Showing 30001 words to 33000 words out of 72993 words

Chapter 11 - Auntyn Yara Book1 Complete Hausa Novels By Sadnas.doc

Sadnas   

06 Sep 2025

874

lallai yasan za'azo nemanshi shiyasa ya gudu,manosh yace ina kenan kake tunanin zai tafi?yace numan zai koma inda yakai maryam,wanine yazo wucewa manosh yace kai ina wanda yake zama anan?mutumin yace d'azu ya fita da kayansa dewa ya zuba a mota da gudu yabar nan. Manosh yace muje yusuf,nan danan sukabi bayan saddam gudu sosai manosh yakeyi da mota.

Basu maryam kad'aiba,harta ni *sad-nas* seda nace *alhamdulillah* wani irin ajiyar zuciya maryam ta sauke tare da k'arayin godiya wa ALLAH sannan suka fito. Lubna tace kwad'o fa naji sunce ansa ajikin k'ofan to taya za'ayi mufita kenan,maryam ma abun ya bata mamaki tace towaya mana kwad'o kenan?
Gwada bud'e kofar tayi cikin mamaki taga kofan ya bud'u,kallon juna sukatsayiyi ita da lubna dukkansu mamakine ya bayya a fuskarsu,maryam tace shikenan gaskya muyi hanzarin barin nan,dan nima su yah ibrahim suna jirana. Lubna ta rik'o hannunta tace kije maryam niki barni anan dan bazan koma gidaba wlh bro marwan zai kasheni. Maryam tace ki dena fad'a haka lubna aiba a son ranki bane fyad'e aka miki kawai ki fad'a musu gaskya,lubana tace wlh na gwammace insha wani abun in mutu amma sam nikam bazan iya komawa gidaba maryam bazaki ganebane,ba'asan ina da alak'a da saddamba,idan kuma aka sani to za'amin kallon mutumiyar banza za'ace dama mun saba iskanci dashine baza'a tab'a uarda fyad'e yaminba wlh nan ta fashe da kuka sosai..

Tausayinta ya kama maryam tace toke meya had'aki dashi lubna?
Lubna tace wlh kawai yaketa bibiyata waishi yana sona,ni kuma danaga 'yan shaye shayene se tsoro ya kamani dan kar sumin wani abu shiyasa na tsaya muka dai gaisa duk dan mu rabu lfy,so dewa idan maza suna takuramin saddam shine mai taimakona dayake anganshi ana tsoronshi dan ansan zai iyayin kissa ma indai a kainane,kuma babu wanda yasanshi a gidanmu hakan ya bani daman sakewa dashi dan taimakona da yakeyi,nima ina mishi kyautan kud'i sosai amma sam baya so sabodashi wai sona yakeyi muyi aure shinefa naketa binsa a hankali danmu rabu lfy. Lokacin dana tabbatar da kece macen da price manosh yake k'auna se kishi ya kamani saboda yadda na dad'e ina k'aunarsa shinefa na biya saddam kud'i harda kukata na gaya mishi k'arya tare da b'ataki agunshi,shi kuwa yace seyayi maganinki shine ya d'aukeki dukda taimakona amma gashi gashi tun ina duniya Allah yayi miki sakayya maryam dan Allah kiyi hakuri ki yafemin.
Maryam ma kwalla takeyi dan yadda lubna ta bata tausayi,rungume juna sukayi lubna tanata kwalla ga azaba da takeji a jikinta. Dukkansu se suka tsinci kansu cikin nishad'i alokacin da suke rungume da junansu,harta kukan da lubna takeyi seta denashi wanda basan dalilin tsayawanshiba. Maryam ta saketa tace karki damu lubna nayafe miki har cikin ziciyata wlh fatana shine Allah yasa kar saddam ya ambaci sunanki idan an kamashi,idan kina da number'n shi kiyi sauri ki kirashi. Haka kuwa akayi number biyu duk a kashe suke seta sake kiran d'ayan liyin cikin sa'a ta shiga,ya d'auka tare da cewa hello my luv kiyi hakuri da abinda na miki kece kika tunzurani alokacin danaga kyakkyawan suranki kuwa sena sake haukacewa naji bazan iya kyalekiba,wlh dama d'aukeki nayi muka tafi kawai muci gaba da zamammu dan gaskya baiwarki daban bby kin had'u sosai. Zazzafar hawayene suke zubowa daga idanunta tace saddam ka cuceni ka cuci rayuwata wlh bazan tab'a yafe makaba mugu azzalimi d'an iska Allah ya tona asirinka...kuka ma tsanani ta fashe dashi,shi kuwa saddam se dariya yakeyi tare da cewa Allah sarki lubna bby kiyi hakuri kinji,koda an kamani nayi miki alk'awarin bazan tab'a anbatar sunanki a cikiba koda kuwa kasheni za'ayi tunda dama bani da iyaye shikenan nima sena bisu,ki kwantar da hankalinki kuma ki goge nanmaba a wayanki karki sake kirana dannima yanzu zan yarda sim d'in ne ki kula da kanki kuma ki yafemin my luv byeee.

