Showing 6001 words to 9000 words out of 72993 words

Chapter 3 - Auntyn Yara Book1 Complete Hausa Novels By Sadnas.doc

Sadnas   

06 Sep 2025

891

kece matarshi ko kuma wane yace mana ke zai aura, amma babu wanda ya tab'a sallama a gidansu se manosh.

Lubna ce kwance a d'akinta daya sha kayan duniya tana tambayan miher a waya toya ake cikine,miher tace wlh da gaskene amma nima majid yak'i gayamin mum ne na tambaya take cemin wai ai har sunje neman izini a girei yarinyar take. Ran lubna se tafasa yakeyi tace shikenan nagode,miher tace bro manosh yayi tfy yau kuma zai jima dan haka ki shirya yana dawowa sekizo,tace insha Allah miher nagode sannan sukayi sallama.
Hankalin lubna in yayi dubu ya tashi setace wlh dolene in fara shige shige gun malamai dan samo kan manosh kota halin k'ak'a koma wacece wannan yarinyar zan ganta ai kuma zanga dame tafini,kyaune ko gashi ko hasken fata ko kuma dukiya koma dai menene zakici ubanki wlh tunda kika shiga tsakanina da masoyina.

Manosh yana isa ya kira mum nashi sannan ya kira maryam,yace aunt na iso lfy,kunya taji sosai dan bata kirashiba tace to Alhamdulillah,yace baki damu danibako aunt,gashi ko kirana bakiyiba,tace am sorry bahaka bane,yace to menene,tace kayi hakuri zan gyara,dad'i yaji sosai yace toba komai I LUV U,kunya taji tayi shuru tana jinsa,ya kira sunan aunt,tace na'am,yace bakiji abinda nace bane,tace "me too" tare da katse wayan dan kunya dataji, shi kuwa dariya yakeyi yanaji sonta na k'aruwa a ransa...
[7:07am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNT'YN YARA??8]???]

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd


11-12 Auntyn yarane take koya musu karatu a cikin gidansu dan har black bord babanta ya mata dan koyar da yara,gidan nasu d'an daidaine ba wani gidan masu hali bane,amma dai koda yaushe gidan tass yake. Tsakar gidan flour ne na silinti se'a shinfid'a katuwar taburma ana karatu.

Marwan ne a hanya zuwa girei duba abokinsa da bayaida lfy,ya kira manosh a waya amma yayita ringing bai d'aukaba. Bayan yaje sund'an tab'a hirane se yayi mishi sallama ya kama hanyan koma,kiran salla yaji muryan k'aramin yaro nan danan imani ya k'ara ratsa marwan yace kai bari dai na k'arasa kawai nayi la'asar tunda an kira. Har gun masallacin ya isa ya paka motarshi ta gefe seya hango wani yara,ya k'ara gun masallacin yayimasa sallama yaron ya amsa tare da cewa salla zakayi,marwan yace eh wanene ya kira sallah yanzu,yaron yace nine,marwan yace masha Allah amma kana da murya mai dad'i menene sunanka,yace sunana ABDALLAH,marwan yace suna mai dad'i gaskya inaso mu kulla abota dakai,abdallah yace to shikenan ya sunanka,yace marwan,abdallah yace kaima sunanka da dad'i ga buta kayi alwala a nan girei kake,yace a'a ina jimetane,abdallah yace ayyah nikam anan girei nake kagama gidanmu can ba nisa,marwan yace to ashe zan dinga zuwa kana koyamin k'ira'a,dariya abdallah yayi yace sedai kaje gun Auntyn yara ta koya maka itace malamata,yace waye kuma Auntyn yara,abdallah yace itace malamata kokuma ince malamar yaran unguwannan harma dana nesa.
Marwan yace bari dai muyi sallah ko semuyi hira,yace to sega yara sun fito daga gidansu maryam mata sun wuce gida maza kuma sun nufi masallaci. Kowannen sallama yayiwa 'yan masallacin sanan suka hauyin alwala,marwan yana ta ganinsu abun ya burgeshi sosai.
"Bayan an idar ne marwan yace da abdal muje can muyi hira se in tafi. Bayan sun k'arasane yace ina jinka kagani na mijine kuma babba kanaga auntyn yaran zata koya min karatun, yace a'a kam kayi girma sedai in zaka dinga zuwa masallacinnan daga magrib zuwa isha kullum ana karatu da kuma litattafai masu yawa. Dad'in hirannasu sosai marwan yakeji yace to yaran can da suka fito daga gidancan fa kodai koyarwa ake acan,yace eh auntyn yara ce mai koyarwa bayan azahar zuwa la'asar,biyanta akeyi,abdallah yace a'a fisabilillah dai ai auntyn yara kowa natane kuma kowa ya santa babba da yaro babu wanda zai iya gaya maka halinta don ta cika goma cip cip. Dariya sosai marwan yayi yace matar aurece,abdallah yace a'a budurwace kuma kuma kasan me,marwan yace a'a,abdallah yace auntyn yara macece mai tarin ilimin addini dana boko gata da son mutane sam bata da kyamar d'an adam aduk yadda ta ganshi,kuma tana son taimakon dan adam,gata kyakkyawa sosai amma kuma 'yar karamace.
Dariya sosai marwan yayi yace kai abdallah duk ita kad'ai kodai ka kara da nakane,yace wlh da gaske ko inkirata ku gaisa ne,marwan yace a'a kace mata me?abdallah yace ince mata tazo abokina yana so su gaisa,marwan yace zata fito,yace eh zata fito bari inje.

