Showing 15001 words to 18000 words out of 78127 words
Chapter 6 - BIYAYYA Book Complete Hausa Novels by HAERMERBRAERH.txt
yi ba, kawai samun waje ne irin na Iya.
"Tashi maza je kiwa Iya a bin karyawa,gata can wai zata shiga kitchen da Kan ta in Baki je ba,kin san ta na da hawan jini, Dan Allah daure ki yi sauri"
Dik da ran ta be so ba amma bata nuna komai ba, ta amsa da "to" nan da nan kuma sai yaji ba dadi, yarinya mai biyayya kamar wannan amma ana ta muzguna mata, wai shin ya zai yi ne da halin Iya? Iyan ta ce kullum ita zata na yi mata abinci dan ta iya girki, yana nan zaune ya na tinani har ta gama komai ta shirya zata tafi, ya Kira sunan ta, juya wa ta yi tare da sakar masa faffad'an murmushi,
" Eamaan ki qara hakuri, ba yanda zan na hana hakan faruwa, mahaifi.....,"
Da sauri ta katse shi da tacewa,
"Dan Allah ka bari ai ba wani abu bane hakan, ni a gidan mu bana kai wa haka ina bacci,in muka yi asuba ba mai komawa bacci,da sassafe nake haɗawa Daddy abinci har na tafiya Office, yanzu ba ga shi ba inna je ina jifan tsuntsu biyu da dutse ɗaya ba, zan yi mata nata girkin kaima kuma zan yi maka wanda zaka tafi da shi, duk da dai kana wani qi wai kai babba da tafiya da abinci ko? to yunwa ba ruwan ta da girman ka,kuma ai dole macen kirki tai tarayya da mijin ta wajen kyautata wa mahaifan shi in dai tana son ya shiga aljanna, tinda shi na miji bayan Allah da manzon sa, iyayen shi kawai zai bi ya samu aljanna, dan haka ka daina ban hakuri daga yau dan Allah, in ba haka ba gobe da botle water irin na su Ilham zaka je Office da irin lunch box ɗin su"
Ta qarasa maganar ta cike da wasa, dariya ya yi ita kuma ta fita ta bar shi yana mamakin halaye irin nata, ta iya b'oye damuwar ta, dan tabbas yasan kukan jiya ma wani abu ne ya same ta a can amma ba wai abinda ta fada masa ba, kad'a kai yayi ya miqe cike da girmama ta a ranshi.
Tana zuwa bayan ta gaida Iya ta bata umarnin ta d'umama mata tuwon ta, sannan ta yi mata farfesun kifi, da kunun shinkafa, amsawa ta yi da "To Iya"ta shiga ta haɗa mata duk abinda take so ta kawo mata parlour ta ajiye a inda take karyawa,cikin mamaki babu godiya Iya tace,
" Oh ni ji yarinya kamar wata inji, ke baki gajiya da aiki ke ? Ko dake in ma kin gaji za dai kiyi dolen ki,sai ki tashi ai ki tafi uwar son miji, yarinya qarama dake sai jaraba,wani har yana gaya min jiya baki yi bacci ba, Oh ni yaran yanzu akwai jarabar tsiya,"
Eamaan Kan ta na qasa idon ta ya kawo kwalla ta yi sauri maida su, ta d'aga kai ta kalli Iya da ke bin ta da harara,tace,
" Iya me za a dafa maki an jima?"
" Oh ho, ko dambun shinkafa zaki min ma de waya sani, sai anjiman dai in kinzo na ga me za a dafa,"
Miqewa Eamaan ta yi zata tafi,har ta kusa fita Iya tace mata
" ke zo nan, dubamin dakin Saheebee ya taso ya karya, ki tambaye shi me zai ci se ki haɗa masa"
Cike da kasala ta nufi hanyar d'akin nashi...........
