Showing 33001 words to 36000 words out of 78127 words

Chapter 12 - BIYAYYA Book Complete Hausa Novels by HAERMERBRAERH.txt

17 Oct 2025

1444

k'wance da kan shi sannan cinyar ta,daga qarshe itama baccin ne ya dame ta ta miqa hannu ta d'akko masu pillo ta saka masu a wajen suka kwanta, bacci suka yi har asuba, sannan suka tashi suka yi brush su ka yi sallah, azkar ta yi ta taba karatu wanda shima ya qoqarta kwatantawa yin hakan, bayan sun gama ne ya miqe yayi mata sallama ya tafi, Hafsat ce ta shigo suka gaisa da qanwar ta ta tace,

" Akwai wani abu da kike sha'awar ci ne yau?"

" Eh dan Allah ki soyan chips ki baɗe shi da mai da yaji, amma kar ki soyan kwai bana son qarnin, kuma banda tea kawai zallan ruwan randar sanyinnan dana ce driver ya siyo jiya ya ishe ni, ina ce kin zuban ruwa a ciki,"

"Oh ni Hafsat wannan kwad'ayi na bani mamaki, eh na zuba maki ruwan maman biyu,"

Dariya suka yi sannan Hafsat ta qarasa shiga ta zauna a gaban Eamaan,

" Eamaanii meke faruwa ne ke da Alhaji? Kar fa ki zama kina bashi had'in kai kuna shiga haqqin sauran matan shi dan na ga yana yawan zuwa nan ko ba lokacin girkin ki ba, kinsan shiga haqqin wani haramun ne ko?"

Ta fuskanci inda yayar tata ta dosa,dan haka sau ta zauna ta sanar da ita dik abinda yake faruwa a gidan, Hafsat ta yi matuqar jinjinawa qanwar ta domin tayi qoqari ainun wajen cika dalilin da ya sa aka aura mata Alhajin, miqewa ta yi bayan ta yi addu'ar Allah ya kyauta, taje ta yi mata abinda take so taci ta kawo mata.


Bayan komawar Alhaji sashen Hajiya Qarama wanka ya shiga ya sake yi sannan ya shirya cikin manyan kayan da suka fito da quruciyar da ta yi masa saura a tare da shi,yana tsaka da fesa turaruka Hajiya Qarama tace,

" Alhaji ina son zuwa gidan mu na dad'e ban je ba Mama nata yin waya akan yaushe zan kai su Sabeerah, kaga week end ne zata ji daɗi idan na kai su yau, kai kan ka ka jima baka je gaida Mamana ba idan ka kai mu kuka gaisa sai ka tafi in yaso inna gama na kira driver ya dakko mu,"

"OK to ki shirya mu je na aje ku din,"

Cike da murnar samun nasara ta fara shiri ita da yaran, kwana biyu yaran na son zuwa gaida Aunty Eamaan amma an hana su sam,haka suka gama shirin su suka fita harabar gidan, Alhaji sai da ya sake leqa Eamaan suka gaisa again sannan ya fita,kan ya dawo Hajiya Qarama ta cika ta yi famm, a duniya ta tsani wannan mahimmancin da Alhaji ke baiwa Eamaan,kwafa ta yi tace muzuba mu gani idan tusa zata hura wuta kuma a juri zuwa rafi da tulu dan kuwa watarana zai tarwatse a qasa,shiga ya yi motar ya ja su sai gidan su hajiya qarama, maman ta ta ji dad'in ganin ta sosai,nan take sai Alhaji ya cire zargin komai da ke ran shi a ada game da yawan fitar ta, bayan sun gaisa ne kawai yayi masu sallama ya tafi,a can qasan layin su Hajiya Qaramar ne ya ga wani abokin shi nan ya tsayar fa mota a gefen titi suka tsaya gaisawa saboda an dad'e ba a haɗu ba.

