Showing 30001 words to 33000 words out of 78127 words

Chapter 11 - BIYAYYA Book Complete Hausa Novels by HAERMERBRAERH.txt

17 Oct 2025

1451

Eamaan na ɗauke da cikin watanni 3 zuwa 4 ba? Meye plan din mu akan hakan ne dan dai gaba d'ayan mu yanzu mu masu laifi ne a wajen Alhaji da ya san me muke aikatawa a bayan idanun shi kashin mu ya bushe,  Qarama kin dai san baki da gadon yaran nan a gidannan dan ko in Alhaji ya fad'i ya mutu ni ko Sahabee ba bari zamu yi a raba da shegu ba tin da mun san komai,"

Wani mugun kallo Hajiya Qarama tai wa Hajiya Babba, sannan tace,

" Yo me zamu yi banda mu qoqarta zubda cikin tin kan yazo duniya? Ko dake na kula ku tsoron ta kuke ji har yanzu,"

Sahabee ne yayi mata kallon baki da hankali,

" ke kan ki tsoron ta kike yi balle mu,akan me ba zamu ji tsoron mace kamar Eamaan ba, macen da ta san me take yi, tasan ta kan tafi da abokin gaba ba tare da tada jijiyoyin wuya ba ko hargowa,tasan yanda zata saka duk wani wanda basa shiri da ita cikin fargaba da tashin hankali, dan haka ni ina ganin kar wadda ta yi yunqurin taba abinda ke cikin ta,koma dai menene Yayah dan uwana ne, dan haka zan so ace yau ko da d'a d'aya ne ya ga jinin shi shima a duniya ,dan haka ku kiyaye kar na ji labarin wani abu ya sami cikin nan,"

shiru suka yi, kowacce da abinda take saqawa,Hajiya Qarama ce ta buɗe baki tayi magana cikin fargaba da tsoro tace,

"Ni yanzu ku ban shawara dan Allah, ya zan yi na sanar da Alhaji Saminu ina ɗauke da yaran shi guda biyu ba tare da ya qi karb'ar su ba?"

" Kar kiji tsoron komai ki sanar da shi komai a wannan dawowar da zai yi in ya sani shikenan fargabar ki ta qare,idan yaso kina faɗa masa ki bashi sharuda biyu, na farko dai ko ya Karb'a cewa yara nashi ne ko ki masa barazanar tona maku asiri, ki nuna mai ke baki damu ba dan wani ya sani shi kike jiyewa,"

Gaba ɗayan su sunyi na'am da shawarar Sahabee, sannan suka shiga hirarrakin duniya daga qarshe suka tashi da fadan nasu na jaraba akan yara, Sabeerah ce ta shigo da gudu ta sanar da su dawowar su Eamaan da yayar ta,a sanadin gudun da tayi ne ta take Hajiya Babba a rashin sani,nan take tako ɗauke ta da mari, aiko nan fada ya rincab'e, Sahabee ya zame jikin shi ya fice,dan shi baya son wannan fadace2n nasu kamar kaji.

Gyara gidan Hafsat ta  shiga yi dik da babu sani dattin a zo a ganj sai qura,Alhaji na shiga kuwa ya duba abubuwan da babu sai ya yi wa driver waya yace ya zo Eamaan ta zayyana masa abubuwan da take so, nan da nan aka bashi kuɗi ya tafi siyowa, Alhaji na manne da ita kamar za a kwace ta, sai faman sannu yake mata tare da shafa marar ta yana yin wani irin farin ciki na ratsa zuciyar shi.

