Showing 60001 words to 63000 words out of 72993 words

Chapter 21 - Auntyn Yara Book1 Complete Hausa Novels By Sadnas.doc

Sadnas   

06 Sep 2025

881

amma fatanmu shine kusan gaskya akan cewa lubna 'yar cikunkuce k'anwa ga maryam.....
Su baba dai kasa cewa komai sukayi hakama su dad d'in manosh. Shi kuwa dad d'in marwan jiyake kamar ya tsaga k'asa ya shiga dan kunyan abinda mahaifiyarsa da kuma matarsa suka aikata,ga kuma 'ya'yan cikinsa su majid,"oooh" wannan abin kunya dame yayi kama?
"Maryam tanakuka ta kalli iyayenta inda kansu yake sunkuye dan basusan me zasuceba,musamman baba,yana ganin girman hajiya iya sosai,bazai iya yin komai akaiba illa yafiya. Maryam tagane komai akan halin da iyayenta suka shiga,hakan yasa ta matso kusa da iyayenta inda kowa yake binta da kallo,tace baba mama,nidai har abada???ihawaye sosai takeyi,inda hajiya iya taji zuciyarta na bugawa sosai,maryam tace nayafe musu har abada baba,kuma ina sake baku hakuri akan kuyafe musu,lallai marwan yayimin wani magana kafin ya tafi ya kuma nemi yafiyanmu tun kafin inji wannan lbrn,seyanzune nagane meyakenufin da wannan kalaman nashi,sannan yanzu haka bamu san w??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ani hali suke cikiba baba,dan lokacin da marwan yabar k'ofar gidannan gabad'aya baya cikin hayyacinsa,dan Allah baba kayafesu kaida mama domin ceto rayuwar marwan da rashida danko numbernsu baya shiga,seyanzu na gano dalilin ciwon marwan baba dan Allah baba ka yafe musu..... tana kaiwa nan ta mik'e zuwa d'akinsu tana kuka ita kuwa lubna kallonsu takeyi cikin tausayawa,tace baba kayi hakuri a yafe musu kodon rik'eni dasuka babu kyama babu wulakantawa se d'inbin soyayya da suka nuna min fiye da d'ansu bro marwan,ta sake juyawa ta kalli dad d'in marwan tace daddy har gobe bazan dena kiranka da sunan daddyba,haka kuma kema mummy ina k'aunarku har gobe,nagodewa Allah daya had'ani da 'yar'uwata dukda kun rabamu,kuma cikin k'ankain lokaci nayi koyi da halayenta nagari,daddy samun 'yar'uwa kamar aunty abin alfaharine agareni. Yau zan gayawa kowa abinda baku saniba,daddy nayiwa aunty mugunta har halakata naso nayi sakamakon son zuciya irin na hajiya iya,lokacin da aka nei aunty aka rasa nice nasa akayi kidnaping nata har zuwa jejin yankari,amma cikin ikon Allah aunty ta dawo gida lfy,kuma ita tasan cewa nice nasa a saceta saboda kar ayi aurensu da bro manosh dan k'aunarshi danakeyi acikin raina. Amma hakan baiyuba kuma tak'ita gayawa kowa abinda ya faru harda iyayenta ta b'oye musu saboda bata so ta b'ata tsakanin iyayenu da kuma aminantakar dake tsakanin bro manosh da bro marwan,haka kuma wanda nasa aikin ya yaudareni ya b'ata min rayuwata ta hanyar yimin fyd'e wanda duk alhakin auntyne ya kamani,shiyasa ban gayawa kowaba se ita auntyn,saboda ina tsoron fad'a muku agida daddy,sannan aunty itace kawai wanda ta fad'o min araina wannan lokacin,bayan na kirata nagaya mata komaine,sam batasa komai a rantaba tazo har inda na mata kwatance itata staftaceni ta rufamin asiri ta hanyar had'i aure da yah ibrahim dan tasan zai rufamin asiri zai kuma zauna dani zuciya d'aya.....
Lubna ta tsaya anan tana shehshek'an kuka inda hajiya khadima taketana kai har kusan duk wanda yake palon seda yayi kwalla dajin lbrn da lubna take bayarwa.
" lubna tace wannan sirri dana gaya muku yau babu wanda yasan dashi dagani se aunty,koshi yah ibrahim d'in baisan komai akan sace auntyba,amma dai yasan abinda saddam yamin ya kuma amince ya aureni. Nabaku lbrn nanne badan komaiba sedan innuwa hajiya iya da mummy cewa Allah yasa mana k'aunar junanmu tunba yauba nida aunty,sedai shaid'an yayi tasiri akaina har nake neman halakata dan soyayya,amma duk kukuka janyo hakan,dabaku rabamuba da tare zamu tashi inji jina kusa dani...kin cuceni hajiya kun tarwatsa min rayutawa nidai bazan tab'a yafewaba wlh.. mama ce ta kamota tana rufe mata baki tareda goge kwallan idanunta tace lubna ya isa haka tashi kije gun 'yar'uwanki kinji? Bamusu ta mik'e ta fita nata kuka,su yah ibrahim ma fita waje sukayi dukkansu 4 sukayi zugum a waje babu wanda ya iya cewa komai acikinsu....

