Showing 51001 words to 54000 words out of 78127 words
Chapter 18 - BIYAYYA Book Complete Hausa Novels by HAERMERBRAERH.txt
su d'ibar kayan su zuwa cikin parlour, bayan shi suka bi bayan Hafsat ta nuna wa driver d'akin da zai sauka, gidan ba Wani kantameme bane gida ne madaidaici me kyau, farfajiyar gidan bata wuce wajen aje motoci biyu ba,bayan ya ajiye kayan ne ya kama hannun matar shi ya na bin fuskar ta da kallo alamar ya yi kewar ta sosai, murmushi suka yi wa juna kafin ya saki hannayen ta ya dauki kayan su ya shigar musu d'aki, already sun yi waya da Hafsat ta Sanar da shi zuwan su tare da Eamaan d'in, d'akin ta bi bayan shi d'auke da Fatee a hannun ta ,ta masa godiya tare da qaramin murmushi, yana fita ta samu ta kwanta a gadon bayan ta kwantar da Fatee, kan ya fita sai da ya sanar da ita in ta gama.akwai abinci ta fito su ci, ta amsa masa da "To na gode"sannan ya fita, murnar dawowar Hafsat ce ta cika shi da zumud'in ganin ta kamar zai taka da gudu ya Isa gare ta yake ji, daki suka shige suka barni tsaye sororooo.
Eamaan wanka ta yi wa Fatee itama ta yi, tana ta ma ta dariya kuwa, da surutu kala kala, shiryawa ta qarasa yi itama ta fita parlour riqe da hannun Fatee,kamar yanda ya fad'a kuwa abinci ne me rai da lafiya kamar ba namiji bane ya dafa shi, zama ta yi a kujera ta kunna TV Dan ta Jira su.
Hafsat kuwa da mijin ta suna d'aki ana soye wa, an jima ba a gamu ba, Dan ma Hafsat na ta bashi hakuri ya Jira se an jima, kar Eamaan ta yi ta jiran su da kyar ya hakura ya taya ta wanka, ya bar ta ta qarasa, kafin ta fito ya dakko mata kayan da zata saka marasa nauyi, ya fesa musu turaruka, ya ajiye, ta na fita ya nufe ta ya na sake bin jikin ta da kallo, tare da fad'a mata yanda ya yi kewar ta, itan ma bayyana masa irin yanda ta yi kewar sa ta yi, sannan suka sake tambayar juna bayan rabuwa.
Ta na kammala shiri ya saqale hannun ta a nashi suka fita parlour, Eamaan na ganin su ta miqe ta sake gaishe shi, Yaya da ta kira shi da shi se ya bashi dariya, ya ce Dan Allah kar ta tsufar da shi, dariyar itama ta yi, ta ce dole ta kira shi da Yaya tinda mijin yayar ta ne shi, abinci suka ci har Fateema, suna gamawa ta miqe ta musu sai da safe, ko ba Dan komai ba ma ta gaji, sannan ta na kallon irin kallon zalamar da mijin Hafsat din ke bin Hafsat d'in da shi, be Kamata ta b'ata musu lokaci ba.
"Ba Zaki sha tea din naki ba na qa'ida Zaki kwanta Eamaan?"
