Showing 57001 words to 60000 words out of 72993 words

Chapter 20 - Auntyn Yara Book1 Complete Hausa Novels By Sadnas.doc

Sadnas   

06 Sep 2025

884

gidan marwan. Nanma da kukan ta shiga gidan amma tad'an tsagaita sukadai gaisa da rashida sannan tagaida bro marwan yanata k'are mata kallo ita kuwa sam tak'i kallonsa. Rashida tace lubna yanaga idanunki sunyi jah haka? Lubna tace bakomai,yah ibrahim ne yabasu lbrn abinda ya faru,ahankali marwan ya mik'e zaune yace kunga manosh? Ibrahim ya tabbatar mishi da zance,mamaki sosai sukayi dukkansu,rashida tace Allah sarki maryam Allah ne kad'ai yasan yadda takeji acikin ranta yanzu haka,dabadan rashin lfyarkaba danaje na d'ebemata kewa dan nasan tana cikin damuwa da tunani musamman ma yau data ganshi dan tana matuk'ar k'aunar captain sosai,hawayene yakebin idanun rashida,ita kuwa lubna fita tayi da gudu tana kuka bata tsaya ko inaba se cikin mota. Da sauri rashida tabi bayanta tana tambayarta ko lfya? Shi kuwa yah ibrahim lamarin ya fara damunsa sosai. Marwan yace ibrahim ina neman wata alfarma agurinka akan lubna,dan Allah duk wani abu da zata maka kayi hakuri kamata uzuri ninasan irin k'aunar da lubna takeyiwa aunty. Ibrahim yace bakomai wlh zamu tafi,haka dai sukayi sallama suka tafi rashida dai bataji komai daga gun lubna ba.

Yah ibrahim ne da lubna kwance akan gado yana cewa haba y luv yau kwana nawa kenan rabonda wani abu ya shiga tsakanina dake? Tace to ai period nakeyi shiyasa,yace amma fa kwananki uku kenan da gama period d'in nabarki ranan jiya kuma agidansu aunty kika kwana sannan kuma yau kicemin bakya mode? Cikin sanyin murya tace dan Allah kayi hakuri wlh damuwace tamin yawa bazaka tab'a gane kainaba shiyasa nake baka hakuri idan kuma ka yarda zaka gamsu kai kad'ai shikenan bisimillah nidai bazaka samu tallafinaba yau. Ibrahim baiji dad'in kalamantaba gashi yanada bukatarta hakan yasa ya daure ya juya yayi kwanciyarsa.
Shurun dataji yayine yasa tasan cewa fushi yayi,ahankali take kiran sunanshi my luv dan Allah kayi hakuri karkayi fushi kamin uzuri tunda ban tab'a maka hakanba se yanzu banaso kayi fushi domin bana son tsinuwan Allah ya tabbata akaina kaji my luv tana rungume da bayansa ajikinta. Yace naji amma ki sakeni dan kina kara tayarmun da hankaline,bamusu ta sakeshi tare dayin godiya se wayansa ta fara ringing. Da sauri ya da'uka dan ganin mahaifin manosh ne mai kiranshi,bayan sun gaisane yake sanar dashi cewa tafiyansu india ran monday ne shida baba mama da maryam da kuma lubna,yah ibrahim yayi godiya sosai sanan ya ajiye wayar ya juyo yana kallon lubna yace tfyarmu ran monday amma banda ke,ta marairaice tace habamana my luv najifa lokacin dayacemaka da lubna saboda yasan kila zaku wuce 4month kuma dama ka'ida ba'ason miji yabar matarsa har tsawon watanni hud'u,yace to aike babu amfani zuwanki tunda kina hanani hakkina, dasauri ta rungumoshi tana dariya tace wlh nadena amma pls karka barni my luv kaga ai zan taya mama kula da aunty ko? Shima murmushi yayi sannan ya matseta ajikinshi suka fara sarrafa junansu kamar zasu had'iye junansu....
[7:14am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas

_ASSALAMU ALAIKUM masu karatu! kud'an min hakuri mana, dole kunsan babu wani abu yadayafi karfin *ALQUR'ANI* aduniyannan domin munsan cewa duk wata cuta ko damuwa da d'an adam ya tsinci kansa aciki tofa maganin matsalarshi yananan cikin *Qur'ani mai girma*. Dan haka kuyi hakuri kudena bina kuna min magana akan *prince manosh* plss,aljanu gaskyane kuma Qur'ani yana tarwatsasu har abada, masucewa sun dena karanta buk d'in tunda *manosh ya b'ace*,karku damu dole zai dawo komai jimawa???i_
*kusani kuna raina akoda yaushe a kuma duk inda kuke*B??0soB???




79-80 Bayan yah ibrahim da lubna sun samu cikakkiyar gamsuwa da junansune suka wuce toilet bayan sun tsabtace jikinsu ne se suka sake shirin kwanciya amma duk sun kasa bacci babu abinda yake musu yawo a kwakwalwa se b'acewar manosh da shukrah da sukagani d'azu agaban idanunsu kamar a fimlm.
Wannan abu ya dami mutane dewa sosai harta wanda abin ya faru aaban idanunsu sun kasa yadda da hakan ya faru dan gani sukeyi kamar amafarki. Hakan yasa akakai lbrn gidan *radio gotel* wanda basusan da faruwan abun bama tofa gashi yanzu sunji agidan radio magadai ya baza ko ina agarin *Adamawa*. Hakan yasa majid yaje gidan *TV GOTEL* akayi hira dashi inda yake cewa aabansa akayi komai ba kuma tatsuniya bace gaskyane domin abokinsune wanda kusan kowa ya sanshi tunda sojane mai kwazo sosai. Hakan yasa akayita rok'on jama'a cewa sutaimaka a addu'a akan b'acewan captain manosh,kokuwa d'aukeshi da aljana tayi tsawon wata uku kenan harda kwanakima. Wanda matarsa itace maryam muh'd attah wanda akafi sani da AUNTY'N YARA mahaddaciyar qur'ani, cikin kwanaki biyu ko ina se faman rok'on ALLAH aeyi akan manosh da kuma duk 'yan'uwa musumai da irin hakan ya shafa,domin idan idan ka shiga damuwa tofa karkayiwa kanka addu'a batare dakasa 'yan'uwankaba.
Maryam kuwa tun wannan lokacin ta sake shiga matsanancin damuwa fiye danada. ita kuwu lubna yah ibrahim yayi iyakan k'ok'arinsa dan yaji ta bakinta saboda canji dayagani tattare da ita musamman akan aunty, amma sam ta'i gaya mishi komai dan batamasan ta ina zata faraba.