*Hhhhh Sahabee ai by now ya kusa isa garin yarbawa wallah*😆😆
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 7:
Dab zata k'wank'wasa qofar d'akin ne ta tsaya ta haɗe fuskar ta tamau kamar bata taɓa dariya ba, ta sa hannun dama ta fara k'wank'wasa qofar, shiru-shiru ba a amsa mata ba kuma bata ji motsin kowa ba,ta nan tsaye tsawon minti uku bai buɗe ba, murda hannun qofar ta yi ta leqa sai taga ba kowa,in fact ba kayan shi ma kwata-kwata a d'akin kamar yanda ya Saba baza su duk inda ya so, kwankwasa toilet ta yi nan ma taji shiru, budewa ta yi a kasada ta leqa sai taga wayam babu kowa, komawa ta yi parlourn ta sanar da Iya bata ga kowa ba, kallo Iya ta bita da shi can tace ta tashi ta tafi kawai,
" Allah ya shiryi yaronnan, barikin tashi ta motsa kenan shiyasa ya tafi babu ko sallama,"
Eamaan na fita kai tsaye bangaren Hajiya babba ta shiga da yake kusa dana Iya, a zaune ta gan ta tana karyawa da bread da kwai, ta hada tea mai kauri tana korawa sai baza hanci take yi, kanta babu dankwali kamar ko yaushe, ga shi kan nata babu wani gashin arziqi, kitson duk ya haɗe , amma fuskar nan tata tasha kwalliya, an damb'ara jagira an saka jan baki a saman idon,sannan a bakin ma ta saka jambaki an ja baqi a saman janbakin, jagirar ta ja ta doguwa sosai, gashi ta lafta mai a saman ta,sai yauqi take tana gatsa biredin cikin yanga ita a dole ta yi kyau, tana ganin Eaamaan ta d'aure fuska tamau, gaida ita Eamaan ta yi Hajiya Babba ta amsa a shaqe, Eamaan na ganin haka ta miqe ta fita,tana jiyo sanda Hajiya Babba ta ja tsaki ta hau zagin ta ko juyawa ba ta yi ba ta faɗa ɓangaren Hajiya Qarama, tana shiga suka yi Ido hud'u da Sabeerah da ta Sanya uniform dan zuwa makaranta, da gudu Sabeerah ta isa gare ta ta d'ale ta,Eamaan kuwa sama ta d'aga ta tana yi mata wasa,suna a haka Ilham ta tako da yanga itama ta je kusa da Eamaan ta dan duqa ta gaida ta, amsawa ta yi cike da jin daɗi a sannan ne Sabeerah ma ta gaida ta,
" Ina Mum?"
" Tana d'aki tana d'akko mana hijabs ɗin mu,"
"Ok"
zama ta yi dan ta jira sai gata ta fito fuskar ta babu yabo babu fallasa suka gaisa, Eamaan ce tace masu su biyo ta ta basu wani abu su tafi da shi makaranta ihun murna su ka sanya suka haɗa baki wajen faɗin,
" U ar the best Aunty Eamaan,"
"Thank you ba komai sai kun shigo, ina jiran ku,"
Shafa Kan Sabeerah ta yi kafin ta wuce sashen ta,d'an murmushi Hajiya Qarama ta yi dan kuwa tana jin dad'in yanda take kula da yaran ta, bayan ta koma ne ta ga har Alhaji ya shirya ita yake jira, a gaggauce ta koma kitchen ta d'akko abinda ta bada umarni masu aiki su haɗa mata sai ta kawo masa ya karya ta haɗa masa wanda zai tafi da shi, tana haɗawa tana tsokanar shi, sallamar su Ilham ce ta katse su, sweets da suka siyo jiya da chocolates ta d'ebo ta basu,sukai mata godiya suka tafi, Alhaji shi ma yana jin daɗin yanda take son yaran shi ba kaɗan ba,a ranshi yana ayyana gaskiya Eamaan ta daban ce.
