Showing 27001 words to 30000 words out of 78127 words

Chapter 10 - BIYAYYA Book Complete Hausa Novels by HAERMERBRAERH.txt

17 Oct 2025

1453

da shi a gidan nan har ta janye hankalin Alhaji daga kammu,"

Yawu hajiya babba ta had'iya mai d'aci domin kuwa dik masifa da tijarar ta bata da qwarin guiwar tinkarar Eamaan da maganar komai,cikin jinjina kai Hajiya Babba tace wa Hajiya qarama,

"Lallai baki san wace ce Eamaan ba ashe ke har yanzu,to bari kiji ba dani za ai wannan abun ba, amma in kin dage nima abun na ci min tuwo a kwarya na dai kasa magana ne kawai sai na raka ki ina gefe ki yi mata tatas ɗin mu dawo,"

" Eh na yarda muje ki rakanin ni zan yi mata Magana,haka kawai muna zaune yarinya qarama tazo ta janye mana hankalin miji? Ke ni fa na kula dake da Sahabee wani tsoron ta ma kuke ji, Iya ma kwana biyu ta yi sanyi akan yanda take yi mata masifa a da, to ni ba na tsoron ta, dama ina d'aga mata qafa ne saboda tana son yara na, amma yanzu ba wannan maganar,"

Tashi suka yi suka nufi hanyar sashen Eamaan,sun same ta ta na zaune ta ɗora qafafun ta a kan center table tana kad'a su a hankali tare da miqar da su ta kuma komawa ta lanqwashe su cikin salo,zaune take daga ita sai guntun wando pink da rigar wandon,wadda iyakar qirjin ta ta rufe sai dogon hannu da hula da take da shi,cikin ta da bayan ta duk a waje suke gwanin burge mai kallon ta,gashin ta kuwa ta d'aure shi wasu sun fito sun zuba a gefen fuskar ta suna reto gwanin sha'awa,dik wannan karairayar da take yi da kashe muryar ashe waya take yi da Alhaji, dan kuwa yanzu ko bata kira shi ba shi zai kira ta su sha soyayyar su.

Wata iriyar mutuwar tsaye suka yi dan jin maganganun da take yi wa Alhajin na qarshe, shagala suka yi da kallon shigar da tayi da kuma kyakkyawar surar ta da yanda ta iya sarrafa jikin ta naturally ba wani iyayi da gwalangwaso, ashe haka Alhaji yake shan kallo a jikin wannan halittar mai tsananin kyawun diri?

Lallai kishi ko faɗa da Eamaan abu ne mai matuqar wahala a wajen su dan kuwa sun kwana biyu ita kuwa a ganiyar quruciyar ta take,Eamaan kuwa tana ganin su sai ta kashe wayar ta duqa kaɗan ta na gaishe su,Hajiya Babba kam gefe ta yi dan har yanzu tana shakkar Eamaan,ba ma zata iya buɗe baki ta amsa gaisuwar da take yi mata ba balle tayi mata faɗa,Hajiya Qarama ce ta kalli Eamaan a sheqe cikin kishi da b'acin rai tace,

" ke karuwar gida hawainiyar ki ta kiyayi ramar mu,kina daga cikin gida kina zabga karuwanci kina son karb'ar mana miji daga zuwan ki, yanzu gaba ɗaya hankalin shi ya tattara ya koma wajen ki, to bari kiji da kyau, ahir ɗin ki da shiga gona ta dan kuwa ni ɗin nan da kika ganni bani da kyau bani da mutunci, ki tambaya ki ji ba ragowa tsakani na da duk wadda zatai qoqarin rabani da Alhaji,"

Murmushi Eamaan take ta zabgawa, na ganin tsantsar haukan su da wautar su,cikin murmushin ta miqe daga durquson da tayi dan gaida su tace,

