Showing 69001 words to 72000 words out of 72993 words

Chapter 24 - Auntyn Yara Book1 Complete Hausa Novels By Sadnas.doc

Sadnas   

06 Sep 2025

893

yana dariya yana kallon marwan yace to ashe kaine d'an iskan daka karya mana doka tun'a wancan lokacinma bamusaniba,dariya sukeyiwa junansu sosai inda inda manosh yake kallon muh'd yace kodai in fad'i nakane abokina? Muh'd yace ohonka idanka tonama ai kanka ka tonawa... hakadai suketa hira cikin hara da dariya. Can se wayar marwan ta fara ringing,kodaya duba numbern waje yagani hakan yasa yayi saurin amsawa yace hello,muryan yah ibrahim yaji yace marwan,marwan yace yane mutanen india kun isa lfy? Yace lfy lau wlh yawanci numbernku baya tfy kaima da kyar na sameka wlh ka dawo daga tfyarnaka ne? Marwan yace eh wlh yau na dawo yasu mama ya aunty da lubna? Ibrahim yace suna lfy lau wlh auntynema bata jin dad'i wlh zazzab'i taketayi tunda muka bar nigeria wlh. Subhanallah ya jikinnata to? Yace da sauki inasu muh'd,yace kowa lfy kun samu masauki mai kyau ko? Yah ibrahim yace alhamdulillah wlh,manosh yace banishi mugaisa pls? Ibrahim yaji kamar muryan manosh,shi kuwa marwan baisan cewa babu wanda sukayi waya da 'yan india ba shine mutum na farko. Manosh ya karb'i wayan yace hello yah ibrahim,ibrahim ya kira sunanshi cikin mamaki yace manosh dakai nake magane? Manosh yayi mirmushi yace nine wlh ya kun isa lfy ina apple d'ina? Yah ibrahim yaji dad'in aranshi yace Alhamdulillah bari na kaimata kozata ji sauk'i gaskya nayi farincikin jinka captain Allah abin godia. Shima manosh dad'in yajin a ransa mara misaltuwa yanata so yaji muryan apple nashi,yah ibrahim yayi sallama a d'akin da aunty take kwance lubna ko sallah ko takeyi mama da baba kuwa suna can d'akinsu ko kuma ince masaukinsu yah ibrahim lfy kaketa sauri haka? Yace barima in had'a da gudu aunty kashi zakuyi magana,batare datasan wayeba ta karb'a dan atunaninta ma dad d'in manosh ne.
"Tace Assalamu alaikum"
wani sautin saukan numfashi taji"sannan akace "wa'alaikumus salam _my one nd only apple_.
Wayan ta cire daga kunnenta tana karewa wayan kallo sannan ta sake mayarwa kunnenta tace peach...? Sautin sauk'an kiss kawai taji akunnenta har cikin ranta taji wani ni'ima mara misaltuwa take ta fara hawayen farin ciki tace peach kaine kodai mafarki nakeyi? Manosh ya mik'e daga inda ya zauna kusada marwan ya shige d'akinsa su kuwa sebinshi da kallo sukeyi suna taya abokinsu murnan jin muryan matarsa...
[7:18am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas




97-98 "Peach yanaji kayi shuru?"
"Apple how are u"
"Ya jikinki my luv?"
Alhamdulillah peach kaine dagaske?"
"Nine apple,Allah ya dawo dani tare da taimakon addu'oinku agareni."
"Murmushi tayi tace yaushe zakazo india peach,ina shaik'in son ganinka my luv"
Karki damu *aunt* zanzo insha Allah kema kinsan nafiki son inganki ko?" Dan haka inaso ki kwantar da hankalinki yanzu haka k'ok'arin da naketayi kenan wlh.
Dariya tayi maicike dajin dad'i tace kai Alhamdulillah Allah abungodiya peach nayi matuk'ar farinciki wlh Allah,ina fata dai kana lfy?"
"Dariya yayi tare da cewa i'm fine aunt kikwantar da hankalinki lfyata lau jealousynah." Ya k'are maganar yana mata dariya
Itama dariyar tayi tace ka fara koh?
"Apple yasu mama da fatan duk kuna lfy,ina kuma sisterna lubna?"
Shuru tayi nad'an lokaci sannan tace kowa lfya sis lubna ma tanata murnan dawowarka gata tadameni waisedai in bata wayan,amma bazan bataba dan nima bangaji dajinkaba tukun."
"Manosh yayi dariya yace toki gaishesu,sannan kicewa sis lubna kawai nagaisheta yanzu bana son jin kowa se apple d'ina,dan haka tayi hakiri senazo magaisa."
Dad'i aunty taji,farin ciki ya kasa k'auracewa fiskanta tama mance da yah ibrahim yana tsaye agefe se shagab'a da kalaman soyayya kala-kala suke jefan junansu dashi abin ban sha'awa...

Marwan yana duba account nashi seyaga 0.00
"Yace lallai captain wato seda ka tabbatar wayan ta gama amfani kafin ka dawomin da ita koh?"
Manosh yace sorry luv ne yayi nisa nama d'auka ko muna tarene ashe awaya muke.
Dariya suka sa dukkansu muhsin yace shiyasa naga kamar ma seda kayi wanka kafin ka fito. Hahhhhhh!

"Washe gari aka sallami dad d'in marwan dayake ya samu lfy.
Gida aka wuce dashi inda mahaifin manosh da sauran 'yan'uwa suka bashi hakuri akan ya maida matarsa wato hajiya khadija mahaifiyar marwan
"Cikin saukin kai kuwa ya maidata inda marwan yaketa murna."
Sedai hajiya iya tana kwance ba lfy,tunda abun ya faru itama take jinya kad'an kad'an dan tak'i barima asan bata da lfyan se yanzu da ciwon yacigaba sosai.
Hakadai aketa faman jinya dan dad d'in marwan ya d'aukota daga girei ya dawo da ita gidansa inda take samun kyakkyawan kulawa daga gun mum d'in marwan.

"Manosh kuwa anata kan masa magani akan abinda ya sameshi gameda lfyanjikinsa akan abinda shukrah ta mishi."
Maganin *islamic* ake mishi wanda yake wanka da kuma shafa wasu mai da aka harhad'a dan jinnu,shine yake shafawa akan mazantakarsa dan dama sam kamar ya dena aiki.
"Wata rana manosh yana bacci seya tsincikanshi dayin mafarkin shida aunt kuma suna tarayya irin na ma'aurata acikin mafarkin nashi"
Kodaya farka kuwa,seyaga dagaske ya b'ata jikinsa wanda dole seyayi wanka."
"Yawansa ya d'auko a gefen gado ya kira apple"
Da sauri ta daga tare da cewa peach?"
Muryansa mai d'auke da sha'awarta yayi maganan cikin yanayi na kashe jikin mai sauraro yace "apple"
Seda ta had'i yawu sannan tace na'am ina kwana?"
"Lfy keda waye agurin?"
"Nida lubna ne"
"Ina so inyi magana dakene"
Ta kalli lubna sannan ta mik'e zuwa toilet dan babu inda zataje tunda a hospital suke."
"Tace ina sauraronka lfy?"
"Apple ina cikin jin yunwarki domin yau da mafarkinki na farka kuma koda na tashi senaga harna b'ata jikina pls do some for me apple."
"Murmushi tayi tare da cewa Alhamdulillah peach,insha Allah ka samu lfya kenan" yace no apple pls try something"
"Hhhh peach da... ya katseta da pls *aunt?"*
"Jikinta ya mutu tace ok...
Hmmm! Kunnuwana sun kasa d'aukan abinda *aunty* takeyiwa *prince manosh*, daga wayan aunty nake iya jiyo muryan manosh yanata tsanbatu,ita kuwa cewa take ya isa haka peach.
"Manosh yace no apple no."
"Yeah karka min asara dewa mana,kabar min sauran domin nima ina jin k'ishinsu sosai."
Hhhhhhh! Manosh yayi dariya yare da cewa *ok* my luv,thankyou so much luv u.
Koda taji ya katse wayar seta hau yin dariya tace eyyah peach kasamu lfy Allah nagode maka...
"Koda aunty ta fito daga toilet seta lubna tsaye tana nunata da yatsa tana cewa wato hakane koh?"
"Tofa lallai bazai yuba,domin inanan koda yazo babu abunda zai wakana harse malamai sunyi sharhi akan airenku tunda kusan *4month* kenan bakwa tare dan haka se an sake sabon aure."
"Maryam taja kunne lubna tace ba'aso k'ananan yara sunayiwa manya lab'e."
Bayan maryam ta wucene akabar lubna da ido tanabin aunty da kallon mamaki,ita kuwa aunty wayanta ta rungume a k'irji tace _"oh my peach,i missed you more"_ tare da rufe idanunta tana mirmushi tana kad'a kanta ahankali... lubna kuwa se ta bud'e idanu tana kallon ikon Allah...