"Jirginsu marwan ya sauka a abuja, inda suka sauka a hilton. Tun da marwan ya fita bai dawoba rashida ta shiga damuwa gashi wayarsu duk ya karb'e ya cire sim.
Saukowa tayi dama da kud'i a hannunta sosai,taje ta sayo k'aramin waya da sabon sim mma tama rasa waye zata kira,hakan yasa tafara kuka ko abinci bataciba.
Marwan kuwa tunda ya fita da motan wani abokinsa da yake aiki acan din yaketa tfy,baima san ina yake zuwa. Gabad'aya hanklinsa atashe yake,halinda ake ciki yanzu agida yola,sannan ko wani hukunci dad nashi zai yanke akan mum oho,yanzu abokansa sunsan komai,gashi babu lbrn aminsa dazai iya gayawa damuwarsa wato manosh. Kuka yakeyi sosai kamar k'aramin yaro,baya ko kallon gabanshi hakan yasa wata mota k'ok'arin kaucewa marwan amma sam yagagara saboda yadda marwan yake sake dososhi,se alokacin hankalin marwan ya dawo jikinsa ya fara fad'in innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ya kauce da sauri tare da tsyawa a gefe shima wancan din ya tsaya yana zagin marwan,shi kuwa se hakuri yakebashi amma sam se faman masifa yakeyiwa marwan,dak'ar dai ya hakura ya tafi. Shi kuwa marwan zama yayi acikin mota yana zubda kwalla.....
[7:18am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas




85-86 "dad d'in marwan yakasa cewa komai sabida bayida abin fad'a akan mahaifiyarsa". Mahaifin manosh ne yacewa mahaifin maryam dan Allah alhaji kuyi hakuri da abunda muka aikata muku,dukda dai mahaifiyarmuce dukkanmu tunda ta haifemu" amma tabbas sunyi kuskure mafi girma arayuwa,babu da wani abu da zamu iyace cewa sedai muyita baku hakuri daku yafemana sannan 'yarku dama tadawo hannunku tunda tana auren d'anka ibrahim. Za'a iya sanar da dangi amma ataimaka ab'oyewa mutanen waje. Mahaifin maryam yace bakomai alhaji wannan yawuce,sedai fatan Allah yasa mukiyaye gaba,Allah yasa wannan ya,zama darasi akan wasu,saboda munbarwa Allah komai wlh nafe duniya da lahira,amma fa idan da wanine aka mishi haka tofa bazai yafeba,sannan dole se hukima ta shiga shicin zance wanda hakan zai iya janyo wata babban rigima tsakanin familys harma yakai gidan yari.
Amma alhamdulillah yazo gidan sauki tunda duk gashi Allah ya had'a zuri'a a tsakaninmu" bazamu iya cewa komaiba se Allah ya kare nagaba,sannan nagode da kulamin da yarinyata da kukayi,nagane manufar hajiya iya da kuma dalilinta.
Sedai ba haka ya kama a bullowa lamarinba,ita a tunaninta lokacin ina fama da talauci ta yadda bazan iya rik'e koda yarinya d'ayaba,se kuma gashi Allah yabani kyauta biyu a lokaci guda,tofa musani Allah baya d'aurawa bawa abinda bazai iyaba,tunda shiyabani su toshizai bani hanyar da zan renosu,alokacin bani dashi,yanzu kuma ina iya rike mutanen daba jininabama,kamar yadda kuka rikemin lubna. Bakomai hajiya Allah ya yafemu gabad'aya. Har k'asa hajiya iya ta sauko tana kuka tare dayin godiya,hakama mahaifiyar maryam tace tayafe bakomai. Nanne dad d'in manosh yayi magana kansan a sunkuye dan kunya,yace mungode sosai alhaji Allah yabar zumunci,wani lokacin mata basu da tunani,duk abinda zuciyarsu ta rayamusu shi kawai sukebi tabare dasunyi shawara da kwakwalwarsuba,aduk lokacin da zuciya ya raya maka abu maikyau ko mara kyau tofa ana so mutum yayi shawara da kwakwalwarsa domin zuciya zata kaika ta baroka,yanzu kai dakayi hakuri wlh inda wanine bazai hakura,kuma kaduba abinda lubna tayiwa maryam,da maryam ta fad'a awannan lokacin toda abu ya lalace tun daga wannan lokacin se daga baya kuma za'aji kunya,kuma dukkune sanadin faruwar hakan. Hajiya da girmanki amma ki aikata irin wannan abu haka babu dad'inji,sannan kuka b'oyemin akan tsintota akayi wannan wani irin tunanine haka? da wani akayiwa hakan da sunanmu ya gama b'aci,yanzu haka kunyan had'a ido dasu nakeyi wlh mungode sosai Alhaji zamu tafi,yana kaiwa nan ya fito suka biyoshi a baya,bai k'arasa gun motaba ya yanke jiki zai fad'i da sauri su majid suka tallafoshi aka sashi cikin mota ida muhammad yaketa faman dubashi yace ai jininsane yahau sosai. Subhanallah ake ambato agun,da sauri suka shige se jimeta inda akayi hospital dashi.
Dad d'in marwan baida hawan jini sam,amma yau gashi dr yace hawan jinine ya kamashi sosai.
'Ya'yan nashi sunyi iyakan k'ok'arinsu agun dan kula da mahaifin abokinsu.
"Shi kuwa mahaifin manosh,yana cikin damuwa wanda har yake jin ciwon kai mai zafi,amma haka ya daure yana nan akan abokinsa.
"Su maryam kuwa fitowa sukayi daga d'aki sukazo gun hajiya iya kamar yadda babansu ya umarcesu.
Dan tun lokacin dataji abinda ya sami d'an nata shikenan aka rasa gane kanta. Hakuri aketa bata,itama hajiya khadijan sam ta kasa sakewa,hakan yasa tace zata komar da hajiya iya gidansu can na jimeta tunda akwai masu girki,ita zata tafi asibiti gun mijinta.
Haka aka rakosu har waje suka tafi. Maryam sebin motar nasu da kallo takeyi har sukayi nisa sannan lubna ta kamo hannunta tace aunty kidenasa damuwa aranki pls komai ya wuce kamata yayi ace kina murnan samun k'anwa.
Jiki sanyaye ta juyo suna kallon junansu tace lubna,bakya jin komai gameda abunda ya sami daddynkine? Lubna tace daddyn bro marwan dai. Maryam ta dafa kafad'arta tace lubna har gobe har jibi shima daddynkine sannan inaso ki nuna damuwarki sosai akanshi kamar yadda kike nunawa akaina inhar kinasona da gaske. Jikin lubna yayi sanyi ta wuce gida tasa himar nata har k'asa tace mama baba zanje duba daddy,babu wanda ya hanata,seda tazo dabda maryam tace zanjene saboda ke saboda kuma shi daddy bayi da laifi sansan zanjene dan bro marwan bayanan,nasan koba komai zan d'ebemasa kewa.
"Maryam tanata bin lubna da kallo harta dena kallonta zata shiga gida kenan setaji ana kiran sallan la'asar,koda ta juyo dan ganin mai kiran sallan seta wannan tsohonne dai wanda ta taimakawa a farkon littafin...