Kusan wata biyu kenan ba labarin Sahabee ba waya ba saqo, hankalin Iya ya yi matuqar tashi da rashin shi,musamman da ya zama baya koda kiran tane a waya, samun Alhaji ta yi da maganar ya kwantar mata da hankali, ya nuna mata zai bincika ya ji ko lafiya yake, a ranshi ko yana ayyana,
'Dan ɗan bariki ya yi nesa da gida haka ai ba abin mamaki bane duk inda yaje zai dawo ne'
Iya ta yi matuqar zurfi a tinanin ta tajiyo qamshin girki,da jin yanayin qamshin girkin ta tabbatar da cewa Eamaan ce ta shigo,miqewa ta yi ta nufi kitchen ɗin cikin zafin rai, Eamaan na ganin ta ta durqusa ta fara gaida ita, bata amsa ba ta fara magana cikin fushi kamar za ta Kai wa Eamaan duka
"Ke ! me ki kai wa d'ana ya bar gida? Me kika mai ya bar gidannan ba waya ba saqo? Tinda yake ko ya tafi kullum sai ya min waya amma wanan karon ba ko pilasha,(Flashing) kuma dan tsabar munafirci da kika zo ba ki je kin gaida ni ba sai yanzu ne da kika gannj zaki wani zube kina gaida ni?"
"Iya ki yi hakuri naje na gaida ki na ji shiru da alama kinyi nisa cikin abinda kike tinawa,bana son katse maki ne yasa na taho dan nayi aikina, Iya ban yi mashi komai ba, ko ganin shi ban yi ba ma lokacin da zai tafi, inshaa Allah Iya zai dawo gida lafiya ki daina sa tinani da yawa a ranki, saboda lafiyar ki,"
Ta dan ji daɗin maganarta Eamaan ta qarshe, ko ba komai a qalla ta samu wanda ya tina mata ba ta da isasshiyar lafiyar sa tinani aranta,a hankali ta ja jiki ta bar kitchen din, tana matuqar son Sahabee fiye da kan ta, dan ko wanne laifi zai aikata a wajen ta bai komai ba, d'akin shi ta shiga direct, ta hau dudduba kayan shi, ba abinda take gani sai kayan shaye-shaye da wata leda doguwa, mai kamar madara ce a ciki ko me oho, ledar nada kyalli da ɗaukan ido,(condom) ajewa ta yi ta ci gaba da dudduba d'akin, a gefen gado ta zauna tana ta tinani kan wani lokaci kan ta ya fara ciwo a wajen ta kwanta bacci ya dauke ta.
Eamaan na gama girki ta je d'akin Iya ta duba koina har toilet bata gan ta ba? D'akin Sahabee taje ta duba acan tagan ta kwance tana bacci, ta cika d'akin da munshari, zata ja qofar kenan Iyan ta farka kiran ta tayi haka Eamaan ta koma ciki ta kama ta suka bar d'akin suka koma nata.
magungunan ta ta yi umarnin Eamaan ta d'akko mata zata sha dan bata jin daɗin jikin ta,fita ta yi ta fara debo mata abincin da ta dafa, jellop din taliya data ji kayan ciki da kayan lambu ta zubo mata sai tashin qamshi take yi, ga tea data haɗa mata dan ta kula ko karyawa bata yi ba, sannan ta d'akko mata ruwan roba,ta na shiga ta ja qaramin Table dake d'akin gaban Iya ta dora mata abincin sannan ta binciko mata magungunan, Iya abinci ta nad'a sosai, dan kuwa abincin Eamaan ko baka jin yunwa ka fara ci zakaji kamar kar ka daina ci saboda daɗin shi, balle da 'yar Gusau din dama, tas ta share plate din ta kora shayin sannan ta sha maganin, a hankali ta fara jin nutsiwa na zuwa mata, ruwan wanka Eamaan ta haɗa mata sannan ta yi mata sallama ta fice, Hajiya Qarama ce ke girki a ranar,dan haka Alhaji yana ɓangaren ta,da dare Eamaan ta dafa ruwan tea kawai sai ta soya kwai da ta saka ma timatir mai yawa da albasa, ta soya ruwa-ruwa bayan ta saka kayan qamshi da ɗan maggi ta zauna ta ci sannan ta sha tea, wanka ta yi tai brush ta saka kayan bacci riga ce qarama iya cinyar ta, sai wandon rigar shima iya cinyar ta, sai ta saka hula kalar kayan jikin ta, ba qaramin kyau ta yi ba a wannan daren, tana zama a bakin gadon ta sai ta yi addu'a ta shafe jikin ta da shi sannan ta bi lafiyar gado, kwanciyar ta kenan Alhaji ya shigo yi mata sallama, ya jima a sashen ta yana faɗa mata yanda ya yi missing ɗin ta ya kuma matsu jibi tayi ya dawo gare ta, and he wish a nan zai kwana yanda tai kyau ɗin nan ya yi matuqar yabawa, cike da shauqin son kasancewa da ita ya tafi bayan ta raka shi har bakin qofa, yana fita ta koma ta kwanta,zuciyar ta cike da tinani kala-kala ita tata jarabawar kenan numfasawa tayi sannan tace,
