Showing 3001 words to 6000 words out of 72993 words

Chapter 2 - Auntyn Yara Book1 Complete Hausa Novels By Sadnas.doc

Sadnas   

06 Sep 2025

870

isa kuwa ta samu mota se jimeta.

Koda ta isa kekenape ta hau ta k'arasa gurin, amma sai mai keke yace bashi da canji,tace toya zamuyi kenan tana ta waige waige seta hango manosh yana rabawa masu bara sakadan 200 sabbi gal,ta kalli mai nape tace malam dan Allah kayi hakuri bari inje can in nemo canji,yace to bakomai. Nan ta nufi gurin manosh yanata raba musu kud'i tayi sallama tare da cewa bawan Allah,d'agowa yayi da sauri danjin muryan Apple ya kalleta batare dayin maganaba,tace sannu dai dan Allah canji zaka taimakamin dashi, ya kalli k'udin hannunta dubu d'aya,amma seyace wannan dai sadaka nake rabawa sannan banida wani canjin,tace to dan Allah ko 200 d'inne ka bani gashi ka rike 1000 d'in zan biya mai keke ne. Juyawa yayi yana kallon napen seyace rik'e dubun seya mik'a mata 200 d'in,tace nagode sannan taje tabiya mai nape ya bata canjin 150 seta dawo tace to kayi hakuri bari na shiga gun flower'nnan sena baka kud'inka,yace to se tayi saurin wucewa ciki yanata binta da kallo. Da yake sun santa tana shiga dama sun h'ada komai tunda babanta ya sanar dasu a waya dama. Bayan su gaisa se d'aya yace tokije ki nemo mota mana, tace akwai motoci anan muje kawai,suka bita dashi taga wani mota tace girei zaka kaini da wannan flowers d'in. Manosh yana ganin haka yama drivernshi waya take yazo da HILOX fara,yace kaje ka kaso flowers d'in can kasa a mota, har an fara sawa seya zo yace oga yace oga yace asa miki a mota,tace waye kuma oga,yace gashican shine mai gurinnan gabad'aya. Shuru tayi suka kwashe suka zuba dukka a hilox d'in setacewa mai motan data tsayar dan allah malam kayi hakuri,yace bakomai yarinya karki damu,tace nagode sannan ta k'arasa gurin manosh tace dama kaine mai nan gurin? Eh yace da ita tare da cewa kuje a kaiki gida koh,tace nagode sosai ga 200 d'inka,yace karkimin godiya,arayuwa idan kin samu dama toki taimaki mutane uku,suma kuma kice musu su taimaki wasu ukun ya k'are maganan yana murmushi,dad'i taji sosai har cikin ranta tana binshi da kallo harya shiga motarsa ya tafi. Gun hilox d'in ta nufa driver ya bud'e mata ta shiga ya rufe tace nagode sannan suka kama hanya yace ina zan kaiki,tace girei,yace ok sannan yaja suka tafi tana mai farin cikin jin kalaman manosh. Suna cikin tfy wayan driver yayi k'ara ya d'auka tare da cewa hello sir,se kuma yace eh nan girei ne sannan yace ok sir seya saka wayan a aljihunsa har suka k'arasa kofan gidan flower'n babanta sannan tace anan zamu tsaya,yace ok tare da tsayawa,dama babanta yana jiranta a shagonsa,drivern ya gaida baban maryam sannan suka kwashe flowern tare. Maryam da babanta sukayi godiya sannan ya tafi. Maryam taba babanta lbrn komai tun ranar da suka had'u da manosh,babanta yace to Allah ya saka mishi da alkhairi tace ameen sannan suka gyara ko ina sannan suka wuce gida.

Manosh yake tambayr drivernshi kaga gidansu? Yace no,sir a shop d'in babanta tace in tsaya shiyasa,inane shop d'in,nan yayiwa manosh kwatance,manosh yace gud shikenan kana iya tfy. Shima side d'insa ya wuce amma bata palonsu mum nashi ba ta d'ayan gefen yaje ya watsa ruwa ya kwanta yana tunanin apple.
[7:07am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd


7-8 Ita kuwa maryam tun bayan rabuwansu taketa tunanin had'uwansu na yau,taji dad'i sosai dataga yana bada sadakannan,gashi handsome guy musamman brawn eye nashi,sedai ta lura baya sonyin dariya sam.