Maryam tana sanye da aldoguwar riga jah ta nad'a gyalen akanta tana k'okarin fitowa,se abdallah yayi sallama ta amsa tare da cewa abdalla rashida fa ta shirya kuwa,abdallah yace wlh ban saniba zaku fitane,tace eh zamuje jimeta duba zahida ba lfy,yace to muje dama gunki nazo zaku gaisa da abokina. Mamaki ya kama maryam tace aboki kuma,yace eh,tace to muje se suka fito a tare.

Marwan ya zubawa budurwan kallo har suka k'araso tayi mishi sallama ya amsa sannan suka gaisa,tace to abdallah mun gaisa nizan wuce,abdllah yace to ai shima jimeta zaije abokina ka sauketa dan Allah. Marwan yace tobakomai abokina auntyn yara muje,batayi mamakin jin sunata a bakin marwanba,se tace a'a wlh da wata k'awata zamu tafi yanzuma gidansu zanbi kafin mu wuce,abdallah yace abokina yayatace bari naje na kirata yana juyawa sema ga rashidan tahowa,yace kama ganta,murmushi maryam tayi tace daga yin aboki se kuma a d'aura mishi nauyi,abdallah yace to ai hanyanku d'aya,marwan yace sosai kuwa kuma ai zan samu lada ko,abdallah yace kwarai lokacin rashida ta iso suka gaisa sannan abdallah yayi mishi sallama har ya juy se kuma yace abokina bani numbern wayanka,marwan yana fad'a mishi shi kuwa yana sawa a wayansa sannan yace nagode sena kiraka,marwan yace tonagode sena sake zuwa.
Rashida ta kaftawa maryam ido akan ta zauna a gaba,badan tasoba hakata zauna ita kuma rashida tana baya suka tafi. Koda suka fara tfy babu wanda yayi magana acikinsu,se marwan yace auntyn yara ina zakuje a cikin jimeta,tace gurin NTA ,yace ok gaskya abdallah yarone mai hankali yaron ya shiga raina sosai wlh,maryam tace mungode,yace yace inzo zaki dinga koyamin karatu,tayi murmushi tace toba damuwa seka zo,marwan ya d'auki wayanshi yace hello Majid yane,majid yace ka dawone,yace na kusa isowa dai,yace ok idan ka shigo kamin waya,marwan yace ok sannan ya katse wayan.

Babu wanda ya k'ara cewa komai har suka iso har gidan,sannan suka fito tare da cewa mun gode fa,yace bakomai wlh kozan dawo in maidakune,maryam tace a'a za'a mai damu mungode sosai,yace to shikenan nima na gode.
Har seda suka shige gidan sannan yabar gurin yanata yaba kyau da nutsuwan maryam da kuma halaiyarta da abdallah ya gaya mishi.

