Showing 51001 words to 54000 words out of 72993 words

Chapter 18 - Auntyn Yara Book1 Complete Hausa Novels By Sadnas.doc

Sadnas   

06 Sep 2025

875

fitar da *aunty* waje ayimata aiki wannan shine burina na farko na biyu kuma Allah ya bayyana mana captain,tsantsan farin ciki maryam ta rungume lubna tana hawaye saboda an sosa mata inda yake mata k'aik'ayi. Wani irin dad'i sosai lubna taji lokacin da suka rungume juna da jinin jikinta,tana maganan zuci tana cewa ancuceni da aka rabani dake 'yar'uwata bazan iya gaya miki komai ayanzuba saboda damuwan da kike ciki,sannan dukka cewa hajiya khadija ba mahaifiyata bace ina sonta sosai har cikin raina saboda k'auna data nunamin wanda ko d'an cikinta bro marwan albarka,sun nunamin gata na k'arshe hakan yasa bazan gaya miki komai yanzuba dan naji tace ko daddy nama baisan da zancenba to amma yaya hakan ya faru kenan ya za'ace daddy baisan cewa niba 'yarsa bace? Yah ibrahim ne ya katse lubba da zancen zuci da takeyi idanunta rufe tana kance a kafad'ar maryam.
Afirgice ta d'ago da kanta tana kallon maryam,mamakine ya kama maryam d'in daduk wanda yake tsaye agun. Lubna ta wayance tace muje na rakaki gida *aunty* dan kema baki da lfy muje ki kwanta ki huta my luv muje,yah ibrahim yace kaka dan Allah kiyi hak'uri bari na kaisu gida zan dawo,maryam zatayiwa kaka magana kenan se lubna ta janyota da k'arfi tace muje nikam dan idan ina gidannan tofa abin bazai mana kyauba nan gaba,haka maryam ta bita a baya kamar wata wawiya se cikin motan yah ibrahim.
Yah ibrahim yace meyake damunkine my luv,mum naku ta kirani tana tambayana kokinzo gida nace mata a'a,munyita kiran numbernki bakya d'auka kuma mum tace mana rai a b'ace kika bar gida kina kuka shine tasa marwan yaje ko ina ya nemo mata ke hankalinta ya tashi sosai wlh waime yake faruwane my luv,kuma menene hajiya iya tayi miki haka? lubna dake zaune a baya itada maryam seta rushe da kuka tace wlh an cuceni my luv kuma bazan tab'a yafewaba,gara cutan da saddam yamin so dubu akan wannan cutan da akamin wlh, kuka sosai takeyi kamar ranta zai fita wanda yasa hankalin yah ibrahim da maryam tashi sosai tare da mamakin jin kalaman lubna. Maryam ta janyota jikinta tanata rarrashi har suka iso gidansu maryam,dukkansu suka wuce cikin gidan inda yah ibrahim ya wuce palon baba su kuwa suka wuce d'akin maryam,wani sanyi da ni'ima lubna ta tsinci kanta a ciki,maryam tace barina dubo mama ina zuwa,lubna tace to.
Fitan maryam kenan wayanta ya fara ringing,lubna tana dubawa taga *PEACH & CREAM* ai da gudu ta fito ta nufi d'akin mamansu tana cewa hello,ai kawai setaji muryan manosh yace apple, da gudu da murna take kiran aunty ga bro manosh...,
[7:14am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas

*dedicated to sweet sis maryam tahir (hajja)*???]??/\



67-68 koda suka isa gida maryam kuka kawai takeyi,su abdallah kuwa suna gidansu mum dan ba'ama zo dasuba.
Iyayen maryam sun tausaya mata sosai,musamman yah ibrahim,ahankali aka fara shirye shiryen tfyansu kano domin aduba lfyar maryam kamar yadda shukrah tagaya musu,mama da yah ibrahim da kuma muh'd ne suka tafi kano inda dad d'in manosh yabiya musu kud'in jirgi se aminu kano.
Kamar da wasa doctor ahmad babban dr ne wanda kowa yasani, ya iya aikinsa sosai batare da b'ata lokaciba cikin 2days akayiwa maryam duk wani gwajegwaje daya dace,maganan shukrah dai ya tabbata domin k'odan maryam kusan dukma sun samu matsala wanda dolene se'an mata sabon dashe,ma'ana se'an sa mata wani k'odan.
Hankalin mama ya tashi sosai,tanata hawaye,yah ibrahim da muh'd ne suke rarrashinta tare da kwantar mata da hankali,kwanansu biyar suka koma yola.
Mamaki sosai akayi dajin matsalar maryam,mahaifinta yace zai fitar da ita zuwa *india* domin ayi mata aiki,amma sam maryam tak'i tace ita babu inda zataje se manosh ya dawo.
Su marwan sunyi iyakan k'ok'arinsu zuwa masallatai da kuma malaman sunna akan abinda ya sami amininsu manosh,sun raba kud'ad'e sosai kota ina zuwaga marasa k'arfi domin atayasu da addu'a Allah ya baiyana manosh.