Hafsat dake kallon yanda yake yi wa Eamaan dai ya sa take jin kunyar shi sosai, a ganin ta tsaf zai yi sa'an Daddyn su amma ya samu yarinya sai wani soyayya yake zubawa kamar saurayi,a haka ta kammala gyara wajen ta koma d'akin dakin da yake nan zata na zama, Alhaji ji yake kamar ya yi ta zama a wajen ta kar ya je wajen sauran matan, dan yaso matuqa da ya dawo ace girkin ta ne, kuma lafiyar ta qalaou yasan tabbas zata cika mai alqawurran da ta yi masa, amma ba yanda zai haka yayi mata kiss sannan ya ɗauki jakar shi ya yi ɓangaren hajiya Babba wadda ba jimawa su sahabee suka koma bangaren su suka barta ta hau 'yan gyare-gyaren da ya kamata mace tayi dan tarbon mijin da ya dawo daga tafiya,fuskar nan ta sha fenti kamar kullum sai tashin qamshi take yi,cikin ranshi yaji daɗin samun ta a haka, dan kuwa gwanda masa ita sau dubu akan Hajiya Qarama, abincin da masu aiki suka yi na gida ta yi masu izinin kawoma,a haka yaci saboda bashi da zaɓi,yana gamawa ya yi wanka ya kwanta nan take bacci mai daɗi ya ɗauke shi saboda tinda ya dawo daga asibiti yake kwana wajen Eamaan to baccin ba wani sosai yake.
yi ba.

Hajiya Babba na ganin haka ta kulu sosai,wato ya dawo ma bai zo gare su ba sai da matar so ta bashi izini shine ya wani baje yana kwasar munshari kamar shekararren jakin dawa,qwafa ta yi ta cire kayan ta ta kwanta gefen shi, ai kuwa Hajiya bata hakura ba sai da ta san yanda ta yi ta tada shi daga baccin nan mai daɗi da ya samu, dama me neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, nan take ya biye mata suka raya wannan daren, mamaki take yi na yanda Alhajin nasu sam baya tsufa,ko Sahabee da yake saurayi Alhaji ya fishi komai, amma dan jaraba da rud'in shaid'an bazata hakura a kan mijin ta ba sai ta qara da qanin shi.

Washe gari yana idar da sallar asuba ya ɗauki hanyar ɓangaren Eamaan dan yaga ya ta kwana da jikin nata,a parlour a kwance ya ganta a saman abun sallah ta yi lamo tana azkar,gaba daya jin jikin ta take yi babu k'wari shi yasa ta kwanta a wajen, zama ya yi a gefen ta ya janyo ta ya ɗora ta a cinyar shi yana shafa bayan ta,sake mannewa tayi a jikin shi kamar wata mage, a hankali ta buɗe idon ta ta kalle shi, tausayin ta ta gani kwance akan fuskar shi, murmushi tayi masa sannan ta gaida shi, bai amsa ba sai kawai ya haɗe bakin su waje ɗaya yana sumbatar ta a hankali, a hankali ya zame bakin nashi daga nata, sannan ya amsa da,

" Babeen Alhaji sannu kinji Allah ya baki lafiya, ya sa maki kaffara, Inshaa Allah zaki samu sauqi da wuri kin ji?"

D'aga masa kai ta yi idon ta fal hawaye dan kuwa tana jin jiki, Hafsat ce ta fito daga kitchen ɗauke da plate data dafa mata taliya irin jellop ɗin nan na manja da attaruhu sai naman qaramar dabba, dan sha'awar manjan take sosai shi yasa tace a yi mata me manja, tana shigowa taga Alhajin da Eamaan a rungume da juna sai ta rikice  tace,

" I...I.... ammm sorry ban san ka shigo ba,"

" Barka da safiya Hafsat, ya aiki? sannun ki Allah ya baki lada ya sa ai bikin ki a sa'a,"

Ta ji dad'in addu'ar shi sosai amma fa yana matuqar bata kunya ita kam,a kunyace tace,

"Ameeen na gode,"

Murmushi Alhaji yayi yace mata,

" ki daina jin kunyata fa dan kuwa kin dinga ganin irin wannan abubuwan in dai kina gidannan,"

