakiyansu sannan sauran suka tattaro tarkacen su saddam da wannan mutumin a bayan motan suka kama hanyan.
Maryam ta share kwallanta kanta a sunkuye dan gabad'aya a takure take. Manosh yace da driver idan kaga wani shop ka tsaya agun,yace ok sir.
Maryam ya kalla yace apple me zakici,tace ni banason komai,yasan cewa fushi tayi yace dolene kici wani abu dan kina jin yunwa sosai,tace ni banajin yunwa muje kawai,nan driver ya tsaya suka fita shida manosh nad'an wasu lokuta sannan suka dawo amma drivern bai shigo motaba.
"Anosh yace apple karb'a kici,tayi kamar bata jishiba,ya sake cewa bana so mu fara haka dake pls apple ki barni inyi aikina inyaso zan barshi daga baya amma ba yanzuba kinji? Ko kallonshi batayiba tace amma nace maka babu hannunshi fa,yace yes aunt i know bincike kawai zanyi akan wanda yasasu kuma shi yasan kowanene,tace nima na sani ai saddam sunanshi kafin kuzo suka gudu,yace eh saddam dinma akwai wanda ya sashi ai,tace pls peach indai kana sona to kawai kabar maganan tunda Allah yasa nadawo nina yafe wlh,murmushi yayi yace ok apple eat first okey,tace nifa bazanci komaiba seka janye,yace tona janye karb'i apple d'in kici pls,karb'a tayi yana mata murmushi sannan shima ya fara cin nashi ita kuwa sam ta kasa ci tana rike dashi. Ta lura da cewa yana kallonta dan haka tace nifa bazan iya cin komai ayanzuba senaje gida,bakinshi ya matso dashi daidai kunnenta yace "kinaso inyi fushi dake koh?" Kunya taji tace wlh bazan iya cin komaiba kayi hakuri,shuru yayi bai sake ce mata komaiba sunata tfy har suka iso *yola*.
Dad'i sosai maryam taji suka wuce da bawan Allah can barac nasu inda ya mik'awa manosh wayan maryam yave lokacin da take wayane ya karb'e wayan,bayan ya ajiye wayan shine na d'auke. Manosh ya karb'a sannan yazo suka wuce girei itadai maryam tanata tausayawa mutumin can dasuka kama,ahanyane manosh ya bata wayanta,tanata godiya tace a ina ka samo dan ai wayan tana hannun saddam ne,nan yagaya mata komai daidai lokacin suka iso k'ofar gidansu maryam a girei...
[7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

*dedicated 2 matan kwarai grp*???b??.\


43-44 k'ofan gidansu maryam a cike yake da jama'a kowa yana jiran dawowar auntyn yara,koda akaga motan sojoji ya tsaya da sauri aka nufo motar anata hamdalah da mata murna sosai,musamman abdallah hannu ya d'aga sama yanayiwa Allah godiya.
Su manosh suna tsaye daga waje yanaganawa da jama'a,ita kuwa ta wuce gida dasu rash da sameera daidai sauran jama'a. Maryam ta rungume mahaifiyarta tana murmushi bayan nan ta zauna bada lbrn abinda ya faru amma sam tace batasan bayasa a mata hakanba,nan dai kowa yayita tofa albarkacin bakinsa. Can akajiyo hayani a waje nan take kowa ya fito,yarane da almajirai suketa tsalle da wak'a.
_Alhamdulillah auntyn yara ta dawo,ta bayya,Allah mungode maka daka dawo mana da auntyn mu lfy lau_.
Hahahah sunatayi manosh ya nufin gurin se zuba musu kud'i yaketayi yara se k'ara murya sukeyi suna d'iban kud'i yah ibrahim ne yazo ya koresu yace toya isa haka mungode kowa ya wuce gida,nan suka watse suna murna. Dariya manosh da ibrahim sukayi sanan suka wuce gunsu baba suna magana,maryam ta wuce band'aki tayi wanka tare da d'auro alwala tazo tayi sallolinta sannan taci abinci sosai dan dama tana jin yunwa.
Bayan ta koshine tace mama da sauran wani abincinne zan zubawa manosh a kula ne,mama tace eh akwai,nan taje ta had'o a kula ta kawowa maryam tace gashi,godiya tayi tare da mik'ewa taje palon babanta tare da sallama suna zaune da yah ibrahim da kuma abokinsa soja wato yusuf maryam ta ajiye musu abinci sannan ta koma ta d'auko plate da kuwa ruwan sanyi tare da exotic d'in da hajiya khadija ta kawo musu.