"Na gaji mun had'u da safe"
Murmushi kawai Hafsat ta yi, ta kula Eamaan na Allah Allah ta Basu waje ne, Dan haka da Kan ta ta miqe ta kunna gas ta Dora ruwan tea, ya na gama dahuwa ta zuba a mug ta Dora a qaramin trey ta nufi d'akin Eamaan d'in, ta na shiga ta tarar har ta yi bacci, se surutai take a baccin nata,
" Alhaji ka dawo pls, ka zo wajen mu muna kewar ka,"
Tana ta surutai idon ta na hawaye,tausayin ta ne ya kama hafsat, ta toshe bakin ta dan kukan da take son yi, sai da ta maida kukan ta ta daga Eamaan d'in, wadda tai firgigit ta tashi, tana zaro ido,
" Hafsat yanzu naga Alhaji, yana ta mun murmushi, yana min bye bye,ina ta ce masa ya dawo yana kadan kai yana ban hakuri,yace na kwantar da hankali na shine kwanciyar hankalin shi,"
"You see, hakan na nuna maki kukan da kk yawan masa baya so, addu'ar ki kawai yake so, dan haka ki sawa ran ki hakuri shima ya samu dadin kwanciya, kinji,karbi ki shana hado maki tea din naki,"
Karb'a ta yi ta shanye sannan ta miqa mata mug d'in, ta koma ta kwanta,
"Na gode 'yar uwa ta, Allah ya bar mu tare"
Shafa kafad'ar Eamaan Hafsat ta yi, ta ja mata abun rufa ta dauki Fatee ta wuce da ita q kafad'ar ta, dik da Eamaan ta hana saboda Gani take in ta farka zata Hana su sakewa, Hafsat ta ce mata ba komai zasu kula da hakan, Kan ta koma mijin Hafsat ya Kai wa driver abinci da ruwa, ya nuna masa dik abinda zai buqata sannan ya koma ciki,bayan sun kashe komai na wuta suka kulle gidan suka wuce d'aki kwantar da ita suka yi, bayan Hafsat ta yi mata shimfida da lallausan bargo, ta sa mata pilo, su kuma suka haye gado, kwata kwata mijin Hafsat ko a fuska be nuna Jin haushin dakko Fatee da Hafsan ta yi ba, shi dai fatan shi a zo a bashi haqqin shi.
Da safe Eamaan ta riga kowa tashi, ta shiga gyara gidan, dik da bai wani datti ba, ta je ta fara hada abin karyawa, nata ta zuba ta zauna tana ci suka fito, cikin wanka da kwalliya, mijin Hafsat dauke da Fatee Hafsat dauke da jakar shi, suna ma Fatee wasa, tana ta dariya da shirmen labarin da take Basu na yarinta, sai suka bata sha'awa, zama suka yi, ta gaida su, mijib Hafsat na tsokanar ta mai baccin wuri, abinci suka fara ci, Hafsat ta tashi da gudu tai toilete dake cikin palour ta yi ta kwara amai, sai da ta gama ta fito, tana nishi, mijin ta daya ke tsaye bakin qofar ne ya kama ta yana ta jera mata sannu,
" Ya kamata fa a kaita asibiti,tin da taje take amannan da safe, komai ta ci sai ya dawo, in ta yi da safen nan shikenan Bata sake yi se washegari to kuma zata ci komai lfy,"
Damuwa ce kwance akan fuskar shi, yace to ta gama ya sauke ta a sibitin ya dawo da ita, haka suka yi kuwa, bayan sun je likita ya mata tambayoyi, da gwaje2 suka.gane tana dauke da qaramin cikin, wata biyu,suna dawowa Eamaan taji labari ko sai murnar damun cikin ya mantar da ita damuwar ta, sosai sike godewa Allah da wannan kyauta, ranar kam mijin Hafsa aiki ruwa ta sha, dan bai je ba.
Zaune yake a qayataccen gidan nashi, wanda na kula duk kyaun gidannan ba matar aure cikin shi, yana karanta qur'anin da aka fassara zuwa harshen turanci, gaban shi swimming pool ne,sai dan qaramin table a gefen shi, da ya dora cup da ruwa a gefe, ya sa sun glasses, saboda akwai rana kadan, duk da yana qasan lema ne, kyakkyawan matashin da ya aje gemu irin na ustazan nan, ya gaji da kyau, tsam ya daina karatun ya shiga duniyar tinanin abinda maqocin su Kuma abokin shi ya sanar da shi jiya..........
A karanta da hakuri...Kun San tsohon rubutu ba zai daidai da sabo ba.[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 21:
Anwar ne zaune a kujera a parlour yana hutawa,tunani yake yi mai zurfi kafin daga baya ya d'akko wayar shi da ke saman qaramin table ya hau danna digits d'in abokin shi, ringing biyu tayi ya ɗauka , cikin shaqiyanci irin na abokai ya ke tsokanar Anwar,
" Yahhhh ustaz ya ne....Ya Bauchin kuma? ina fatan dai by now Ustaz ya samo mana ustaziya acan da zamu sha biki, kasan fa 'yan bauchi ustazai ne."