Dariya ta ɗan yi kaɗan sannan ta ajiye masu abincin zata koma ya ce ta hada mata tea, komawa ta yi ta had'o mata tea ta kawo mata,Alhaji ne ya Karb'a tare da yi wa Hafsat godiya ya fara bata a baki,Eamaan buɗe baki tayi ta dinga Karb'a har sai da ta ci abincin sosai tinda tana so dama,tea ɗin ne kawai bata sha sosai ba, wanka ya ɗauke ta yaje yayi mata, ya sa mata kaya marasa nauyi a jikin ta dan ta sha iska ya kamo hannun ta suka fito zuwa bedroom ɗin ta, taje mata kai ya yi ta d'aure da kanta,ya taimaka mata ta kwanta, yana shafa kan ta zuwa bayan ta a hankali nan take ta yi bacci, miqewa ya yi ya ja qofar a hankali ya fita, yace ma Hafsat kar ta tashe ta ta samu bacci idan ta tashi a bata maganin rana,sanan ya qara yi mata godiya sosai ,Hafsat ta ji dad'in ganin yanda yake kula da qanwar ta sosai,sai dai tana mamakin duk ba wanda yazo duba qanwar ta ta kaf gidan, daga Iya se  Alhajin suke jinyar ta kamar mutan gidan basu san bata da lafiya ba, kyab'e bakin ta ta yi ta dan buɗe d'akin Eamaan ɗin a hankali ta leqa ta,sai tagan ta kwance ya tare ta da pillo kamar wata jaririya, sannan ga shi alamar yanda ya shafa mata gashi duk ya tarwatse, murmushi ta yi ta rife qofar ta koma d'akin ta suka hau waya da Kamal din ta suna ta shan soyayyar su.

Alhaji kuwa na komawa sashen Hajiya Babba ya tarar da ita a cikin dakin ta ta cika tayi famm kamar flour da aka sanya wa yisssss, cikin faɗa ta hau cewa,

"Dan me zaka dinga yi mana rashin adalci a gidannan ne eye? Akan me zaka tattare komai naka  ka damqawa yarinya qarama baka da lokacin mu sai nata ,yanzu duba tin asuba sai qarfe 8 ka dawo sashe na akan me? Ko girkin tane? gaskiya ba zan dau wannan rashin adalcin ba daga gare ka akan 'yar cikin ka ka zauna kana rawar jiki,"

Cikin sanyin murya ya furta,

" Hajiya ki yi hakuri mana, kina ganin yarinya ce kuma ciki gare ta tana buqatar kulawa ta sosai a wannan gab'ar,"

"Yarinya? Yarinya fa kace, Eamaan ɗin ce yarinya? Yarinya ce tasan ya zata sami ciki da tsoho kamar ka? To bari kaji na faɗa maka Allah yasa a zanin goyo take bata fara haqora ba tsabar yarinta dole ka tsaida mana adalci,in ba haka ba gaskiya akwai abu mara dad'i da zai faru a gidan nan wanda ba zaka so faruwar shi ba,"

Tana kaiwa nan ta faɗa band'aki ta bar shi a wajen, shi kuwa Alhaji zama ya yi kawai yana nazarin maganganun ta yana so ya gano laifin shi, buɗe qofar uwar d'akin nasu akai babu sallama ba komai aka shiga, Alhaji na d'aga kai idanun su ya sarqe da na juna..........
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    BIYAYYAH    💅🏼








WRITTEN BY HAERMEEBRAERH









Page 13:







"Me ya shigo da kai har cikin bedroom ɗin  mu Sahabee?"

" Ah Yayah dama kana nan, ai na yi ta sallama a can parlour na ji shiru kuma da fari na ji kamar hayaniya sanda na shigo ana daga muryoyi,to da nai ta sallama na ji shiru shi ne yasa na zaci ko wani abu ne ya faru kawai na shigo kai tsaye,"

wani irin kallon ka raina min hankali Alhaji ya yi masa sannan yace,

"Babu komai to je ka kawai,"

Hajiya Babba ce ta fito daure da towel, tana ganin Sahabee ta daburce bakin ta ya hau rawa tana son tayi magana ta kasa, nan da nan Alhaji ya sak'awani zargi cikin zuciyar shi game da abinda ya faru,shin me ya sanya qanin nashi shigowa kai tsaye ba tare da neman izini ba? Me yasa Hajiya rikicewa daga ganin Sahabeen a d'akin tin kafin ta san dalilin zuwan shi?  Ɗauke kallon shi ya yi daga na ta, ya yada jikin shi kan gadon ya rufe idon shi yana tinani, a gaggauce ta saka riga ta fita waje, a farfajiyar gidan ta ga Sahabeen ya na ta Kai wa da komowa, cikin faɗa Hajiya tace masa,

" kai wanne irin soko ne Sahabee, me ya kai ka zuwa yanzu?"

