Showing 54001 words to 57000 words out of 72993 words

Chapter 19 - Auntyn Yara Book1 Complete Hausa Novels By Sadnas.doc

Sadnas   

06 Sep 2025

880

muke jira kekanki kisan duk duniya babu wanda captain zai bud'ewa zuciyarshi ta shiga ta zauna se *aunty* . Haushi da takaici yasa shukrah katse wayar
Yah ibrahim ya tsinci kanshi dayin murmushin tare dajin dad'in sanin cewa ba manosh bane yayi magana da aunty shukrah ce. Take ya kira baba a waya ya gaya mashi komai,baba baiyi mamakiba dan yasan babu abinda aljanu basayi, take yaje ya sanar dasu maryam dan hankalinta ya kwanta.
Ai kuwa dad'i sosai taji tare dayin add'ua Allah ya kare mata mijinta ya kuma dawo dashi garesu.

Marwan kuwa yana kwance ne kawai amma yakasa bacci dan irin abubuwan dayaji yau da kuma gani. Tun bayan barin su lubna gidan yaketa tambayar hajiya iya kakarsa meke faruwane danshi kansa yasan akwai wani abu dayasa lubna tayi mata hakan amma sam hajiya iya tak'i cemishi komai se kukan nadama da taketayi babu sassaushi. Haka marwan ya gaji ya tafi gida gun mum nasu,koda ya gayawa mum nasu abinda lubna tayiwa hajiya iya sam mum batayi mamakiba,shima marwan d'in ya lura da yanayin mum d'in nashi wanda yasashi tambayar mum nasu yace wai meke faruwane mum nakasa fahimtar komai tabbas akwai wani abu dayake faruwa mum dan Allah ki gayamin.
Marwan ya kamota suka zauna yana share mata kwalla.
Mum ta dubi marwan tace zan gaya maka marwan amma sekamin alk'awarin bazaka bari mahaifinka ya d'auki mummunan mataki akainaba, cikin rashin fahimta marwan yace banganeba mum?
Mum tace marwan dad naka yana k'aunarka fiye da komai a duniya,idan yasan abinda na'aikata tonasan zamana dashi yazo k'arshe, kaine zaka iya hanashi rabuwa dani d'ana saboda k'aunarka da yakeyi.
Marwan ya sauke ajiyar zuciya yace namiki alk'awari mum har abada bazan bari ku rabu da dad ba. Mum tace nagode marwan, sannan ta fara bawa marwan lbr kamar haka...
[7:14am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNRY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas


*dedicated to AUNTY SIS*


_nagaba yayi gaba na baya se lbr our sweet aunty, kece ta farko kuma kece ta karshe,babu wata bayan ke *aunty sis*,muna alfahari dake akoda yaushe...



75-76 marwan ya rasa mema zaicewa mum nashi,dan tsabar yadda jijinshi yayi sanyi kamar k'ank'ara. Cikin sanyi murya yace mum danasan abinda kika aikata kenan daban miki alk'awarin dana d'auka mikiba,amma koba komai ke mahaifiyata babu abinda zan iyayi ko kuma ince miki,sedai kiyi hakuri amma sam abinda kukayi baidaceba sam wlh mum abin babu dad'i ji. Matsowa yayi kusa da ita yana kwalla kamar yadda takeyi yace mum kidena kuka inaso kimance da cewa kin bani wannan lbrn,ki d'auka cewa har yanzu sirrine kamar yadda kuka rufeshi keda hajiya iya,dan gaskya mum nibansan ne nake cikiba a yanzu haka. Komin dad'ewa gaskya zai fito wanda bansan yazan tsinci kainaba a wannan lokacin da kowa zaisan me mahaifiyata da kakata suka aikata.
Jiki babu kwari ya mik'i zai fita tayi saurin kamoshi tace dan Allah kaban mafita ya d'ana. Mum wlh babu wata mafita danasan zan baki akan wannan lamarin domin baki bani wani ilimi akan hakanba lokacin da kuka bani tarbiya keda dad. Mum tace nasan ban kyautaba shiyasa nake neman nafita marwan? Marwan yace mafita shine kisami dad ki gaya mishi komai tun kafin lubna tatona muku asiri mum.
Bayan fitan marwan ne mum taketa kukan dana sanin akan abinda suka aikata. Shikuwa marwan gida ya koma da zazzab'i mai k'arfi daya rufeshi,seda rashida ta kira dr muh'd a waya yazo gida yayi masa allura da kuma magunguna inda suke mishi sannu. Sam marwan ya kasa had'a ido da abokan nashi saboda tun a yanzu kunyansu yakeji bare kuma ace gaskya ta bayya kowa yaji.
"Lubna ce kwance tana bacci ad'akin maryam hankalinta kwance,ita kuwa maryam se mamakin kulawar da lubna tayi da ita takeyi acikin zuciyarta tare dajin sonta a ranta. Wayan lubna ce yake k'ara koda maryam ta duba setaga yah ibrahim ne,daidai nan lubna ta farka tare dasa wayan a kunne tace hello,yace kin tashi lfy yasu aunty,tace lfyansu lau ya mama,yace tana lfy ina hanyan zuwa d'aukanki da fatan kin shirya? Ta murza ido tare da kallon maryam tace wlh yanzu na tashi ko wanka banyiba kabari se anjuma kad'an pls...? Yace ok naji amma ki tabbata kin shirya dan zamubi gidan marwan mu gaisheshi bayida lfy tun jiya zazzab'i mai k'arfine ta rufeshi wlh. Subhanallah!tobari kawai na shirya nan da 1hr sekazo.
Maryam ta kalli lubna tace lfy? Lubna tace bro marwan ne ba lfy zazzb'i sosai,maryam tunda nake ban tab'aganin rashin lfyanshiba bro marwan yana sona sosai har cikin ranshi dukda zafinshi amma akan gaskya yake komai na???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?shi i respect him so much aunty,maryam tace eyyah nima barina shirya muje tare inyaso zanbi gunsu miher zuwa yamma sena dawo.