" Mama bari na je kasuwa na dawo, zan d'an sai wa abokiyar zamana wasu abubuwan da take kwad'ayi kin san me ciki,"

"  To shikenan Amma fa kar ki dad'e,"

Shine abinda maman ta ta ce ita kuma ta sa kai ta bar gidan,tana fita soron gidan su ta fesa turaruka masu daɗin qamshi sannan ta dauki sweet mai qamshi a jakarta ta saka a bakin ta( kun ji dai Hajiya Qaraman shagali abinda take yi ko? ta iya yi ma wani qato shiri mai kyau amma banda mijin ta) mai adaidaita sahu ta tare ta hau ta fad'a masa inda zai kai ta, babu b'ata lokaci ya yi hanyar gidan Alhaji Saminu na shaqatawa da ita, gilmawar ta Alhaji Abdullahi ya gani a cikin adaidaita sahu, cikin hanzari ya yi wa wannan abokin nashi sallama ya bi bayan su, daidai qofar gidan  ta tsaya ta sallami mutumin ta fad'a gate d'in da yake a bud'e ,dan ya san da zuwan ta yana ciki yana jiran ta, gidan ko mai gadi babu saboda baya son sa ido,tana shiga Alhaji ya qaraso da motar shi, ya shige ciki shima..........



*Chaiiiii shift let me faint i beg, dan na san Alhaji sai ya suma sau tara, na yi masa karar ɗaya ya cike goma*😱😱😭
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    BIYAYYAH   💅🏼






WRITTEN BY HAERMEEBRAERH






Page 14 :






Tana shiga ta yi sallama Alhaji Saminu ya fito daga shi sai gajeren wando, yana ganin ta ya buɗe mata hannu alamar ta je gare shi, babu b'ata lokaci ta cire mayafi ta yar a qasa ta nufe shi da sassarfa zata rungume shi taji an daka mata wata gigitacciyar tsawa,Alhaji Abdullah ne yace,

"Idan kika kuskura kika taɓa shi a gaban idona sai na kashe ku gaba ɗayan ku,"

Cike da fushi da d'acin rai yake yin maganar dake nuni akan zai iya aikata abinda ya furta akan nasu, kallon shi ta yi a kidime da tsantsar tashin hankali dan kuwa shine mutum na qarshe da take son gani a yanzu a kuma wannan halin da suke ciki,Alhaji  Saminu ne ya qarasa takowa gaban Hajiya Qarama ya sunkuyar da kan shi ya yi kissing ɗin lips d'in ta,ganin haka ne ya sanya Alhaji Abdullahi jingina da kujerar kusa da shi saboda ganin qarfin halin Alhaji Saminu, gaba ɗaya ji ya yi jiri na diban shi, Hajiya Qarama d'an baya ta ja daga jikin Alhaji Saminun idon ta sai zubda hawaye yake yi, haƙuri take son ta bud'e baki ta bashi amma inaa ta kasa,

"Na san me ya kawo ki waje na Hajiya, kuma wannan ranar nake ta jira sai dai to my biggest suprise sai ga shi kin zo min da babban gift na zuwa da Alhaji"

Ya juya ya kalli Alhaji Abdullahi da isa da ta qama sannan yace,

"Ban fada maka ba?  I vow to destroy your life and family from the day you destroy mine, Alhamdu lilLAAH i have succeeded in destroying your family, yanzu sauran abunda ka mallaka ka jira ni ina nan tafe kan dukiyar ka,maza ka tarkata matar ka ku bar min gida kafin na sakar maku durwan kare na, yayi maku fata-fata,"

Komawa d'aki yayi ya dakko rigar shi ya saka,Hajiya Qarama ce tayi qarfin halin cewa,

"Me ke faruwa ne a tsakanin ku mara daɗi har haka?me yayi maka kake fadan hakan?"

