Showing 15001 words to 18000 words out of 72993 words

Chapter 6 - Auntyn Yara Book1 Complete Hausa Novels By Sadnas.doc

Sadnas   

06 Sep 2025

885

sha'awar da nakeyiwa maryam ameen. Ta katseshi da cewa ya naga kayi shuru,yace bakomai kawai bana so ki tafine harse marwan ya dawo,murmushi tayi tace toshikenan kamin hira,yace kedai zaki min,tace ni nawa sun k'are ai,yace to mata biyu nake sofa in aura dake da kuma wata kin amince? Murmushi tayi tace eh na amince mana ai halal ne kana iya yin hud'uma,dariya sosai manosh yakeyi,wanda yake burge maryam dan manosh ya had'u wlh sedai sam bai fiye yin dariyaba wanda ta lura hakanma dan itace yakeyi se kuma dasu marwan ko miher. Manosh ya tsargu da irin kallonsa da maryam takeyi yayi sauri tsayawa da dariyan nashi yace "apple why are looking at me like that?" Kunya sosai taji dan batama san ya akai taketa kallonshi hakaba,kuma aduk lokacin take kallonshi sha'awarta tane kawai yake kamashi. Maryam tace ina son ganinka aduk lokacin da kake dariya dan kanamin kyau sosai manosh,jiyayi kamar ya rungumeta dan yadda yake ji,amma seya daure yayi d'an murmushi tare da d'aukan wayarsa ya kira marwan yace ganinan zuwa mutafi sannan ya katse wayar maryam tana kallonshi,shi kuwa bai sake kallontaba hannayenshi suna kan siterin mota yace apple am goying,mamaki taji amma setace tonagode Allah ya kiyaye hanya yare da bud'e kofar mota ta fita se nanne shima ya fito tare da d'aukan abubuwan da mum ta bata yake mata har zauren gidansu ya ajiye.
Tace nagode tana murmushi,kallonta yayi batare dayayi murmushi yace *minfu miyatti* sannan ya wuce motarshi ya shiga yaja yana mata bye,ita kuwa murmushi kawai take mishi daga k'arshe ta d'aga masa hannu sannan ta wuce gida.

Maman maryam tayi farin ciki sosai dajin yadda aka k'arb'i maryam hannu bibbiyu,ga kuma zannuwa da less masu tsada ga sarka da turare da mum din manosh ta bata.
Maryam ta koma d'aki tana kwance se kuma ta tashi ta bid'e kit nata ta d'auko memori tasa a wayarta ta sake tabbatar da cewa lallai wannan shine mahaifin manosh,hawayene suka fara zuba a idanunta se taji wayanta na k'ara,koda ta duba *peach &cream* ne seta d'auka tare da share hawayenta tace hello,manosh yace apple mun tafi,tace to Allah kare nagode,yace ameen *i luv u* murmushi tayi tare da cewa *she luvs u 2* dad'i yaji yace thankyou apple,tace always *peach* wayyo Allah manosh kamar zaiyi hauka yana mirmushi ya katse wayar yatana lumshe ido,marwan yace bari in karb'eka dan naga kamar ka gaji,dariya sukayi dukkansu sannan manosh ya fizgi motar kamar zasu fire sama,marwan yace a'a mudaije a hankali kaga dukkanmu tuzuraire hhhhhh

Maryam kuwa wasu zazzafan hawayene suke zub'o mata tinda ta ajiye wayar. Tace inason sosai manosh,yanzu ya zanyi kenan? Wayarta ta d'auka ta kira uncle ibrahim bayan sun gaisa tace dam inaso miyi magane in baka cikin mutane,yace ok bari na kiraki.
Bayan ya katsene ya sake kiranta yace yes aunty ina jinki,tace ka tuna da wannan vedion dana tura maka a wayarka,yace ai devio d'aya kika tab'a turamin na wanda ya buge mahaifina ko? Hawaye ya sake zubowa a fiskarta tace eh shi,yace eh har yanzu yana wayana ai,tace bakowa bane wannan mutumin illa mahaifin manosh yah ibrahim. What! Mahaifin manosh kikace,tace eh shine na tabbatar da hakanne yau danaje gaida mahaifiyarshi yah ibrahim bazan iya b'oye makaba dannima mahaifinka mahaifinane sannan mun dad'e muna nemanshi se gashi kuma ashe shine mahaifin manosh,kukane yaci karfin maryam take ta katse wayar. Hankalin ibrahim ya tashi sosai ya rasa meyake mishi dad'i musamman dayaji maryam tana kuka,don ya dad'e dasa son maryam a ranshi tun mahaifinshi yana raye ya sanar dashi,amma se mahaifinshi yace karka damu ibrahim ka gama karatunka tukunnan maryam 'yace aguna nima zafin samun kwarin gwuiwa idan ka gama karatu ka samu aiki se inyiwa mahaifinta magana tunda amininane. Hakan yasa ibrahim ya hakura yabar abin a ranshi amma kash *muna namu Allah yana nashi* hankalin ibrahim atashe ya wuce gidansu maryam.....
[7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

