Showing 18001 words to 21000 words out of 72993 words

Chapter 7 - Auntyn Yara Book1 Complete Hausa Novels By Sadnas.doc

Sadnas   

06 Sep 2025

888

k'arasawaba taji cikinta ya kame kamar an soka mata wani abu,innalillahi wa'inna ilaihirraji'un taketa nanatawa a zuciyarta.
Manosh yace ya kikayi shuru,tace bakomai ina zuwa,bata jira mezaiceba ta mik'e ta wuce gida yana binta da kallo. Koda ta k'arasa gun mamanta ta wuce a d'aki ta cire doguwar himar nata ta fad'a kan gado tana cewa mama cikina ya kameni sosai yana min ciwo. Hankalin maman ya taahi sosai tayi kanta tana mata sannu tare da tofa mata addu'oi,tace bak'on ya tafine? Cikin jin ciwo take magana tare da kame cikinta tace basu tafiba suna zaure.
Mama ta rasa yadda zatayi seta d'auki wayanta ta kira baban maryam ta gaya mishi komai,shima hankalinsa a tashe ya kira number yah ibrahim yace lallai yaje gida.

Bada b'ata lokaciba yah ibrahim yazo a zaure sukaci karo da manosh. Su gaisa sannan yace ina maryam d'in? Manosh dabaisan komaiba yace ta shiga ciki,yah ibrahim yace kasan bata da lfy,yace eh na sani harma abokina ya dubata yanzu. Kan yah ibrahim ya d'aure seyace bari in shiga ciki dai dan yanzu babanta ya kirani yake cemin bata da lfy sosai cikinta na ciwo,a razane manosh ya mik'e yace ciki kuma,tacewa yanzu kenan ko,ibrahim yace eh sannan ya wuce ciki akabar manosh cikin damuwa sosai.

Maryam se juyi takeyi tana addu'oi,har ya ibrahim yayi sallama,mama ta fito tace bari na fito da ita sannan ta koma tasawa maryam himar,shi kuwa yah ibrahim da sauri ya kira rash a waya yace tazo yanzunnan kuma cikin shiri.

Bada b'ata lokaciba sega muhammad yazo sakamakon wayan da manosh yayi mishi. A tare sukazo da rash ta gaishesu sannan ta wuce ciki,maryam ta fara hangowa babu yadda take mama tana rik'e da ita ita maeyam bata iya ko mik'ewa tana sunkuye kuma rik'e da cikinta.
Da sauri rash ta k'arasa ta riketa sosai tana mata sannu. Hankali mama a tashe tace gaskya zan biku muje asibitin nan dan hankalina zaifi kwanciya,waya tama baban maryam,sannan ibrahim yaje ya sanar dasu manosh komai,se manosh yaba ibrahim keyn motanshi yace ya d'auki su mama a ciki shi kuma zasu tafi da muh'd. Haka kuwa akayi su manosh suka tafi shida muh'd sannan ibrahim ya bud'e musu motar, da sauri abdallah yazo dan yadda yaga mama da rashida suna rik'e da auntyn yara,baice komaiba ya karasa yace lfy mama,tace wlh maryam ce ba lfy zamuje asibiti. Subhanallah nima zan biku, ibrahim yace shiga baga to,abdallah ya shige gaba su mama kuwa suna baya suka kama hanyan jimeta.

Asibitin da muh'd yake aiki sukaje, aka wuce da ita kai tsaye. Ae a lokacinne manosh da muh'd suka gaida mama sannan muh'd ya wuce duba maryam.
"Yana shiga rashida ta fito ta wuce gunsu mama,shi kuwa manosh kunya sosai ya kamashi gaahi k'ananan kayane a jikinshi,nan ya kira su majid cikin k'ank'anin lokaci suka zo dukkansu ukun.
Marwan majid da muhsin sukaje suka gaida mama sannan suka gaisa da ibrahim. Rashida tana gefe ita da abdallah sannan marwan ya k'araso suka gaisa ranta a b'ace,amma seya d'auka kodan rashin lfyan maryam ne.

