Showing 42001 words to 45000 words out of 78127 words

Chapter 15 - BIYAYYA Book Complete Hausa Novels by HAERMERBRAERH.txt

17 Oct 2025

1459

kaɗan ta karbe ta ta rungume ta tana lallashi, gaba d'aya yarinyar ta sauya ta koma kamar wadda ruwan nono baya isar ta, ita kan ta Eamaan ɗin duk ta sauya,'yar qibar nan da tayi duk ta sauka,to damuwa tayi mata yawa kuma ga gidan miji komai ya ja baya ba kamar da ba, gaida su ta yi cikin natsuwar ta da ladabi da biyayyar ta Daddy cikin sakewa da tausayawa ya amsa mata,Ammaah kam da Mama cikin share hawaye suka amsa mata dan sun kasa b'oye damuwar su akan halin da suka ganta, itan ma idon ta ya cika da kwalla amma sai ta sanya hannunta ta share, tambayar ta suka yi mai jiki ta amsa musu da cewa,

"Da sauqi alhamdulillahi dama abin da ya kawo ni kenan akan Maganar Baban Fateen ne, muna son muje gashi wannan satin amma bamu da kud'in mota, ga kud'ad'en da ya biya na asibitin da muke zuwa sunce ya qare an kuma rubuto wasu magunguna,yanzu haka daga wajen sayar da gwalai-gwalai na dawo na sayar da nawa kud'in dana had'a naga akwai sauran cikon 20k kafin su isa na maida shi asibitin shine nace bari na zo dan Allah Dad......,"

kan ta qarasa maganar ta yayi sauri ya katse ta da faɗin

"Kar ki roqe ni dan Allah Mamana, fad'a min buqatar ki yanzu na biya maki ita in dai bai fi qarfina ba, kome kike so ni zan yi maki shi a duniyar nan, in dai bai sab'awa Allah ba,wanda na san ma ba za ki taɓa bijiro da sabon Allah wajen mu ba, dan haka taso ki karb'a ki yi sauri ki je a kai shi asibitin, Allah ya qarawa rayuwar ki albarka ya baki ladan biyayyar da kika kasance kina yi mana a koda yaushe, Allah yayi miki albarka, Allah yayi miki albarka,domin babu addu'ar da zaka yiwa ɗan uwan ka musulmi data wuce ka nema masa albarka a wajen ubangiji,albarka ta qunshi komai na duniya da lahira da bawa zai samu na alkairi, Allah yayi miki albarka da zuri'ar ki baki ɗaya Mamana,"

Cikin tsananin kuka da jin dad'in kalaman mahaifin nata ta je gare shi ya miqe tsaye ya rungume ta tsam a qirjin shi tare da sumbatar goshin ta,ya sa hannu a aljihun shi,ya zaro kuɗin da shi kan shi bai san ma iyakar su ba ya bata, Ammaah ce ta koma ɗakin ta ita da Mama suka d'akko mata kuɗi,kayan abinci da sauran su suka bata suna sanya mata albarka tare da yi mata fatan samun sassauci a rayuwar da take fuskanta, godiya tayi masu sosai ta tattare komai zata tafi, Daddy ya sa driver ya maida ita gida.

Cike da murna ta shiga sashen Iya da ta kai shi ajiya dan kar ta barshi shi kaɗai, nan ta same shi kwance a kujerar shi ya yi kashi a jikin shi yana ta kuka ,dan kuwa Iya ta kasa koda motsa qafar shi ce balle ta d'aga shi ta gyara masa,fuskar shi tayi jawur har ajiyar zuciya yake saukewa sabida kukan da yayi, da sauri ta qarasa wajen shi tana tambayar shi lafiya yake kuka haka? Tana qarasawa inda yake ta ji wari, kauda kan shi yayi gefe saboda nauyin ta da yaji ya kama shi,ita kuwa sai tayi murmushi ta sauke Fatee da ta yi bacci a wajen Iya ta tura shi suka koma sashen ta ta fara gyara masa jikin shi,sai da ta gama yi masa tsarki da wanka tass sannan ta canja masa wajen kwanciya, ta dauki kayan daya b'ata ta je ta wanke su ta shanya ta koma ta d'akko tiraren wuta ta kunna a dakin ta fesa na fesawa, daga nan ta koma ta d'akko Fatee da ke bacci ta kwantar da ita a gado ta koma ta yi wanka,cikin shirin doguwar riga ta fito ta zauna kusa da shi ta kama hannun shi tace,