" Hajiya Qarama kenan amma gaskiya na yi matiqar mamakin zuwan ku nan dan yi min gargad'i akan wai ina qoqarin mallake maku miji, na farko dai ma ku kunsan ni da Alhaji auren had'i ne ba wai son shi ne yasa nake duk abinda nake yi ba, ina yi ne dan taimakon ku da kare mutunci na,yau ace kamar ni Eamaan a ga mijina yana yawo yana raba jikin shi ma kowacce jaka da god'iya ni ina zaune a gida kamar hoto to na faɗi,dan haka dole na kare masa mutuncin shi wanda shine namu, ke hajiya qarama kina ɗaya daga mu'assasin yawon Alhaji, domin kuwa ko a yanzu kin isa misali,dan Allah dubi kayan jikin ki tinda ya tafi baki yi wanka ba da alama balle canja su,kuma a haka kike rayuwa koda yana nan, kin kasa gane cewar Alhaji mai tsafta ne, ta ya kike tsammanin ya kusance ki da datti haka? Ai dole tinda shi mai ra'ayin bin mata ne ya fita ko qarfe nawan dare ne akwai masu saidawa a waje yaje ya biya buqatar shi ya dawo.

Sannan da kike kirana karuwar gida Allah ya kiyaye kalmar karuwa ta rab'e ni, dan kuwa ni na fi qarfin karuwa, domin kuwa su zina suke yi ni kuwa jima'i nake yi da mijina halas d'ina babu tsoro sai nutsuwa,ba zunubi sai lada,dan haka kar ki sake kirana da karuwa tinda ni na fita gata da matsayi na fita sanin me mijina yake so menene idan na yi yake rikita shi, na fita bashi abinda ya dace,in kuma baki yarda ba zaki gani zai ci gaba da bin wasu qadangarun barikin ko zai daina? In kuka bani had'in kai sai mu haɗu mu riqe mijin mu mu zauna lafiya,in baku bani had'in kai ba na riqe shi ni kaɗai.

Sannan masu zuwa su yi ciki a waje su na qifad'in yaran su yaran cikin gida ne ina sane da su suma,su kuma masu zina a cikin gida su ci gaba kar su fasa"

Wata irin faduwar gaba ce ta kama Hajiya Qarama, bata san sanda ta zauna a bakin kujera ba saboda jiri da Wani duhu da ta fara gani,Eamaan kuwa ta kalle ta ta qura mata ido yanda take yiwa dik wani mara gaskiya, gaba ɗaya jikin Hajiya Qarama ya kama rawa,shin a ina yarinyar nan ta san sirrin ta? Yau ta shiga uku ta lalace sirrin boye ya fito fili,kullum suka yi faɗa da Hajiya Babba idan tana yi mata gorin haihuwa sai dai Hajiya Babbar ta zarge ta akan yaran ba yaran Alhaji bane amma ba dan ta san asalin gaskiya ba,murmushi mai sauti Eamaan ta yi ta kalle su dika tace,

" ku kiyayi Eamaan dikan ku,ni ina aiki da hankali da hangen nesa ne ba da wawanci ba, sanda Alhaji yasan abubuwan da kuke aikatawa tabbas bai isa ya ce komai ba dan shine sanadi,shi ya jawo kuka lalace a qarqashin ikon sa domin kuwa zina bashi ce,kunga kenan bashi ya biya da ku,indan Kun gama abinda ya kawo ku ku rufe min qofa saboda sauraye ni na yi ciki dan banda lokacin ku"

Eamaan sai ta yi shigewar ta uwar d'aka ta barsu zaune cike da tsoro da mamakin ta, da kyar suka ja tsumman rayuwar su suka bar wajen,Hajiya Babba ce tabi bayan Hajiya Qarama suka shiga bangaren ta,cikin jimanta abinda ya faru Hajiya Babba tace wa Hajiya qarama,

"Me na faɗa maki game da yarinyar nan? Ai duk inda kike zaton ta ta wuce nan, yanzu sai ki bani labarin ya akai kika haifi yaran nan dan mu san mafita,saboda in bamu ɗauki mataki akan ta ba asirin mu zai tonu gaba ɗayan mu,"

kallon Hajiya Babba ta yi ɗauke da alamar tambaya, kenan itama nata asirin ya tonu Eamaan tasan sirrin ta,cikin sanyin murya Hajiya qarama tace,