Dedicated 2 *ANEELURV*??.\



27-28 Uncle ibrahim yana isa yayi sallama,maryam ta fito tare da amsa sallamar,tunda ganin fiskarta ya tabbatar tayi kuka. Kallonta yakeyi mai cike da kauna,yace ina mama,miryarta k'asa ba tare data kalleshiba tace tana d'aki. Ibrahim yace aunty meyasaki kuka,shuru tati ta kasa cewa komai,ya sake cewa aunty pls banaso in sake ganin hawaye a fiskarki wlh na yafewa mahaifin camtain amma saboda kece kawai wlh dabadan keba danayi k'aransa,aunty kin wuce duk yadda kike tunani aguna sannan babanki ya rik'emu kamar uba tun bayan rasuwan mahifinmu dan haka ki wantar da hankalinki kinji wlh komai ya wuce zan samu baba anjuma muyi maganan.
"Maryam ta d'ago da kanta tana kallonshi tace nagode sosai yah ibrahim,basan dame zan biyakaba a duniyannan Allah yabar zumunci. Murmushi yayi mata tare da cewa ameen aunty pls kicire komai a ranki karki nunawa captain wani canji sannan karki sanar dashi kinji,to tace dashi yace to ai seki murmushi dan fishi bai kamacekiba,dariya takeyi wanda yake kara mishi kaunarta a ranshi nan sauyin kallon da yake mata ya canja,wanda ita ita da kanta ta lura da hakan,take jikinta yayi sanyi,shi kuwa juyawa yayi ya tafi batare daya sake cewa komaiba.

Tunani sosai maryam ta shiga akan yanayin yah ibrahim tace kodai sona yakeyi to? Kai a'a da sona yakeyi aida ya dad'e da fad'a kawai dan kila dan kokarinane yasa yake sona haka amma kuma meyasa yakemin wannan kallon da manosh yake min sannan ya tafi babu sallama?
Wayanta ta d'auka ta kirashi bugu d'aua ya kayse ya kirata ta d'auka da sanyin murya tace yah ibrahim katafi babu ko sallama? Yace am sorry aunty bazan iya tsayawa inaci gaba da kallonki bane,tace todai ai semuyi sallama koh kamar dai yadda muka saba. Murmushi yayi yace tokiyi hakuri aunty nayi laifi,murmushin ta mayar mashi tace ba komai ya wuce dama shiyasa na sake kiranka. Yace tona gode aunty ina so in miki wata tambaya pls ki gayamin karkiji kunyana,tace to inaji, "you love camtain right?" Shuru tayi dan bata tab'a tunanin jin wannan tambayan daga garesaba,yace aunty kinyi shuru,tace yah ibrahim yana da wani haline mara kyau kodai kasan wani abu mara kyaune game dashi? Yace "aunty" namiki tambaya kimin tambaya,cikin sanyin murya tace yah ibrahim bazan iya b'oye maka komai a duniyannan ba "yes ina sonshi" amma wlh idan yana da wani aibu kagayamun ko kuma baba,tunda dama ai nace kayi bin ike akanshi. Ibrahim yace hakane aunty wlh bayi da wani aibu ko hali mara kyau kawai dai na tambayekine,tace tomeyasa kamin tambayan? Yace yanzu nayi laifi kenan,yace bakayiba nima ina so ka gayamin me dadilin tambayan? Yace idan muka sake had'uwa zan gayamiki yayinda nake kallon fiskarki kinji,tace toshikenan nagode,yace ok bye sannan ya katse.