Dariya Alhaji Saminu ya yi sosai sannan yace,

"Lallai ne ashe fa ke baki san tarihi ba, to bari kiji me mijin ki yayi min har na fara neman ki dan baqanta ran shi, a shekaru masu yawa da suka wuce, lokacin mijin ki na tsakiyar akuyancin shi daga zuwa gidana mu ci abinci, ya qyalla ido akan qanwata kuma amana ta da iyayen mu suka rasu suka bar min, amma haka wannan d'an akuyan ya sata a gaba, sai da yayi mata ciki har sau uku yana kai ta ana zubarwa babu wanda ya sani, a na huɗun ne basu samu nasarar zubarwar ba, jini ya ɓalle mata sakamakon ji mata ciwo a mahaifa da aka yi, "

Share hawaye suka yi kusan a tare shi da Alhaji Abdullahi wanda tin da Alhaji Saminu ya fara bada labarin ya hau tina yanda abubuwa suka kasance a tsakanin su a shekarun baya wanda har yanzu idan ya tuna kuka yake yi na tsantsan nadamar lalata kamilar yarinya da ya yi, Alhaji Saminu ne ya ci gaba da cewa,

"Tin daga wannan aikin da aka yi mata ta dinga zubda jini kuma taqi fadawa kowa sai a ranar da zata koma ga Allah ne take neman gafarar mu ni da mata ta,a nan ne ta faɗa mana komai da ya faru tsakanin ta da kai, a dai-dai lokacin da qanwata ta mutu wannan bunsurun ya sake ɗaukan wata d'iyar abokin mu ya fita da ita qasar waje yana sheqe ayar shi da ita, duk sai da qanwata ta zo rasuwa ta faɗi abinda ke faruwa, domin kuwa qawar ta ce, a haka ta mutu bai zo ba daya dawo, sanda na je na same shi da zancen lokacin ya fini komai a rayuwa, kuɗi suna, mulki da iko sai yayi min korar kare, tin daga lokacin na quduri niyyar sanadin komai na farin cikin ka, ina fatan ɗaya tarkon dana d'ana a cikin gidan ka shima ya tashi bayan na dukiyar ka dana d'ana maka nan da wasu kwanaki ko watanni, Allah ne kawai masanin sanda zai tashi bummmm,se dai ka ga dukiyar ka ta zama tarihi"

Maganganun shi sun yi matuqar tsorata Alhaji Abdullahi da Hajiya Qarama , Hajiya Qarama kuwa ji ta ke kamar ta kashe Kan ta ta huta dan takaici, Alhaji Saminu ne ya daka masu tsawa gaba ɗayan su yace su tashi su fitar masa a gida,

" Ohhh na manta Hajiya ko zaki ɗan tsaya ne mu ɗan yi na yau kan ki tafi?"

Sai ya isa wajen ta yana shafata cikin wani irin yanayi na duniyanci,janyewa take tana kuka sosai Alhaji ya rintse idon shi, ya miqe da kyar yana hada hanya ya fita daga gidan direct mota ya faɗa hankalin shi a tashe,da taimakon Allah ya isa gida, ita kuma gidan su ta koma ta d'ebi yaranta ta yi gidan Alhaji da su, kowa ya tambaye ta meya sa ta kuka taqi kulawa, ganin haka yasa suma yaran kawai suka fara kuka, a haka suka isa gida yara kuka Hajiya kuka, yana zaune cikin mota yana ta rusa kuka dan ya kasa fita balle ya shiga ciki be san wa zai tinkara da wannan musibar da ta same shi ba, a haka ta shiga gidan ita da yaran,d'aga rinannun idanun shi ya yi ya kalli hanyar da take son bi yace,

"Ashe matar nan bata da kunya? Me kuma ya dawo da ita gidana bayan ta ji na san komai? Maybe ta na da death wish ne ya sa ta dawo,"

Cike da fishi ya ɓalle murfin motar ya nufe ta,wasu kyawawan maruka ya tintsira mata sai da ta kifa qasa, ya bita ya take mata qafa ihu ta zabga wanda ya sanya Sahabee da Hajiya Babba dake tsaka da holewar su suka miqe tsaye a firgice a gigice,nan take suka ɗauki kayan su suka mayar, Sahabee ne ya fara fitowa waje sannan Hajiya Babba, ball suka ga Alhaji na yi da Hajiya qarama yaran ta na ta ihu suna kiran Daddy kar ka kashe Mum din mu, ihun su ne ya fiddi Iya da Eamaan da Hafsat farfajiyar gidan suma, sai masu aikin gidan dake lab'e suna kallo ikon Allah