"Ina zaune a d'aki ne kika fad'o min a rai sai na ji ina buqatar ki ko na minti gomane,to da yake d'azu na ga shigar shi wajen waccan yarinyar na san zai dad'e, Iya na can ta sani a gaba da zance bana ma gane ina ta dosa,to shine yanzu da ta shiga ciki ta kwanta dan ta huta kawai na yo nan, ban zaci ya dawo ba,"

Hararar shi ta yi,Sannan ta ce,

" kai wane irin shiriritacce ne, amma dai kasan a qa'ida in yana nan baka zuwa ko so kake yi asirin mu ya tonu ne,"

Sosa qeyya ya yi ya sunkuyar da kai ,ita kuwa sai ta buga tsaki ta juya ta yi ciki, Alhaji duk yana kallon su ta window yana ayyana abubuwa da dama akan su, tana shiga sashen nata ya koma ya kwanta, duk da baya jin hirar su saboda tazarar dake tsakani,kallo ɗaya zaka yi musu ka gano akwai wani abu dake wakana a tsakanin su, Idon shi ya rufe kamar yanda ta bar shi, ta koma ta ɗauki mai ta fara shafawa a jikin ta da ya bushe.

Hajiya Qarama ce kwance a gado tayi ruf da ciki tana waya cike da Jin dad'i kamar wata budurwar da ke  yin hira da saurayin ta.

" Yanzu kana ganin za ka kai wani satin a gari ne?"

" A'a gaskiya ina jin jibi ma zan koma, akwai matsala ne, ko kina son ganina ne?"

" kwarai da gaske ina son ganin ka, dan akwai magana mai matuqar mahimmanci da za mu yi da kai,"

"To shikenan sai ki samu lokaci ki fito mu gana ko,"

Sai da suka  taba zantukan su na lalacewa kafin daga baya su yi sallama da juna, cike da fargabar me zai je ya zo ta yanke shawarar yanda za ta fita, ita zata karbi girki da dare dan haka ran ta kwal tana ta murna zata samu damar tambayar fita unguwa, Alhaji kuwa fatan shi bai wuce ace tayi wanka ta yi brush kafin dare, ga mace har mace amma ba gyara, dan gaskiya Hajiya Qarama bata da muni ga jikin ta mai kyau sai baqar qazanta da wari.

A haka lokacin komawa sashen ta yayi sai ya tattara ya dawo bangaren ta, ba laifi tayi wanka tayi brush harda su sabon kitso,amma fa gaba ɗaya bata qamshi gata nan ne dai kawai a lallab'a auren zamani,a wannan karon Alhaji ya sha karairaya da gata dai-dai iyawar ta, har suka yi shirin kwaciya bacci,sai da komai ya gama kan kama ana soyayya warin hammatar ta duk ya cika masa ciki saboda sai ya zamana kamar tana aikin qarfi ne tana haɗa zufa warin na fitowa, cikin fada ya fara yi mata magana,

"Wai ke sau nawa zan yi maki magana ne akan kina amfani da turaruka a jikin ki ne ? Ga su nan da yawa har ban san iya adadin su ba saboda naki ma na musamman nake siyo maki amma ke sam baki san meye amfani da tirare ba ko saka abun da zai ɗauke warin hammatar ki kamar Alimun ko lemon tsami, sai dai ki zauna kina wari malam meye hakan?"