Muh'd ya fito su manosh suka k'arasa da sauri donjin meke damunta harda yah ibrahim d'in da abdallah. Mama da rash kuwa suna tsaye a gefe guda.
Muh'd yace *ulcer* kawai babu wani abu, kuma dole zata zauna a asibiti dan se'an k'ara mata ruwa har leda biyar. Sannan yayi mata allura yanzu dan har tayi bacci ma, ibrahim yace to mun gode kayi duk wani abunda ya dace pls yanzu medame ake buk'ata? Muh'd yace haba aiba komai wlh already nasa mata ruwan karka damu babu wani abu da ake buk'ata kudai tayamu da addu'a kawai. Godiya sosai ibrahim yayi sannan yace bari naje na sanar da mama dan hankalinta a tashe yake,muh'd yace muje inyi mata bayani.
Bayani sosai muh'd yayiwa mama tare da cewa ta kwantar da hankalinta maryam zata samu lfy insha Allah. Godiya mama tayitayi sannan ya tafi gunsu manosh.
Manosh yace zan iya ganinta,majid yace jeka ka kanga inba hakaba ai bazamu gane hankalinkaba ad'an lokaci kad'an kashi harka fita hayyacinka kamar ba sojaba, dariya sukayi baima kulasuba ya wuce d'akin tana kwance babu himar a jikinta se atamfa d'inkin doguwar riga daga sama ya bada shape amma k'asan a bud'e yake. Karon farko kenan da manosh yaga maryam babu himar ajikinta,mara ce sosai gata 'yar karama bata da jiki sam,amma k'irjinta a cike suke. Bai k'arasaba ya janyo k'ofar ya koma gunsu majid yace muje ko,dan muma mamanta damar shiga, haka sukayi musu sallama suka wuce yacewa ibrahim ya rik'e key din motarsa dan zirga zirga,amma sam ibrahim yak'i seda ya bashi key din,shi kuwa manosh ya karb'a suka tafi.

Auna tfya mama da rash suka wuce d'akin da maryam take harda ibrahim da abdallah.
Tausayin maryam ya kama rsah sosai tayi dana sanin gaya mata kallomin jiyan dukda dai tasan bashine silan rashin lfyanba amma tana k'aunar maryam a ranta sosai.
Manosh kuwa ya gayawa mum nashi da kuma miher,sannan yacewa dad nashi yana so ya bashi kyautar mota guda d'aya dan zaibawa su maryam ne dan abinda ya faru yau,da baijeba kenan se sunyita neman motan hawa. Dad d'in manosh business man ne sosai kuma yanda gidan saida motocin,sannan yana k'aunar manosh sosai,dan haka yace manosh yaje ya d'auki duk motar da yake buk'ata. Godiya sosai manosh yayi dama suna hira da abdallah sosai kuma abdallah ya gaya mishi motar da maryam take so saosai a ranta shine *307 red* dan haka ya wuce yaje ya d'auko mata red d'in kuwa guda d'ayan kenan ya rage aka rubuta sunan maryam akan takardun da komai sannan yazo dashi gida ya nunawa mum da miher sukaita murna tare da addu'oi yace bari ya watsa ruwa sesu tafi shida miher...
[7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

*dedicated to seemby luv & leemcy*???i???i



31-32 miher tayi shiga na alfarma,daidai nan lubna ta kirata a waya tana tambayanta ya maganan zuwa tambayane nasu bro manosh,nan miher take gaya mata cewa ai maryam bata da lfy tana hospital d'in su bro muh'd yanzu hakama ina jiran prince ya fitone mu tafi.
Lubna tace eyyah Allah ya bata lfy,a ranta kuwa tace Allah yasama ta mutu.
Koda wasa lubna bata gayawa miher cewa tasan maryam ba,kuma bata yiwa miher tambayoyi akan maryam d'in sam,dan gudun zargi.