"To kanya sarkin zuba, ai kama jira in amsa maka gaisuwar taka ko? dama na kira ka ne akan labarin da ka bani game da Eamaan kwanaki ,tin da ka fada min nake ta tunanin anya gaskiya ne kuwa?"
" Man da gaske ne mana, yanzu haka tana garin Bauchi a gidan yayar ta Hafsat,saboda jiya an wangale gate d'in gidan na hango ta tana ta kuka tana masifa ma wani Alhaji, ina nan zaune ina mamaki akan abinda na gani, saboda gaba ɗaya Eamaan ta sauya akan yanda muka santa,na kai minti biyar a wajen bayan Alhajin nan ya tafi,dake qofar buɗe aka barta shi ya bani damar ganin ana saka musu kaya a bayan mota,ana gama loda kayan ne suka yi sallama da mutanen gida suka shige mota driver ya ja suka bar gidan, tafiyar su da mintuna na zauna a qofar gidan su,to dake ka san baba me gadi mutumin mu ne, a wajen shi nake samun labarin dik abinda na fad'a Maka kwanaki har ya min qarin bayanin ai jihar Bauchi suka nufa zata je Bauchin gidan Hafsat dan ta huta da hayaniyar da keta faruwa."
Ajiyar zuciya Anwar yayi cikin zuciyar shi yace,
'Lallai wannan babbar dama ce a gare ni ta dawo da soyayya ta sabuwa dal a zuciyar Eamaan.'
Abokin shi ne yace,
"Man yaa dai na ji ka yi shiru? Lafiya dai ko?"
"Lafiya qalaou kayi min qoqari na gode sosai Allah ya qara mana zumunci, sai mun yi waya, Assalamu alaikum,"
Sallamar abokin na shi ya amsa suka kashe wayar, murmushi ne kwance a fuskar shi, da kuma addu'ar da ta zama sirrin shi,domin kuwa dik tsawon waɗannan shekarun bai taɓa mantawa da ita ba, soyayyar ta kuma bata taɓa gushewa daga zuciyar shi ba.
Girki take a kitchen su kuma suna zaune a plour da Fatee sai sa su dariya take yi, Kamal ne yace da dan qarfi yanda Eamaan dake kitchen zata iya jiyo shi,
" Eamaan ko zaki d'akko takardun ki ne a nema maki aiki ki fara, nema maki aiki ba zai min wuya ba in Allah ya yarda, akwai Wani cousin d'ina da ya bud'e Wani asibiti ko anan se na nema maki,zuwa aikin shima zai taimaka maki wajen rage maki kad'aici ko baby?"
"Kwarai da gaske wannan m shawara ce mai kyau."
Inji Hafsat,Eamaan kuwa sai da ta kammala abunda take yi,sannan ta dakko abincin ta fito parlour ta same su, kunun acca ne Hafsat ke so ta yi mata da alala, da rana su kuma tayi masu rice and stew da salad da pepper meat mai cike da veges a ciki,gefe ɗaya kuma Apple drink ta hada masu domin tafi son haɗin gida akan lemon kwali ko na roba,a tsakiyar su ta aje sai kowa ya ja plate suka fara ci,bin ta ya yi da kallo, dan har lokacin bata bashi amsa ba,a hankali ta furta,
" Yayah ka d'an bari ba yan zu ba, sai naje gidan Yayah Babba na gama mata hutun ta na dawo, saboda kaga ba lallai bane na ci gaba da zama anan dindindin, wataqila zan koma kano,"
kallon ta ya yi da harar wasa sannan yace,
" kina nufin ba zaki zauna a wajen mu ba har Allah yasa ki samu d'an bauchi ki aura kin ga shikenan Hafsat ta samu 'yar uwa a kusa."