Kukan taci gabadayi,maryam ta rungumeta tanata rarrashinta. Aduk lokacin da maryam ta rungumeta setaji wani sanyi a ranta har bata so maryam ta saketa wlh,maryam tace lubna ya isa haka miyi mubar nan muje gida ki gayawa mahaifiyar komai karki b'oye mata,lubna tace wlh bazan iyaba maryam sedai inbar garinnan inje wani gurin,maryam tace ina kuma zakije bayan ga iyayenki anan lubna dolene mahaifiyarki ta sani wannan ba maganene da zamuyi shuru akaiba,saboda idan asirinmu bai tonu yau ba,tofa tuabbas zai tonu watara wanda hakan zaifi miki ciwo da zafi ina nufin kamar idan kikayi aure dolene mijin daya aureki zansan cewa keba budurwa bace wanda hakan zaija miki babban matsala wlh,amma idan kika gayawa mahaifiyar komai zaizo da sauki insha Allah.
Lubna dai tak'i yadda da shawaran maryam,haka maryam ta gaji ta rabu da ita tace to shikenan Allah yasa karki d'auki ciki lubna,dan inhar kin d'auki ciki tofa nida kaina zanje har gidanku in gayawa iyauenki komai bazan b'oyeba,amma inhar baki da ciki toni na cire hannuna akai sedai kiyi k'okari ki dinga shiga cikin ruwan zafi safe da yamma insan samunema ki nemi ganyen magarya ki tafasashi da jan kanwa kina zama a ciki insha ALLAH zaki had'e amma fa bazaki koma kamar budurwaba sedai kuma zaki had'u sosai. Lubna taji dad'i sosai tace nagode sosai maryam gaskya keta dabance wlh nagode sosai,maryam tayi murmushi tace karki min godiya lubna,amaimakon godiyan da zakimin,inaso idan kin samu dama toki taimaki mutum uku suma kuma kice su taimakawa wasu ukun. Murmushi lubna tayi tare da sake rungume junansu suna masu matuk'ar farin ciki dukkansu.
Ahankali suka fito babu kowa agun dan haka sukayi sauri suka k'araso bakin titi suka suka sami nape se gidansu lubna.
Suna tafya lubna daga gani kasan tfyarta ya canja dukda dagewa da takeyi dan kar'a gane amma dole duk wanda ya ganta zesan akwai wani abu. Sun isa palo inda taga mahaifiyarta na zaune tana kallo,sallamarsu shiya juyo da fiskanta gunsu...
Maryam tace hajiya khadeeja,hajiya khadeeja tace maryam tare da mik'ewa ta rungumeta sema a lokacin ta lura da lubna a gefe data tsaya tana kallonsu. Mum d'in lubna ta saki maryam tare da k'are musu kallo dukkansu,suma kallonta sukeyi dan sun tsorata sosai da irin kallon da take musu. Maryam tace hajiya dama lubna 'yarkice,kuma kece mum d'in marwan? Hajiya jikinta a sanyaye tace eh nice dama kunsan junane keda lubna? Tace a'a ta had'u da tsautsayine machine ne ya bugeta ni kuma ina sayya lokacin senaji ta fad'o ta jikina,to dai naga ta k'asa mik'ewa shine na rakota gida. Mum d'in lubna tace subhanalillah tare da zuwa gun lubna tanata dudduba jikinta tana mata sannu to Allah ya kare na gaba yanzu inane yake miki ciwo? Lubna tace k'afatace mum da k'yar nake takawa,tace sannu ai dole muje a duba miki kafan agun masu duban kafa koma kinyi targad'e waya sani. Shuru lubna tayi yayinda mum ta zaunar da ita tace sannu maryam ki zauna bari in kawo miki abun sha,ashe kuma haka ya faru,maryam tace eh wlh,mum tace to Allah ya kare na gaba Allah ya toni asirinsu,maryam ta kalli lubna tace ameen sannan mum ta wuce.
Maryam tace nizan tafi idan kinga period naki seki gaya min,koma dai me ake ciki zamuyi waya dan yanzu kin zama k'awata lubna,murmushi tayi tace nagode maryam kin zama kamar 'yar'uwata na jini wlh bazan tab'a mantawa dakeba,wlh a tsorace nake har yanzu,maryam tace ki dena tsoro mudai jira tukunna nayi miki alk'awarin zanyita tayaki da addu'a Allah ya bamu mafita akan wannan lamarin,lubna tace ameen. Sega mum ta shigo da abin tab'awa kad'an maryam taci tace nizan tafi hajiya nagode sosai da hidimar da kikayi a gidanmu,mum tace bakomai maryam kigaida mutanen gidan dukka,tace zasuji,mum tace bari insa driver ya maidake,tace a'a wlh dasu yah ibrahim mukazo idan mun gama zaidawo ya d'aukemu yanzu kasuwan zan koma,tace eh to bari drivern ya maidake kasuwan,tace to hajiya nagode sannan ta kalli lubna tace to Allah ya sauwaka ya kiyaye nagaba,lubna tace ameen nagode.
Mum d'in lubna ta rakata hargun mota sannan suka tafi. Hankalin mum d'in lubna a tashe tare da tunani mai zurfi a cikin ranta ta shige gun lubna tana mata sannu.