Addu'oi sosai aketayi ba dare ba rana, kusan kullum ake kiran number manosh amma sam baya shiga yau kusan sati kenan.
Abdallah da alfiya kuwa tunda akace musu daddynsu yayi tafiyane shikenan suka yadda tunda dama yanayin tfya yayi 2to3month ma baidawoba,dan haka sam basu damuba.
Ahankali mahaifin manosh yake shirye shiryen tfyansu maryam india batare da sanin mahaifin maryam ba.
Idan kaga maryam da miher dole ka tausaya musu sun rame sunyi wani iri,barema maryam da damuwan yayi mata yawa kuma dama kunsan batada auki.
Miher tana son bro nata wanda kowa yasan da hakan,shiyasa majid yake iya k'ok'arinsa domin kwantar mata da hankali,hakama maryam kullum nasiha iyayenta suke mata da kuma yah ibrahim dasam baya son ganinta cikin damuwa,hakan yasa zaibada k'odanshi guda d'aya asawa maryam,amma sam koda aka gwada baiyi daidaiba.
K'awayen maryam gabad'aya sun zama abin tausayi domin ganin irin halin da maryam take ciki,rashida tace da marwan ita aje a gwadata idan har a'a iya sawa maryam k'odanta to wlh ta bayar da guda d'aya tunda zasu iya rayuwa da d'ad'd'aya, marwan yace karki dau luv zamu samo mafita amma ina tausayin aunty sosai wlh,friend na manoh dukkansu basa iya kocin abinci saboda rashin abokinsu,kowa yasan irin shak'uwar da take tsakaninsu.