Manosh ya fito cikin shigar indians da blue sari na maza yayi kyau sosai,ya mik'awa mihaer key d'in *benz* nashi yace taje zai bita a baya. Mirna sosai tayi yau bro manosh yabarta tayi driving da kanta. Tana gaba yana binta a baya da *307*din apple nashi.
*Atiku abubakar mall* suka nufa inda manosh ya kashe kud'i sosai harta flaks seda suka saya mata da cups su plate dukdai wani abu da zasu buk'ata a hospital haka mihar tayi ta d'auka, se kallonsu akeyi don yadda sukayi kyau shi kuwa captain ko dariya bayayi se amsa waya da yakeyi. Mihar tana biye dashi bayan sun biya kud'ine suka tafi tana gaba yana binta a baya har,suka isa hospital d'in.
Lokacin yah ibrahim da abdallah sun koma girei domin suyiwa maman rashida bayani kuma tayi abinci dasu. Manosh yacewa miher ta shiga idan maman maryam bata d'akin tozai shigo,ai kuwa seta shiga da sallama da kuma kayayyaki sosai a hannunta har rashida ta tayata da wasu,sannan ta sake komawa ta kwaso sauran nanma seda rash ta tayata sannan suka gaisa maryam tana bacci har yanzu,mihar tace yamai jiki,rash tace da sauki wlh,tace Allah ya sauwaka mama fa? Tace mama sun fita da baba amma inaga sun kusa dawowa.
Da sauri mihar ta fita taje ta sanar da bro manosh,kafin su shigo maryam ta farka tana cewa mama zansha ruwa,dama yah ibrahim yad'an sayo abin tab'awa kad'an dan haka rash ta mik'a mata ruwan tasha sosai sannan ta koma ta kwanta rash tana mata sannu da jiki,tace yawwa.

Manosh da mihar suka shigo da sallama,kunya sosai maryam taji tace rash mik'amin himar d'ina,da sauri tad'an rataye matashi a k'irjinta sannan suka k'araso.
Rash suka gaisa da manosh yace ya mai jikin,tace da sauki yace to Allah ya bata lfy tace ameen sannan rash tace mihar mud'an basu guri ko,tare suka tashi suka fita sannan yazo ya zauna akan kujeran da yake kusa da gadonta yana kallonta. Kunya sosai taji ta dai daure ta tashi ta zauna tare da gyara rufe jikinta tace ina wuni,kallonta kakeyi tare dajin k'aunarta yana ratsashi yace lfy apple ya jiki,tace da sauk'i.
Yace wato dama kina jin jiki shine kika cemin kaine yake miki ciwo ko,mirmushi tayi tace amma ai da sauki yanzu. Yace drip d'in harya k'are ne? Tace eh yace se bayan isha za'a samin wani,yace ok Allah ya baki lfy apple,tace ameen tare dajin kunyanshi sosai danba himar a jikinta dukda dai ta rufe jikinta amma yana iya hango kananan kitson dake kanta gata da bak'in gashi.

Ya maida kallonsa kan wayanshi yace ina wayanki,nan ta mik'a mishi ya karb'a ba tare daya kalletaba ya shiga galary, pic d'in da rashida tayi mata da kayan daya saya matane ya gani pic d'in sun mishi kyau sosai atake ya turasu zuwa wayanshi sannan yasa mata credit na 3k seya mik'a mata yace kimin kyau a hotonnan ya nuna mata wayanshi.
Murmushi tayi tace nagode meyasa ka tura baka sanar daniba,yace tokiyi hakuri bazan sakeba. Batace komaiba se kuma tace nagodefa da d'awainiya Allah ya saka da alkhairi,shuru yayi kamar baiji metaceba yana ta dannan wayanshi.
Ita kuwa se kallonshi takeyi dan yadda yayi kyau sosai. Batate daya kalletaba yace apple nifa bana so ayita kallona,kinya sosai taji dan tasan bai kalletaba,tace nifa ban kallekaba,yace kin kalleni mana aina ganki,tace ta ina kenan yace ta idona mana, dariya tayi tana ci gaba da kallonshi se wayanshi yayi k'ara ya d'auka yadai miher,tace bro mum da dad nata sun dawo dayake sunsan kana ciki se basu shigoba,yace ok tnx sannan ya katse wayar tate da mik'ewa tsaye yana kallonta. Itama shi take kallo tace ina zakaje,yace zan tafi in barki ki huta mana,kawai jin bakinta tayi tace mishi pls karka tafi yanzu,yace meyasa bakya so in tafi,tace haka kawai,ka zauna kamin hira.
Ba musu ya koma ya zauna yaci gaba da danna wayanshi yana magana batare daya kalleta yace su mama sun dawone kuma suna waje shiyasa nake so in tafi dama ina son inga baba. Tace to ai bakomai suma bazasu shigoba inhar sunsan kana ciki,yace eh hakanne yasa zan tafi ai. Yanayin manosh yana burgeta sosai da wasu irin abubuwansa,sam seyaso kallonta kafin ya kalletan,sannan kamar bakoda yaushe yake son magana ba. Shuru tayi tanata kallonshi sosai tana yaba kyansa a ranta,seyace tunanin me kikeyi apple,shuru tayi,yace pls ki dinga cin abinci sosai sannan ki dena cin yaji dan abdallah yacemin kina cin yaji sosai. Mamaki tayi sosai,tace yaushe kukayi hira dashi haka,yace ina ruwanki,tayi murmushi tace to zan dena insha Allah tunda yana nemar yimin illa. Manosh ya mik'e yace apple am goying amma zanyi missing naki wlh yau bazamuyi hiraba kenan tunda mama tananan bazan iya kiran wayankiba amma zan dawo safe kinji, tace to nagode sosai. Yace Allah ya baki lfy tace ameen sannan ya nufi kofar fita,harzai bud'e kofa tace eeem....tsayawa yayi cak tare da juyowa yace yes akwai wani abu ne,mirmushi ta mishi tace bakomai seda safe,shima murmushin ya mata tare da cewa idan akwai ki gayamin,tace akwai abinda nake so amma zanyi maka texsn,yace ok ina jira sannan ya fita.