"Sweet na sha gaya maka ka daina damuwa dan ka yi bayan gida,ba ga ni ba zan wanke maka ko akwai wani abu dake damun kane da baka sanar dani ba? Ko kuma dai ladan da nake samu ne baka soooo"

Ta fad'a cike da shagwab'a,hawayen shi ne ya sake sakkowa saman kuncin shi cikin maganar shi da kamar koya yake yi ya labarta mata abinda ya faru da bata nan,

" Iya ce na ce ta wanke min jiki na sai ta hau toshe hanci tana fad'a akan me yasa da girma na zan yi kashi a jiki na, sai dai na bari ke ko sahabee ku dawo ku gyara min ita bazata ci kashina sau biyu ba a rayuwa,Sahabee ma daya dawo ta saka shi ya gyara min shima cewa yayi saidai na bari ki dawo Allah ya kiyaye ya wanke min kashi, tin da kika fita na yi shi sai da kika dawo na samu kika wanke min, Eamaanii na Allah yayi miki albarka,Allah ya sa ki gama da duniya lafiya Allah kar ya gajiyar dake hidima dani, a yanzu ne na qara tabbatar da cewa Iya da Sahabee ba zasu riqe min jinina ba ko bayan babu ni a raye, ki tabbatar ba wanda ya raba ki da Fateema ko bayan babi ni Eamaan ki jajirce wajen kula da ita da tarbiyyar ta, na roqe ki Eamaan kar ki rabu da Fateema a hannun Iya da Sahabee ko bayan babu ni a raye,"

Ya qarasa maganar shi cikin matsanancin kukan da ita kam tini ta ke yin shi, kwantar da jikin ta ta yi a gefen na shi tace,

" Sweet ka daina kuka, ka daina saka damuwa a ranka indai kana son ciwon nan ya barka, kasan damuwar ka zata hana ka samun sauqi akan kari ko? yanzu dai gashi alhamdulillah muna ta samun ci gaba,yauwaa har zan manta ma ban faɗa maka ba ɗazu da na fita gida  naje gaida su Ammaah da zan tafi Daddy ya bani wannan,da naqi karb'a ma nace muna da kuɗi sai suka dage sai na Karb'a shine na amso,"

Eamaan tayi haka ne dan kar ya ji ba dad'i a ran shi ,yaji cewar ta je wajen iyayen ta ta roqo kuɗin da zata kula da shi da mahaifiyar shi da sokon ɗan uwan shi, godiya yayi tayi mata da iyayen ta dan kuwa ya ji dad'in kuɗin da suka bata sosai,yace to ta yi wa drivern su waya in yana kusa sai ya zo ya kai su asibitin, wayar ta ta d'akko ta kira shi yace zai iso nan da awa ɗaya da 'yan mintuna.

Dai-dai lokacin daya ambata ya iso gidan nasu sai suka d'unguma zuwa asibiti, Eamaan cikin ranta ta qudirta daina barin Alhaji da Iya tinda dan taga yanzu basu da shi shine ta ke nuna masu halin ko in kula ita da Sahabee, in ta je gaida Iyan ma takan same su suna cin dad'in su sun manta da su da rayuwar su, basu damuwa da su ji ko sun ci abinci a ranar ko basu ci ba.