Maryam se taji dad'i sosai a ranta tace dama hajiyace mahaifiyar marwan da lubna,gaskya sunyi sa'an iyaye domin hajiya khadija macece mai kirki sosai sannan tason maryam ita. Wayan maryam ne ya far k'ara ta duba taga samira ce,tace hello samira kuyi hakuri ganinan na kusa isowa,samira tace okey. Bayan ta ajiyene call d'in manosh ya shigo ta d'auka tare dayin sallama,ya amsa sannan yace Alhamdulillah apple mun kama saddam,k'irjinta ya buga sosai tace haba peach,yace wlh kuwa yana can gurin horo,tace tokun saki wannan mutumin,yace karki damu bazan cutar dashiba,gobe zan sakeshi insah Allah,tace to nagode sosai Allah ya saka da alkhairi,yace ameen apple kin gama sayayyanne? Tace eh nagama amma yah ibrahimma ya shigo jimetan kawai zamu koma tare,yace ok toshikenan ki gaishesu senazo kinji,tace yaushe zakazo,yace sedai zuwa gobe insha Allah,tace har gobe kwana d'aya fa kenan ban gankaba,dad'i yaji data nuna damuwarta agareshi,yace kinaso inzone,tace eh amma bakomai yau da goben duk d'ayane,yace to lnagode zanzo gobe da safe kinji,tace Allah ya kaimu,yace ameen aunt ki gayamin wani abu,tace *i luv u* tare da katse wayar dan kunya dataji. Dariya yaketayi tare da sauke wani ajiyar zuciya yace *i luv u 2 apple* yusuf yace tofa ai bata jikaba sedai ka sake kiranta,manosh yayi murmushi yace waya gayamaka taji mana,dariya sukayi tare da wucewa..

Maryam tayiwa drivern godiya ta tafi gunsu rash tayi d'an sayayya kad'an sannan suka kira yah ibrahim yazo suka wuce gida a motar da manosh ya sayawa maryam.
Kowa gida ya wuce maryam taje ta watsa ruwa tare da alwala tayi sallah tayi addu'oi sosai. Abdallah ne ya shigo sunata hira da auntyn shi har magrif sannan ya tafi masallaci.
Anata zuwa yiwa maryam da iyayenta barka harda malamai manya. Koda yaushe suna waya da lubna tana tambayarta akan shiga ruwa zafi,tace eh tana shiga sosai dan yanzu kamma tfya normal takeyi. Dad'i sosai maryam taji kuma sam bata gayawa kowa komai akan lubna,hakama shi saddam duk azabar da ake gana mishi yace shine kawai yayi ra'ayin sace maryam wabu wanda ya sashi,hakan yasa suka kaishi gidan yari aka kulleshi acan,shi kuwa d'ayan tuni an sakeshi har gidansu maryam yazo yayita mata godiya tare da tabbatar mata da cewa daga yau ya zama mutumin kirki ya dena d'aukan abun tsakaninshi da mutane sedai taimako. Dad'i maryam taji sosai tare dayiwa Allah godiya...

***
Bayan wata d'aya lubna taga period nata yazo kamar dai yadda ta saba. Murna sosai tayi tare dayiwa Allah godiya sannan ta kira maryam ta gaya mata komai, murna sosai itama tayi tace shikenan lubna nagode,lubna tace nice da godiya damuwa d'ayane yanzu shine idan nayi aure,maryam tace inga kawai ki gayawa mahaifiyarki danki samu mafita,lubna tace sam bazata fad'aba,maryam tace to shikenan duk yadda ake ciki zamuyi waya se'anjuma.