Mahaifiyar manosh kuwa ta zama Allah sarki domin sun d'auki son duniya sun d'aurawa manosh dayake shine d'ansu na fari.
Kuma duk wanda yasan manosh ko kuma wata alak'a dake tsak'aninsu tofa dole ya shiga damuwa. Cikin sati biyu lbrn manosh ya baza ko ina dayake sojane mai kwazo ga kuma taimakon marasa k'arfi,sam bayida kyama kamar dai matarsa wato *auntyn yara*.
Lubna ce kwance a gidansu tana cewa mum nata gaskya mum lokaci yayi daya kamata in taimakawa maryam akan taimako da rufin asirin data min,mum zanje inba maryam k'odata guda d'aya,bazan iya bari anemo k'odan wani dabamu saninshiba asawa maryam.
Hajiya khadija tace lubna lfyarki kuwa bana so ki sake sa bakinki cikin maganannan,kuma wace irin taimako maryam tayi miki haka? Lubna cikin muryan kuka tace mum kinsan me,ada bani da wata mak'iya irin maryam saboda yadda nake k'aunar bro manosh araina,babu wanda yasan hakan dagani se miher naso in sanar dashi amma dayake shiba mijina bane senaji cewa ya samu mata a girei,nayi bak'in cikin hakan sosai tunma bansan wacece yake nemaba,ranan muka had'u da maryam da kuma friends nata a yakubu shopping plaza na yarda keyn motata batare dana saniba ta biyoni ta bani anan ne muka san juna da maryam harna karb'i numbernta. Mum daga bayane na san cewa maryam itace yarinyar da bro manosh yake so,tun daga lokacin tsanarta ya shiga zuciyata nayi niyan d'aukan mataki sosai dan in raba maryam da bro manosh. Lubna tayi shuru tana kuka sosai cikin tausayawa tace mum kinsan me? Nice nasa akayi kidnaping maryam lokacin da aka kusayin aurensu,nasa akayi nesa da ita yayinda nake samun duk wata lbr agun miher wanda ita kanta basan inada hannuba,tun daga numan nasan aka sakeyin nesa da ita mum zuwa jejin yankari dake jihar bauchi,amma dayake Allah ba azzalumin bawansa bane dukda cewa ita maryam tasan cewa nine nasa ayi mata hakan amma sam tak'i gayawa ko iyayenta da suka haifeta ta b'oye zancen cikin ranta domin bataso asamu matsala tsakanin familynmu da kuma familyn su bro manosh saboda tasan irin shak'uwa da soyayya dake tsakanin bro marwan da kuma bro manosh hakan yasa tayi shuru tabar komai aranta mum.
Marwan yana tsaye abakin k'ofa ya kasa shigowa yana sauraron lbrn da lubna take baiwa mum nasu,wanda mamakine sosai abaiyane a fiskarsa.
Lubna taci gaba da cewa mum bayan maryam ta dawo gidane,shi wanda na basu aikin yace inje muyi magana domin maryam tasan komai kuma k'ila zata tauna musu asiri,tsoron kar sunana ya fito dan yadda nake tsoro bro marwan yasa ranan na fita naje can inda saddam yake ya bayan GG..kuka lubna ta fashe dashi tace mum koda naje juice ya siyaya mana nidashi,ban kawo komai a rainaba saboda k'ishin danakeji a wannan lokacin kawai sena canye wannan juice d'in,shikenan ban sake sanin inda nakeba kodana farka senaji jikina wani iri mum saddam ya cuceni yamin fyad'e....
Mum ta kama salati tare da kwalla a idanunta itama lubna haka tace naso na kira miher amma senayi tunanin bazata rufamin asiriba dole za'a sani,shine na kira maryam ban b'oye mata komaiba na gaya mata komai,kinsan me mum hankalin maryam ya tashi sosai take tazo inda nake mum ta taimakamin ta kimtsa kaina hawayene cike a idanunta tare da tausayawa,muna tare da ita su bro manosh sukazo gun nida maryam muna ciki d'akin ab'oye a toilet munata addu'a saboda maryam tayiwa bro manosh k'aryan cewa tana cikin kasuwa suna sayayya se kuma gashi yazo inda muke a d'akin saddam,hankalin maryam ya tashi sosai badan komaiba sedan jinin dake kan katifar saddam kuma gashi ni babu yadda nake alokacin jikina rawa kawai yakeyi. Cikin ikon Allah mukaji suna cewa saddam ya gudu kenan tunda gashi harda kwad'o ajikin kofan,kuma wlh mum babu wanda ya kullemu ta waje,seda suka tafi muma muka fito da sauri shine maryam ta kawoni har gida tayi miki k'aryan cewa bigeni akayi da mota naji ciwo a k'afa,kuma mum maryam itace ta had'ani da ibrahim wanda yake matsayin yayanta,bata b'oye mishi komai akan batun fyad'en da aka minba ta gaya mishi komai,tare da neman amincewarsa akan ya aureni,k'aunar da ibrahim yakeyiwa maryam ne yasa ya aureni badon yana sonaba,kuma wlh mum koda na rana d'aya ibrahim bai tab'a nuna kyamarsa akainaba se kauna da kulawa na musamman kuma har gobe babu wanda yasan da wannan zance fyad'e dagani se maryam da ibrahim duk maryam tayi hakanne don ta rufamin asiri mum da kuma k'aunar da take min,gaskya mum maryam macece wanda ba'a samun irinsu a zamanin yanzu,ina ganin k'aunarta aduk lokacin da muka had'a ido da ita.
Dan haka zan iya yiwa maryam komai koda hakan zaisa in rasa rayuwatane to lallai zanbawa maryam k'odata guda d'aya watak'il zan iya biyanta da alkhairan datamin arayuwa......