"Marwan ahankali yake tfy harya isa gun abokinshi yace kaini masaukina.
Bamusu ya kaishi batare dayace mishi komaiba,saboda yadda yaga marwan yasan bazai samu kowace amsa daga bakinshiba.
"Bayan ya saukeshine marwan ya fita yace nagode,abokinsa yace yaushe zanzo to?" Dan numberka kona kira bana samu. Marwan yace zan kiraka sannan ya shige.
Rashida tanata safa da marwa setaji nocking,da sauri taje ta bud'e kofa taga marwan atsaye kansa a sunkuye dukya galabaita yayi wani iri kamar maiyin azumi. Hakan ya tabbatar mata da cewa baici komaima,kallonta yakeyi cikin tausayi ga kwalla dasuke yawo a idanunsa. Tausayinshi ya kamata,ta rungumeshi sam ajikinta tana kuka tana cewa waime yake faruwane luv,dan Allah ka sanar dani bana son yadda nake ganinka ahakannan pls luv, baice da ita komaiba se kwallan da yake zubarwa,ahankali ta cire masa kayan jikinsa itama haa ta jashi zuwa toilet inda ya zama kamar jariri haka ta wankeshi tas sanan itama ta wanke jikinta ya d'auki towel itama haka suka fito a tare,yasa kaya tasake janshi wuza gun cin abinci amma sam yakici da k'yar tasashi yaci kadan sannan ya koma gado ya kwanta.
Bayan ta gama komaine tazo inda yake tana tsunbatan sassan jijinsa a hankali tana kallonshi har cikin ido. Shi kuwa sam hankalinsa baya jikinsa,lips nashi ta far kissing ahankali cikin nutsuwa,shi kuwa idanunsa arufe yana jin yadda take mishi,kamar a mafarki yaji muryan manosh yana cewa marwannnnn
Azabure,ya mik'e rash tace lfy luv,yace my luv manosh naji yakirani wlh ahine. Rash ta mik'e tace manosh fa kace,to a ina yake? Allah yasa dagaskene luv dabanda zaikai aunty farinciki maza muje muduba,bamusu yanufi k'ofa ita kuwa tasa himar ta fito,se juye juye sukeyi suna duba kofofin d'akinan ko zasuga fitowarsa koma suji muryanshi.
Can yasakejin marwannn,ai kuwa yana juyawa seyaga manosh yana k'ok'arin fitowa daga wani d'aki amma sam j'afarshi baya motsi kaman an manda da superglue. Da gudu suka k'arasa gun,amma ina take kofan ta kulle kanta. Bugawa marwan yakeyi kamar zai b'alla kofan amma ina,sunan manosh yaketa kira yanacewa prince gani ka bud'e kofan pls kaida waye? Shuru babu amsa,seyaga k'ofa ta bud'u da kanta,dasuka shiga shiga amma babu alaman mutane acikin d'akin.
Marwan yace ina bazai yuba wannan duk sharrin shukrah ce,duk yadda akayi suna nan,lallai bazan bar nanba senagano captain,nan suka zauna sunata addu'oi,ita kuwa rash tsone ya kamata sosai dan tabbas itama taga manosh da idanunta...