murmushi suka yi,
"Ohhhh ashe son kai ne abuunn, shi yasa ake son na samu aiki a bauchi ko, to naqi wayon kano ma Mama da Amma na jirana,sannan Hafsat bata da Wani dangi da ya wuce Kai da 'yan uwan ka, mu haka aka koyar da mu a gidan mu, dangin mijin mu su ma 'yan uwammu ne in bamu d'auke su 'yan uwa ba wahala zaman zai yi mana Ina fatan ka gane"
Dariya suka yi ya kalli Hafsat tabbas ya kula da hakan, shi yasa Hafsat bata tab'a nuna banbanci tsakanin dangin shi da nata ba, Kuma ya kula dangin shi na son ta sosai kamar dama can a cikin su take, kallon ta ya yi ya marairaice fuska akan ta sa baki, d'aga hannayen ta ta yi tana juya ido da kai, sannan ta dan kyab'e baki tace,
"Ba ruwana kai da qanwar ka ne, in ta yarda zan fi kowa farin ciki da hakan, in bata yarda ba faqat,ka lallab'a abarka da Kan ka, kalan in shiga ku kunyata ni ko?"
kauda kan shi ya yi zuwa wajen Fatee yana ma Fateen wasa wai shi irin ya yi fushin ɗin nan, dariya suka hau yi masa, ita kuma Hafsat ta d'an mintsine shi kadan, ya saki qara yana sosa wajen yana kallon ta,cikin dariya Hafsat tace,
"A haka ka ke son ta zauna in wani ya kawo mata raini wa zai rama mata, daga d'an wannan mintsinin zaka sake mana ihu se kace Wani budurwa"
Ta na ganin alamun ramawa ze yi ta miqe suka yi ta zagaye wajen suna dariya,Eamaan kad'a Kan ta ta yi sannan ta kai cup din lemon da ta d'ebo bakin ta,cike da murmushi da nishad'i take kallon su suna burge ta sosai,tinanin yanda Alhaji ya ke yi mata wasa ne ya faɗo mata a rai, cikin kasala ta sauke cup din, idon ta ya tara ruwa sosai, a hankali ta miqe zata shiga d'aki,sai a sannan ne suka kula da yanayin ta, ba su hana ta barin wajen ba, waje suka samu suka zauna manne da juna suna maida numfashi, bayan ta shige ne Hafsat tace,
"Da alama wasan da muke yi ne ya tina mata Abban Fatee, domin kuwa bawan Allahn nan duk da ya tsufa ya nuna mata irin yanda yake son ta,ya nuna mata shi saurayi ne a zuciya, dan jin dad'in ta ba abinda baya yi mata, haka zai goya ta kamar wata jinjira ya na jijjiga ta, na sha ganin shi ya na mata abubuwan da ko da saurayin ta aura ba lallai ta samu kulawa haka ba, Fatee ce ta hau cinyar Hafsat ta kwantar da kan ta, Hafsat d'in ta shafa bayan ta da tausayawa.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Eamaan na samun nutsuwa da kwanciyar hankalin da iyayen ta da 'yan'uwan ta keyi mata fata a bauchi,kullum a Sky crown suke siyan bread dan basu da nisa sosai, haka shima gidan Anwar ba nisa da wajen.
Wata rana mijin Hafsat ya fita office basu tashi da wuri ba suna ta bacci sai wajen 10am suka farka har Fatee, dan daren ranar sun sha hira ne sosai har lokaci ya ja basu kwanta da wuri ba, shiyasa suka makara basu samu tashi da wuri ba, dubawa suka yi suka ga ya yi sultan chips sannan ya dafa Tea daya sha kayan qamshi, ya rubuta ma matar shi saqon yana son ta ya fita aiki sai ya dawo dan haka ta kula da kan ta da su Eamaan, murmushi ta yi ta aje takardar, ta rufe flask din abincin ta samu waje ta zauna,
"Ni yau sky crown bread nake son ci, so nake na ji laushi da dad'in shi a baki na,musamman mai inibi da mai kwakwar nan,"
Yawu ta hadiya kamar wadda ta gan shi a gaban ta amma an hana ta ci,
"To bari na je na siyo maki mana,sauran kuma kafin na dawo ki cinye abincin zaki dafa min wani, dan na kula yanzu kin zama hamburin hayam, ki bari na dawo mu ci tare dan yunwa nake ji nima,in ma bamu qoshi ba sai na yi mana wani ."