Tsaki ya yi ya zare jikin shi daga nata ya sauka daga gadon,da gudu ta bi shi zata maqale shi ya fizge ya bar inda take, kayan shi ya saka ya fice daga dakin,direct ban garen Eamaan ya je ya kwankwasa, Hafsat ce ta buɗe masa qofar idanun ta dauke da bacci, dik da haka sai da ta gane yana cikin damuwa, gefe ta koma ya shige ciki ko kula ta bai yi ba, direct d'akin Eamaan ya nufa,can ya hango ta tana zaune kan sallaya tana karanta qur'ani idanun ta ƙyamas bata jin bacci, agogo ya kalla yaga sha biyun dare ya ɗan gota, d'aga kai ta yi ta kalli cikin idanun shi,nan take yanayin fuskar shi da ya shigo da shi kamar mayaqi ta koma kamar ta qaramin yaron da kallon mahaifiyar shi ya saukar masa da natsuwa,kallon juna suka sake yi yaji farin ciki ya mamaye baqin cikin da ya zo da shi,cikin sanyin murya ya furta,

" Tabbas Eamaan ke alkhairi ce a gare ni, ko raina ne ya ɓaci na gan ki hankali na sai ya kwanta,may i spend the night here with you please? Dan in baki barni ba yanda nake jina ɗin nan waje zan tafi,"

Ya qarasa Maganar cikin muryar tausayi, qur'anin ta ta rufe ta ajiye a gefe sannan ta yi masa nuni da hannu ya je gare ta,kamar qaramin yaro haka ya isa gare ta ya kwantar da kan shi a cinyar ta, ita kuwa nan take ta sanya lallausan hannun ta tana shafawa a hankali

"Eamaan ina jin tsoro, ina matuqar jin tsoro, bana son abinda zuciya ta ke zargi game da matana ya zama gaskiya, in hakan ta kasance tabbas zuciya ta bugawa za ta yi na mutu, "

Hawaye ne ke gangara daga idanun shi zuwa fuskar shi daga nan sai su yi masauki a cinyar ta,itan ma hawayen take share wa dan kar ya gani, amma inaa ya riga da ya gan su,

" Eamaan kema kina zargin su akan cin amanar aure na ko? Please Eamaan tell me what you think maybe  going on in this house, coz i am going insane na rasa me yake faruwa na san cewa tabbas something is fishy in this house amma na kasa gano menene,"

Kama kan shi ta yi sosai ta manna da qirjin ta tana ci gaba da shafa bayan shi bata ce komai ba domin kuwa bata da abin fad'e ɗin,sai da ya yi kukan shi ya qoshi sannan ya gyara kwanciyar shi har a wannan lokacin bashi da walwala, babyn su ne yai first kick din shi aiko dukkan su suka zabura,cike da murna suke shafa cikin,

"Alhamdu lilLAAH kaga baby tana baka hakuri ko, tace Daddy ya yi hakuri akan koma me ke faruwa dashi ya barwa Allah lamuran shi,abinda ake so kowanne bawan Allah yayi shine ya kiyaye dokokin Allah, to sai Allah ya kiyaye shi, sannan tace na sanar da kai ka zama mutum mai kare kanshi daga zina Allah zai kare masa iyalan shi da zuri'ar shi baki d'aya daga zinar, dan haka ina ganin saqon d'iyar ka ya isa ya sanya ka daidaita lamuran ka, ka rabu da zunubai ka yawaita istigifari, Allah mai yawan gafara ne ga bayin shi da suka nemi yafiyar shi, Allah Al-haleem ne, mai yawan kauda kai akan zunuban mu, bana son kana tada hankalin ka akan abunda bai zama gaskiya ba ka ji Babyna?"

Maganganun ta sun samu kyakkyawan mazauni a ran shi, a cikin zuciyar shi ya qudirta yau kam ya yi alqawari tsakanin shi da Allah ya daina neman mata har abada, kalmar ta ta qarshe ce ta sa shi murmusawa wai baby,rungume ta ya yi yana ta yi mata godiya, ita kuma ta ci gaba da shafa kan shi, a haka ya yi bacci yana jin kamar an dauke masa wani qaton dutse akan shi,miqa hannu ta yi ta dau qur'anin ta ta ci gaba da karantawa, shi kuma yana ta baccin shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login