Showing 24001 words to 27000 words out of 72993 words

Chapter 9 - Auntyn Yara Book1 Complete Hausa Novels By Sadnas.doc

Sadnas   

06 Sep 2025

886

sukaji gabansu ya fad'i atare suka hau fad'i *Hasbunallahu wani'imal wakim* suketa nanatawa...
[7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

*dedicated 2 billylosh*B???


37-38 hankalin manosh a taahe ya kalli d'aya daga cikin sojojin yace ina tausayawa duk wanda yayiwa maryam haka wlh.
Miher ce zaune ita da mum nata a palo suna jimamin abinda ya fari da maryam se wayanta ya fara k'ara da sauri ta d'aga tare da cewa hello lubna,lubna tace miher ya gida naji bro marwan yana cewa anyi kidnaping maryam d'in da bro manosh zai aura? Miher tace wlh kuwa lubna,lubna tace subbahanalillah yanzu su waye sukayi wannan aikin,miher tace wlh har yanzu dai shuru tukunna amma ansan inda maryam d'in take yanzu haka,lubna tace haba alhamdulillah a ina aka sameta,miher tace bawai an sametabane fa,andai gano inda take a *numan ne*. Lubna tace har numan aka kaita kai Allah ya tona asirinsu zanzo gobe insh Allah,to sekinzo nagode.
Koda lubna ta ajiye wayan miher se ta kira wani tace hello *saddam* ya akayi har su bro suka gane cewa maryam tana numan,aikinka baiyiba saddam domin yanzu haka su captain suna numan dan haka kuyi gaggawan d'agata daga numan ku k'ara gaba da ita zan tiro maka da kud'i yanzu a account naka saddam idan asirinmu ya toni zansha wuya agun bro marwan wlh seya kusan kasheni pls indai da gaske kana sona tokayi wani abu plss saddam. Murmushi yace karki b'ata bakinki bbynah, yanzu zamubar adamawan ma kwatakwata karki damu sweetheart zan nuna miki cewa da gaske nake k'aunarki bari na nemo wani abokina,lubna taji sanyi a ranta tace nagode sena jika.

Maryam kuwa dama ta kashe wayan gabad'aya tasa a cikin pant nata. Yadda aka ajiye mata abincin haka sukazo suka samu,yace wato bakici abincin bako,bai jira jin abinda zata ceba ya toshe mata baki da hanci da wani hankachif fari take ta mance inda take seya d'auketa cak se mota suka kama hanya,cikin ikon Allah kuwa ba'a tsaidasuba har suka bar numan.
Tfy sukeyi hankalinsu a kwance suna dariyan mugunta yana cewa *captain manosh* zanga iya kwarewarka kafin in shiga hannunka kuwa sena gama lalata budurwan naka tukunna dan nasan idan na shiga hannunka tofa tawa ta k'are shiyasa nima zanyi abinda nakeso tunda dama banida iyaye se kawai in bisu bayan na shana hhhhhhh...

Manosh se kiran line na maryam yakeyi amma shuru, seyayi tunanin kodai tana tare da mutanenne shiyasa bata bud'e wayanba. Nan dai yace bari yad'an k'ara jira. Anan ne muhsin ya kirashi yace "dude" na raba hotunanta kota ina yanzu haka ma ana haskawa a gidan *TV GOTEL* , *NTA* da kuma *ATV* duk anta haska hotunanta,manosh yace nagode abokina pls kuyita tayamu da addu'a sannan kuyita bada sadaka Allah ya bamu sa'an gano inda take,muhsin yace ka kwantar da hankalinka abokina insha Allah zamuga maryam cikin k'oshin lfy dan maryam tana da halayya masu kyau.