"Alhamdu lilLAAHi ala kulli halin,"
Bayan Alhaji yaga rufe qofar ta sai yayi bismilla ya topa a qofar sashen nata sannan ya wuce ɓangaren Hajiya Qarama,samun ta yayi tana zaune babu kwalliya kamar yanda ta sabar mashi,sannan babu wankan dare, ba qamshi ita a tattare da ita sam babu komai, kuma wai a haka jiran miji take yi ,mijin da ya je sallama da sauran matan shi ya isko Hajiya Babba ta cab'a adonnan nata na kwalli da jan jambaki, an sha lace an sha d'auri ya kalli kudu maso gabas, duk da cika kwalliyar da ta yi a hakan ya ji ta burge shi,a qalla bata yin wari kuma ta yi kwalliyar ne domin shi,ta ɓangaren Eamaan kam ba a magana dan kuwa ta haɗu ta kowanne fanni sai godiya kawai, tsaki yaja ya kwanta, can kuma kamar wanda aka mintsina ya miqe ya saka kayan shi ya ɗauki key ɗin motar shi ya bar gidan sai tashin mota mutan gidan suka ji, ko da me gadi ya fito daga bayi sai ya manta da zuwa ya jaddada rufe gate ɗin gidan, fitar Alhaji da kamar mintuna sha takwas, Mai machine ya ajiye Sahabee a qofar gidan,sallamar Mai machine ya yi ya tura qofar gate ya shiga gidan ,dan kuwa yaga a ɗan bud'e qofar take, yana shiga har ya nufi hanyar bangaren su wata zuciyar ta kad'a shi ya nufi bangaren Eamaan, dan ba qaramin kewar ta ya yi ba a wannan watannin, ko neman matan na shi yake yana kwance da mace zai ta ayyana Eamaan ce, amma inaa dik da haka baya wani samun gamsuwa, haka zai ta abu ɗaya cikin jin haushi ya tashi ya bar mace kwance da takaici, yayi iya qoqarin shi na cire ta a rai, amma ya kasa, musamman in ya tina da deadly look ɗin ta da a yanzu yake matuqar burge shi,nan take ya tuna da marukan da ya Karb'a wajen ta hankalin shi ya dawo jikin shi,anya kuwa zai samu nasara akan Emaan a haka dai ya leqa sashen ta ta window, kwance ya ganta ta kifa cikin ta ta d'age qafafu sama tana kad'a su da ice cream a hannun ta tana sha, hannun ta ɗaya kuma da wani littafi na su na school of nursing tana dubawa,ya dad'e yana kallon ta anan ya gane yau Alhaji ba a bangareta yake ba,wani dariyar mugunta ya saki, ya tattaka a hankali ya murda hannun qofar, a bude ya ji ta,murmushin shine ya qaru ya sa kai ciki, ya mayar da qofar ya rufe,kashe fitilar yayi, ya hau laluben hanya, yana kaiwa bakin qofar shiga d'akin ya ga duhu ya mamaye ko ina, alamar ta kashe fitila itama, ta bangaren Eamaan kuwa tinda ta ji kashe fitilar parlor ta san ba lafiya ba, sannan ta ji ana taku a hankali, tinanin ta ya bata kawai b'arayi ne suka shigo, wayar ta ta laluba ta kira Alhaji,sai dai tana ta ringing bai d'aga ba, ajewa ta yi ta miqe, ta d'akko tiraren ta, ta lab'e a bayan qofa bayan ta kashe wutar, hasken waje ke ratso labulayen yana shigowa cikin d'akin nata ,zuciyar ta kamar zata fito waje dan tsoro, hawaye ta fara yi dan kuwa hankalin ta ya yi matuqar tashi, qirjin ta sai d'agawa yake saboda shiga damuwar da ta yi, a hankali ya murd'a qofar ya qarasa shiga ciki d'akin nata...............