Bayan ta fitane yah ibrahim ya zuba musu ba laifi kuwa sunci sosai sannan sukace zasu tafi. Maman maryam tazo suka gaisa sannan ta musu godiya,manosh ya kira maryam ya sanar da ita cewa zasu tafi ta kwanta ta huta,godiya sosai ta mishi yare da jajdada mishi cewa karya cutar da bawan Alla can,murmushi yace yace "yes my princess"tambayoyi kawai zai amsamin nayi miki alk'awarin bazan cutar dashiba matuk'ar zai amsamin tambayoyin da nake buk'ata agunshi. Dad'i taji sosai tace yaushe zaka sake zuwa? Yace se jibi akwai wani abune,tace yes ina son *flower* murmushi yayi yace angama aunt gobe mum da miher zasuzo zan aikota dame kuma kike so? Tace da *peach d'inah*,dariya yayi itama haka sannan suka tafi. Yah ibrahim ya shigo gida sunata hira dasu rash daga k'arshe suka tafi.....

Washe gari da safesartuday ne,dan haka su marwan suka da safe sukayiwa maryam barka sannan suka d'anyi hira suka tafi. Da misalin 11:00am mum d'in manosh da miher sukazo nanma dai suka zauna kad'an,miher dasu maryam sunata hira a d'akinsu yayinda ta mik'a mata flowern da bro nata ya bayar akawowa marya,dad'i sosai taji tare da lumshe ido su miher da rash se dariya sukeyi mata suna zolayarta. Awa d'aya su miher sukayi sannan suka tafi sesu zahida da amina sukazo,bak'idai sosai suketa zuwa da abin arziki babu wanda yake zuwa empty.
Hajiya iya ce zaune a gaban maryam tanata kuka tana rungume da maryam,maryam da mamanta duk kansu ya
d'aure da irin kukan hajiya iya. Amma se suka d'auka kodon k'aunarda takeyiwa maryam ne.

Saddam ne zaune a d'akinsa ya kira lubna a waya yace kina ina,tace ina gida me nakeji wai maryam ta koma gida? Yace kizo mu had'u dan muyi magana,tace ok amma bazan fito da motaba zanzo yanzu semu had'u,yace ok.
Babu wani b'ata lokaci lubna ta shirya cikin after dress black tahau nape se daidai gate d'in gg ta kira saddam a waya tace ina daidai gg,yace wlh motata tayi pashi bamma bar gida ko zaki k'arasone semu fito tare,bata soba dai amma dan bataso asirinta ya taunu setace to gashi kayiwa mai napen kwatance. Nan suka d'auki hanya har inda saddam ya kwatanta musu,se kuwa gashi ya fito daga d'akinsu yazo yabiya mata kud'in dan ita batada canji.
Bayan mai nape ya tafine saddam yace ki shigo mana kar wani wanda ya sanki ya ganki anan kinga se'a ganki kamar mutumiyar banza,haka tabishi a baya suka shiga sannan ya kulle k'ofan ta key,lubna data zauna aiseta mik'e tare da cewa ya kuma ka rufe kofan saddam? Take ya canja ido yace ashe ki muguwace munafuka ban saniba,kece kike gayawa maryam inda muke kaita dan azo a kamani in fita daga rayuwarki ko lubna,hakazakimin,wlh to bazan barki hakaba sena lalata miki rayuwarki kafin in bada kaina. Kuka lubna ta farayi tace haba saddam wlh bansan komai akan abinda kake fad'aba taya za'ayi in kira lubna kuma,dan Allah karkamin haka saddam wlh karyane duk wanda ya gayamaka karya yakeyi wlh,nan dai lubna ta rikice ta fara kuka. Shuru sadda yayi yace kiyi hakuri lubna na d'auka koda gaskene wlh,bakomai share hawayenki mu tafi domin yanzu ni suke nema abokina ya yaudareni wlh amma zanyi maganinshi baisan wayenibane shiyasa,juice ya zuba mata da sauri ta karb'a tasha batare dayin wani tunaniba ta shanye tas dama datajin k'ishi. Shi kuwa saddam wayo ya mata dan kartayi kuka ta tona mishi asiri dan haka ya juba magani a ciki ai kuwa take lubna ta fara fita hayyacinta,saddam kuwa ya tashi ya fara cire kayan jikinshi tas tana iya ganinsa bakomai a jikin,nan hankalinta ya tashi tana k'okarin tashi amma ina seta fad'a kan katifarshi kamar macacciya,da sauri ya rabata da kayan jikinta tas se lashe baki yakeyi kamar tsohon maye,yahau shafeta tare da wani irin gigicewa da ganin kyakkyawar suranta. Cikin k'ank'anin lokaci ya rabata da budurcinta gashi ya kwashi romo sosai danshi a tunaninshi an dad'e da sanin lubna saboda irin shigan dayaga takeyi. Bayan ya gamsune yayi saurin watsa ruwa ya shirya tare da kwashe kud'ad'en dake jakarta ya d'auki akwatinsa ya gudu da motarshi.