Ana saura kwana uku tafiyansu aunty india,sega hajiya khadija agidan hajiya iya. Koda hajiya iya ta ganta seta fashe da kuka itama ma hajiya khadijan kukan takeyi,bayan sun gama koke kokensune hajiya khadija tace da hajiya iya dan Allah hajiya muyi k'ok'arin fad'an gaskya tunkafin su auntyn yara subar k'asar watak'ilama tfyarsu kenan bazamu sake had'uwa kuma gaskya bazan so hakanba yazama dole mufasa wannan dad'ad'd'an kwan kowama yaji warinta ban damu da abinda zai biyo bayaba nidai mu sauke wannan zunubin da muka d'aukawa kanmu. Hajiya iya tace shikenan khadija karki damu nina haddasa komai kuma zan wankeki da yardan Allah....garakam! Gara kugayawa duniya abinda kuka aikata kaka,konima zan samu lfy,juyowa sukayi sukaga marwan tsaye akansu ranshi a b'ace yake magana yanacewa wlh baki kyautaba kaka kinso kanki dewa awannan lamarin natabbata koda daddy zai zauna bashi da d'a aduniya bazai tab'a yarda da wannan abinba wannan aiba sonshi kikeba hajiya danba haa ake son mutumba,hajiya iya cikin muryan kuka tace jikana marwan bason mahaifinkane yasa nayi hakanba sedan son da nakeyiwa mahaifiyarka da kuma toshewar kwakwawa irin nawa. Marwan yace babu toshewar kwakwalwa anan kaka,domin wannan abun da kikayi se mutum mai wankakken kwakwalwane zai iya aikatashi kawaidai son zuciyane irin naki da kuma rashin tausayi,kaka matar dabasan yanda akayi ta haihubama dan tsabar azabar datasha kiduba yadda ake kwatanta rad'ad'in haihuwa wanda kema kinsan hakan tunda kin haifa amma shine kika sace mata yarinya haba kaka! Wani irin shaid'anune suka shiga kanki awannan loacin!? Mum ce ta mik'e tace marwan kayi ahankali kakarkacefa duk lalacewa. Afusace yace tabbas kakatace shiyasa nake gyara mata kuskurenta mum ba lubna da iyayenta kad'ai kuka cutaba hardani da dad! Gabad'aya kun gama b'ata mana suna mum,kuna tunanin zaku gayamusu gaskya suyi hakuri abar maganan to mum sauran jama'an garifa?? Shikenanfa sunanmu yab'aci kun cucemu kuma wannan sunan bazai tab'a gyaruwaba domin yariga dayazama tabo! Kuka sosai marwan yakeyi tare da juyawa hanyan waje yace nizanyi tfy yau nida rashida se bayan wata d'aya zamu dawo kigafarceni mum...

Hawaye yakasa tsayawa daga idanunsu dukkansu sunabinsa da kallo harya fita.
Mum tasan halin d'anta marwan sarai,sam bayason zalinci,gashi dama rashin amininsa manosh yafi komai d'aga mishi hankali,yanzu kuma gashi tasake k'ara mishi damuwa wanda har yasashi rashin lfy kuma gashi yatafi ya barta.
Rashida ce zaune ita da aunty tana gayamata irin sauyi sosai da take gani agun marwan,ko hakkin aurenta ya denabata kwata-kwata,sannan bayason duk wani magana dazata gayamishi seyace dan Allah kirabu dani. Aunty tace kiyi hakuri rash,watakila yanada damuwane kuma kinsan maza idan har sunada damuwa tofa basa buk'atar *sex* domin shi sex jindad'i da kwanciyar hankali shine ke kawosa wanda ba mijinki ne kad'aiba duk mazan duniya haka suke. Dan haka kiyi hakuri *kimishi uzuri pls?* Sannan kikai kukanki gun Allah,Allah ya daidaita al'amurorin mijikin su koma yadda suke insha Allah komai zai daidaita,kuma banaso ki sake gayamin duk wani hali dakike ciki keda mijinki domin babu wanda zai miki maganin damuwanki se ALLAH.
Rash taji dad'in kalaman maryam har cikin ranta kuma taji sanyi azuciyarta,sannan tabbas itama se yanzu take danasanin gayawa maryam sirrinta da mijinta tunda wannanma shine karo na farko dasuka fara samun matsala itadashi. Sallamar marwanne ya tsaidasu suka fito zuwa palon baba.
Marwan yace aunty zamu tafi,dan Allah ki k'ara hakuri mucigaba da addu'a insha Allah captain zai dawo garemu musammanma gun apple d'inshi da kuma abdallah alfiya. Murmushi sosai tayi dan tasan yanaso yasata farincikine,tace insha Allah kuma nagode sosai Allah ya kiyaye hanya akulamin da k'awata sosai pls,murmushi yayi na k'arfin hali yace baki da matsala indai wannanne aunty. Rash tana murmushi ta mik'e tare dacewa barinaje na d'auko jakata.
Bayan fitar tane marwan ya sunkuyar da kanshi k'asa yace aunty dan Allah kiyi hakuri da abinda zakiji bayan tfyarmu,aunty banaso ki tambayeni komai zakiji komai bayan mun tafi,kuma dan Allah kiyafi wanda suke da hannu cikin abin badanniba sedan ALLAH,shiyasa zanyi wannan tfyn saboda inaga yin hakan zaimin d'an sauk'i araina,sannan banaso kigayawa kowa abinda na gayamiki ayanzu,ki rik'eshi amatsayin irin sirrin da kika rikewa *lubna* abaya. Yana kaiwa nan ya mik'e yafita waje ita kuwa jikinta gabad'aya yayi sanyi dai-dai nan rashida ta shigo tace to aunty semunyi waya kenan,ta daure tace to Allah ya tsare Allah ya dawo daku lfy,rash tace ameen sannan suka fito waje rash ta shiga mota marwan yaja dasauri suka tafi inda akabar aunty atsaye jiki babu kwari maganganun marwan ne suketa mata yawo a kwawalwar ta...
[7:18am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas


81-82 Jiki sanyaye aunty ta koma cikin gida dama mama bata nan,dan haka ta wuce d'akinta ta kwanta tana tuno kalaman marwan. Tace me yake nufi da wad'annan kalaman nashi? Kuma me yake nufi da sirrin dana b'oyewa lubna? Kardai na fyad'en da saddam yayi mata? Towaya gaya mishi indai hakane? Duk wannan tambayoyin ita kad'ai takeyiwa kanta bayan tasan bata da amsoshinsu.
Hakan yasa tayi shuru tanata tunani,daga bisani aka kira sallah ta mik'e taje tayi alwala tayi sallah tare da addu'oi sosai kamar yadda ta saba musamman akan *peach* d'inta,sannan tayi akan maganganun marwan cewa Allah yasa taji alkhairi.

Yau asabar mum d'in manosh tazi duba aunty tare dasu abdallah da alfiya. Sunyi murna sosai da ganin juna dan sund'an juma basu had'uba,sakamakon mum d'in manos datace subar aunty ta huta sedai akan kawosu suyi kwana biyu. Sunyi kyau sosai se k'ara girma sukeyi. Abdallah yace mum wai yaushe daddy zaidawone gaskya ya dad'e sosai ni ina son ganinshi ya d'aukeni muje yawo inga sauran abokansa sojoji da wannan ogan nashi yana da kirki sosai domin yana sona,rananma yazo gidan su mum din dad yayi mana sayayya sosai kaya masu kyau yace dad namu yakusa dawowa amma gashi har yanzu shuru. Aunty ta rungume d'anta ko ince sanyi idaniyanta domin jinshi take kamar abdallah marigayi,tace kad'an k'ara hakuri kad'an kaji aiyukane suka mishi yawa amma ya kusa dawowa kaji? Alfiya kuwa fushi takeyi waisam se an kira mata dad nata sun gaisa tunda ya tafi basuyi wayaba kulum rikicinta kenan,hakan yasa aunty ta kira muhsin sakamakon yakan kwaikwayi muryan manosh wani lokaci,bayan ya d'auka da hello aunty,kawai setaji hawaye yana bin idanunta amma seta daure tace hello daddyn abdallah da alfiya,jikinshi yayi sanyi kuma yasan cewa su abdallahne suka sata kiran babansu domin sun tab'ayin hakan agaban jama'a bayan sunbar gurinne dad din manosh yace se'a dinga had'asu da muhsin ta waya tunda muryansu kusan d'ayane.
Muhsin bai iya cewa komai se tausayinta daya kamashi,tace dama ashe bakayin waya dasu abdallah ko,gaskya yanzu dai ga alfiya se fushi takeyi barina bata. Da murna ta karb'a tace daddy,kwallane ya zubo daga idanun muhsin amma seya daure yace sweetynah yakike,tace lfy lau daddy inaka shiga haka kaki dawowa nidai gasky muna so kadawo domin mu koma gidanmu da mummy kuma kaga gidansu mummyn daddy basu da swiming pool kuma inaso inyi wanka,dariya sosai muhsin yayi yace karki damu nanda wata d'aya zan dawo kinji,kidai inaso idan kikayi sallah kice Allah ya dawomin da daddyna lfy kinji,tace idan nayi zaka dawo? Yace da wurima kuwa,ai kuwa setayi murmushi tace da kana kusa dani dase mun tafa daddy,yace yanzuma zamu tafa mutafaaa,ahankali ta ajiye hannunta akan screen shima haka kamar suna kallon juna setayi dariya tace *i luv u daddy* yace *i luv u too my swthrt* sannan yace ina abdallah,tace gashi can yayi fushi wai bazaiyi magana dakaiba sedai ka dawo kuje yawo a mota,yace kie mishi yayi hakuri ya karb'i wayan,tace daddy yaqi ga mummy,yace to kicewa abdallah ina gaisheshi kuma shima yayimin addu'a zan sayo mishi mota karami wanda zaku shiga ku biyu kuma ina sonshi kinji? Tace to daddy mungode byee. Bayan alfiya ta mik'awa mummyntane setace to daddy kafa dawo dawuri dan kaga abdallah yana fushi dakai ka dinga kira ta wayan mum seku gaisa,yace insha Allah aunty,tace nagode se anjuma.