Komai na tfyar manosh ya kammala.
"Kowa sako yake basa zuwaga aunty dasu yah ibrahim"
Sak'on addu'a kala-kala yanata godiya aminansane suka rakashi har abuja,bayan ya tafine sukuma suka dawo yola.

"Saukar manosh a india kenan yayiwa wani abokinsa *hakim* waya,batare da b'ata lokaciba hakim yazo ya d'aukesa basu wuce ko'inaba gidan hakim,bayan yayi wanka ne sam yak'i cin abinci ruwa kawai yasha yace shida apple nashi zaici abinci insha Allah.
"Tafe suke shida hakim har hospital d'in,dama acan shi hakim yake aiki,kuma tunda manosh ya dawo ya nemi number'n hakim ya gaya masa komai, dan haka hakim ya nemi su yah ibrahim kuma kullum seya zo dubasu,yah ibrahim dasu baba dai sunsan cewa hakim abokin manosh ne saboda ya gayamusu,amma aunty da lubna basu saniba.

"Isarsu hospital d'in suka had'u da ibrahim nan suka rungume juna da manosh,suna ta murna sannan nufi gunsu baba.
Manosh ya gaishesu cikin girmamawa sannan suka d'anyi hira kad'an se yah ibrahim yace muje gacan d'akinda su aunty suke fitowana dai sunata bacci dukkansu.
"Da sallama suka k'arasa,amma duk suna bacci abinsu"
Daga gefen gadon auntyne ya hango pix nashida ita dasu badallah sunyi kyau sosai. Murmushi yayi tare da sauke ajiyar zuciya
Ahankali ya k'arasa inda take kwance sanye da pakistan red riga da wando baisanta dashiba yasan tabbas a nan india suka saya na lubna blue amma duk tsarin iri d'ayane.
Sam ya kasa dena kallonta dan yadda yaga ta k'ara kyau sosai,aranshi yace garin ya karb'eki apple.
"Ahankali ya ibrahim yaje inda lubna ke kwance yamata magana a kunne yace(my tashi manosh ya k'araso)
Kamar jira take ai kuwa seta bud'e ido taga yah ibrahim yana mata murmushi,sannan ta dubi sauran dr hakim se kawai taga bro manosh yana shafe gegen fiskan aunty da yatsan hannunshi ahankali.
Ai da sauri ta tashi tare da murna tace "bro manosh?"
Ahankali ya juyo yana kallonta yana murmushi wanda yake k'ara mishi kyau yace na'am *sis lub*
"Ai kamar a mafarki aunty tajiyo muryan peach, kafin ta bud'e ido hakim yayi sairin janye manosh shiya tsaya a inda aunty take kwance,shi kuwa manosh ya b'uya a bayan hakim."
Koda aunty ta bud'e ido setaga yah ibrahim ne da dr se kuma lubna"
Amma sam tana jin wani irin k'amshin turare wanda ta tabbatar agun peach nata kawai take jinshi.
"Yah ibrahim yace aunty doctor ne yazo dubaki"
"Tace yah ibrahim kamar naji an kira sunan peach yanzu"
"Lubna tace sedai a mafarki k'ila kikaji, se kuma tayi murmushi tare dayiwa aunty'n alama da kanta wato yana bayan doctor hakim"
" take aunty ta gane manufar lubna dan haka ta tashi da sauri tasa silipas nata tayiyo bayan doctor hakim da sauri shima manosh ya fito ya rungume matarshi tsam ak'irjinsa itama haka ta k'ank'ameshi tana mai farinciki azuciyarta da fili,su kuwa dariya sukasa inda hakim ya koma gefe d'aya ya tsaya sunata kallonsu inda manosh ya rufe idanunsa luf yana juyata a hankali.
"Ganin hakan yasa yah ibrahim kamo hannun lubna batare dayai maganaba suka fito waje dukkansu domin subawa amaryam da ango guri...?
[7:18am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: ??@]???]AUNTY'N YARA??8]???]