Basu samu dawowa a ranar da suka je asibitin ba saboda wasu gwaje-gwajen da aka yi wa Alhajin,koda suka kammala da asibiti sai ta kirawo driver yazo ya maida su gida, suna shiga ciki ta kwantar da Fatee dake ta bacci sannan ta dawo ta kai Alhaji band'aki ta cire masa kaya itama ta cire nata, wanka tayi masu gaba d'ayan su,da taimakon kujerar da yake hawa ta je ta saka shi a kwamin wanka dan ta gasa masa jiki da ruwan d'umi a cewar ta zai ji daɗin jikin shi sosai tana gama saka shi ciki itama ta shiga, sukai wankan su a tare kamar yanda suke yi ada, Alhaji ya ji dad'in hakan sosai,Eamaan kuwa sai qoqarin yi masa abubuwan da zasu faranta ran shi take yi musamman ta bangaren bashi labarai na ban dariya, kukan Fatee ne ya fito da ita da sauri daga band'akin tana daura towel, ɗauke ta gan ta hannun Sahabee yana zare mata ido tare da ce mata,


"Ke shiiiiiii ! Ki yi min shiru nace me shegen kukan tsiya,"

Eamaan na ganin haka sai ta koma da baya ta sako hijabin ta da ta cire,dik da haka Sahabee da ya ganta sai da ya haɗiyi wani mugun yawu,tana isa gaban shi ta sa hannu ta kwace 'yar ta tace masa,

" ka kiyaye ni fa Sahabee har yanzu ba ka gama sanin abinda zan iya aikatawa ba idan ka takura min na ga alama,"

Zata juya ta ajiye Fatee kenan ya janyo hijab ɗin ta ta baya, tana juyowa kuwa ta yanka masa wani irin mugun mari,cikin tsananin mamaki da kad'uwa Sahabee ya dafe kuncin shi yana kallon ta, cike da b'acin rai Eamaan ta nuna shi tace masa,

"kai ɗan akuya ka ajiye tsalle-tsallen ka a waje kar ka shigo min dashi cikin gidan nan,idan ba haka ba kuwa watarana zan illata ka,"

Cikin zafin nama ya damqo ta ta ko ajiye yarinyar dake ta kuka a kujera ta damqe wuyan shi shima ko alamar tsoro babu a idanun ta, Alhaji na can yana jiyo dik abinda ke faruwa sai kwala mata kira yake yi,Sahabee kuwa jan ta ya yi zuwa gaban Alhajin yace,

"ke har kin isa dan ina son tarayya da ke ki dinga mari na kamar kin samu ɗan ki,kin zaci qarfi na ki ka fi da nake kyale ki ko me? tin zuwan ki gidan nan nake maitar kusantar ki na sha gwadawa bana dacewa, to yau se na fanshe marukan da ki ka jima ki na zabga min da jikin nan naki da ki ka d'auke shi kamar zinare,ko da da kika ga na yi atempting kusantar ki kin min waɗannan abubuwan na ji tsoro na kyale ki saboda wannan nakasasshen mijin naki na da lafiya ne,in ya ji zai iya hukunta ni akan abinda nayi miki, amma yanzu ai baki isa ki sa ni na fasa abinda na yi niyya ba, zan kusance ki a gaban shi tinda in ban manta ba ka tina d'iyar Sabi'u, da ka sa aka d'akko ta uban ta ya bika har gidan shaqatawar ka amma baka fasa fasa masa budurwar 'yar shi ba a gaban shi, dan haka a yanzu nima zan yi abinda naso da matar ka na ji d'ad'anon zumar ta ko mad'acin ta a gaban ka, yau dai nima zan ji meye ke cikin wannan kyakkyawar surarar da ake b'oye mana,"

Sahabee na magana yana qoqarin cire wa Eamaan hijab ɗin dake jikin ta tare da k'wace wuyan shi da ta shaqe ya banqare mata hannayen ta ya zame towel ɗin jikin ta surar ta ta bayyana a fili, Alhaji ne ya rintse ido da qarfi cike da azabar da zuciyar shi ke yi masa yake baiwa Sahabee hakuri da karyayyen harshen shi da baya fita sosai.