Ita kuwa hakuri kawai take bashi amma yaqi ma yin magana, dan wani abu yake ji ya tokare masa maqoshin shi,Eamaan ce ta tako a hankali cikin ɗan cije lebe dan yanzu ciwon kai ke damun ta,yana ganin Eamaan ya nufe ta da sauri kamar qaramin yaro, ya fada jikin ta, saurin tsaida jikin ta ta yi saboda kar su faɗi,hannun ta dika biyun ta sanya ta zagaye jikin shi da su, kuka ya saki mai qarfi yana ta yi ba qaqqautawa, ita kuma bata hana shi ba sai buga bayan shi da take yi, Iya abun nan ya d'aure mata kai matuqa dan kuwa bata gane komai ba, cike da Umarni ta kira sunan shi, ya d'ago sai ajiyar zuciya yake yi ya kalle ta Iya tace,

"Abdullahi sanar dani meke faruwa ne haka a gidan yau kuma?"

Eamaan ce ta kama hannun shi ta ce ma Iya,

"Iya mu shiga daga wajen ki ko kinga kowa na kallo har da masu aiki, ina ganin in ya zauna ma zuciyar shi zata fi sanyi ya ji dad'in sanar da ke komai,"

kallon Eamaan d'in Iya ta yi ta kad'a kai sannan ta yi gaba,dikkanin su d'iba suka yi zuwa part din Iya,kamar Sahabee ya gudu haka yake ji saboda kar asirin shi ya tonu, dan tabbas ya san asirin Hajiya Qarama ne ya tonu, suna isa kowa ya zauna Iya ta maimaita tambayar ta, Alhaji cikin kuka ya sanar da ita su Sabeerah ba yaran shi bane, ya qara da Sanar da ita wanene uban su, Salati Iya ta ɗauka,nan da nan ciwon ta ya tashi, da gudu suka nemo maganin ta suka hau dura mata, ana jera mata sannu, Eamaan ce tace a kaita daki ta kwanta ta huta in ta samu bacci tinda dana bacci ciki zata samu sauqi inshaa Allah, d'aki Sahabee ya kaita hankalin shi a matuqar tashe, qin komawa parloun ya yi ya zauna nan wajen Iya, Alhaji Abdullahi kuwa miqewa tsaye ya yi ya nunawa Hajiya Qarama hanya ya sanar da ita ya sake ta saki uku, kuma ko tsinke ba zata ɗauka a gidan ba tinda shi ya siyo mata dik abinda take taqama da shi dan haka ta fitar masa a gida yanda ta shigo, kuka take kamar ranta zai bar jikin ta amma ba wanda da ya tausaya mata,kowa ta kan shi yake yi a wajen, musamman Hajiya Babba da ta sa a ranta in dai aka kori Qarama zata tona masu asiri, nan ko bata san hankalin Hajiya qarama yayi tashin da ta manta da rayuwar su balle ta tona masu asiri, tankad'a ta Alhaji ya yi waje sannan ya yakice yaran dake ta kuka suna kiran Daddy kayi hakuri bazata sake ba, muma ba zamu sake ba, Eamaan ce ke kuka dan sabo da yaran da ta yi,yana ganin hawayen ta kuwa ya haukace da faɗin,

"ku tafi nace shegu tsinannu kuna saka min mata kuka, tankad'a kan su ya yi, ya  kira masu aikin gidan maza tare da basu Umarnin a fitar Masa da su daga gidan,ya miqe ya nufi bangaren Eamaan,dan tinda ta ga ya haukace da korar yaran da mahaifiyar su ta bar wajen tsabar tausayi, tadda ita ya yi tana ta kuka bai hana ta ba,dan ya san ko giya ya sha ba zai dawo da Qarama ba ta tafi kenan, sai da ta yi mai isar ta sannan ta miqe ta yi toilet ta gyara fuskar ta ta fito, tana fitowa ta gan shi kwance sai hawaye ke tsiyaya daga idanun shi,

"Dama abun da na aikata a baya na nan na bina ban sani ba? neman lokaci irin wannan yake ya d'aid'ai ta ni? to me ne ne Saminu yace sauran ɗaya bomb din? Me zai faru kuma bayan wannan cin amanar da Qarama tayi min?"