Written by sad-nas

_zanyi amfani da wannan dama agaremu dukka, dan Allah 'yan'uwana musulmai koda bakwa karanta littafina toku daure ku d'an bani *1minit*_
*"'yan'uwana dan Allah kada mu dinga mance sa (baba buhari) acikin addu'oinmu nayau da kullum aduk lokacin da mukayi sallah."*
*"Harta yaranmu,komai k'ank'antarsu mudinga sasu yiwa shugaban k'asanmu addu'a Allah ya bashi lfy,Allah ya k'ara masa nisan kwana,Allah ya kareshi daga dukkan sharri da'ake tunkararsa dashi,Allah ya d'aurashi akan makiyansa ameeen."*???a???_


*LAST PAGE*



99-100 "Aunty tayi saurin d'ago da kanta tana k'arewa peach nata kallo cike da farinciki afiskarta."
"Shikuwa sake kwantar da kanta yayi ak'irjinsa yana cewa "please apple let me be okey?" Murmushi tayi tare da sake nitsewa sosai ajikinsa tana addu'a acikin ranta."
"Sund'auki lokaci sosai ahakan sannan tace "i luv u peach" "i luv u sooo much!"
"Ahankali ya d'agota suna kallon junansu cikie da shauk'in juna yace "d'ume avi?" Idanunta suka kawo kwalla tace "miyid'ima gorko am."
Kwallan daya cike mata ido yakebi da kallo tare da rik'o fiskarta da hannayensa biyu yace "sake fad'amin kalaman masoyiyata" fiskanta abin tausayi tace "ina sonka peach,k'auna ta hak'ika" ahankali hawayen suka fara kwaranyowa daga idanunta,amma dukda haka bata d'auke idanunta daga kallonsaba."
"Harshensa yakai gun hawayen yake lashesu cikin wani irin salo na k'auna"
"Ita kuwa mannuwa sosai tayi dashi tana shafe bayansa da k'ananan hannuta."
"Manosh ya sake kallonta har cikin ido yana murmushi yace "pls say it again apple"
"Murmushi tayi tare da lakace mishi dogon hancinsa da yatsan hannunta sannan tace "i maryam muh'd attah, luvs d prince d captain nd my sweet peach manosh soo verry much more...!"
Hhhh??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????hhhh!
"Manosh yayi dariya tare da d'agata sama dama kunsan bata da auki sosai,dan haka se juyi yake da ita acikin d'akin yana cewa "you are d best among d bests my heart." Akoda yaushe godewa Allah nake dayabani ke amatsayin matata ta duniya da kuma gidan aljannah insha Allah."
"Allah ya barmu tare apple"
"Tace ameen peach"
"Ya sake cewa Allah yasa mubar duniya tare rana d'aya lokacima d'aya"
"Ta sake cewa ameen"
"Yace Allah yara mana yaranmu ya albarkaci rayuwarsu bayan ranmu"
"Aunty tace ameen"
"Yace Allah ya biya iyayenmu da gidan aljannah"
"Tace ameen ya Allah"
"Yace Allah kabiyawa 'yan'uwa musulmai buk'atunsu na alkhairi duniya da lahira,Allah wanda basu da lfya Allah ka basu lfy,Allah ka gafarta mana zunubammu wanda muka sani da wanda bamu saniba, Allah ka d'aukaka musulunci tare da musulmai, ka k'ask'antar da kafurci tare da kafurai Albarkacin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S A W)...
"Manosh da aunty'n suka amsa da ameeen,nima sadnas nace ameeen,kufa masu karutu?"