Manosh ya gaida mama cikin girmamawa sannan ya gaida da baba tare da cewa dama yana son magana dashi,daidai nan yah ibrahim yazo da abinci sosai a kwando suka gaisa sannan ya wuce.
Miher da rash suka shiga da mama sega yah ibrahim,miher ta gaishesa sannan ya ajiye abincin tare da cewa aunty ya jikin dai,tace da sauki sosai,yace to Allah ya baki lfy tace ameen sannan ya fita gunsu baba inda suke magana da manosh. Godiya sosai baba ya dingayi tare da cewa ibrahim kagafa mota ya kawowa maryam wannan kyauta yayi girma dewa wlh dukda dai kace mahaifinkane yayi mana mun gode sosai,nanma ibrahim yayi godiya sosai,sannan yaje ya kira mama itama baba ya gaya mata godiya,sosai sukayi wanda baizai misaltuba,manosh yaji dad'i sosai a ranshi sannan ibrahim ya rakashi hargun motarshi sukayi sallama,sannan ya kira miher a waya,nan ta musu sallama tace zasu da mum nata da safe,rash ce ta rakata har wajen mota sannan suka tafi.

Koda baba ya gayawa maryam kyautar da manosh yayi mata da taimakon babanshi mamaki sosai tayi,babanta ya nuna mata takardun motan dukda sunanta a jiki,dan kunya bata iya cewa komaiba anata tayata murna sannan baba yace zasu tafi shida ibrahim seya tuk'a motar maryam d'in shi kuwa baba yahau nashi suka tafi ibrahim yanata mamaki.

Manosh yayiwa maryam texs kamar haka
_am still waiting my apple_
_akan abunda kike so_
Koda maryam ta karanta setaji a yanzu kam bazata iya cewa komai se tace

_Allah ya saka da alkhairi_
_wannan kyauta yayi girma dewa my peach banajin zan iya sake tambayar wani abu_
Bayan manosh ya karantane seya ce
_pls apple kigayamin indai kina so inyi farin ciki dan ina k'aunarki sosai apple nd i can do anything just for you sweetheart_
dad'i sosai maryam taji sannan ta sake tura mishi
_ba wani abu bane illa flower_ _i love you nd i love flowers so verry much peach_

Koda ya gama karantawa murmushi yayi yace indai wannan ne sekin gaji dashi dan lambunsa guda zanyi a gidanmu my apple,da haka yayi bacci.
Washe gari da safe ya shirya seda ya tambayi maryam tace su baba sunzo sun koma,ita da mama da rash ne,yace ok ganinan zuwa tace to sekazo.