Maryam dai da tunanin maganansu ta kwana a rai kuma daahi ta tashi.
Rashida ce taje gun maryam,lokacin tana zaune a gaban *computer* tana sanye da blue jeans da kuma jan top mai dogon hannu ta nad'e kanta da *light brown* gyale k'arami,rashida tace kai amma kinyi kyau a kayannan bari in miki *picture* ai kuwa maryam tayi dariya fararen hakwaranta suka bayyana rash ta dauka tare da cewa gaskya ki turawa captain wannan pic din dan yayi kyau sosai wlh. Murmushi maryam tayi tare da kab'ar wayan rash tana ganin pic din, nan suka koma kan k'aramin gadonta tana shirya books nata rashida se d'aukata takeyi,maryam tace ke ya isama mana.
Dariya rash tayi sannan suka fara hira nanne maryam take gaya mata cewa mahaifin manosh ne ya buge mahaifinta kumata gayawa yah ibrahim,hankalin rashida ya tashi sosai ta mik'e tsaye tace mahaifin manosh fa kikace,maryam tace eh wlh wlh shine kinsan jiya naje gaida mum nashi acan naganshi. Rashida tace wlh bazai yuba,ya rabani da mahaifina shikenan aahe manosh bai sami mahaifi nagari wlh tunda har zai iya yin kissa sannan kuma ya gudu mugu mara imani wlh Allah ya isa mana. Maryam tace dan kiyi hakuri rash kidena fad'a haka,rash tace ai wlh ba mutumin kirki bane tunda haka yake Allah yasa camtain karya d'auko halinsa dan wlh indai halinsu d'aya to ina tausaya miki m??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????aryam. Maryam tanata bata hakuri amma ina rash se kuka takeyi harta fara cewa to yanzu kinsan hakan tome kuke ciki da captaim maryam? Maryam tace kamar ya rash? Rash tace har yanzu kina son captain, maryam tace rash wani irin magane haka kuma pls kiyi hakuri ki nitsu pls,rash tace in nutsu,hakan ya nuna har yanzu kina tare da captain kenan maryam mahaifina fa mahaifinkine,kuma har zaki iya ci gaba da soyayya da d'ansa,lallai nagode danke mahaifin na raye shiyasa keto marwan d'inma daga yau bani bashi tunda shi abokin manosh ne koma ince amininsa dan haka kema daga yau *bani bake maryam* tana kaiwa nan ta ta fice tanata kuka sosai.
Mamakine sosai ya kama maryam dajin kalaman rash,dan tunda suka taso ko musu bai tab'a shiga tsakaninsuba kowa ya sansu kuma yasan shak'uwarsu sannan maryam tana son rash sosai fiye da sauran k'awayenta dan haka se abin ya dameta sosai, dama mamanta ta tafi angiwa dan haka ta rufe gida tabi bayan rash.
Kuka sosai rash takeyi itama mamanta bata gida dan yare suka fita da maman rash d'in sunje barkan haihuwa. Maryam tace haba rash yau har zaki iya furta cewa *bake bani* akan manosh,rash nasan ina son manosh amma wlh soyayyar da nake miki yafi wanda nakeyiwa manosh,domin shi zan iya rabuwa dashi amma ke na d'aukeki tamkar k'anwatace da muke ciki d'aya meyasa zakice haka dan Allah? idan rash jajur dan kuka tace wlh karyane maryam dakam nasan kina sona amma banda yanzu dan haka ki fita kibar mana gidanmu ki fita bana bukatan in sake ganinki dake da kowa nakima ki fita anan da k'arfi ta hank'e maryam har waje se jinta tayi ta mannu da mutum ta bayanta. Da sauri ta goge hawayen idonta tare da juyowa se sukayi ido hud'u da yah ibrahim take hawaye yaci gaba da gangarowa a fiskanta ta juya tana kallon rashida da tsoro ya gama kamata dan ganin yah ibrahim datayi.
Wucewa maryam zatayi da kukanta se yah ibrahim yayi saurin rik'o hannunta yace auntyn kiyi hakuri meya had'aku? Karon farko kenan danamiji ya rike hannu maryam bata iya cewa komaiba se kokarin fisgan hannunta takeyi agun yah ibrahim tace dan Allah ka sakeni yah ibrahim zan tafi gida,yace no aunty dan Allah ki tsaya yana rike da hannunta ya juya rai a b'ace yana kallon k'anwarshi rash yace ke meya faru,jiki na rawa ta gaya mishi,ya e shine yau da hannunki harkin iya hankad'e maryam rash? Ina ruwanki azan,yana rik'e da hannun maryam harya isa gun rash *belt* d'in jikinshi ya zaro rash ta fara kuka tare da cewa dan Allah yah ibrahim kayi hakuri wlh bazan sakeba.