Hira sosai sukayi da zahida sunata nishad'i gwanin sha'awa,zahida tace samira tacemin sunje mubi ko,maryam tace eh wlh se gobe zasu dawo, zahida tace ku tashi muje YAKUBU SHOPPING LPAZA zan sayi always da kuma kayan ado sun k'are,rashida tace ashe dai kin warke to muje kar muyi dare.
"Shopping sukayi dukkansu d'an daidai sedai maryam tayiwa yaranta tsaraba. Harsunzo fita se maryam taga key wata ya fad'i daga cikin bag nata batare data saniba, da sauri ta d'auka ta bita hargun motar k'irar HENESI tace 'yar'uwa kin yarda key d'inki,yarinyar ta juya suka had'a ido ta karb'a tare da cewa ayya nagode sosai kuma kinga keyn motatace wlh bansan ya fad'iba nagode sosai,maryam tace karkimin godiya 'yar'uwa inaso kema ki taimaki mutane uku a rayuwarki sannan suma kice su taimaki wasu ukun,murmushi tayi tace to shikenan ya sunanki,tace sunana maryam,tace eyyah ni kuma sunana LUBNA,tace ok sannu lubna se anjuma,lubna tace dan Allah bani number ki mana,nan taba maryam wayanta tasa mata number sannan tayi flashin,maryam tace zanyi saving lubna ko,lubna tace eh nagode sannan ta wuce gunsu zahida suka tafi.
[7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd


13-14 maryam basu koma gidansu zahida dan gudun kar dare yayi musu daga nan sukayi sallama har suna k'ok'arin tare mota sega drivern manosh yayi parking tare da fitowa suka gaisa se yace oga ne yace inzo in maidaku gida. Murmushi maryam tayi tace to mungode,har zata bud'e gaba seyace no madam ku zauna a baya bakomai,batasoba amma haka suka zauna ya kaisu har gida sannan suka mishi godiya.

Marwan ne ya kira abdallah a waya suna hira yake tambayarshi cewa auntyn yara tana da saurayine? Abdallah yace eh akwai dai masu sonta dewa amma babu wanda take tsayawa dashi gaskya,meyasa to,yace wlh ban saniba nidai ban tab'a ganin tana hira da waniba a matsayin saurayi kana sontane? Marwan yace aboki kashe wayan zan kiraka kaji,abdallah yace to tare da kashewa.
"Marwan ya d'auki call d'in manosh yace captain busy busy nakiraka d'azu dan naje girei dama in tambayeka akan apple ne kuma inje mu gaisa se kuma baka d'aukaba. Manosh yace wlh ka bari kawai aikin namu ne se'a hankali harka dawo kenan,eh tun d'azuma,manosh yace ai kuwa gidansu ba b'oyayye bane a girei sunanta maryam amma amfi saninta da auntyn yara. K'irjin marwan ya buga yace auntyn yara,manosh yace eh wlh tanada son yarane shiyasa ake kiranta da hakan. Marwan yace ok sedai inka dawo semuje kawai,yace to shikenan sannan sukaci gaba da hiransu.
Bayan sun gamane ya sake kiran abdallah yace abdallah kabar wannan maganan auntyn yaran kaji,abdallah yace meyasa,marwan ya bashi lbr tas akan maryam da manosh abokinsa ko kuma ince amininsa. Abdallah baiji dad'iba dan ayau kawai amma se yaji yana son marwan kuma yanaso su kasance tare da auntyn yara. Marwan yace ya kayi shuru,yace bakomai wlh naso had'aka da aintyn yara abokina kana da kirki sosai,marwan yayi murmushi yace karka damu abokina shiyafi dacewa da auntyn yara danshi bai tab'a furtawa mace kalmar soba se akanta,ni kuwa nayi sosayya abaya har an gama komai da komai na auranmu ana saura 2weeks tayi zazzab'i na kwana d'aya shikenan ta tafi ta barni,tun lokacin ban kara furtawa wata mace kalmar soba shekara guda kenan. Lbrn yabawa abdallah tausayi yace Allah ya jikanta da rahama,yace ameen. Abdallah yace amma abokina dan Allah in tambayeka mana,marwan yace ina jinka,abdallah yace kana son auntyn yara? Marwan yace eh shiyasama na kiraka dan inji ko an mata miji,to ashe itace aminina yake bamu lbrnta kaga gara danyi shuru dan haka maganar ya zama sirri a tsakaninmu kuma kagayawa auntyn yara koda mun sake had'uwa wataran karta nuna mun tab'a had'uwa kaji? Abdallah yace Allah sarki abokina insha Allah zan gaya mata kasan me,yace a'a,yace da har ina tunani idan airenku ya tashi da auntyn yara zakayi mana walima namu na MAZA wanda zanyi karatu sosai dan yadda nake son auntyn yara kuma k'awar yayat ce. Dariya sosai marwan yayi yace to ai yanzuma bai b'aciba za'ayi insha Allah ka zauna cikin shiri kawai zan gayawa abokina ayi mana waliman mazan kaji,dad'i abdallah yaji yace wlh kana da kirki nagode,marwan yace nima na gode seda safe.