Koda manosh yazo cikin kakin sojojinshi yake se kallonshi yakeyi,office muh'd ya wuce yace yadai abokina ya wifey nane da jiki,muh'd uace tofa tu ba'a baka ba,kar dai harka shirya kenan se tafya,manosh yace wlh kuwa driver yana waje daga nan airport zamu wuce,muh'd yace ok jeka ka fito se in rakaka,manosh ya wuce d'akin da sallama dama mama ta fita tunda maryam tace manosh yazo taje can d'aya d'akin gun wasu matan da y'arsu ba lfy suma.
Manosh ya shigo kenan rash ta mik'e tare da gaisheshi sannan ta fita,ita kuwa maryam flowers d'in kawai take bi da kallo da kuma yadda yayi kyau a kakin sojojin. Akan kujeran ya zauna suka gaisa seya ajiye mata flowern a gefenta,da sauri ta d'auka tana murmushi tare da shinshinawa taji wani k'amshi mai dad'i wanda yasa ta limshe idanunta tace _thankyou so much captain_,murmishi yayi yana kallonta yadda take ta murna da ganin flowers d'in,itama shi take kallo yare da d'auko *ring*mai kyau na maza ta mik'a mishi batare datace komaiba. Hannun yasa ya karb'a tare da cewa thankyou apple naji dad'i sosai,yasa a yatsan hannunshi tare da pecking d'in yatsan nashi yana mata murmushi tare da cewa ya jikin,tace naji sauk'i sosai wlh,manosh yace alhamdulillah zuwa gobe za'a sallameku insha Allah nizanyi tfy kuma zankai 1week kafin in dawo su dad zasuje gun baba dan asa mana rana kinji?
Sam maryam bataso tfyan manosh ba haka kurun tad'an canja fiska,shi kanshi ya lura da hakan seya sauya muryanshi yace "apple r u aokey?" Tace yes am fine ina zakaje? Yace zanje kaduna ne,karki damu kinji zan dawo insha Allah addu'arki nake buk'ata apple,kallonshi takeyi tare da tausayin kanta tace Allah ya kare min kai,yace ameen suna kallon junansu ciki so sannan tayi saurin kawar da kanta gefe tana kallon flower daya kawo mata,manosh bazai iya jurewaba dan haka ya mik'e tare da cewa nizan tafi apple ga wannan,ya ajiye mata kud'i a gefen gadonta sannan ya nufi kofar fita. Har yakai gun k'ofan kanta na kallon flowern,seya juyo yana kallonta sam taqi kallonsa har ya gama kallonta sannan yaja k'ofa ya fita harzai kulle kenan seta d'aga kanta suka had'a ido cikin tausayin junansu yace _i love you so much apple_
_tace i love you too manosh_
Harda d'an kwalla a idonta sannan yaja kofar da sauri ya rufe,ita kuwa hawayene suka zubo mata kona menen oho....
[7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

*dedicated to mom sudais* *(awansB???)*



35-36 Hankalin maman maryam ya kasa kwanciya,seta kira baban maryam a waya tana tambayanshi ko maryam ta iso? Baba yace a'a bata isoba,hankalinta ya sake tashi tace malam yaci ace ta iso ai,shi kanshi hankalinsa ba'a kwance yakeba,amma seyayita kwantar mata da hankali da daddad'an kalamai yana cewa kinsan fa maryam da taimako da kuma tausayi,zaiyu wani abinne ya tsaida ita a hanya amma bari nabi sawunta.
Mahaifin maryam ya rufe shop nashi yabi hanya ai ko seyaga almajirai sunata d'iban abinci a k'asa kuma ya tabbatar da cewa wannan kulan abincinshine. Wayansa ya d'auka ya kira matarshi ya tambayeta cewa me kika dafa minne yau,tace shinkafa da miyace mai had'e da wake,katse wayan yayi ya kama fad'in *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* tare da duduba guraren kozai hango maryam amma sam se *rivom* nata daya hango wanda shida kanshi ya sayo matashi.
Hankalinshi ya tashi sosai,ya kira number'n maryam yanata ringing amma ba'a d'aukaba har kusan sau biyar. Haka ya wuce gida a rud'e inda ya had'u da yah ibrahim da abokanshi suka gaisheshi ya amsa amma suna ganinshi sunan akwai abinda ke faruwa,ibrahim yace baba lfy kuwa,yace lfy lau ka biyoni gida.

Haka suka juya abokanshi suna tsaye daga waje su kuwa suka wuce gida. Mama tana jin sallama ta fito tare da cewa malam lfy,nan ibrahim ya gaisheta sannan baba ya gaya musu duk abinda ya gani a hanya sannan yayita kiran number'n maryam shuru. Addu'a suketayi dukkansu tare da tunanin to ina maryam take?
Ibrahim ya kira rashida da sameera a waya suka ce mishi sam maryam bata zoba,ya sake kiran zahida da amina suma sukace bata zoba,nan ya wuce gidan hajiya iya nanma batanan,koda hajiya iya taji lbrn hankalinta a tashe harda kukanta dan yadda take son maryam a ranta.

Nan tayi lullub'i ta wuce gidansu maryam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login