Iyaye maryam kuwa hankalinsu yad'an dawo jikinsu da sukaji lfyarta k'adau amma dai har'a yanzu suna cikin tashin hankali sosai. Duk girei seda akaji zance sace maryam auntyn yara,dan haka aketa addu'oi babba da yaro kai harta almajirai idan sukaji lbrn tofa suna komawa gun malaminsu suka gaya mishi,yace musu kwarai yaji a radio dan haka kota ina addu'oi maryam take samu.
Hajiya iya kuwa tafi kowa tashin hankali ana zaton,ko menene dalili oho? Kuka takeyi safe da dare tare da addu'an Allah ya baiyana maryam.
K'awayen maryam sun zama abin tausayi musamman rashida data tina kalmomin data dinga gayawa maryam ranan,dan haka ta dinga kuka tare da kewar aminiyarta. Hakama abdallah ya shiga wani hali sosai dan ganin maryam yakeyi kamar yarsa da cike ciki d'aya,yah ibrahim nema yake lallashinsa dan kowa yasan irin k'aunar da take tsakaninsu hakama ita maryam d'in tana ji da abdallah fiye da,sauran yaran.
Manosh baiga kiran maryam ba har 12:00pm dan haka yasan cewa akwai matsala,kuma shi yasan babu wadda ya gayawa cewa maryam tana numan daga iyayenshi se iyayen maryam se kuma friends nashi,dan haka abin ya dameshi sosai gashi faruq yace mishi wayan maryam a kashe yake bazai iya gane inda takeba dole se wayanta yana kunne.

Da misalin 2 na dare suka isa wani jeji tare dabi cikin jejin daba kowa se wani d'an k'aramin gini daba'a k'arasashiba nan suka tsaya suka fitar da 'yan kayayyakin da suka taho dashi suka dai kimtsa gurin se suka kwantar da ita akan bargo sannan suka zauna a gefe.
Saddam ya kira lubna yace hello bbynah mun iso lfy,tace sannu da hanya a inakuke yanzu? Yace muna jihar bauchi cikin gefe da *jejin yankari* ido lubna ta zaro tace har bauchi,yace yes bazasu tab'a tunanin zamuzo bauchiba,dad'i taji har cikin ranta tace nagode bbynah aikinka ya gyaru,murmushi yayimata yana busa sigarinshi yace bbynah gaskya bazan kyale yarinyarnanba dolene sena tab'ata fa,hankalin lubna ya tashi tace no bbynah kafa cemin ni kad'ai ce yarinyar da kake so taya za'ayi kashe min haka kuma,wato dama kana cin amanata kenan ko? Saddam yace wlh ba haka bane bby shikenan wlh bazan mata komaiba amma kinsan ked'in kince dole semunyi aure kafin muyi wani harka kuma gaskya ni a matse nake wlh,lubna ta murgud'a baki tace karka damu idan mun gama wannan aikin zakasha mamaki da irin gift d'in dazan baka wlh bbynah,nan saddam yaji dad'i yace okey my luv shikenan sekin jini,tace ok but pls karka mata komai indai har kana sona,yace wlh bazan mata komaiba karki damu bbynah.

Maryam bata farkaba har asuba,ta jita ak'asa nan ta tashi da sauri tana addu'oi tare da k'arewa gurin kallo setaji hawaye a fiskan,kukan tane ya tashi mutum guda d'aya da yake kwance daga gefe dan sauran kam duk sun shiga gari neman abinci.
A gigin baccin yazo inda take yace ke 'yanmata yane? Kallonshi takeyi tare da cewa bawan Allah inane nan kuma? Yace nan jihar bauchine ta gefen jejin yankari. *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* maryam taketa fad'i sannan tace karfe nawane yanzu? Ya duba wayanshi yace 5:30am,tace ina zan samu ruwa nayi sallah,nan ya d'auko pure water ya mik'a mata tare da ciro bindiga a aljihunsa yace kinga wannan,wlh idan kikayi wani kuskure sena pasa kanki dashi,jikinta na rawa tace to alwala kawai zanyi inyi sallah.
Komawa yayi ya kwanta ita kuwa jiki na rawa ta koma gefe tana alwala. Bayan nan ta koma cikin ginin tare da lekashi taga dai bacci na damunshi sosai,dan haka ta ciro wayanta ta kunna tare da da turawa manosh texs sannan ta kashe wayar tahau yin sallah.

Manosh daya kasayin bacci yana zaune a mota a numan seyaji texs ya shigo wayanshi,da sauri ya duba

_hello peach,sun d'aukeni daga numan zuwa jejin gefen yankari dake jihar bauchi gurin babu kyan gani a tsakiyar jeji muke cikin wani kango da babu ko rufi asaman pls peach do something ka kulamin da iyayena plss da kuma abdallah nah byeee_.....