" A gaskiyar magana Hajiya yaran nan bana Alhaji bane, Yaran abokin shi ne d'an majalisa dake a Abuja da zama, in ya shigo Kano sai ya min waya na je mu had'u,ni kuma sai na faɗa maku na tafi gidan mu,"

A razane hajiya Babba ta miqe tana bin ta da kallo, ita kuma sai kuka take yi, cikin kukan tace,

"Dan Allah ki rufa min asiri kar wani ya san maganar nan, ba wanda ya san zancen nan sai ku biyu,dan ko Alhaji Saminun ban sanar wa ba, in Alhaji yaji na shiga uku, na yi miki alqawarin zan riqe maku amanar ku ke da Sahabee,"

Hajiya Babba qara rikicewa ta yi da jin kalaman Hajiya qarama, kenan itama tana sane da neman juna da suke yi ita da Sahabee amma bata taɓa magana ba dan tasan itama tana fita nata yawon, dafe kan ta ta yi bata ce komai ba ta fice daga sashen Hajiya qarama, abun yayi mata yawa a zuciyar ta,shin meke faruwa ne a gidan nasu se kace ana annobar zina a gidan ? wanne irin shaid'anin ne ya shigo masu gida wai ace matan mutum ɗaya na yawon banza, suna mu'amalar aure ba da mijin su ba?

Hajiya Babba na cikin tinanin nan Sahabee ya same ta, ya na shigowa hannun shi ya sa a qirjin ta da ta daure cikin bra ya matsa ya kai bakin shi jiki kamar mijin ta na halal ya hau sha, a hankali ta saki ajiyar zuciya ta kalle shi, nan da nan kewar shi da ta yi na kwanaki ta taso mata har tayi sanadiyyar jan shi suka fara tattab'a junan su,tashi tayi ta nufi qofa ta rufe da key gudun afkuwar matsala sannan suka fara masha'ar tasu, ba kaɗan ba Sahabee ke yin dik abinda yaso da Hajiya Babba,nishin ta kawai ke tashi a d'akin hankalin ta kwance babu wata fargaba a tare da ita,da sauri Sahabee ya danne bakin ta da nashi, a haka yake yi mata rad'a kan ta yi ahankali kar ta jawo masu mutane, d'aga mai kai ta yi suka ci gaba da abinda suke yi, basu suka rabu da juna ba sai da aka yi isha'i sannan ya d'aga ta, duk ta yi laushi har ma ta fara bacci ya lallab'a ya sa kayan shi ya fice.

A ranshi yake ayyana,

'Ohh ka ji ikon Allah malam mace sai d'anneman muni amma gata nan zam zam da ita,'

Yana shiga ɓangaren su ya tadda Eamaan ta gama had'a wa Iya abinci ta d'aga kai ta kalle shi,nan take gaban shi ya yanke ya faɗi dan kuwa a zaton shi yau ma ta gan su,hankalin shi a tashe ya durqusa gaban ta zai fara magana ta bashi wani kallon kar ka kuskura, miqewa ya yi ya had'iye maganar shi sai kyarma yake yi,cikin dakewa Eamaan tace masa,

"Me ka yi min da zaka wani durqusa min haka salon Iya ta fito tace na yi maka wani abu? Kar ka kuskura ka sake yi min haka ni babu komai tsakanina da kai da ya wuce fatan shiriya, ba ni na halicce ka ba, dan me zaka ji tsoro na sama da wanda ya baka lafiyar da zaka bauta masa amma kake saɓa masa da lafiyar? Kar ka kuskura ka sake ganina ka nuna kana shakkata, domin ni din ban da wuta banda aljanna, ka qi bin dokar mai wuta da aljanna kaga sai ya saka ka a inda yaga dama,"

Rab'awa tai ta gefen shi ta shige ta je ta sanar da Iya ta gama haɗa abun kari sannann ta ja mata qofar ta tafi, ba laka a jikin shi ya wuce dakin shi ya rufe, Iya kuwa da ta fito sai da ta biya ta d'akin shi tai bugun duniya shiru yaqi bud'ewa,yana can kwance a gado maganganun Eamaan ke ratsa shi sosai,Iya ce ta harari qofar d'akin nashi tace,