Ba mum kad'aiba harta marwan dake tsaye a waje ya shigo rai a b'ace,take lubna ta gudu bayan mum dan yadda ta ganshi tasan sarai yaji komai dan haka ta fara kuka sosai tana cewa waiyo mum dan Allah karki bari ya dakeni wlh ina da ciki mum,bro marwan dan Allah kayi hakuri.
Mum tace karka tab'ata marwan nace ka kyaleta! Cak marwan ya tsaya yana kaima lubna sakon harara yace baga irintananba mum,daga taimako gashi ta b'ata mana suna tayi abin kunya,ke bari kiji ingaya miki dabadan cikin dake jikinkiba wlh yau dase na kusan karyaki wawiya mara hankali dole kibar mana gidanmu dan dama ke 'yar tsuntuwace ni kad'ai iyayena suka haifeni tsintattiyar mage kawai ya fita rai a b'ace ya fisgi mota.
Daga lubna har mum kuka sukeyi lubna tana bin mum da kallo mai d'auke da tambaya tace mum menaji bro marwan yake cewa? Wainiba 'yarku bace? Tsuntoni kukayi hakane mum? Mum da kuka yaci karfinta tace hakane lubna keba 'yarmu bace.
Lubna ta tsaya da kukanta tace tosu waye iyayena mum,a ina kuka samoni mum,meyasa kuka b'oyemin mum? Mum cikin kuka ta rik'o hannun lubna tace shi kanshi dad naku baisan iyayenkiba lubna domin ce mishi nayi na tsuntokine,lubna keba 'yar kowa bace se 'yar Alhaji muh'd atta. Zaro ido lubna tayi tace wanne kenan mum? Mum ta rungumeta tace wanda dai kika sani mahaifin maryam *auntyn yara* ku 'yan biyune lubna maryam itace babba sannan ke uwarku d'aya ubanku d'aya da ita lubna ki gafarceni dan Allah,cikin mamaki lubna ta janye jikinta tace taya hakan ya faru kenan mum? Kina nufin kowa yasan hakan kenan? Mum tace babu wanda ya sani dagani se hajiya iya kakarki lubna. Kuka sosai lubna takeyi tare da barin palon da gudu......
[7:14am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

*dedicated to sis fatima tahir*B??0Bq??


71-72 Da sauri auntyn yara ta waigo donjin me lubna take cewa,kai se sukayi gwaru akansu atare sukakai hannu goshinsu don sunji zafi dukkansu.
Maryam ta karb'i wayan hannunta tare da cewa sannu lubna ita lubna sannu take mata suna masu kallon junansu cike da murmushi,maryam tabar d'akin da sauri ta koma d'akinta tare dasa wayan a kunnenta tace cikin zumud'i tace *hello peach*, muryan manosh yace apple ya kike yasu abdallah,lfyanmu lau peach nah ina ka shiga ka barmu da tashin hankali da kewa,yace kiyi hakuri apple yanzuma na kirakine dan in gaya miki cewa ki mance dani a rayuwarki kwatakwata kamar baki tab'a had'uwa daniba domin bazan sake dawowa garekuba apple ki cireni a zuciyarki su abdallah kuwa ki gaya musu cewa na mutu kuma mamaci baya dawowa ta yadda zasu manceni daga k'arshe kuma ki samu miji wanda kike ganin zai rik'e min su alfiya ki aura koda d'aya daga cikin abokainane wannan shine dalilin dayasa na kiraki kinji apple,ya k'arashe maganan cikin murya maiban tausayi.
Ita kuwa maryam tunda taji abinda ya fara fad'a taketa zubda hawaye harya k'arasa. Jin tayi shurune ya sake kiran sunanta apple pls am sorry,na zab'i hakanne dan in cetoki daga sharrin shukrah bawai don wani abuba...bai k'arasa maganaba naryam ta katseshi da cewa ya isheni haka peach bana son sakejin komai daga gareka indai akan wannan magananne mubarta kawai,yanzu ka gayamin ya yake a ina kake me kuma shukrah tayi maka haka peach? Yadda manosh yaji muryan apple bashi yasan tana cikin tashin hankali,yace karki damu da sanin halin da nake ciki apple dama abinda na kira in gaya miki kenan ina miki bankwana ta karshe.
Da sauri da kuma ihu tace pls peach karka katse wayannan ka saurari abinda zance maka,ina cikin wani hali sosai peach na rashin lfy,k'odata gabad'aya sun b'aci dole se an min dashe,yanzu haka ana shirye shiryen fita dani india ne dan haka ka saurareni wata k'ila maganata dakai na k'arshe kenan zaiyu idan najema bazan dawoba dan haka inaso ka yafemin dukkan wasu abubuwa dana maka na rashin sani,sannan ina so ka sani har inbar duniya babu wani d'a na miji dazan iya zama dashi bayan kai kuma har inbar duniya bazan dena yin addu'a Allah ya d'auraka akan shukrah daduk wani abu mai cutarwa ameen,inaji ajikina cewa zaka dawo garemu peach,sedai bana tunanin zaka sameni sedai iyayenka da kuma yaranmu peach dan Allah ka kula min dasu domin kune farin cikina daga k'arshe ina k'aunarka k'auna ta hak'ik'a wanda baya k'arewa _i love you so much peach_, alfarma d'aya zan nema agunka shine inji kalmar soyayyata abakinka pls...?
Kwalla sosai manosh yakeyi idanunshi kamar attarugu,amma ina bazai iya gaya mata kalmar so ko d'ayaba,dan haka yace ina miki fatan alkhairi apple se anjuma......
Kuka sosai maryam ta fashe dashi tana cewa peach dan Allah karka barni ka tsaya ka gayamin cewa kana sona dan Allah my captain,kuka sosai takeyi tana kallon wayan. Mama da lubna da suke tsaye akanta tun ihunta na farko sune suka rik'eta sunta rarrashi dan sunji dukkan hiran maryam da manosh d'in.
Yah ibrahim da babane suka shigo dajin muryan kukan maryam suna tambaya ko lfya? Nan lubna ta gaya musu komai,inda mamaki ya kamasu sosai. Yah ibrahim yayita kiran numbern amma sam baya shiga,maryam dai se kuka takeyi tana ta surutai kamar wanda ta zare tana cewa baba manosh yace in samu miji inyi aure yana nufin ya sakeni kenan baba,menayi mishi dazai min haka baba,nagaya mishi halin da nake ciki amma koya kula baba,innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Lubna tana rungume da yarta itama kuka takeyi sosai,sam bata son ganin naryam cikin damuwa musamman ma datasan cewa yartace uwarsu d'aya. Hakadai ranan lubna bata koma gidantaba shi ibrahim d'inne ya koma saboda mahaifiyarsa ita kad'aice se mai musu girki. Daga baba har mama abin ya basu mamaki ganin yadda lubna takeyida maryam,bayan iyayenta sun rarrashetane se suka barsu a d'aki ita da lubna.