Manosh ji yayi kamar zaiyi hauka dan yadda yakejin k'irjinji yana tafasa. Kwana d'aya kawai amma dukya fita hayyacinsa haka ya juya ya koma girei ya dad'a baiwa iyayen maryam hak'uri tare da kwantar musu da hankali,sannan yasa aka kira mishi abdallah yace kayi hakuri abdallah maryam tana cikin jarabawane amma komai zai wuce ina tabbatar maka da cewa auntynka zata dawo insha Allah kuma dukda halin da take ciki sam bata mance da kaiba tace ingaisheka abdallah. Rungume manosh abdallah yayi yana zubda kwalla shima manosh daurewa kawai yayi sannan ya kalli yah ibrahim yace ka kula dashi dan sak'on maryam kenan akanshi.
Manosh ya shige mota ya wucegida a galabaice,toilet ya shige ya watsa ruwa sannan ya fito yasa jaket maroon da black yana k'ok'arin fitowa sega mum nashi da miher,nan ya koma lallausar gadonshi *milk colour* yad'an jingina yana kallonsu.
Kuka miher ta farayi tare da ciro wayanta ta d'aukeshi hoto taje har kusa dashi tace kalli yadda ka zama fa bro, kwallan idonshi ya share tare da kamo hannun miher yace karki damu zan koma normal ne bayan na samo apple d'ina. Mum tanata kallonsu tare da tausayawa d'an nata tace Allah ya baka sa'a *son*, yace ameen mom nina tafi sena dawo,har waje miher ta bishi tanata kuka harya tafi....
[7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

*dedicated to Hasiya Ahmad & Maryam Adamu Girei* (TAHIRA)???b??.\??/\


39-40 Bayan maryam ta idar da sallah ne taketa hamman yunwa,dan tunda ta baro gida bata sake cin abinciba se ruwa data sha,gata da *ulcer*.
Lek'owa tayi taga har yanzu bacci yakeyi,dan haka taje inda yake tanata crwa 'bawan Allah3?2' ahankali ya bud'e ido tare da tasowa ya zauna! Kallon juna suka tsayayi domin sun tabbata akwai inda suka tab'a had'u dukkansu d'in. Can maryam ta tuna shine mutumin da mota ta tab'a bigeshi a hanya harta taimaka mishi yahau mashine aka kaishi hospital tabbas shine wannan. Wani sanyi taji a ranta tare dayin mirmushi tace bawan Allah dama kaine ka rabani da iyayena? Shuru yayi yana kallonta cikin mamaki yace dama kece yarinyar da aka d'auke? Kallonshi ta tsaya yi tana mamaki tare da cewa aka d'auke ko kuka d'auke bawan Allah.
Bayansa yaketa waigawa sannan ya mik'e tsaye cikin hanzari yace banina d'aukekiba abokin aikinane,maganar gaskya nidai ba mutumin kirki bane wannan ranan da muka had'u dakema sata naje nayi aketa bina tare da fasamin jiki,dak'ar nasamu na gudu shine na b'ullo ta girei har muka had'u dake kuma na miki k'arya kika tausaya min tare da taimakona.
Maryam tayi shuru tana sauraranshi tace to bawan Allah dan Allah ka gayamin abu guda d'aya wanene yasa a kamoni? Shiru yayi yace bazan gaya mikiba sedai in taimakeki in baki wayana ki kira duk wanda kike buk'ata indar har kinaga za'a iya taimaka miki,shuru maryam tayi tace to ai nabar wayata a gida ban kuma san numbern kowaba sena iyayena da k'awayena.
Shuru yayi nad'an lokaci sannan yace toki gayamin numbern iyayenki,nan ta gaya mishi numbern babanta yasa ya kirashi,bugu d'aya ya d'auka lokacin suna tare da dad d'in manosh yaje yi musu jaje. Maryam tace baba nice yanzu haka ina jihar bauchi cikin jejin dake gefen yankari,baba yace to wannan numberfa? Tace baba karka damu lfyata lau babu abinda ya sameni sedai ina jin yunwa sosai har k'irjina ya fara min ciwo,subhanallah maryam haka suka barki da yunwa dan basu da imani tun jiya? Baba sunban abinci amma bazan iya cibane ka gaida mama kuma dan Allah karka kira numbern nan domin na d'aya daga cikinsune ya taimakamin idan ka kira suka gane zasu kasheshi. Hankalin mahaifinta a tashe yace shikenan maryam na fahimceki amma dan Allah ki daure kici abinda suka baki kodan lfyarki,to baba ya mama take,lfy lau karki damu damu maryam ki kula da kanki,insha Allah zaki dawo garemu da izinin Allah,Allah ya amshi addu'ar mahaifina na gode....bata k'arasa maganarba ta katse saboda kuka daya ci karfinta.