Rash ta tsorata sosai dan tasan halinshi sarai, kukda dai bai tab'a dukantaba tunda take. Maryam tayi saurin shiga tsakaninsu tana hawaye tace dan Allah ya ibrahim karka dake pls,tsawa ibrahim ya dakawa maryam wanda dukkansu seda suka tsorata yace aunty ki matsa! Rash ta rike maryam sosai tana bashi hakuri. Maryam tace kayi hakuri yah ibrahim amma sedai ka dakemu dukkanmu tana kuka sosai.
Jikinshi yayi sanyi dan yadda yaga maryam take kuka haka ya sake *belt* din a k'asa rash kuwa da gudu ta fita ta wuce d'akin mamanta ta kulle da key. Maryam ma tazo zata wuce amma seya tareta,kuka takeyi tace yah ibrahim zan tafi gida,yace *aunty am sorry pls akan abinda rash tamiki*,maryam batace komaiba tace pls kaban hanya in wuce,yace sekin share hawayenki,bai jira me zataceba yasa hannunsa yana share mata,tayi saurin kawar da kanta gefe tare da buge hannunsa daga kan fiskanta,amma ina seya sake mayarwa tare da rik'e hannunta yace pls aunty ki dena kuka wlh har cikin raina nake jin kukanki sabo da yadda nake *k'aunarki tunda dad'ewa*. Da sauri maryam ta d'ago da kanta suna kallon junansu sosai har cikin ido,hakan ya sake rikitar da ibrahim sosai aise ya tsinci kanshi da fara matso da fiskarshi dedai nata da niyan kissing nata. Idanunta ta zaro tare da bigeshi gefe tayi saurin barin d'akin da gudu ta wuce gida,shi kuwa wani ajiyar zuciya ya sauke huuuuuh! tare da nadaman abinda yake son aikatawa...
[7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

Dedicated 2 *billy tabacco*??.\


29-30 Maryam tana komawa gida ta wuce d'akinta dama mamanta bata dawoba,ta kwanta tana kuka sakamakon tunawa da kalmomin rash agare. Dan bata tab'a zaton cewa wani abu zai shiga tsakaninsuba.
Wayartace ta fara ringing kodata duba se taga manosh ne,haka tak'i d'aunkan call d'n nashi har sau 3.

Bayan azahar ya sake kiranta seta d'auka hello,yace apple ina kiga shiga haka,tace sorry bacci nakeyi dan kaina da yake ciwo,ya kake yasu mama,yace eyyah sorry apple ya jikin naki,tace da sauki sosai,yace zanzo da yamma kinji,tace to nagode sekazo.

Dab la'asar manosh yazo abdallah yana kiran sallah,alwala yayi yayi sallah sannan suka zauna hira da abdallah inda yake tambayarshi ina marwan,makosh yace yana gun aiki,nan dai sukai ta hiransu manosh se dariya yakeyi seda aka watse sannan maryam ta fito babu ko fara'a a fiskanta.
Ta k'arasa da sallama,suka amsa sannan abdallah yace auntyn yara yanaganki haka babu ko murmushi, tace bakomai abdallah banajin dad'ine,yace sannu Allah ya baki lfy,tace ameen sannan ya kalli manosh yace toni zan tafi seka sake zuwa,manosh yace to bari na baka sako,yace to,sannan manosh ya bud'e motarshi ya fito da leda da gani kayayyaki ne a ciki yan kanti ya mik'awa abdallah. Abdallah ya karb'a yace wazan kaiwa?manosh yace nakane na baka kyauta,godiya sosai abdallah yayi yace auntyn yara ki tayani godiya,mirmushi tayi tace mungode Allah ya saka da alkhairi suka amsa da ameen sannan abdallah ya tafi.
Maryam tace ko zamu shiga cikin gidane,yace yau kuma,tace eh ko kuma muje zaure in shinfid'a maka taburma wlh bana jin dad'ine,manosh yace amma kinje hospital ne,tace banjeba dan ko su mama basu saniba,yace tomeyasa,tace babu komai,kallonta yakeyi tun daga sama har k'asa sannan ya d'auki wayarsa ya kira muh'd ya gaya masa cewa inda hali yazo girei ya duba apple nashi sannan ya katse wayar tare da cewa to muje zauren karki fad'i min anan,murmushi tayi sannan ta wuce gaba shi kuwa ya fito da sayayyan fruits daya mata da sauran abubuwan kwad'ayi yabi bayanta lokacin taje d'auko taburma da karamin carpet ta shinfid'a mishi carpet din ita kuwa ta zauna a taburman.