Manosh ne a palo da mum nashi da kuma miher yana cewa mum jibi zan tafi ABUJA saboda aikana da oganmu yayi kuma zan kai 1week kafin na dawo,mum tace to Allah ya taimaka Allah yakare,yace ameen se miher tajiyo wayanta na k'ara a cikin d'aki da sairi ta mik'e manosh yana binta da kallo yace mum dama akwai wata yarinya dana ganine shine nake so asani a addu'a in alkhairine to Alah ya tabbatar,dad'i sosai mum taji tace to Alhamdulillah gaskya naji dad'i sosai Allahya tabbatar da alkhairi lallai mahaifinka zaiyi farin ciki dajin hakan. Manosh yace amin mum nagode nizan fita,tace to Allah ya kare,yace amin sannan ya fice tare da gads nashi basu tsaya ko inaba se hospital d'inda muhammad yake aiki. A office ya samu muhammad bayan sun gaisa yace yane ina zakaje haka,manosh yace inaso kumin rakiyane gun surukina,dariya muh'd yayi yace da wuri haka,manosh yace banbi takan marwanba dan nasan bayi da lokaci a yanzu shine kake min tsiya,muh'd yace ai nima aiki nakeyi sedai ka nemo naji nasan "he's free",manosh yace wlh zan maka rashin mutunci ka tashi mana,tofa price da zafinka irin na sojoji muje kar tsumin naka ya tashi yanzu ka sani tsallen kwad'o,dariya manosh yayi sannan muh'd yace bari nayiwa nurse d'incan magana zan sameka a waje. Bayan muh'd ya fitone yace to kana nufin inbar motana kenan,manosh yace eh sannan suka wuce NNPC suka d'auki muhsin dan shine accounta general agun yake aiki. Mota uku ce se kuma majid suka d'auka a gida amma banda marwan shi banker ne sam babu lokaci, dan haka suka sallami mota d'aya suka tafi da guda 2.
Shidai wannan driver'n dayakai maryam shine yake musu jagoro har suka isa,cikin sa'a kuwa shagon a bud'e yake maryam ce a ciki tanata fesawa flowers d'in ruwa tana sanye da toyobo himar milk colour dogone har k'asa kuma mai hannu bakama iya ganin kayan da yake jikinta. Da sauri ta fito dan a tunaninta flower aka zo saya,ahankali suke fitowa majid ne ya fara fitowa tare dayin sallama sannan suma suka fito da irin sarin indian nan na maza jajaye se binsu da kallo takeyi harta hango manosh wana shi farin sarine a jikinsa duk wanda ya gansu dole su burgeshi. D'an murmushi kad'an tayi tare da amsa sallamar majid tace sannunku,majid yace yawwa,setace ina kwananku,suka amsa lfy amma manosh bai amsaba kallonta kawai yakeyi,bayan sun gaisane tace lfy dai ko,muhsin yace lfy lau munzo sayan flower ne,tace flower kuma ai naga kuna tare damai sayarwan,muh'd yace eh hakane amma mu naki mukeso,murmushi tayi wanda yake k'ara mata kyau batare datace komaiba,majid yace zan iya sanin sunanki dan nidai sunana majid,tace ni kuma sunana MARYAM amma auntyn yara akekirana,majid yace wow maryam babban suna,muhsin yace lallai yanzu mun zama 7 emms kenan,bata gane maganan muhsinba amma setayi shuru,muhammad yace meyasa ake kiranki da auntyn yara,tace yarane suka samin sunan,majid yace alamu ya nuna kina son yara kenan,murmushi tayi tace eh,majid yace munzo gurin mahaifinkine,tace ok yaje gida amma inaga yana hanyan zuwa nan. Muhsin yace nidai sunana muhsin,wannan kuma muh'd seya nuna manosh dayake tsaye yana waya da miher tana cewa wato bro shine ka tafi ko sallama babuko,yace wannankuma sedai ya gaya miki da bakinsa,murmushi tayi tace lallai fa dukknku "emms" muhsin yace eh shiyasa nace yanzumun zama 7 emms kenan akwai d'ayanmu shi bai samu zuwaba sannan akwai k'anwarmu ita M ce. Dariya tayi wanda ya baiyana fararen hakwaranta tace masha Allah,manosh ya gama waya yana binta da kallo yace ni ai bata gaisheniba bare in gaya mata sunana,kanta ta kawar gefe tana mirmushi tace ina kwana,yace seda na rok'a,shuru tayi ta rasa me zatace,majid yace tunda dai ta gaisheka ai shikenan,yace to lfy ya kike,tace fy lau kodai zaku k'arasa ne naga har yanzu bai dawoba wata k'ila akan yanya kuke,muhammad yace ta ina gidan yake,tace hanyan nan dai zaku mik'e duk wanda kuka gani a hanya ku tambayeshi gidansu auntyn yara za'a nuna muku,majid yace to mun gode amma ke kad'ai anan bakya tsoro,tace tsoro kuma aiba komai tana murmushi,muhsin yace to maryam auntyn yara bari muje idan muna dawowa zan sayi flower'n,dariya tayi tace to sekun dawo sannan suka shige motan shi kuwa manosh ya matso kusa da ita yana kallonta,kunya sosai taji tace kai bazaka tafi bane,yace zan tafi amma inaso in miki tambaya kafin in tafi,tace to ina jinka amma kanta na kallon wani gurn,yace akwai wanda yayi sallama agidanku akankine? Shuru tayi tare da kallonshi cikin kunya tace a'a amma ban saniba ko tagun babana,ahankali yake maganan yace akwai wanda yake zuwa gunkine? Tayi saurin mayar da kanta gefe tace a'a,murmushi yayi yace Alhamdulillah nagode AUNT semun juyo,shuru tayi batace komaiba ya wuce ya shiga mota suka tafi tanata binsu da kallo tana jin farin ciki a ranta kome dalili oho.