Mahaifin maryam hankalinsa a tashe ya kira manosh ya gaya mishi komai,manosh yace karka damu baba insha Allah zata dawo kudai tayamu da addu'a.
Shi kuwa bawan Allah kallon maryam yakeyi tare dajin tausayinta ya bud'e ledanshi ya d'auko *maltina da biskits* d'aya ya bata ta karb'a tare dayin godiya,yace bakomai ki koma inda kike dan nasan sun kusa dawowa zanyi iya k'okarina dan in taimakeki ki dena damuwa kinji? To nagode sannan ta koma taje ta zauna tare da bud'e malt d'in da biskits tana sha.
Wayarta ta bud'e sega texs d'in manosh dana miher,na miher ta fara bud'ewa inda taga hoton manosh sanye da maroon jaket,ita kanta maryam tasan manosh ya shiga wani hali daga ganin hoton nashi,sannan ta karanta texs nata kamar haka
_slm 2u my aunt_
_bansan mezance mikiba aunt,amma ina cikin damuwa sosai musamman yadda naga bro manosh ya zama kamar bashiba dan rashinki_. _Aunt munanan munata addu'a Allah ya d'auraki akansu,kinga dai yadda bro nah ya zama wlh tun jiya baici komaiba har yabar gida yanzu_. _ina sonki wifeynmu,pls koda empty rexs ne ki aiko min dan inji sanyi a raina_. Yours miher....

Koda maryam ta karanta setaji kwalla ya zuba mata,nan ta tura mata da
_thankyou so much sis,nagode sosai da kulawarki,kuma nayi farin cikin ganin pic d'in peach,dan yasani farinciki sosai wlh_. *nagode*

Koda taga texs d'in manosh batayi reply ba se kawai ta kirashi. Katsewa yayi ya kirata ta d'auka tare da cewa *captain*, sanyi yaji har cikin ranshi yace yes apple a wani hali kike yanzu? Karka damu ina halin lfy,sedai nayi fushi dakai,meyasa mena miki apple? Saboda kabar cikinka da yunwa rabonka da abinci tun breakfast d'in safe meyasa hakan peach? Am sorry apple amma kema ai bakici komaiba,eh amma yanzu haka ina shan malt da biskits,naga pic naka yanzu miher ta turo min peach a jiya kawai amma ka canja. Yadda yaji muryanta kamar zatayi kuka yacewa sojan da yake driving tsaya anan ka karb'o min malt da biskits,sannan yace "apple am goying to eat now okey" pls banaso kisa damuwa aranki muna hanyan bauchi kinji? Murmushi tayi tace "thankyou peach" cikin sanyin murya. Sunanta ya kira a hankali *aunt*, cikin muryan kuka tace uhmm,yace pls stop it apple i will soon come to u okey? Har yanzu kukan takeyi "tace okey i have to peach byee...
Bayan ta katse wayanne ya had'iye tausayinta a wuyanshi daidai lokacin aka kawo malt da biskit d'in ya bud'e ya fara sha,bayan ya gamane ya karb'i driving d'in gudu yakeyi kamar zai tashi sama..

Can kuwa koda maryam ta ajiye wayan da sairi ta kashe ta mayar pant d'inta dan taji zuwan mota.
Saddam ne tare da sauran abokanshi 3 suka dawo,wannan d'ayan da suka bari yana kwance ya mik'e yare da cewa ya kuka dad'e ne haka? Saddam yace wlh bari kawai,ta tashi kuwa,eh ta tashi tayi sallah,saddam yace gaskyafa ni a matse nake wlh dan haka kawai zan sauke gajiyata akanta wlh,d'ayan yace haba saddam karkayi haka pls da safiyannan idanma hakane ai gara ka bari se dare kai kanka zakafi jin nishani idan duhu yayi. Saddam yace hakanefa,to gaskya dole na koma cikin gari in nemo wata dan wlh a matse sosai nake kasan abunka da sabo,yana kaiwa nan yaje ya duba maryam tana rakub'e a gefe tana kuka. Dariya sosai saddam yayi yace garama ki dena wannan kukan domin anjuma zakiyi wanda ya fishi sauti hhhhhhhh