Maryam tana kwance a d'akinta abdallah ya kirata ya gaya mata komai. Mamaki tayi sosai tace eyyah dama shine abokinsu d'ayan kenan da suka gayamin bai samu zuwaba, abdallah yace eh shine,tace bakomai abdallah nagode kaji ka gaisheshi,yace zaiji sannan tace yau dai barita kira manosh.
"Ringing d'aya ya d'auka tare da cewa slm aunt,yadda yake kiranta yana mata dad'i sosai ta amsa wslm ina wuni,yace lfy sannan ya katse ya sake kiranta. Ta d'auka tana murmushi tace ya aiki,yace alhamdulillah yasu mama,tace lfyansu lau min godefa kasa an dawo damu gida,yace bana son godiyanki aunt,meyasa bakicemin zaki fitaba,tace bakomai,yace to daga yau idan zakije wani wuri kidinga gayamin pls,tace to shikenan,yace me kokeyi aunt,bakomai,yace zakiyi bacci kenan,tace eh,yace bazaki min hiraba,mirmushi tayi tace name kenan,yace ina kikaje yau,tace munje duba k'awatace zahida bata da lfy,yace eyyah sorry Allah ya bata lfy ta ina take a jimeta,nan dai ta mishi kwatance yace ok nasan gurin ai akwai wani abokin dad nawa acan,tace eyyah,yace daganan kuma se kukayi ina,tace YAKUBU SHOPPING PLAZA,yace me kika saya kuma dawa kuka had'u mutane nawa suka tsaidake? Dariya tayi yana mirmushi yace "yes tell me" tace babu wanda ya tsaidamu sannan mun had'u da wata sunanta lubna, uace lubna? Tace eh nan dai ta bashi lbrn,yace ok akwai wata lubna dana sanine k'anwan marwan abokina da bai samu zuwaba ita k'awar miher sista nace shiyasa na sake tambayanki,tace eyyah tama bani number"nta. Yace hakan yana da kyau ai Allah yasa ita ce,tace ameen.
Sunanta ya sake kira aunt,tace na'am,yace kin iya amsawa da NA'AM d'innan kamar ke kika k'irk'iri kalmar,dariya tayi sannan yace me burinki na gaba aunt,shuru tayi batace komaiba,yace tambayarki nakeyi fa,tace karatu,yace ehen seme,shuru tayi seyace aure,tace uhm,dariya yayi yace mezai hana kiyi auren sekiyi karatun a d'akin mijinki,kasa cewa komai tayi dan kinya,yace aunt bakice komaiba,tace tome zance,yace kice eh zanyi aure se incigaba da karatuna,dariya tayi sosai shima ya tayata,tace hmm,yace "whats is hmm?' Tace bakomai, yace aunt ki bari muyi aure sekiyi karatu kinji inaga hakan zaifi koh,batace komaiba,yace kokinaga bazan yadda kiyi karatubane,sisterna miher tana karatu 100 level kima majid ne zai aureta amma dole tayi karatu dokan dana kafawa majid kenan kuma ya amince,so kinga bakida matsala dani indai akan karatune aunt. Dad'i sosai taji tace to zanyi tunani akai,yace ok my apple kiyi tinani tare da shawara "i will be waiting okay?"tace ok nizan kwanta,yace to aunt ma'assalam,tace bissalam tare da katse wayar tana mai farin ciki tare da k'ara jin sonshi na ratsata.

Washe gari maryam ta shirya taje gun wata makwabciyansu mai suna Hajiya iya. Tsuhuwace mai kirki dason mutane kowa yasanta a unguwan,kuma kowa yasan yadda take k'aunar maryam sosai ta d'auketa kamar jikanta. Gata kala kala takeyiwa maryam dayake tana da d'a a yola mai kidin ne sosai dan haka maryam take morewa agunta.
[7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd


15-16 Lubna ce kwance a gida tana chartn setaga numbern maryam akan list nata. Nan take ta kirata suka gaisa sosai sannan maryam ta mata godiya.
Samira ta dawo daga mubi dan haka sukazo gun maryam ita da rashida sunata hira se wayan maryam ya fara ringing,tana dubawa taga zahida ce,tasa a handfree suka gaisa,se take gaya mata cewa majid marwan muhsin da kuma muh'd sunzo su gaisheta,maryam batayi mamakiba dan dama manosh ya tambayeta unguwansu. Maryam tace eyyah sun kyauta Allah ya biyasu su,tace ameen gaskya k'awata sun had'u,dariya su samira sukasa tare da cewa kai zahida kodai...zahida tace wlh kuwa muhsin ya kyasa yanzuma muka gama waya dashi,dariya suka sakeyi se maryam tace shikenan abu yayi kyau to Allah ya tabbatar da alkhairi,zahida tace ameen nagode sosai.
Koda maryam ta ajiye wayan dariya sukayi tare da shewa sukace lallaifa abu yayi kawaye da abokai hahahah. Maryam tace ya isa mana duk randa mukayi waya da manosh seyace in gaisheku,sukace to amaryan captain muna amsawa,kallonsu takeyi tana murmushi tare da cewa amarya tun bamuje ko inaba,rashida tace ai zakuje,dariya sukayi sannan ta d'auki kiran manosh tasa a hands free slm,yace wslm aunt kin tashi lfy,lfy lau ya aiki,yace kai kibari akwai akwai gajiya ban samu na kiraki da safeba wlh ban zauna bane hope kina lfy,tace lfy lau,yace yasu mama,tace duk k'alau suke,yace bakije gun baba a shop bane,tace eh se zuwa anjuma,yace ok,tace yanzu zahida take gaya min cewa su majid sunje sun dubata mungode fa,yace bakomai wlh muhsin wai yana ciki,dariya tayi tace to Allah ya tabbatar musu da alkhairi,yace ameen,ina samira da rashida da amina,tace muta tate dasu amma banda amina,yace to banisu mu gaisa,tace to sannan ta mikawa samira sukasha hida yanata mata raha,tace ab'asan soja da dariyaba amma kai gashi kanada far'a,yace kika sani kodan ina son k'awarkine,tace no bahaka bane,yace toya akayi kika sani,tace kowa ya shaidi soja baya wasa kuma ba dariya,manosh yayi murmushi yace to ai ni k'aramin sojane,manya ne suke hakan kuma sud'inma ba dukka bane. Sameera tace ina fata dai zaka rik'e mana friend namu da kyau,yace base kin fad'a samira "because i luv her over" dariya tayi tace to Allah ya barku tare musha biki,yace ameen nagode sosai,tace yawwa ga rashida. Rasha tace captain zance nece kodai prince manosh dan sunan naka na larabawane,dariya yayi sosai yace duk wanda kika kira,tace captain d'in dai ina wuni,yace lfy ya kuke ya apple d'ina,tace lfyanta k'alau ya aiki,yace alhamdulillah,tace to Allah ya sanya alkhairi adai rik'e mana ita amana dan kaine mutum na farko data amshi soyayyarshi,yace insha Allah rash bazaku samu wata matsala daga gareniba dan nima itace mace ta farko data fara shiga jinina,rash tace jini gabad'aya, yace "yes ina ji da ita sosai pls ku kula min da ita sosai" rash tace to gaskya munji dad'i Allah ya barku tare,yace ameen nagode da addu'arku,tace bakomai gata nan.
Maryam tana murmushi tace hello,yace eeeeh aunt ya akayine,tace babu,yace friend naki suna da kirki sosai wlh kun burgeni gaskya saura zahida da amina ki turo min number'nsu dukkansu kinji,tace ok mungode,yace banace miki bana son godiya ba,tace ai ya zama dole,yace nidai banaso,tace to shikenan byee yace byee.

Yaune manosh ya dawo daga abuja,nan kuma dad nashi ya dawo daga tfy. Manosh yaje har palo ya gaida dad d'insa sannan ya gaya masa ra'ayinshi akan maryam,dad yace a ina take,yace a girei ne,k'irjin dad nashi ya buga amma seya ce to badamuwa zanyiwa iyayen abokanka magana semuje,manosh yace yace to dad nagode,dad yace Allah ya sanya alkhairi yace ameen sannan ya wuce d'aki ya shirya da sauri cikin kananan kaya yasha turare sannan ya d'auki kits d'in tsaraban maryam yayiwa mum sallama yace zanje girei ne,tace to Allah ya kare,yace amin ya fita. Miher ta bishi har waje tace bro gun yarinyar ne,yace ke sunanta maryam ba yarinyaba, tace to ka gaisheta,yace yawwa k'anwata barima in baki numbernta ki dinga kiranta kuna gaisawa kinji, mihar tana son bro manosh sosai dan yana sonta kuma yana kulawa da ita sosai sam bayaso yaga an b'ata mata rai,dan haka itama taga ya dace taso abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login