Har k'ofar gidan aka kaisu tare dayin sallama da Alhaji muh'd ATTAH. Ya fito yaga dai bak'ine dan baisansuba,da sauri suka sunkuya dan gaishesa,amma dayake mahaifinnata mai ilimin addinene seyace a'a a'a karku sunkuyamin wlh ku mik'e dan Allah,dad'i sosai sukaji azuciyarsu kuwa sukace lallai akwai SUNNAH agidannan,bayan sun mik'e yace to bisimillah ku shigo,suna biye dashi a baya har palonshi,inda ya musu nuni da kujera suka zauna sannan suka gaggaisa. Mahaifin maryam yace sedai ban ganekuba wlh, wani yarone ya shigo da sallama tare da kawo musu FARO WATER mai sanyi yana ajiyewa tare dayin gaisuwa ya fita. Muhammad yace eh baba abokinmune yazo neman izini akan maryam, baba yace Allahu Akbar ayya kuma sam maryam bata gaya min zaku zoba wlh,muh'd yace eh gaskya ita kanta bata sanmuba muna dai ganintane se mukayi tambaya akanta shine shine mukazo amma dai sun tab'a had'uwa dashi abokinmu. Baba yace Allah sarki toba damuwa an muku izini zaku iya zuwa a nan kuke ne? Muh'd yace eh muna nan a cikin jimeta tare da iyayenmu, ni sunana muh'd wannan majid,wannan muhsin sannan abokinmu kuma muh'd manosh. Baba yace to alhamdulillah bakomai Allah ya tabbatar da alkhairi,suka amsa da amin baba mun gode sosai, sannan ya tashi ya shiga cikin gida gun maman maryam ya gaya mata cewa tazo su gaisa,himar tasa baba yana gaba ta tsuguna daga waje shikuwa baba ya shiga cikin palon yace ga mahaifiyarta ku gaisa,sunkuyar da kai sukayi k'asa dukkansu sukace ina kwana mama,tace lfy kun zo lf,sukace lfy lau,tace to madallah sannunku da zuwa,sukace sannu mama sanna ta shige ciki bayare dasun gantaba. Majid da muhsin suka d'auki ruwan sukace to baba mu zamu tafi,baba yace to madallah mun gode sosai Allah ya kiyaye hanya kugaida gida,suka ce amin baba sannan suka fito baba ya bisu har kofar gida sannan ya koma ciki. Ajiyar zuciya manosh ya sauke suka kalleshi suna murmushi angon maryam,dariya yayi sannan yace majid kira mana yaran can mana,take sukazo muhsin ya bud'e but d'in mota yara suka dinga shiga da kayayyaki gidansu maryam. Bayan sun gamane baba ya fito yace haba ku kuwa harda d'awainiya haka to Allah ya saka da alkhairi mungode,sukace bakomai baba sannan baba ya koma gida,yaran kuwa kud'i majid ya rarraba musu naira d'ari d'ari sabbi se godiya sukeyi da murna sannan suka tafi.

