Showing 78001 words to 78127 words out of 78127 words
Chapter 27 - BIYAYYA Book Complete Hausa Novels by HAERMERBRAERH.txt
ya dawo gidan mutane da zama, gaba ɗaya Sahabee d'an gaye d'an bariki ya sauya, wanda duk ya san shi da se ya wahala Kan ya gane shi yanzu, hannun shi da ya yi targad'e ya samu matsala, ga wani wawan yanka da na gani ya duri ruwa a gefen kumatun shi, ko yaushe yaji shi Oho? Sai dai in ce Sahabee Allah ya shiga lamarin ka ya shirya ka.
*Nan na kawo qarshen wannan novel nawa mai suna BIYAYYAH, ina roqon Allah kuskuren da na yi a ciki ya yafe min, alkairin da ke ciki ya min albarka ya jiqan magabatana ya qarawa Mamana lafiya da Imani yayi mata kyakkyawan qarshe, ina roqon Allah da ni da makaranta ya Sanya mu daga cikin bayin shi muminai salihai.*