Muhsin ya sauke ajiyar zuciya tare da tausayamusu dukkansu,se kuma ya shiga tunanin lokacin da suke hira dukkansu suna cewa captain kam ai dole ya k'ara aure,seyace musu wlh apple na ita kadai ta isheshi,kuma ko wani irin rayuwa ko hali zata tsinci kanta nan gaba koda kuwa zata zama batada matancin kwata-kwata to wallahi ita kawai nakeso ba wani abuba,guys ina k'aunar apple yadda bakwa tsammani fatana mukasance tare da ita har a lahira, basan wani irin k'auna nake mataba bansan taya zan fahimtar daku akan k'aunar da nake mataba, ama dai nasan cewa bazan iya rayuwa babu *aunty ba wlh* shiyasa fatana idan mutuwa zata d'auki d'aya daga cikinmu tota d'aukemu atare da apple d'ina.
Bayan muhsin ya gama wannan tunaninne se hawaye yazo masa ido,yace Allah sarki abokina Allah yabayyana mana kai ameen.

Su alfiya yini sukayi dan sunzo yiwa aunry bye ne akan tfyarta india,sun kuma mata addu'a kamar dai yadda mum d'in manosh tagaya musu. Dakyar abdallah ya yarda yabi mum,saboda yace shisam zaibi mum nashi india yanata kuka dakyar suka tafi. Bayan tfyansu ne aunty taketa faman nata kukan inada mamanta taketa rarrashinta tare a mata nasiha kamr yadda ta saba,aunty tace mama ina iyakan k'ok'arin ganin cewa na dena,amma sam bana iyawa mama taya za'axe aljani ya d'auke d'an adam ne tayaaaa seta fashe da kuka,inda maman nata take cewa haba maryam,karki fad'i haka mana,maryam d'ina nasanta da ilimi da d'aukan kaddara maikyau ko mara kyau,dan haka kicigaba da addu'a Allah yana tare damu maryam koai zai daidaita insha Allah kiyi k'ok'ari kici wannan jarabawan maryam kinji? Tace to mama nagode da kika tunatardani amma nina kewar captain mama wlh inaso inganshi mama koda so d'ayane,itama mama seta tsinci kanta cikin hawaye sakamakon tausayin 'yarta. Amma ahakan tayita gayamata kalamai masu sanyaya zuciya harta dena kukan.
Yaune lahadi su maryam sun gaa shiri tsaf hakama su yah ibrahim da lubna.
Dama baba ya sanar dasu yah ibrahim da kuma umma mamansa cewa suzo akwai magana kamar yadda hajiya iya ta sanar dashi.
Hakama d'an nata wato mahaifin marwan harma da dad d'in manosh dayake aminaine duk aka taru agidansu *auntyn' yara* inda lubna take zaune kusada aunty tana kallon hajiya khadija da kuma hajiya iya dan taga ta ina zasu fara.
Mum d'in marwan dai kanta a sunkuye ta kasa sakewa sam dan batasan mezai biyo bayaba,duk dai ana zaune a palon baban maryam kowa kuma ya damu yasan dalilin wannan taron. Sallaman muhsin da majid da kuma muhammad ne ya katse su,bayan sun samu guri sun zauna ne aka fara gaishe gaishe,koda muhsin yace aunty ina wuni,seta amsa cikin muryan kuka saboda ta tuno da mijinta,kowa kuma yasan dalilin hakan,lubna ce tayita rarrashinta sannan hajiya iya ta d'ago kanta idonta jajur,kowa ya d'auka akan b'atan manosh ne zatayi magana,inbanda lubna datasan dalilin taron. Hajiya ta fara magana kamar hakaaaaaa...
[7:18am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas




83-84 "Bakomai yasa na had'a wannan taroba sedan wata magana mai girma ko kuma ince na taramu ananne saboda in tonawa kaina asiri akan abinda na aika".
Hawayene yasa hajiya iya tsayawa tana mai goge kwalla,inda d'an nata wato mahaifin narwan ya shiga damuwa. Hajiya iya tacigaba da magana cikin muryan kuka ta kwashe lbr tun daga farko har k'arshe kamar yadda mahaifiyar arwan ta bashi lbr dalla-dalla. Tun bata k'arasaba kowa ya kama fad'in innalillahi wa'inna ilaihirraji'un",hajiya iya tace dan Allah kuyi hakuri karkuce komai harsenaga.
Taci gaba da cewa nasan zakuji wani iri kilama bazaku yaddaba sakamakon yadda na muku bayanin amma wannan shine gaskyan lamari. Dan Allah kugafarceni kuyafemin wannan laifi mai girma dana aikatashi cikin jahilci da kuma sonkai irin nawa.....
Tunda hajiya iya ta fara magana idon aunry yake zubar da kwalla kamar pampo har kuma yanzu,nanne take tunanin kodai mafarki takeyine,amma sam ba mafarkibane wannan gaskyane,amma kuma anya abinda hajiya iya ta fad'a gaskyane? Lubna ce ta katse maryam da maganan zuci da takeyi,tace aunty kida shakku akan abinda ta fad'a domin babu k'arya ko kad'an aciki fase gaskya zallah. Shine dalilin dayasa naje gidanta nake gaya mata maganganu ranan,sakamakon bazan iya gayawa kowa abinda mahaifiyata da kuma kakata suka aikataba shiyasa na rik'e abun a raina dan banaso sunansu ya b'aci dukda dai nagane gaskyan amma hajiya khadija ta rik'e tamkar 'yar cikinta hakan yasa nayi shuru ban gayawa kowaba,sannan wannan shine dalilin dayasa bro marwan ya k'irk'iro da tfyarsa wanda ko aminansa basu san dalilin wannan tfyanba saboda kunyan abinda familynsa suka aikata baisan ta yadda zai fiskanci mutaneba.......Aunty ce tasa hannunta akan bakin lubna tana kwallah sosai idanunta sunyi jah,ta kalli hajiya khadija da hajiya iya sannan tace hajiya shin dagaskene...? Atare suka d'aga kai ma'ana ehh gaskyace" hajiya khadija ta k'ara da cewa maryam nasan bamu cancanci yafiyaba amma dan Allah kuyi hakuri wannan shine dalilin dayasa muke k'aunarki sosai aranmu nida hajiya iya,shine dalilin dayasa bamaso ace yau munganki cikin kinci dan musan bamu kyauta mikiba dan Allah alhaji kuyi hakuri mun yadda da duk wani hukunci da zaku yanke mana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login