"Ba abinda zai fatu sai alkairi, dan haka ka kwantar da hankalin ka ka ji,"

Da wannan ta ɗauke hankalin shi da salon ta da ya yi kewa.

Ba dan k'warewar da Eamaan ta nuna masa ba da kuma son da yake yi mata baya jin akwai abunda zai ɗauke masa takaicin wannan ranar, ranar dai Hafsat barin bangaren su Eamaan tayi ta koma na Iya, dan gaba ɗaya Alhaji ya haukace a kan Eamaan, idan Alhaji yana gaban Eamaan jin shi yake yi kamar jaririn ta, zai iya yin komai gaban ta.

A kwana a tashi cikin Eamaan ya kai wata bakwai kullum Alhaji cikin nasiha yake mata akan ta kula da abinda ke cikin ta,dan yasan ko bayan ba shi babu mai kula masa da abinda suka haifa a dangin shi,ba masu son shi domin Allah sai dan abinda ya mallaka,a kullum takan nuna masa ta fahimtce shi ya daina saka damuwa a ranshi.

Watan da zai kama ne za a yi bikin Hafsat dan haka ta koma gida dan fara shirin biki,ranar da zata tafi Eamaan kuka ta dinga yi domin kuwa ba ta son rabuwa da yayarta ta,lokacin da aka fara gudanar da bikin kuwa Alhaji ya sakar masu kuɗi sosai da su suka qarasa yin siyayyar da basu yi ba, angon Hafsat kuwa idan suna waya Eamaan dariya take yi musu sosai, dan da ganin yanda yake abubuwa zai yi naci,Iya ko yanzu jikin ta ya qara yin sanyi, ba safai take zagewa ta yi ta yiwa Eamaan masifa ba,Eamaan ta dawo da yi mata abinci kamar yanda take yi ada dan tace albarka take nema.

Tin safe Eamaan ke shirin tafiya gida saboda gobe za a fara bikin Hafsat, Alhaji bai so ba amma babu yanda zai yi haka ya barta ta tafi,shi kuma ya sanar da ita zai koma Abuja dan bai ga abinda zai zauna yayi ba a gidan bata nan.

Hajiya Babba da Sahabee kuwa sak hakan yayi musu daɗi saboda sun samu freedom ɗin yin abinda suka ga dama a gidan babu mai sanya musu ido, fatan su ma shine idan ya tafi ya dad'e wannan karon bai dawoba.


Alhaji ba qaramin warning din Hafsat yayi ba akan ta kular masa da Eamaan da abinda ke cikin ta kar a wahalar masa da mata da aikace-aikacen biki sannan ya qara da cewa,

"A kuma dinga bata abinci akan lokaci, kar kuna damun ta idan tana bacci, banda yawan sata aiki Hafsat, kinga dai bata jin dadi,i don't want to lose my baby pls"

Cike da tausayawa Eamaan ta kama hannun shi ɗaya ta kwantar da kan ta a gefen jikin shi tace,

" Ba zaka rasa komai ba Alhajina, kwana biyar kawai zanyi ko ka dawo ko baka dawo ba zan dawo gida ni, ka sa wa ranka salama kar wani ciwon ya zo yana damun ka ka ji?"

D'aga mata kai ya yi tare da manne ta a jikin shi ya na sumbatar ta, Hafsat rufe fuska ta yi da hannu d'aya tana fad'in,


"Oh ni Hafsat ina ganin rayuwa a wajen bayin nan na Allah ! Thank god na baro gidan ku na dena ganin wannan rayuwa da kuke bani kunya da ita,"

Alhaji ne ya kalle ta yace,

" kinyi magana  ne ?"

'Aaa'aa ni ban ce komai ba,"

Dariya suka yi gaba d'ayan su, sannan  Hafsat ta taya Eamaan shigar da kayan ta cikin gidan.

Aqofar masallacin gidan su ta gan shi yana saka takalmin shi, suna haɗa ido suka ji wani abu daga kan su zuwa qafar su mai nauyi qarshe ya danne zuciyoyin su, saurin kauda kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login