Dariya Hafsat ta yi tace,
"Ni ki ka ban bread dina ma ko kallo baki isheni ba,"
Dariya suka yi ta ɗauki kudi da hijab ta saka ta fita, tafiya take a qasa don ba wani nisa gare su ba ta ga wata dalleliyar mota ta wuce ta,a hankali kuma sai motar ta fara yowa baya, qin d'aga kai ta yi ta kalli motar sai ta ci gaba da tafiyar ta,tana isa sky crown ta nufi wajen da zata sai bread ɗin ta shi Kuma ya fito daga motar yana son tsallaka wa inda take,Eamaan ta kula da cewar wani na bin ta a baya,cikin sauri ta samu wani lungu a wajen ta boye qirjin ta na bugawa dan tsoro,shi kuwa Anwar dubawa ya hau yi ko ina bai gan ta ba,tsaye yake yana kalle-kalle cikin shigar shi ta qananan kaya ya ɗora hannun shi a qugu dayan kuma a goshin shi,a haka ya fito yana ci gaba da duba ta ko zai samu dacewa ya ganta, tinanin ana jiran shi a asibiti ne ya katse shi daga neman da yake yiwa abar ƙaunar shi da ya gani bayan shekaru ,motar shi ya shiga ya tada ya tafi zuciyar shi na tabbatar masa da Eamaan ya gani.
Bayan tafiyar shi ne ta fito daga maɓoyar ta ta wuce wajen siyan bread ɗin ta,har aka gama bata zuciyar ta bata dena tunanin wake bibiyar ta ba,ana bata ta biya kuɗi ta karb'a ta koma gida cike da tsoro,miqawa Hafsat bread ɗin ta yi ta wuce d'aki jikin ta duk ya yi sanyi, dama haka unguwar masu kuɗi take gaba d'aya sai kaga mazan kusan dikkan su masu son matan tsiya ne, kawai ba dama aga mace ta d'an haɗu ta fita ba ruwan su da dare ko rana zasu tsaya su dame ta,tsaki ta ja kawai ta fad'a gado, ta yi lamo, ta rasa ma tinanin me take yi.
Muryar Hafsat ce ta dawo da ita cikin hayyacin ta tace,
" Eamaan me ya faru ne naga kin dawo kawai kin kwanta baki zo mun karya ba me aka yi maki?"
Zama tayi a saman gadon cikin damuwa ta baiwa Hafsat labarin abinda ya faru, murna ta gani kwance akan fuskar Hafsat daga baya kuma ta ce,
"Too Allah ya kyauta taso mu je mu karya,"
Tashi Eamaan ta yi suka je suka ci abinci sama-sama,dan kuwa ba yanda taso ci ta samu taci ɗin ba.
Tin da yaje asibiti yake tinanin tabbas ita ya gani ba wata ba,to dama a kusa suke kenan tinda gashi ya ganta a bakery ɗin unguwar su? tabbas in a kusa suke kuwa zai sawa wajen ido yaga daga gidan da take fitowa,a hankali ya furta,
"Ba zai yu na qara rasa ki ba a karo na biyu Eamaan d'ina,Zaki zama tawa wannan karon inshaa Allah."
Tiyata suka yi ma wata mata da ta gagara haihuwa da kan ta,bayan ya koma office ɗin shi ne ya buɗe fridge ya dakko gorar ruwa ya ruwa ya tsiyaya ya shanye yana lumshe ido, key d'in motar shi ya ɗauka cikin sauri ya fice daga office ɗin ya wuce wajen da yayi parking motar shi ya shige...........
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 22:
Direct bakeryn ya koma, yana shiga masu gadi da ma'aikatan wajen suka yi ta gaida shi da