Sam tak'i kallon manosh dukda dai tana son ganinsa dan yau red top ne a jikinsa da black jeans se kamshi yakeyi. Shi kuwa kallonta yakeyi sosai,can dai tace meyasa ka kira muh'd ai naaha magani,shuru yayi kamar baijitaba yana ci gaba da kallonta,da taga yayi shuru seta d'ago da kai tana kallonshi suna kallon juna,murmushi tayi tace nika dena min irin wannan kallon bana so,yace tobase ki hananiba,mik'ewa tayi taje ta yanko mishi kankanan daya kawo mata dasu apple ga greves dadai sauransu tayi jerensu a tirai kamar fiskan manosh sannan taje ta ajiye mishi ta yadda zai gane fiskanshi tayi drawing. Mamaki sosai yayi yanata kallon drawing d'in danya burgeshi sosai harya bashi sha'awan ci,amma kuma bayaso ya b'ata drawing d'in,kawai setaga ya d'ako wayanshi yanata d'aukan pic din friut d'in.
Bayan ya gamane yace fiskan waye kenan wannan,tace na wanda zaisha,dariya yayi wanda ya k'ara mata sonshi azuciyarta,yace haka fiskana yake kenan? Tace eh amma dai fiskanka yafi wannan kyawun gani. Dad'i sosai yaji amma baice mata komaiba,wayansane ya fara ringing ya d'auka ok bari na fito. Kallonta yayi yace bari muh'd ya shigo kuma ki tabbata kin gayamishi abinda yake damunki kinji ko, mamaki sosai tayi har mh'd yazo kenan,tace to sanna ya fita suka shigo tare.
Muh'd yayi sallama ta amsa sannan suka zauna tace ina wuni,yace lfy lau aunty ya jiki ashe bakiji dad'i ba,tace eh amma da sauki,manosh yace ba wani sauki wlh dairewa kawai takeyi danko a gida basu saniba. Muh'd yace haba aunty pls kidena wasa da rashin lfyanki karki sawa kanki ciwo kinji,mirmushi tayi tace kainane fa dama kuma nasha paracetamol,manosh yace towayace kisha? Murmushi tayi tare da kallonshi cikin zolaya sannan ta taahi ta wuce gida. Manosh yanata binta da kallo,muh'd yace haba prince irin wannan kallo haka,manosh yace wlh bata da lfy daga ganinta daurewa kawai takeyi pls ka gwadata sosai. Muh'd yace "calm down dude" zata samu lfy insha Allah. Faro mai sanyi ta kawo musu sannan ta zauna,muh'd yace mungode amma wannan fiskan yamin kyau kamar fiskana. Dariya sukayi dukkansu,manosh yace a'a kaje can samira ta maka naka wannan fiskan nawane kuma bazaka ciba,dariya mh'd yayi tare da d'aukan inibi d'aya yasa a bakinsa yace shikenan zanen ya b'aci. Manosh yace gaskya baka kyautaba,memakon ka jira in fara sha kafin kasha,mikewa maryam tayi ta sake d'auko inibi tazo ta mayar inda mh'd ya cire sannan tace shikenan magana ya k'are.
Dariya sukayi sannan manosh ya far sha cikin nutsuwa take satar kallonshi,dan bai tab'a cin wani abu suna tareba se yau.

Muh'd yace nagode aunty gaskya abin ya burgeni nima zance samira ta dinga min. Manosh yace copy copy,murmushi sukayi sanna muh'd yace aunty meke damunki ne? Tace wlh ciwon kaine kawai,k'irjinta yana mata ciwo amma sam tana jin kunyan cewa harda k'irjinta. Muh'd yayita tambayoyinta tana bashi amsa sannan yace ok ina zuwa bari inje inzo,manosh yace akwai wani damuwane,yace no bakomai sena dawo sannan ya tafi.
"Manosh yace kin tabbata abinda kike ji kenan?"
"Tace eh kanta na kallon wani gefen"
"Manosh yace apple bana so ki b'oyemin komai imma kina jin kunyan muh'd toki gayamin tunda baya nan"
Maryam taga bazata iya b'oyewaba dan yadda take jin k'irjinta,setace da k'irjina yana min ciwo sosai.
"Kallonta yakeyi cikin damuwa,dan yana lura da yanayinta yasan tana jin ciwo tadai k'i fad'ane kawai.
"Sunanta ya kira a hankali yace apple?
Kanta ta d'ago ta kalleshi har idonta yayi jah tace na'am tare da sunkuyar da kanta,yace se kuma inane yake miki ciwon? Tace shikenan....bata gama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login