Auntyn yara kuwa shuru taga baba bai dawoba bare kuma su majid,can seta hango motarsu na zuwa. Bayan sun isone se muhsin ya fito yace to ina flower nawa,tace wanne kake so,ya nuna wani yace wancan,anitse taje ta kawo mishi,yace nawane,tace 500 ne,yace to abani guda 2,nan ta sake kawo mishi,daidai lokacin suma suka fito,se muhsin ya karb'a tare da bata 1000,ta karb'a tace tona gode da ciniki,yace bakomainima na gode da sayarwa,dariya tayi,muh'd yace mun godefa auntyn yara ko kuma ince auntynmu mu zamu wuce toh,tace bakomai to Allah ya kiyaye hanya,sukace ameen se muhsin ya mik'awa manosh flower d'aya ya karb'a yana kallon muhsin d'in,sannan ya mik'awa maryam d'ayan amma bata karb'aba tace ya kuma kake bani,yace ka'rbi se in gaya miki,bamusu ta k'arba yace to dukkanku inaso ku shinshini flower'n sannan ya shige mota suka barsu su biyu rik'e da flower. Manosh yakai hancinsa kan flower'n uana kallonta kefa,murmushi tayi tare dakai flower'n kusa da hancinta tace nidai banji komaiba,manosh yace toni naji,tace me kenan,yace sosayyarki tare da ajiye mata flower'n yana murmushi yace ina wayarki? Agefenta ya hango INFINIX HOTNOTE ya d'auka yasa number'nshi yayi flashing wayanshi sannan ya ajiue mata wayan yace sekin jini AUNT. Murmushi kawai takeyi tana rik'e da flowern,suka sauke glass d'in motan tare da cewa byee AUNT, murmushi sosai takeyi tace tona gode,kamar had'in baki sukace karki mana godiya,idan kin samu hali ki taimaki mutum UKU suma kuma kice su taimakawa wasu UKUN,suna mata murmushi sosai itama haka,shi kuwa manosh hannu ya d'aga mata batasan lokacin data d'aga masa nataba suka tafi.

"Wooow so sweet" ni kaina SAD-NAS sun burgeni bare kuma FANS...
[7:07am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas


9-10 maryam ta tsincin kanta dabin motansu da kallo tana murmushi tare da ajiye flowern hannunta tace kenan neman izini sukaje gurin baba akai?

Manosh kuwa murmushi da jin dad'i kawai yakeyi su majid sunata yaba kyawu da nutsuwa irinna maryam,muhsin yace gaskya abokina kayi sa'a dan wlh ganin maryam yafi jinta. Muh'd yace sosai kuwa muma dai Allah yasa mu samu k'awayenta,dariya manosh yayi daidai nan wayansa ta fara ringing,majid yace kodai maryam d'ince,manosh yace haba kai kuwa meka d'auketa kenan 'yar gaggawa? Majid yace no nidai banceba,manosh yasa wayan a kunne tareda cewa hello abokina ya akayine,marwan yace lbr zaku bani mana mun samu karb'uwa kuwa,manosh yayi dariya yace kaida ka sani kuma,marwan yace aaah "congrats dude" kadai samomin friend nata ko,dariya sukayi dayake suna iya jiyo abinda marwan yake cewa,muhsin yace muma da mukaje bamu samuba bare kuma kai,dariya marwan yayi yace to ai abin rabone,muh'd yace sosai to har yanzu dai rabon namu bai rantseba tukunna kaga majid dayake d'an iskane se dariya yake mana waishi ai yana da miher,marwan yace rabu dashi ba laifinshibane captain ne ya b'atashi ai tunda yace ya bashi miher tun da wuri,any way se kun iso ya banji muhsin bane,muhsin yace abokina aure kawai nakeso nima shiyasa ka jini silent,dariya sukeyi sannan marwan ya katse wayar yana dariya.