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 8:
Qafa ta saka masa ya kife a qasa, cikin zafin nama ya yunqura zai tashi ta fesa masa turaren da ta d'akko a fuskar shi, sannan ta sa bayan hannunta ta buga masa a baya, gwangwanin turaren ta d'aga sama ta kwad'a masa a kafad'a da qarfi, yana son ya yi ihu dan azabar da yake sha hannun Eamaan amma babu dama,saboda baya son asirin shi ya tonu, da lalibe ta kunna fitilar d'akin,Sahabee ya bayyana duqe a gaban ta, haɗe hannayen shi d'aya cikin d'aya yayi yana zubda hawaye a idanun shi ya hau bata hakuri, mamakin ganin wai Sahabee ne ashe ya ke wannan iskancin a cikin wannan daren me ya zo yi to a d'akin nata Sata Ko fyad'e?
Sahabee ya gama cika mata ciki wannan karon dan haka haushin shi take bala'in ji, ta tabbata ba shi da cikakkiyar tarbiyya ko kaɗan, d'aga hannunta ta yi da nufin yin magana sai dai kalma d'aya ta kasa fita daga bakin ta,takaicin shi ya tokare mata kowacce kafa da amon sauti zai fita a wuyan ta,cije leb'en ta na qasa ta yi cike da takaici,yawo ta fara yi a d'akin ta kai ta dawo ta Kai ta dawo a gaban shi,qoqarin tashi ya yi zai gudu,Eamaan na ganin haka kuwa ta yunqura itama cike da wani irin zafin nama da bata san ta na da shi bama ta fizge shi ya yi baya, hannunta ta d'aga ta wanke shi da Mari sannan tace masa,
"Guduwa za ka yi? Ai ba inda zaka je se ka Sanar da ni me ya kawo ka sashe na a wannan Daren har da kashe min fitila, kashe ni za ka yi ko me?"
Sahabee ya tabbata in ya Sanar da ita gaskiyar abinda ya je yi a sashen ta har maganar ta Kai wajen Yayan shi kashin shi ya bushe,ya san dikkan wasu sirrikan shi manya da qanana za su bayyana, dan haka cikin kuka irin na 'yan bariki ya zube a gaban Eamaan ya na bata hakuri, tare da fad'in tsautsayi ne ya kawo shi,amma ba shi da wani qudiri mummuna a ran shi.
Yanda yake bata hakuri ya fara karyar da zuciyarta ta yarda ba shi da wata manufa da ya je, dan haka cikin dakewa ta ce Masa
"Zan rufa maka asiri dan kuwa wannan abun kunya ne ace wai qanin miji na ke bibiya ta,sannan dan rashin lafiyar Iya bazan so maganar nan ta fita ba,sannan ba zan so b'ata zumuntar dake tsakanin ka da ɗan uwan ka ba, amma ka sani duk sanda ganganci ya sa ka qara kallona ka bari muka haɗa ido da kai a cikin gidannan ma, Hmmmmm,"
Wata dariyar da ta matuqar tsorata shi Eamaan ta saki, dariyar da ya kasa gane ma'anar ta,wai yau shi da yake bariki me lasisi a qasar masu kwale shi ake yiwa haka,shi ɗin uban bariki reshe ya juye da mujiya.
A yau ya gane ashe barikin ma suna ta tara, lallai yau ya tabbatar da cewa mace sai ta so duk wani iskanci zai wakana tsakanin ta da namiji,murmushi kaɗai ya isa ya ja ragamar afkawa zina balle har a kai ga yin magana da juna.
Yau ya gane cewar ashe ba kowacce mace