Maryam ta gama shiri tsaf,ita kuwa lubna tana zaune tana k'are mata kallo,maryam tace naga kina zaune,lubna tace eh bazan maida kayan jikinabane shiyasa dan sunyi datti. Maryam ta gane me take nufi hakan yasa ta d'auko mata zanin da manosh ya saya mata tunda ta d'inka bata tab'a sawaba ta batashi tace ga wannan kisa,godiya sosai tayi ai kuwa nan danan ta mik'e tasa sun mata kyau sosai ajikinta ta juyo tace aunty nagode kayan sun amshi jikinki sosai wlh harda rungume maryam,azuciyarta tace nagode sosai 'yar'uwata jinin jikina.
Mama ta shigo tace todai sekunci abinci kafin ku tafi,bamusu sukaci amma maryam kad'an taci dan dama tunda aka nemi manosh aka rasa tadena cin abinci. Ita kanta mama lubna tana burgeta kome dalili oho,ita kuwa lubna sakewa sosai tayi dasu ko'ajikinta dukda ta lura da cewa suna mamakin yadda ta sake dasu tazama kamar 'yargida.
Gun motan yah ibrahim suka nufa bayan sun gaisa suka shige maryam ce a baya suna tfy ta hango manosh daga nesa. Peach ta kira sunanshi cikin mamaki wanda yasa yah ibrahim tsaida mota da sauri suka had'a baki tare da cewa ina yake? Tayi musu nuni da hannu zuwa inda yake tsaye ajikin wata black car. Mamaki sosai sukayi dan tabbas shine tsaye sanye da kakin sojojinsa ya hard'e hannaye yana duba agogon hannunsa bisaga dukkan alamu wani yake jira...
[7:14am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas
*dedicated to ummi hambali*??/\??/\??/\

_Assalam fans nagode sosai da kulawarku,lfyata lau kawai sungullane yake min yawa a'yan kwanakinnan shiyasa bakwajina_.??/\B???
_sannan masu min tambaya akan konice marubuciyar *lalata*, no! Banibace *sad-naf ce* dafatan kun gane_???i