Mahaifin maryam seda ya rabawa makwabta abin alkhairin dasu manosh suka kai,sannan ya rabawa yaran da suka shiga da kayan sannan ya koma shop d'inna.
"Maryam tace sannu baba,yace sannu 'yar baba bak'in da sukazone yasa banzo da wuriba sunzo neman izinine akanki. Shuru maryam tayi dan kunya daya kamata tace baba zan iya tfy gida,yace eh jeki,sannan ta bashi kud'in cinikin seta tafi tana mai jin kunya.
Koda ta is??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a gida mahaifiyarta ta gaya mata komai tare da alkhairin da suka kawo. Murmushi kawai tayi tana bin kayan da kallo,wayar tace ta soma ringing,koda ta duba number'n manosh ne seta tashi ta shige d'akinta tare da d'aukan wayan tace assalamu alaikum,wa'alaikumus salam AUNT,murmushi tayi dan tasan shine setace na'am kun isa lfy,yace lfy lau ya muka barki,tace lfy mun godefa Allah ya saka da alkhairi,yace amin,tace inasu majid,yace duk sun wuce gurin aiki dama akan aikinsu na tattarosu,tace eyyah,yace bazaki tambayeni sunanaba,murmushi tayi tace to ina sauraro,yace a'a ai baki tambayeniba,shuru tayi tana murmushi a hankali,manosh ya sake kiran sunanta AUNT,tace na'am ina sauraon sunanka,yace sunana maryam,dariya tayi wanda shima ya sashi dariyan sannan yace eh mana,tace maryam ai sunan mata ne bana mazaba,yace sunana muh'd manosh mu biyune agun iyayenmu nida k'anwata miher,sannan ni SOJA ne amma friends d'ina suna kirana da prince wannan shine lbrna a tak'aice. Dariya sosai maryam tayi dan yadda yayi bayaninshi da sauri sauri tace masha Allah yanzu kai d'in soja ne,yace banyi kama da sojaba ko,tace gaskya kam,yayi murmushi yace to ai k'aramin sojane ni ba babba ba shiyasa,murmushi tayi kawai batace komaiba,yace aunt ya kikayi shuru kona dameki ne,tace a'a bakomai,yace to kefa,tace sunana maruam ni kad'aice agun iyayena na gama secondary skul muna jiran result,manosh yace ok to Allah yasa muga alkhairi,tace ameen,yace suwaye friends naki na kusa, tace rashida muh'd,amina babale,samira jauro da zahida abba,ya e duk a girei suke,tace rashida da sameera suna gireizahida tana jimeta,amina kuma tana yola. Yace ok kuma ku 5 kenan,tace eh,yace to duk ki gaishe min dasu pls,tace zasuji nagode,yace ok byee,tace byee tare da katse wayan ta sauke wani ajiyar zuciya tana murmushi.

Miher taji dai bro manosh yana waya kuma tasan da mace yakeyi,abin ya dameta sosai seta kira LUBNA a awaya tace k'awata gaskya kina sanya dewa kuma wlh na hango matsala,lubna tace kamar ya matsala,miher tace ina tunanin bro manosh ya fad'a soyayya da wata dan kamar naji suna waya ya kamata kiyi mishi magana yanzu gaskya kar asamu matsala. Hankalin lubna ya tashi tace da gaske kikeyi miher,miher tace wlh kuwa,lubna tace pls miher ki tambayi majid tunda saurayinkine pls kinsan babu yadda zanyi in tuntub'i bro marwqn da irin wannan zancen amma tunda ke budurwan majid ne pls miher,miher tace bakomai zan tambayeshi amma dukda haka "you have to do somethin friend" lubna tace sosai ma kuwa zanyi nagode byee.
Bayan sun gama wayane lubna ta ciza baki tace ina wlh bazai tab'a yuwaba,duk wanda tayi k'ok'arin shiga tsakanina da manosh wlh sena d'auki mummunan mataki a kanta ko 'yar gidan uban wayece ita.

Yaune manosh zai tafi abuja yana sanye da kakin sojojinshi yayi matuk'ar kyau ya fito da 'ayar k'aramar kit d'inshi a hannu ga kuma bindiga a aljihunsa yace mum zan wuce a mana addu'a,tace to Allah ya kare ka kula da ibada sannan kaji tsoron Allah aduk inda kake,miher da take gefe tace mum kullum sekin gaya mishi haka aiya zauna a kanshi,tace to ai addu'ace kuma d'an adam azijine,manosh yace amin mum rabu da ita yarantace,miher tace wlh bro niba yarinya bace "am a big gal"dariya sukayi suka rakoshi har waje driver yaja suka tafi air port. A hanyane ya kira maryam yace aunt kin tashi lfy,tace lfy lau ya mutanen gida,yace lfyansu lau yanzu na barosu ina hanya zan tafi abuja sannan zanyi 1week kafin in dawo karkiga shuru banzoba,tace ok Allah ya kiyaye hanya Allah kuma ya bada sa'an tfy,yace ameen aunt thankyou so much,tace wlcum,yace ki kulamin da kanki kinji,tace to nagode,yace ok byee sannan ya katse wayar.
Ita kuwa maryam seta tsinci kanta dason sake ganinshi dan ad'an lokaci kad'an da had'uwansu amma se taji tana sonshi sosai a ranta,dan tunda take babu wanda ya tab'a zuwa yace yana sonta sedai taji yara suna cewa aunty ai wane yace mana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login