Hankalin maryam ya sake tashi domin taji hiransu. Abinci wani ya kawo mata ya e gashi kici ko fine girl,ko kallonshi batayiba ya ajiue ya k'ara gaba.
Tana jin motarsu ya tashi ya tafi ta lek'o taga duk sun tafi seshi wannan bawan Allah. Wayarta ta kunna ta nemi layin manosh amma sam baya shiga,ta tabbatar da suna hanyane dan haka taje tayi alwala tare dayin sallan walaha tayi addu'oi sosai sannan ta sake gwada numbern manosh har yanzu dai shuru yak'i shiga,haka ta koma gefe tana zaune tanata karatun qur'an a cikin zuciyanta har azahar tayi.

Maryam tanayin alwala yazo yace amma ki gayamin sunan k'awayenki mana,tace lfy? Yace lfy lau,nan dai ta dinga kiransu harta gama yace babu wasu da kike tunanin sun tsaneki? Tace gaskya babu,yace to shikenan jeki kiyi sallah.
Bayan ta idarne seta bud'e wayanta cikin ikon Allah call d'in manosh ya shigo,da sauri ta d'auka tace hello,yace peach kina dai lfy ko? Tace lfy lau manosh kuna ina,pls kazo da sauri domin suna da niyan aikata wani abu a kaina pls..karki damu apple inanan a inda kike yanzu zanzo gareki,mik'ewa tayi da sauri tare da jujjuyawa tana kallon jejin tace ina kake peach?...
Wayan hannunta ya karb'a tare da kashe wayar gabad'aya yana binta tana komawa da baya tana cewa dan Allah kayi hakuri. Ran saddam a b'ace yace wato dama da waya a hannunki ko,to wlh bazaki b'ata min aikiba sedai in kasheki in kashe banza. Bindiga ya d'au zai harb'eta d'aya mutumin yace haba saddam kar kayi haka mana mace zaka kashe kuma k'aramar yarinya,kawai muyi gaggawan barin nan d'in shine mafita,domin yarinyar data saka aikin itace take baiwa masu binciken address d'in inda muke dan a kamaka ka fita daga rayuwarta for good. Kan saddam ya d'aure sosai yace kana nufin *LUBNA AHMAD* tana min wasa da hankali ,yace kwarai kuwa.

Mamaki ya cika maryam ta nanata sunan a cikin ranta *lubna ahmad*? Kawai seta d'iba da gudu ta barsu atunaninta ai su manosh sun iso inda take. Bindiga saddam ya d'aga tare da harbinta ai kuwa seya sameta a saman hannunta kusa da kafad'arta,ihu sosai maryam ta saka tareda fad'uwa k'asa tana kuka. Saddam zai kara mata se d'ayan ya bige bindigan yace meyasa hakane saddam wai kasheta zakayine? Sauran ukun ne sukazo da mota sukace kuzo mu sampe sojoji sunji k'aran bindiga zasuzo kuma,d'ayan yace bari in d'auko yarinyar dan bazamu barta a hakaba ai. Da gudu saddam yahau mottafi suka tafi suka barshi,gashi sam baiga maryam a inda ta fad'iba kamar wanda ta b'ace. Yanata tsaidasu saddam amma sam sunk'i tsayawa sema harbinsa dasukayi a k'afa ta yadda bazai iya guduba. Ai kuwa segasu manosh da gudu ya k'araso yana cewa apple, apple na iso ina kike? Kan mutumin ya nufa tare da d'agoshi yace ina maryam! Take mutumin ya fara b'ari dan yasan shikenan kashinsa ya bushe tunda ya shiga hannun *sojoji*, yace *sir* wlh ban saniba acan ta fad'i nima ita nake nema...
[7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

*dedicated 2 Adon gari group*B??0soB???


41-42 Hajiya khadija ce zaune agidansu maryam tanata kuka,maman maryam se hak'uri take bata,tace yanzu fisabilillahi me maryam tayi haka dahar za'a d'auketa a rabata da iyayenta,se kuma ta sake fashewa da kuka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login