73-74 Marwan auren so da k'auna mukayi da dad naka kuma shi shi d'an wan mahaifinane auren dangi aka mana nida dad naka.
Tun ina 'yan'mata Allah ya d'oramin son yara musamman mata,kowa yasan da haka a dangi. Bayan munyi aure da mahaifinka ne kusan 2yrs kafin na samu cikinka,bazan iya gaya maka burin da muka d'auka akan wannan cikinba,dan muna ta fatan Allah yasa mace zan haifa,amma se yazama kaine marwan na haifa,hakan baisa na fidda ran haifan maceba.
"Marawan har kakai 12yrs ban sake sake samun cikiba,babu irin damuwa da tashin hankali da bamu shigaba harta dangi,dayake ansan yadda nake son mace,gashi dangi kam kowa namiji yake haifa ba mace ko d'aya. Hajiya iya mahaifiyar dad naka tana sona sona tamkar 'yar cikinta sam bata son ta ganni cikin damuwa,har zamuje gidan marayu d'aukan yarinya,amma se mahaifin dad naka wato wan mahaifina yace a'a bai aminceba,hakan yasa muka hakura har wata rana naje girei gun hajiya iya yini...
"Muna zaune se aka zo da sallama wai wata mata tana nak'uda kuma ta galabaita sosai gashi duk mak'otan sunce bazasu iyaba sedai a nemo tsofi,sakamakon mijinta baya kusa,kuma yana fama da kansa ana tunanin idan an kaita asibitima kud'i za'a nema lokacin kuwa kowama yana fama da abinda zaicine. Hakan yasa nida hajiya iya mukaje gun wannan mata mai nak'udan wanda batama san inda takeba ta zama abin tausayi bata cikin haiyacinta sam.
Munfi awa muna kanta cikin ikon Allah ta haifi bby girl kyakkyawa,kwalla ne ya zubo a idona dan ji nayi kamar in gudu da jaririyar,muna cikin murnan kenan sega wani kai ya fito ashe dai 'yan biyune dukkansu mata,murna sosai mukayi nida hajiya iya muna cewa ashe 'yan biyune shiyasa ta wahala haka.
Tofa shine hajiya iya tace dama mijin natan baida hali kuma gashi har yara biyu,dan haka tace in tafi da d'aya tunda babu kowa a waje,duk wanda suke jiran haihuwan harsun gaji sun tafi saboda sunga bata haihuba. Ni kuwa banyi tunanin komaiba saboda yadda nake son mace,a d'ankwalina na nad'e jaririyan nasata cikin himar na koma gidan hajiya iya,acan na mata wanka da komai na koma gun hajiya na d'auki kayan jaririya d'aya dayake sund'an sayi kayan kad'an,na koma na sama mata.
Ita kuwa hajiya iya tayiwa jariya da uwar wanka ta kimtsasu saf,amma har'a lokacin uwar jaririyan bata farfad'owa harse bayan awa biyu,koda taga abinda ta haifa murna sosai tayitayi tare dayiwa hajiya iya godiya.
"Bayan hajiya iya ta dawo gidane,tace maza in tafi da jaririyar gida kar asirinmu ya tonu,tsoro ya kamani nace tome zan gayawa dad naka? Tace zata mishi bayanin cewa an sami jaririyar ne a hanya aka ajiyeta kuma kowa na tsoron d'auka saboda yadda duniya ta canja,shine ita ta d'auka mana tunda tasan muna son 'ya mace. Dayake lokacinma dad naka yana umrah shine komai yazo da sauk'i kuma haka muka gayawa kowa na dangi da kuma abokan arziki harda kuma....
Hajiya khadija ta tsaya anan da lbrnta tana kuka,marwan kuwa jikinsa yayi sanyi yama rasa me zaice mata saboda shidai asaninsa wannan abunda mum nashi da kakarsa sukayi sata kenan satan jaririya. Mum ta lura da yanayin marwa tayi saurin rik'o hannunsa cikin muryan kuka tace marwan karka manta kamin alk'awarin zaka taimakeni amma tun yanzu naga rashin jin dad'i afiskanka,marwan karkace komai ka saurari ci gaban lbrn..
Haka na rik'e jaririyannan na samata sunan hajiya iya muna kiranta da *LUBNA* gata sosai ta samu agun mahaifinka,kuma dukkanmu muna sonta tsakani da Allah..marwan ya katse mum nashi da cewa naji mum kuma na fahimta,yanzu lubna 'yar gidan wayene,su wanene iyayenta a ina suke? Mum tana kuka sosai tace marwan iyayen lubna sunan a raye kuma acikin girei sannan 'yartama tana raye dan lubnan itace k'arama. Marwan ya mik'e tsaye yace mum baku kyauta ko kad'an wlh,wannan abinda kuka aikata bansan me zance akaiba kun kyauce sosai wlh kun raba yarinya da iyayenta da 'yar'uwanta yanzu idan maganannan ya fito waje duniya sukaji mum ya kike so inyi da raina,sunanefa zai b'aci mum ace mahaifiyata ta aikata hakan mum,da wani ido zan dubi jama'a musamman abokaina mum? Kwallane yake zuba daga idanun marwan yace a ina suke? Mum ta mik'e ta kasa dena kuka tace marwan se yanzu nake nadaman abunda na aika busa son zuciyata.
Marwan yace no mum,dukda tarbiyan da kuba lubna kiga dai abinda ta aikatawa *aunty* yanzu da asirinta ya tonu a lokacin da dawani ido zan kalli princ mum,kinsan yadda nake son manosh kinfi kowa sanin shak'uwarmu dashi da kauna dake tsakaninnu ashe ankama lubna ce tayiwa aubty haka daya zanyi,kumafa kiga ita *auanty* ne ta had'a lubna da miji nagari irin ibrahim,mum kinsan yadda ibrahim yake son aunty,wlh daya san lubna ce tayiwa aunty haka wlh bazai tab'a bariba,amma kuma duk wannan bai isaba kika yaudaremu dukkanmu dangi akan tsintota kukayi alhali bahaka maganan takeba haba mum... yanzu waye mahaifin lubna ki gayamin mum?
Cikin nuryan kuka sosai tace bakowa bane *illa mahaifin maryam aunty'n yara* marwan aunty itace twin sister'n lubna ita ta fara zuwa duniya kafin lubna,ta k'are maganan tana zama a k'asa kamar kayan wanki. What! Marwan ya tambaya da k'arfi da fiskan mamaki tare da juyawa yana kallon mum nashi kamar yaga dodo yana fad'in *innalillahi wa'inna ilaihir raji'un*,ita kuwa mum kuka kawai takeyi tana rik'e da hannun d'an nata...
[7:14am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas

*dedicated to ayusher muh'd*???iB??0Rq??


77-78 da sauri yah ibrahim ya tsaida motarsa suka fito dukkansu suka nufi gun da *manosh* yake tsaye,cikin mama maryam ta rik'o hannushi tace peach? Ahankali ya juyo yana kallonta kamar wawa,yah ibrahim yace aunty sakeshi...ai bai k'arasa maganaba seka wata kyakkyawar budurwa ta fito daga wani shago kawai ta d'auke maryam da mari tana cewa ke wace irin shashashace dazaki rik'emin miji?
Ai kafin yah ibrahim yayi magana lubna ma tayi saurin d'auke budurwan da mari tace ai shashashun suna dewa wawiya jaka ke har kinkai a tab'a mijinki,yah ibrahim ne ya shiga tsakaninsu yanayiwa lubna fad'a,ita kuwa maryam sam bataji marinba tamaida hankalinta gun manosh da yake tsaye yanata kallonta baya ko kyafta idonsa. Ahankali ta sake dawowa gefensa tana mai zubda kwalla tace *peach* jikina yana bani cewa kaine dan Allah kacemin wani abu. Kawai setaji yace baiwar Allah banine wanda kike tunaniba,sunana *muawiya* sannan wannan matatace. Kuka mai k'arfi maryam ta fashe dashi tare dabarin gurin aguje zata koma mota nan sukayi kicimus da majid,kallon juna sukeyi har cikin ido tanata hawaye tace majid dan Allah ka k'are mishi kallo wancan ba captain bane duba kakinsafa dan Allah kazo muje nasan zaka iya ganeshi tunda tare kuka taso.
Da sauri majid ya karasa lokacin fad'a sosai akeyi tsakanin lubna da wannan budurwan tace cewa kisa maganata a ranki cewa senayi maganinki,lubna tace ta Allah ba takiba banza mara hankali da kyar yah ibrahim ya janyo lubna ya kaita mota gun maryam se faman kuka takeyi lubna ta zauna a gefenta tana rarrashinta. Majid yaje dabda manosh ya tsaya yana k'are masa kallo tun daga k'asa har sama,shima manosh d'in kallonsa yakeyi kamar dai yadda yayiwa maryam,majid yace *dude kaine*? Budurwan tace yau naga ikon Allah waiku wasu irin mutanene haka,kawai kunzo kun damemu kunat....tsawa mai kyau majid ya daka mata kimin shuru badake nakeyiba! Take ran budurwan ya b'aci idanunta sukayi jah jazur kamar attarugu tayi saurin rik'e hannun manosh tace kadaiga yadda akacimin mutunci amma ka kasa sewa komaiko,shikenan mutafi dan idan nacigaba da zama anan to lallai mutanen dake yankinnan kam zasu shiga cikin matsala. Yah ibrahim da majid suka kalli juna sukace matsala kuma? Daidai nan maryam ta fito daga mota da gudu tana cewa yah ibrahim wlh peach d'inane shine gashi yana min bye bye. Koda yah ibrahim da majid suka maida kallonsu ga manosh da budurwan se sukaga wayam,babu su kuma babu motarsu.
Mutanen dake gurin kowa kafa menaci ban bakaba kusan rabi duk sun gudu,su kansu yah ibrahim sun tsorata sosai,majid yace ina suka shiga? Maryam cikin muryan kuka tace wlh manosh ne yah ibrahim wannan duk aikin shukrah ce wlh sune lokacin da take magana kaida majid kuna kallon junanku se manosh ya juyo yana kallon inda seting motarmu take shine ya d'aga min hannu yanamin bye daga nan kuma suka b'ace yah ibrahim dan Allah kace tadawo min da mijina inda manosh ya tsaya nan maryam taje ta zauna agun daya ajiye kafafunsa tanata kuka,lubna da yah ibrahim ne suka d'agota dakyar suka kaita mota shima majid ya shiga nashi suka koma girei gidansu maryam.