"Manosh ya sauke aunty ahankali tare da matse tsam ajikinsa yace "i miss you 3much apple."
"Tace me too"
"Fiskarta ya rik'o yana mata wani irin kallo mai kashe jiki da brawn eye nashi.
"Kunya ta tsinci kanta aciki"
"Shikuwa seya d'aura harcensa akan saman idonta yana yawo dashi harkan hancinta"
Koda yazo nan seya kira sunanta "aunt?"
Kaita d'ago anitse suka had'a ido dashi,harcensa yasa akan lips nata ya lashesu cikin wani irin salo."
Yad'an juma ahakan sannan ya fara tsotsesu kamar wanda ya samu zuma"
"Itama seta farayin yadda taji yake mata idanunta a rufe.
"Asannu suka fara kissing d'in junansu kamar bazasu sake junansuba,duk sun gama shiga wani hali kusan 10minit."
"Nocking lubna taketayi amma sam basuma jiba"
"Tahad'a da sallama shuru."
Aiseta sake sallama da karfi tare da bud'e k'ofan ta shigo.
"Aunty dai taji shigowar mutum,amma sam manosh yakasa barinta taga wayene"
"Se tsotson abarsa yakeyi kamar "kare yasamu nama"
Ganin haka yasa lubna yin murmushi ahankali ta fita tare da rufe kofan ta yadda bazasujiba."
"Manosh ya saki bakin apple yace koma wayene ai sunsan abinda zai faru bayan had'uwata dake,dan haka ad'aga mana kafa na 3hrs."
"Ido aunty ta zaro tace 3hrs fa kace peach?"
"Yace yes! Yana d'aga mata gira tare da sake maida bakinsu ya had'e guri d'aya suka d'aura daga inda suka tsaya."
"Uhmm! Abun ba sauk'i fah."
Lubna tana tsaye abakin kofa tama rasa ya zatayi,domin dama doctors ne zasu shigo gun aunty shine yah ibrahim yace lubna taje ta sanar dasu,se kuma gashi ta fito tana tsaye abakin kofan."
'Ya ibrahim ya kirata,tace ina zuwa"
"D'akin ta sake shiga da sallama,amma wannan karon setaga aunty kwance ajikin manosh inda shi yake kwance akan gado amma bakomai sukeyiba fase kissing d'in juna."
"Da sauri ya rufe kofan tare da bubbugawa da hannunta tana cewa aunty ga doctors zasu shigo dubaki."
"Ai cikin sauri aunty tabar jikin manosh tare da kamo hannunsa wai ita adole zata d'agoshi daga kan gadon.
"Ai kawai seya janyota ta sake fad'owa jikinsa yayinda shi kuwa yake mata dariya yace kinajin zaki diya d'aganine?" Tace pls peach kaji fa doctors suna waje,kuma nasan hardasu mama da baba za'a shigo yanzu hakafa suna tsayene awaje wlh kunya nakeji pls katashi."
"Bashiri manosh ya tashi tare da gyara jikinsa da sauri-sauri,ita kuwa aunty se dariya take mishi harya k'arasa bakin k'ofa kafin ya juyo yana kallonta tare da d'aga mata gira d'aya ya kuma kashe mata ido sannan ya fita."