Zuciyar Eamaan kuwa a dai-dai wannan lokacin babu komai cikin ta sai wani d'aci da take yi mata dik zafin da take ji na matsar da ya yi wa hannun ta amma a haka ta qoqarta ta juyo cikin hikima da kwarewa a qoqarin ta na son kare kan ta,gwara masa kan ta ta yi a hancin shi nan da nan kuwa ya fara tsiyayar da jini, ta dunqule hannayen ta ta buga masa a dokin wuyan shi, ta sanya guiwar qafar ta ta daki gaban shi da qarfin gaske,nan take ya zube a qasa yana murqususu.

Cikin sauri ta ɗauki towel ɗin ta ta d'aura,ta maida hijab ɗin ta jikin ta, Fatee da ke ta kukan fitar rai ta je ta d'akko, ta ajiye ta a tsakiyar palour dan ta kusa fad'owa daga kujera, Sahabee na duqe cikin azaba sai murgina kai yake yi idanun shi sun yi jawur, jini na ta fita a hancin shi, muciya taje kitcen ta d'akko ta dawo inda yake idon ta ya rufe da b'acin rai ta dinga muqa masa a jikin shi tana faɗin,

"In a zina yau aka haife ka qarewar bariki sai na fidda maka sha'awar ta kai ko da matar ka ce ta sunna ba matar wani ba bazata qara baka sha'awa ba,shege mara imani, mara tausayi, wanda bai san mene ne dokar Allah ba balle ya bita, yanzu d'an uwan ka na cikin halin jinya ka ke so ka qara masa damuwa? butulu kawai masu manta alkhairi,komai zunubin shi in ya tuba ga Allah Allah zai yafe masa,Kai wane ne da ka ke so ka hukunta shi akan abinda ya aikata a baya? Yau se na nakasa ka kaima"

Duka tayi masa sosai kamar wanda 'yan sanda suka kama da mugun laifi,da kyar ya samu ya fita da gudu, ta ko bi shi a guje tana fita tayi karo da Iya a hanya,Sahabee ne ya qanqame ta yana ihu, cikin tsananin mamaki Iya tace,

"Me zan gani haka? Na shiga ukuna yanzu kashen min d'an zaki yi Eamaan? Jama'a ku taimaka min zata kashe min yaro,"

Sai ta saka kuka tana duba fuskar Sahabee da ta daku sai fitar da jini take yi, dik maganganun da Iya ke yi Eamaan bata kula ta ba saboda gudun kar tayi mata rashin kunya, dan yanda take jin zuciyar ta zata iya zagin Iya tsaf, dan haka sai kawai ta koma sashen ta ta kulle qofar da makulli ta wuce ta dauki fatee ta saka mata abincin ta a baki,ai kuwa fir yarinyar taqi kamawa tana ta ci gaba da tsala kuka, itan ma kuka ta fashe da shi, daga can band'aki kuwa Alhaji ta jiyo ya yi wani nishi mai qarfi, da gudu ta aje Fatee ta je wajen shi, tana isa ta duqa gaban shi tana faɗin,

" Alhaji ! Alhaji !Alhaji ! dan Allah ka buɗe idon ka ka kalle ni kar ka yi min irin wannan wasan bana so, bari na saka maka kaya mu je asibiti, please Alhajina stay with me dear i will be right back,"

Da gudu ta je ta d'akko kayan su ita da shi dan ta sanya musu, gaba d'aya gambal habaru ta d'akko bata kula ba tsabar tashin hankalin da take ciki, a haka ta hau saka masa nashi da kyar saboda yanda taji jikin shi ya saki sosai fiye da da,da kyar ta iya dora shi akan kujerar shi ta saka nata kayan ta maida hijab din ta,parlour ta koma ta goya Fatee da ta gaji da kuka ta yi bacci,a guje ta sake d'iba tayi d'akin ta ta d'akko wayarta ta kira drivern su,tayi sa'a kuwa yace mata dama gashi ya kawo balance, tace ya kawo motar daf da side din ta yazo ya taimaka mata su saka Alhaji a mota bashi da lafiya,kafin ya iso ta tattare yan kud'ad'en da suka rage a wajen ta ta saka a jaka ta rataya a kafad'ar ta tana jiran shi,yana zuwa suka ɗauke shi sika saka a motar, Iya da Sahabee na hango su amma basu je ba.