" Jarababbe yau baqin halin naka ya motsa kenan, sai ka ci kan ka ai bari naje na kwashi girkina ni,naga yanzu kowa a gidan yayi sanyi, kowa ka taba kamar a firgice yake ku kuka sani 'yan wahala,"

Tinqis-tinqis ta wuce ta fara cin abincin ta hankali kwance Alhaji ya kira ta suka gaisa, ta sanar da shi yanzu Eamaan ma ta tafi ta gama yi mata abinci,wani dad'i ne ya kama shi,sai ya sanyawa Eamaan albarka,ya sanar da ita gobe zai dawo, sannan kuma yana son ta sa Sahabee ya kai Eamaan asibiti yanzu dan tana can yanzu ta kira shi cikin ta na ciwo sosai, amsawa ta yi sannan ta miqe ta je d'akin Sahabee ta hau bugawa amma duk bugu da kiran da take mai yaqi bud'ewa, waje tai ta kira driver dan ya je ya tada mota zai kai su asibiti da Eamaan, haka nan sai ta ji tana fatan Allah ya sa Ciki ne da Eamaan ɗin ,dan ko ita ta jima tana zargin su Sabeerah ba yaran ɗan ta bane duba da yawan yawon Hajiya Qarama da kuma rashin kama da yaran suke yi da Alhaji da ma zuri'ar su baki ɗaya, bata jin wani kusanci na musamman a tare da su iyaka dai ta na son su saboda yaran akwai shiga rai, tana qarasawa bangaren Eamaan ta tadda ta ta saka kaya da hijab, sai murqususu take yi sannu ta yi ta jera mata, sannan tace ta fita ta shiga mota bari ta koma ta d'akko mayafin ta,da kyar Eamaan ta iya qarasawa ta je wajen motar ta shiga, Iya kuwa ta dakko mayafi ta shiga mota driver ya tada suka bar gidan.

Asibiti suka je bayan bayanan da ta yi wa likitar se likita ta baiwa Eamaan gwajin jini,suka tafi lab aka ɗauki jinin ta aka gwada, bayan sakamako ya fito aka bata ta koma wajen likita, likita ta taya ta murnar samun qaruwa da tayi sannan daga baya ta yi wa Iya izinin shiga Office ɗin nata ta Sanar da Iya Eamaan na d'auke da cikin wata uku da sati biyu,sai dai kuma cikin ya na barazanar b'arewa saboda yawan ayyuka da take yi da damuwa, hankalin Iya a tashe ta dinga roqon su su taimaka mata kar ta rasa jikan nan nata tana son abunta, hakuri likitan ta bata ta  sanar da ita za su yi iyakar qoqarin su dan suga sun kula da ita, tana buqatar hutu ne kawai.

washe gari da Alhaji ya iso kano ko gida bai bari an kai shi ba ya yi asibitin wajen ganin Eamaan,yana shiga d'akin da aka kwantar da ita yayi ido biyu da ita duk ta rame ta yi fari sosai, tabbas ga alama nan komai ya fito cikin wata uku ya kusa rifa na hudu ya d'ago kaɗan ana iya ganin alamun shi, kwallar dad'i da farin ciki ne ta ziraro wa Alhaji a fuska, Iya ta kalle shi itama da murmushi a fuskar ta tace,

"kai ma kaji dad'in ganin matar ka da ciki ko? ABDULLAHI ina son in mun koma gida ka tsannan ta bincike akan su Ilham,"

"Iya ban gane ba? Kamar ya na tsananta bincike akan yarana wani laifi suka yi?"