Koda lubna ta dawo hayyacinta kuka sosai takeyi tare da tsinewa saddam albarka tana tuna yanzu shikenan ya gama b'ata mata rayuwa ya zatayi kenan? Miher ce kawai ta fad'o mata arai harta d'auki wayarta zata kirata kuma seta tuna cewa koda yaushe miher suna tare da majid kuma tasan dole miher zata fad'a wanda idan bro marwan yaji shikenan nata ya k'are. Kuka sosai lubna takeyi gashi jikinta duk jini haka ta rasa yadda zatayi kawai se maryam ta fad'o mata a rai data tuna da abinda wani tsoho ya gaya mata akan maryam,ai kawai seta kira maryam.
Lokacin su maryam sun shigo jimeta dasu yah ibrahim dasu sameera,mamaki tayi sosai da ganin kiran lubna,seta d'auka hello,lubna cikin miryan kuka take magana hello maryam dan Allah ki gafarce akan abinda na miki nasan kinsan komai amma dan Allah ki rufamin asiri dan yanzu hakama Allah ya saka miki akan abinda na miki maryam sadda ya cuceni yamin fyad'e bazan iya kiran kowaba seke,saboda abunda wani tsoho ya gayamin dan Allah maryam ki taimaka kizo saddam ya gudu yanzu haka ina d'akinsane a bayan gg idan aka sani za'a kasheni a gida musamman bro marwan maryam dan Allah ki rufamin asiri. Shuru maryam tayi ta kasa cewa komai,kuma batasan ya za'yi tabar su rash taje ita kad'aiba. Nan tace ok inazuwa tare da kashe wayar, tace yah ibrahim dan Allah ku saukeni anan ku shiga kasuwan rash idan naje na gama zan gaya muku inda nake sumu tafi,yah ibrahim yace to shikenan sannan ta sauka tahau nape se bayan gg,nan dai ta kira lubna tayi musu kwatance suka k'arasa har gun sannan ta sallameshi ya tafi,ta sake kiran lubna nan taji k'aran wayan a kofar gabanta,da sallama ta shiga taga lubna a kwance cikin jini,tsorata sosai tayi tare da dasa key a kofan tana ta addu'a,ta k'arasa ta taimaka mata ta mik'e ta rakata toilet dake kicin d'akin sannan ta tsaya daga bakin kofa tana mamakin abinda ya faru.
Wayartace tayi k'ara ta d'auka hellow peach,yace apple nah kina ina,k'irjinta ya buga tace ina jimeta munzo sayayyane dasu yah ibrahim idan muka gama zan sake kiranka muna cikin kasuwane,yace ok badamuwa,tace ina kake? Yace muna kan aiki yanzu zamuje inda saddam yake zaune ne mu kamashi,tace a ina kuka sameshi peach,yace wai yana bayan gg yanzu haka muna hanyane,tsoro ya kama maryam tace to shikenan sena kiraka,yace ok byee. Maryam tace lubna fito su manosh suna hanyan zuwa nan domin sun samu lbrn cewa saddam yana nan karsuzo su tarar damu anan gashi na mishi karyam idan ya samemu anan tofa ina cikin tahin hankali,lubna take zawo ya kamata haka tayitayi a toilet d'in tana kuka,ita kuwa maryam se kallon windo takeyi tare da k'ara rufe ko ina a d'akin,daidai lubna ta fito tasa kayanta da sauri jikinta se b'ari yakeyi tausayinta ya kama maryam har seda tayi kwalla,seta d'aga zanin gadon taje ta wanke da ruwa tazo ta bazashi akan gadon sannan maryam ta kwashe mata wayanta da sauran kayan makeup nata tasa a bag na lubnan suka yunk'uro zasu fita kenan sega motar su manosh,aida sauri suka wuce toilet sunata addu'a ita kuka lubna zawone ya sake kamata haka tayitayi tana hawaye sosai dan yadda take tsoron bro marwan barema kuma aji cewa an mata fyad'e ne hmmmm...
[7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Writren by sad-nas
&
Hama gee muh'd

*dedicated 2 khafeelat abdulhafis*B???


45-46 tsayawar mutar sukaji,ba lubna kad'aiba ba harta maryam a tsorace take,gashi tayiwa manosh karyan cewa tana kasuwa kuma yanzu idan ya ganta a d'akin saddam kimarta zai ragu a idonsa addu'anma dakyar take iyayi,ita kuwa lubna idan ka gantama dole kayi kwalla dan tausayinta. Muryan manosh sukajiyo yana cewa ya kuma naga padlock a k'ofan,hakan yana nufin saddam ya sake tserewa kenan?yusuf yace ai mu b'alla kofan kawai k'ila sawa yayi a rufeshi ta baya dan muyi tunanin bayanan.
Maryam da lubna aise suka tsure suna *innalillahi wa inna ilaihirraji'un* jikinsu se rawa yakeyi. Bawan Allah ne yace duk yadda akayi saddam guduwa yayi baya ciki domin banga motarshiba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login