Gaban Iya ne yayi wata mummunar fad'uwa sai dai tana tinawa da me Eamaan ta yi wa Sahabee a qaryar da ya zuba mata sai kawai ta kauda kan ta ta bisu da harara,a guje drivern ya nufi asibiti da su, ita ko Eamaan sai addu'a take yi tana kumawa akan Allah ya ba wa Alhajin ta lafiya, hankalin ta gaba ɗaya ya gama fita a jikin ta, tabbas ko ba so akwai shaquwa a tsakanin su sannan akwai qauna ta musamman da take yi mishi a matsayin shi na mijin ta, zuciyar ta na tsananin tausayin shi, tana fatan ya warke ko dan ya ci gaba da zama uba ga yarinyar ta k'walli ɗaya da suka mallaka ita da shi

Eamaan ta fuskanci Alhaji fa baya numfashi dan haka cikin kuka tace,

" ka qara gudu dan Allah kar na rasa shi,"

kuka ne ya qara sarqe ta ta kuwa toshe baki ta dinga rero shi kamar waqa.

Suna isa likitoci suka rufu kan shi sai shige da fice ake akan shi, daga qarshe dai wani daga cikin su wanda ta kula kamar shine babban su a wajen ya je yace mata..........
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    BIYAYYAH   💅🏼








WRITTEN BY HAERMEEBRAERH





Page 18:






Umartar ta ya yi da ta bishi office din shi yana son magana da ita, suna isa ya mata nuni da wajen zama, ta zauna hankalin ta gaba daya a tashe yake, kallon shi take ko qiftawa bata yi, gyaran murya ya yi yace,

" Hajiya a gaskiya Alhaji yana cikin matsala sosai, domin kuwa ada mun samu ci gaba sosai, yanzu komai ya koma mana baya, na sha fada maki kuna qoqarta kauda shi daga abinda zai b'ata ran shi, amma yanzu ki duba ki gani yanda gaba d'aya komai ya koma mana baya, a gaskiya banji dad'i ba sam, kuma a yanzu kam sai dai na baku shawarar akan ku fidda shi waje, domin a samu ya samu sauqi da wuri, in ba haka ba a gaskiya ina jiye maku tsoro sosai,"

kukan ta ne ya qaru sosai, a hankali ta share hawayen ta ta yi masa godiya sannan ta fita, direct gidan su ta tafi, ta je ta samu Iya da Sahabee a palour suna tattauna wa akan Eamaan, yana qara fada mata qarya da gaskiya akan abinda ya faru, Sallama yi ta musu ta shiga, a tare suka daga kai suka kalle ta, Sahabee kuwa a matuqar razane ya kalle ta, Iya ta kula da hakan nan take ranta ya qara ɓaci, wato har Eamaan na da wannan effect din akan d'an nata

" Meya kawo ki nan kuma?"

Kallon Iyan ta yi da tsantsar tsana tace,

"A da na zaci zan kyautata maki har Allah ya ganar da ke ki so ni, na jure duk qunci da wahalar ki, na kasance ban taba kwana da abinda kika yi min a raina ba,a lokacin da kika batamin rai a lokacin nake mantawa kuma na yafe maki, dan haka yanzu ina son gaya maki ni ban riqe ki da komai ba na yafe maki dik abinda kika yi min ko da baki nemi yafiyata ba, amma ku sani wannann gidan akwai mai shi, kuma mai shi d'in nada buqatar gidan shi, kamar yanda baku damu da shi da lfiyar shi ba haka nima ba zan damu wajen sanar daku daga yau zuwa ko wanne lokaci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login