"Manosh yana fita yaga lubna akofar d'akin,makzewa yayi yace ah *sis lub* yaushe kikazo?"
"Murmushi tayi tace awa d'aya da suka wuce."
"Manosh ya sosa gashin kansan sannan yace bisimillah tana ciki sannan ya wuce da sauri ita kuwa tanata binsa da kallo tana dariya ta shige d'akin."
"Shuru aunty tayi tana kallon lubna"
"Lubna kuwa taje kusa da ita ta zauna tana tace uhumm abun dai ba sauk'i sam."
"Aunty taja kunnenta tace tokema meya kawoki a irin wannan lokacin?"
"Lubna tace ganin k'ok'op"
"To ai kingani koh?"
"Lubna tace sosaima kuwa"
"Aunty tayi dariya tace wayyo Allah, luv yayi arayuwa wlh tare da rungume lubna daga zaune."
"Lubna tace sosaima kuwa luv yayi kam,amma kuma kudai bansan me kuka aikataba dan babu aure a tsakaninku tunda 4month kenan bakwa tare, kuma ance idan mata da miji basuyi tarayyaba har sawon 4month tofa babu aure se'an sake."
"Aunty ta gyara zama tace Allah malama lubna?"
"Lubna tace sosaima kuwa,kuma gashi ku bayan kiss ma harda runguman juna,dan haka dole idan malamai sunzo maida aurenku to zan gayamusu harda abunda nagani domin suyi muku sharhi akai."
"Hhhhhhhhhh!"
"Aunty tayi dariya,tace to malama lubna babu wani aure daza'a sake atsakanina da peach domin kuwa aurenmu yananan babu abinda ya sameshi."
"Shi kuwa kiss da duk wani abu da kika gani munyi sharhinsa shine d'unbin lada da muka samu, sannan wannan idon naki maison ganin k'ok'op wataran seya makance."???i
"Hhhhhh! Sukasa dariya dukkansu daidai nan kuma dictor suka shigo dasu manosh."


*.......*
"Bayan sati d'aya dayiwa aunty dashe k'odan 'yar'uwarta lubna kenan yanzu.
"Cikin ikon Allah anyi aikin cikin nasara sedai muce Alhamdulillah." Domin aiki yayi kyau kuma dukkanninsu suna cikin k'oshin lfy,ga kulawa na musamman da suke samu daga gun mazajensu da kuma iyayensu kai harma da doctors d'in."
"Manosh ne zaune da apple nashi tana kishingid'e ajikinsa yana bata tea baki"
"Yace Allah yabaku lfy apple,nima insamu in sauke nauyin daya dad'e akaina."
"Murmushi tayi tace ameen peach d'ina wlh har tausayi kake bani,wata kusa hud'u bama tare gashi kuma yanzu an k'ara mana wasu watannin. Ina tausaya maka peach amma idan kana ganin zaka takura to wlh na amince maka daka k'ara aure domin ka samu biyan buk'atanka dan nasan ku maza bakwa iya jurewa kamar mu mata.....
"Manosh yace haba apple banaso kina sa irin wannan tunanin aranki pls,nasan cewa maganarki gaskyane bakowani namijibane zai iya jurewa,wasu sekiga sun fad'a neman matan banza wasu kuma auren suke k'arawa saboda gujewa sab'on Allah, amma Alhamdulillah kuyita tayamu da addu'a Allah ya karemu daga sharrin shaid'an domin yana tasiri akan kowa sedai wanda Allah ya kare."
"Dad'i sosai taji har cikin ranta,tace insha Allah sweetheartnah."
"Yace amma dagaske zaki yarda in k'ara aure?" Tace ina k'aunarka matuk'ar k'auna peach,sannan kishi halittace daga jikin ko wace mace sedai nawata yafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login