" aunty kuwa koda tsohonnan ya idar da kiran sallah,gunshi ta k'arasa tace baba,murmushi yayi mata yace inatayaki murnan samun 'yar'uwarki. Murmushi tayi mai had'e da tsoro tace nagode,nakuma tuna da abinda ka gayamin a yanzunnan. Yace masha Allah maryam zan tafi,tace baba dan Allah mijinafa,kokasan inda shukrah takai min shi? Dan Allah baba kataima. Baba yace wacece shukrah? Jikin maryam yayi sanyi tace baba aljanace ita,ta rabani da mijina tsawon kusan wata hud'u kenan ba'asan inda yakeba.
Baba yace ta ita maryam bansan komaiba akan wannan kimana tausayamiki sosai,Allah ya bayyana miki shi,kuci gaba da addu'a maryam babu wani abu dazai gagara,sannan kisa a ranki cewa Allah zai dawo miki da mijinki,karki dogara da wani kinji? Jikinta sanyaye tace to baba nagode tare da kwalla a idanunta. Ahankali tabar gun masallacin tayi hanyar komawa gida saboda mutane sun fara zuwa sallah,kan ta karasa kofar gida ta juya amsam bataga baba ba,kuma babu alamarsa tagurin. Mamaki,sosai tayi tayi da gudu ta shiga gida tana kuka ,hankalin iyayenta a tashe suke tambayanta ko lfy,tace gamo tayi da aljani. Iyayen suka tsaya kallon junansu,mahaifinta yace maryam wani irin gamo? Nan maryam ta basu lbr tun daga farkon had'uwansu da baba stohonnan har kuma taimakon daya mata a jejin yankari lokacin da saddam ya harbeta da bindiga a hannu da kuma abinda tsohon ya gaya mata akan lubna.
Mamaki sosai iyayen sukayi,babanta yace maryam anya kuwa lfyanki lau? Tace wlh baba lfyta lau yanzuma shinagani shine wanda kukaji muryanshi ya kira sallah. Baba yace ajani ya kira sallah kuma maryam? Tace eh wlh baba nasan bazaku yaddaba amma wlh shida kanshi yagayamin shiba mutum bane aljanine. Baba yace to Allah ya karemu dadukkan 'yan'uwa musulmai,suka amsa da ameen sannan ya fita zuwa masallaci yanata kalle kalle tare da tambayan jama'a ina wanda ya kira sallah yanzu? Wanine yace tun d'azu yabi tacan,baba yace shibazai tsaya yayi sallan bane? Yaro yace oho mishi tsohone kodai zaije ya dawone oho mishi. Haka dai su baba suka idar da sallah amma wannan wannan tsohon bai dawoba,baba kuwa ya jinkirta yanata karatun qur'an a masallaci harya isar amma baiga kowaba haka ya wuce gida. Lokacin suna cin abincine se maryam tace baba har yanzu lubna shuru kodai sun wuce gidane itada yah ibrahim,mama tace kirasu kiji,bamusu ta d'auki wayarta ta kira lubna,cikin nuryan kuka lubna ta d'auka tace aunty zan dawo anjuma kad'an,maryam tace ya jikinnashi? Lubna tace da sauki yana bacci,maryam tace yanaji muryanki kina kuka lubna? Lubna ta share kwalla tace aunty daddy ya saki mummy. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.......
[7:18am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas

*To you readers! They say LIFE is a mirror: if you frown at it, it frowns back: if you smile, it returns the greeting*.
*Is that true?*???i




87-88 Sakifa kikace lubna,tace eh sannan ta katse wayar.
"Maryam ta kalli iyayenta tace baba wai daddyn marwan ya saki hajiya khadija" duk basuji dad'in lamarinba,amma babu abinda zasu iyayi akai haka suka gama cin abinci suka wuce dan k'arasa shirye shiryensu.
Kusan 10:00pm yah ibrahim ya kawo lubna gida,idan suka dad'e suna magana da baba kafin ya tafi.
Ranan dai basuyi wani baccin kirkiba dan gobe zasuyi tfy.
Maryam kuwa tama rasa meke mata d'ad'i.
"Washe gari da safe mahaifin maryam ya sanar da tfyan da zasuyi a masallaci don yiwa maryam aiki,sannan kuma yasake rokon jama'a ayita addu'a wa surukinsa wato manosh Allah ya bayyanashi. Addu'a sosai aka musu awannan lokacinma.

Da misalin 9:10am yah ibrahim yazo ya kwashesu a mota inda suka wuce hospital suka gaida mahaifin marwan sannan suka wuce airpot. 10:20am jirginsu ya tashi abuja,suna sauka dama komai ya zama ready yah ibrahim ya gama komai suka wuce suna zaune zaman jiran tfya india.

Marwan kuwa suyita addu'a har rashida ta fara bacci,shine ya d'agata yakaita d'aki ya kwantar da ita sannan ya koma yayita zama harya gaji sannan ya dawo shima hakadai suka wayi gari.
"Bayan sunyi breafast ne marwan ya sake komawa d'akin amma bakoai aciki" mamaki sosai yakeyi abu kamar a drama?" Rash ce ta biyoshi hakadai suka sake dawowa d'akinsu inda take ce mishi itata sayi waya kuma tayita kiran numbern 'yan gida baya shiga dan haka ya bata numbern su majid,sam marwan yak'i yama karb'e wayan. Nan rash tayi fushi tace waime kake nufine kakawoni nan ka ajiyeni babu wani bayani jiya haka ka fita ka barni bakaika dawoba seda lokaci ya kure waima ina kajene marwan?
Cikin mamaki yake kallonta yau sunanshi ta kira kai tsaye. Yace luv yau nine kuma marwan? Sannan zargina kike kome dakike min wannan tambayoyin? Tace eh zarginka nakeyi saboda abirkice ka dawo jiya kamar wani bugagge idan ka gaji da zama danine nikam kamaidani gidanmu gabad'aya kacanja kadena bani hakkina idan ka sau matan banza awaje toka sallameni intafi gidanmu nan ta fashe da kuka. Shi kuwa marwan maganganun nata sun mishi zafi sosai gashi dama yana da damuwa,baice da ita komai yafita yabar mata d'akin tanata kuka.

Shukrah waike wani irin muguwace haka? Hahahha lallai kam manosh ka samu baki,wlh indai bazan samekaba tofa sedai in hallakaka itama maryam d'in ta rasaka tunda kai taurinkai kakeji dashi,danka samu na sake maka bakinka ko,tokamin bankwana manosh semun had'u a kiyama..............
Ihu mai k'arfi manosh yasa,awannan lokacin kuwa su yah ibrahim zasu tafi dama wayoyinsu akashe yake. Juyowa yayi yana kallon aunty se faman kuka takeyi tana tsaye,gunta yazo shida lubna sukace lfy aunty muje mana? Kuka ta fashe dashi tace sam bazatajeba ta fasa,mutanen gun suka tsaya suna kallonsu,da k'yar mahaifinta yashawo kanta ta yarda se waige waige takeyi har suka wuce tana kwalla.
Yah ibrahim ma kwallan yakeyi dan yana mugun tausayawa aunty sosai. Haka suka wuce cikin jirgi tana tsakiyan mamanta da kuma lubna jirgi ya tashi..
Rash kuwa tayi kuka harta gode Allah can sekashi ya dawo tanata had'a kayanta ciki kit. Kallonta yakeyi tare da tambayar ina zakije? Ko kulashi batayiba ta gama komai tazo wucewa seya kamo hannunta ya matseta a jikinshi yana cewa haba luv meyake damunkine,meyasa bazakin uzuribane yanzu har zaki iya tfya kibarni? Tace shiyafi komai sauk'i wlh. Yace luv bakigane bane ina cikin damuwa dan Allah kimin uzuri pls my luv,rungumeta yayi tsam yace inada bukatarki atare dani kece zaki kwantar min da hankali amma kuma shine kike gayamin maganganu kike k'ok'arin tfya kibarni? Pls luv kiyi hakuri i luv you so much.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login