Maryam tana kwance a d'akinta wajen 10:pm seta kira yah ibrahim a waya,yayi mamakin ganin kiranta amma seya d'auka yace hello aunty lfy dai koh?
Tace lfy lau kayi hakuri na tasheka,yace bakomai akwai wani abune? Tace dama shawara nake nema agunka akan wani abu daya dameni wanda bazan iya gayawa koda mahaifiyata bane bare kuma wasu amma haka kawai naji zuciyata ta raya min cewa na gaya maka yah ibrahim. Yace to aunty ina sauraronki,tace yah ibrahim wata baiwar Allah ne ta had'u da jarabawa kuma se muka had'u da ita a wannan lokacin da abun ya sameta.
Nan dai maryam ta kwashe lbrn da lubna ta bata tun farkon had'uwansu da saddam har zuwa fyad'en daya mata ta gaya mishi tas sedai bata gayami ko wacece yarinyarba kuma bata gayamishi abunda lubna da saddam suka mataba kawai dai lbrn shak'uwar saddam da lubna ta bashi batare data gaya mishi sunayensuba.
Shuru ibrahim yayi dan yama rasa mezaice,yace amma meyasa tak'i sanar da iyayenta,aunty wannan babban maganace wanda dole se manyanta sunsan dashi,dan haka kigaya mata ta cire wani tsoro a ranta ta sanar da iyayenta tunda ba laifinta bane wannan shine kawai shawaran da zakibata.
Maryam tace yah ibrahim wlh nayi iyakan k'ok'arina dan in fahimtar da ita amma seta nunamin cewa garata gudu koma ta kashe kanta akan ta sanar dasu. Yah ibrahim yace aunty wanene wannan yarinyar? Tace kayi hakuri yah ibrahim bazan iya gaya makaba domin nayi mata alk'arin zan b'oye sirrinta. Shuru yayi yace to aunty gaskya shawaran da zan iya bata kenan dan shine kad'ai mafita agareta. Maryam tayi shuru tace yah ibrahim zan gayamaka kowacece amma inhar zaka taimaketa,yace wace irin taimako kuma ni zanyi mata aunty? Maryam ta gyara murya tace yah ibrahim taimakon da nakeso kamin shine ka amince zaka aureta.
Shuru yayi tare dayin murmushi yace in auretafa kikace aunty? Tace kwarai yah ibrahim,a rayuwata babu wanda nake k'auna da burin ya zamanto mijina irinka yah ibrahim,jira nakeyi ka dawo daga bautar k'asa se'in sanar dasu baba, amma muna namu Allah yana nashi segashi su manosh sunje gun baba batare dana saniba sun nemi izini kuma baba ya amince musu,hakan yasa na amincewa manosh na kuma cigaba da addu'a wanda hakan yasa naji ina son manosh har cikin raina kai kuwa na maka matsayin " *soulmate*" d'ina, yah ibrahim wlh kaina fara so a raina kuma har gobe kai *soulmate* d'inane...
Maryam bata k'arasa maganaba ta fara kwallah,yah ibrahim kuwa wani zazzafar k'aunarta yake shigansa,yace aunty kidena pls ya isa haka kinji? Tace yah ibrahim dan Allah ka amincewa buk'atata wlh yarinyar tanada hankali gata fara ce kyakkyawace sosai bugu da k'ari zaka ilmartar da ita sosai tafannin addininmu. Yace shikenan aunty na amince koda mummunace ita tunda dai ke kika zab'amin ita na yarda zan aureta kidena kuka kinji aunty, "i will do anything just for you aunty" shikenan? Bazan iya misalta muku farincikin da maryam ta shigaba,bata san lokacin datace "i love you so much uncle" dad'i yaji yace to wacece ita yarinyar? Tace sunanta lubna k'anwar marwan ne wanda zai auri rashida. Mamaki sosai yayi yace to shikenan ki kwanta kiyi bacci zanzo da safe kinji,tace to nagode sosai seda safe...
[7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas

*dedicated to mace tagari*B??0so


47-48 Washe gari da safe yah ibrahim yaje suka gaisa da mama sannan sukayi hira sosai da aunty harta bashi number lubna dan dama tun a jiyan ta sanar da lubna komai,dukda dai lubna taji kunya sosai,amma setaga koba komai ai asirinta zai rufu tunda shi yah ibrahim yasan halin da ake ciki kuma ya amince zai aureta a hakan.