Koda baban maryam ya samu lbrn abin shuru kawai yayi danya rasa mezaice,mama kuwa tanata rarrashin maryam tare da cewa lubna kekuwa meyasa kika rama mata marin?yanzu gashi kin mari aljana idan kuma ta d'auki matakifa gaskya bana son wani ya cutu ata dalilin maryam. Lubna tace mama zan iya bada rayuwa indai akan maryam ne kuma matuk'ar ina raye tofa sedai ad'auki raina bazan tab'a bari a cutar da itaba wlh har abada anyina farko kuma anyi na k'arshe wlh Allah ya isa bazan tab'a yafewa Allah ya isa mama....tanata kuka wanda hankalin kowa yadawo gun lubna se zagi da fad'e-fad'e takeyi wanda babu wanda yafahimci abinda take nufi se ita kad'ai.
Maryam ce ta kamota tace lubna ki nutsu mana meyakawo zagi kuma nan lfyanki kuwa? Tace lfyata kalau aunty wlh an zalinceni kuma bazan yafeba Allah ya isa! Da k'arfi ta k'arasa maganan,nan dai hankalin kowa ya tashi akace gaskya akwai matsala,yah ibrahim ya kamota,takisam ta mannu ajikin maryam tanata kuka. Majid yace gaskya akwai matsala kodai shukrah ce ta maidata hakan? Hankalin kowa ya tashi domin kowama abinda yake tunani kenan.
Maryam ta rungumeta tace a'a majid shukrah bata isa ta mata komaiba lubna dan Allah ki bari kicemin lfyarki kalau kinji,lubna ta d'ago da kanta tana kallon maryam tace lfyta kalau aunty babu abinda yake damuna se abu d'aya,maryam tace menene wannan abun? Lubna kamar zatayi magana se kuma ta fasa domin yadda take k'aunar hajiya kadija aranta bataso ta tona mata asiri,nan ta sake fashewa da kuka tace kigafarce aunty bazan iya fad'aba sannan ta mik'e da sauri ta koma d'akinsu tanata kuka mai k'arfi,su kuwa aka barsu da kallon labule,kowa hankalinsa atashe kuma tunaninsu shine kodai shukrah ce tayimata wani abu akan marin data mata?

Bayan sun gama magananne yah ibrahim yace aunty kiramin lubna tazo mutafi,bamusu maryam ta mike jiki sanyaye tanata tunanin had'uwansu da manosh yanzu,tace dama rungumesa nayi lokacin dana ganshi,wayyo Allah peach Allah ya dawomin dakai ya mijina uban yarana i luv u so much peach dan Allah ka dawo garemu. Maryam bata sammata shigo d'akinba kuma ita ta d'auka cewa acikin zuciyarta take wannan maganan bata cewa lubna tajiba. Lubna ta dakata da kukanta tace kiyi hakuri aunty insha Allah bro manosh zai dawo gareki shukrah bata isatayi komaiba wlh,itama kuma lokaci da zaidawone baiyiba kidena kuka pls aunty dukda dai nasan yadda kikeji amma bana so inganki cikin damuwa pls kiyi hakuri mucigaba da addu'a kinji aunty? Rungume juna sukayi sunata kuka sannan maryam tace yah ibrahim yana kiranki wai kije ku tafi kuma dan Allah kugaida marwan kice nima zanzo ko zuwa gobe insha Allah. Lubna dai bata soba amma babu yadda ta iya seta mike ta shiga palon baba rai ab'ace tace baba mama se'anjuma sannan ta fita waje tanata kuka,mamakinta ya sake kamasu dukkansu haka dai suka fito suka tafi tanata kuka.
Tun a hanya ibrahim yake tambayarta dalilin kukanta amma sam tamak'i kulashi har suka iso

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login