"Ina nufin ka nemo wane ne uban su, domin ni ka sani ba wai ina tsananin son yarinyar nan Eamaan bane,amma ina jin tana da cikin nan na ji wata qaunar ta ta kama ni, wanda duk son Hajiya Qarama danake ban taba jin haka ba in tana da ciki, hasali ma zargin ta nake yi da yawon banza ni, sannan ba wai dan wannan alaqar da bana ji game da ita idan tana da ciki ba nake zurfafa zargi na, ka San dai Qarama da shegen son yawo, yanda ka ke saka qafa ka fice ba da sanin mu ba itama haka take sa qafa ta fice, ta sha yin qaryar gidan su ta tafi ka Kira ace bata je ba ko ka manta? To Ina take zuwa? Ko da da farcen qafa ne yaran nan ba sa kama da Kai ko ni ko Wani naka, to dole ne ka tsananta bincike akan su"

wani irin duka qirjin Alhaji yake yi a dik fitar kalma ɗaya daga bakin Iya, nan take ya hadiyi wani yawun wahala,ya sassauta wa jikin shi ta hanyar cire babbar rigar shi ya riqe a hannu, tabbas maganar hajiya akwai qamshin gaskiya a cikin ta, amma in yaran nan ba nashi ba ne to na waye? Waye yake masa d'anyen aiki haka?............








*Hahaiiiii cassssss wanzami fa baya son jarfa*
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    BIYAYYAH   💅🏼




WRITTEN BY HAERMEEBRAERH




Page 12:


Gaba ɗaya hankalin Alhaji ya kasa kwanciya da matan nashi da ya kamata ace a wajen su ya sauka, dan haka a  wajen Eamaan ya kwana ranar ,dik da cewa Iya tayi-tayi dashi ya tafi gida ya huta amma qi, baya son ya tafi ya bar ta a nan daga ita se Iya dan a ganin shi akwai abinda dole shi zai yi mata Iya baza ta iya ba.

Har suka yi kwana uku a asibitin babu wanda yazo duba Eamaan ding a cikin mutanen gidan Alhajin kama daga kan Hajiya Babba har zuwa Hajiya Qaramar balle kuma Sahabee dake a cikin damuwa, qarshe dai dole Alhaji ya yi waya gidan su Eamaan ya Sanar da su halin da Eamaan ke ciki, Hafsat aka umarta data zo ta zauna da ita har ta samu k'warin jikin ta tinda ita ta yi graduating yanzu haka tana aiki a camber din ta na kanta ne, sannan an kawo kuɗin auren ta har an saka ranar auren da wani abokin aikin ta mai suna Kamal, Iya da cewa ta yi a bar ta ba sai tazo ba tinda ga masu aikin gidan cikin su an samu mai zuwa ta zauna da ita, amma Eamaan ta ce a mata alfarmar barin yayar ta tazo wajen ta in zai samu, kan Iya tace komai Alhaji yace ba komai zai je da kan shi ya d'akko mata Hafsar,ita kanta Hafsar ta ji dad'in hakan dan tana son baiwa wa qanwar ta ta kulawa ta musamman.

Ammaah da Mama sun tausaya ma Eamaan dan sun tabbatar aiki take shaqa har hakan ta faru da ita, amma babu yanda za suyi da ya wuce suyi mata addu'ar samun sassauci,dama kowacce mace da qaddarar gidan auren ta,Daddy ma ranshi ya baci da jin cewa wai zata yi b'ari saboda yawan aiki da stress amma sai ya danne saboda baya son ya karya wa d'iyar shi mai BIYAYYAH qwarin guiwar ci gaba da yin BIYAYYAH a gidan mijin ta, sai kawai ya bi ta da addu'a da fatan alkhairi shima.

Wani irin haɗin kai ne yake wanzuwa a tsakanin matan na Alhaji da Sahabee wanda kai da ka gani kasan ba na Allah da Annabi bane akwai wata a qasa,dan kuwa kowa na nan na jin haushin 'yar uwar ta a qasan ran ta.

Tin bayan da aka kwantar da Eamaan sukan haɗu a sashen junan su suyi ta tattaunawa akan matsalar da suke ganin tana tunkaro su a gidan, dan haka yau ma zaune suke a sashen Hajiya Babba suna hira, cike da b'acin rai Hajiyan ta nisa tace,

" Hmmm wai baku san cewar an tabbatar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login