Lokaci yanata tfy,ibrahim da lubna suna waya sosai dan ta turo mishi da pic nata ta whatsapp shima kuma ya tura mata amma bai tab'a zuwa gidansuba. Koda yaga pic d'in lubna mamaki sosai yasha dan kawai seyaji k'aunarta na k'aruwa a cikin ranshi tare da addi'an da yakeyi akanta. Itma lubna ta yaba sosai dan yah ibrahim ba irin mazan da mata zasu k'ishi bane.
Hakanan suketa soyayyarsu,wanda har abdallah yasan lubna suna gaisawa sosai.

Ita kiwa maryam seta tsinci kanta cikin farin ciki da kwanciyan hankali mara misaltuwa.
Ranan taje jimeta aike tana cikin keke nape seta hango manosh tsaye da wata budurwa wanda sam bataga fiskartaba saboda yana tsayene dab gabanta. Kuma ta tabbatar da cewa manosh ne dan taga motarshi sannan kuma ga marwan a gefe yana tsaye rai abace,se taga manosh ya bud'ewa budurwa kofar motarshi na baya harta shiga se kuma ta sake fitowa ya bud'e mata gaba ta shiga. Maryam ta kira number manosh dan tabbatarwa,ai kuwa seta ya d'auka tare da cewa hello,tace ya kake,yace lfy lau zan kiraki anjuma kinji,tace meyasa kana wani abune? Yace eh kiyi hakuri zan kira kinji,tace ok sannan ta kashe wayar tanata binsu da kallo setaga shima ya shiga mazaunin driver yaja suka tafi yayinda marwan yake tsaye agun rai a b'ace.
Hankalin maryam ta tashi sosai ta rasa meke mata dad'i,tace wato dama da manosh yake cemin mata 2 ko 4 zaiyi kenan yana neman wata...?

Da wannan tunanin ta koma girei,bayan ta ajiye aiken da mamanta tamatane seta wuce d'aki ta kwanta har yanzu manosh bai kirataba ita kuwa ta kasa hakura seta kirashi. Hello apple kiyi hakuri wlh am busyne shiyasa ban sake kirankiba,tace busyn me kenan,yace ki bari kawai hidiman dewa pls kimin hakuri zan kira pls,tace bakomai se'anjuma,yace ok tnx luv u,shuru tayi tare da katse wayar.
Abin ya d'an dami manosh amma dayake yana da abinyi sosai sebai sake kirantaba. Har la'asar bai kiraba,ita kuwa maryam abin yana cinta sosai a rai,manosh bai kirataba harse bayan magrib yace da ita am so sorry apple zanzo bayan sallan isha kinji,shuru tayi mishi,ya sake nanata tace sekazo tare da katse wayar,sake kiranta yayi ta d'auka batare datayi magana ba,yace apple are you okey? Tace ues am fine,yace amma naji muryanki wani iri,tace bakomai sekazo...

Abun ya dami manosh sosai dan haka suna idar da sallan isha suka taho shida muh'd da marwan.
Kamar kullum muh'd da marwan sun tafi k'ofan gidansu rash da mota shi kuwa manosh suna zauren gidansu maryam inda ta shinfid'a mishi k'aramin carpet tare da kawo mishi fruit kamar yadda ta saba dantasan yana son fruit sosai shiyasama bata rabuwa dashi a gida.
Manosh yaga canji sosai tattare da ita hakan yasa ya ajiye wayarsa a gefe ya maida kallonshi gareta,ita kuwa kanta na kallon cikin gidansu kyakkyawar gefen fiskanta yake kallo tare da b'akin takalmin dayayiwa kafarta kyau yace apple lfy kuwa,tace lfy lau batare data kalleahiba. Yace toyana ganki haka kodai bakya jin dad'i ne,tace a'a lfyta k'alau,yace tomeyasa tunda nazo yau baki kalleniba kuma gashi sam baki sakeba kamar namiki laifi? Juyowa tayi suna kallon juna har cikin ido sannan tace kwarai kuwa kamar ka sani,seta sake mayar da kanta gefe, murmushi yayi yace pls apple ki bari fushin bai karb'ekiba wlh tomenayi nikuma yau? Ta sake kallonshi da kyau sannan ta juya,murmushin ya sakeyi yace kidena min wannan kallon kina bani tsoro wlh,shuru tayi batace komaiba,yace wai dagaske kike yine aunt,to pls ki gayamin laifina so that in nemi yafiyarki kinji,tace bakomai zan shiga gidane, yace ok to jeki mana yau harse kin nemi izinin shiga gida? Tace ina nufin zanje in kwanta bacci nakeji,shuru yayi yana kallonta cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login