Yah ibrahim kuwa tunani iri iri yakeyi a zuciyarshi,ga kuma damuwan halin dayaga maryam aciki yau ya tausaya mata sosai harma yake tunanin inama dashine ya aureta da shikenan maryam bata da damuwa sam,amma ina haka Allah yake tsarawa kowa rayauwarsa. Wayarsa ce tayi k'ara number manish ne,mamaki yayi sosai tare da d'auka da sauri yace slm,wslm yaji muryan manosh,basu gaisaba manosh yace na kirane don inji cewa dagaskene za'a fitar da aunt india? Ibrahim yace eh hakane,manosh yace to shikenan idan kun dawo ka sama mata miji ka aurar da ita dan nikam bazan dawo garekuba na zab'i in zauna anan domin ceton apple zan iya jure komai ibrahim shiyasa nafiso ace kaika auri aunt ba waniba pls ka auri aunt nasan zaka kula da ita kamarni. Ibrahim yace mekake fad'ane captain insha Allah zaka dawo kuma kadena sa ran cewa wani abu zai same aunty babu abinda zai sameta da yardan Allah zaka dawo kushi gaba da zamanku munata addu'a kuma shukrah setasha wahala wlh muguwa...tsawa maikyau ibrahim yaji akunnensa ana cewa wlh k'arya kake ibrahim wahala kam sedai auntyn yara amma badai niba,kuma zanga yadda zaku karb'o my manosh daga hannuna dama kai kad'aine mai taka min birki kuma ina so kasan cewa my manosh yabarku kenan har abada bazaku sake ganinshiba,sannan ka gayawa mahaifin maryam ya kiyayeni wlh su dena b'ata lokacinsu waisu suna so suga bayana to wlh idan bai dena shiga gonataba sena tozarta maryam d'in da kuke ji da ita. Hhhhh ibrahim yayi dariya yace dama ashe kece shukrah,kece kika ari muryan captain kike so ki b'ata tsakaninsu da aunty,to Allah ya tona asirinki muguwa,ina so kisan cewa aunty tafi k'arfinki shiyasa har yanzu kika kasa mata komai shine kika b'ullo mata tasan muryan mijinta koh,tota Allah ba takiba wannan kad'ai bai isheki shukrah,komai kikayi seya warware hakan yana nufin bazaki tab'a samun nasara akanmu bane kuma mahaifintama yafi k'arfinki hatta shi captain yafi karfinki wlh kawai dai jarabawace Allah ya sauko mishi dashi kuma insha Allah zamuci wannana jarabawan muzuba dake shukrah *QUR'AN* yana sama da komai acikin duniyan kuma dashi zamu karb'o captain agurinki idan kuma kin isa toki hanamu d'aukoshi daga gareki kawai lokaci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login