Showing 39001 words to 42000 words out of 78127 words
Chapter 14 - BIYAYYA Book Complete Hausa Novels by HAERMERBRAERH.txt
wani a cikin su,Alhaji kuwa yana zaune shiru banda karkarwa babu abinda jikin shi ke yi, ma'aikatan hukumar da kansu suka dinga shiga lungu da saqon gidan suna ɗaukan takardu da dik abinda yayi musu, Hajiya Babba kuwa takaicin kwashe mata sarqoqin zinaren ta dik shi yafi damun ta har ya sanya ta kasa yin kukan ma, shi kuwa Sahabee baqin cikin yanda aka k'wace komai ba tare da ya samu wani abu daga wajen yayan nashi ba shi ya sanya shi zabga tagumi yana bin kowa da kallo,daga gidan da suke ciki sai motoci biyu kawai aka bar musu.
Suna cikin wannan halin na jimami aka sake k'wank'wasa qofar parlourn Iya,nan take Alhaji yaji k'wank'wasawar har cikin tsokar zuciyar shi,gani yake yi kamar wata musibar ce ta sake tinkaro shi da iyalan shi,babu wanda yayi jarumtar amsawa mai k'wank'wasawar daga qarshe dai da kan shi ya buɗe ya shiga parlourn cike da isa da taqama, Alhaji Saminu ne yake ta zabga murmushin da yafi dacewa a kira shi da sassanyar dariyar samun nasara kafin yace,
" Alhaji Abdullahi kenan a zaton ka zaka samu kuɗin gwamnati ka sace ka killace dan ka mora kai da iyalan ka ba tare da gwamnati ta k'wace abinta ba? to bari kaji wani sabon albishir da zan yi maka dan na kula baka kalli news ba jiya kana nan kana shanawa da wannan kyakkyawar matar taka ko? Albishir ɗin shine majalisa ta sauke ka daga muqaminka yanzu haka ana can ana jefa quri'ar samun madadin ka,kai kuma kana nan a nade wajen mata,"
Ya na gama faɗin maganganun nashi dake kama da shaqiyanci ya kwashe da dariyar mugunta harda tafa hannayen shi,a harzuqe Alhaji yayi kan shi da niyyar yi masa dukan tsiya,kafin ya qarasa gaban Alhaji Saminu ya yanke jiki ya fad'i a qasa yana ta wani abu kamar mai bugun iska.
Ihu Eamaan ta sanya ta ajiye Fatee ta nufe shi tana jijjigawa, Iya kuwa jinin ta ya jima da hayewa ganin ta gaba ɗaya yayi rauni jinta take yi kamar ba zata kai gobe ba saboda tsananin ciwon kai da bugawa da zuciyar ta keyi dan haka ko yunqurin zuwa wajen Alhaji bata yi ba,dan kuwa ta riga ta san da ta miqe se dai a yi biyu,sunan Allah kawai take ambata dan shine mafitar ta a wannan halin da suke ciki.
Eamaan kuka take tayi sosai ta na yima Sahabee magana akan ya rabu da Alhaji Saminu daya dunqunqunewa wuya ya zo akai Alhaji asibiti,amma ya qi sai naushin Alhaji Saminu yake yi yana zagin shi, shi kuma yana dariya kamar ba jikin shi ake duka ba.
Jikin Alhaji Abdullah ne ya saki ya daina motsi Eamaan kuwa sai ta fasa ihu da qarfi wanda ya ja hankulan Hajiya Babba da Sahabee,Waje Sahabee yaje ya hau kiran masu gadi da driver akan su zo su taimaka masa, suna zuwa kuwa suka hau ciccibar Alhajin suka fita dashi suka sanya shi a mota .
Asibiti suka kai Alhaji nan da nan likitoci suka duqufa akan shi dan duba lafiyar shi, ba shi ya farfado ba kuwa sai da asubar washegarin ranar da suka kaishi asibitin, Eamaan ta ci kuka ta gode Allah har ta hakura ta barwa Allah komai, Fatee kuwa sai kallo take bin kowa da shi,lokacin da likitoci suka sanar da iyalan Alhaji samun cutar barin jikin da ya yi ba qaramin shiga cikin damuwa suka yi ba, likitocin kansu sai da suka tausaya ma su saboda sun san shi farin sani ma kuwa yana daga cikin masu kuɗin dake taimakawa asibitin nasu, ga Alhaji nan kwance samb'al babu imm ba umm umm sai ido,yawu ma baya iya hadiye shi gaba ɗaya sai wani ya zubo,Eaamaan kamar zata haukace haka take jin kan ta, saboda shiga damuwa da tashin hankali,tashiga wani irin yanayi na tsantsan tausaya ma mijin nata,nan take ta hau yi masa addu'ar Allah yasa ta hanyar jinyar nan da ta same shi ya samu gafarar Allah,Allah ya yafe masa dukkan abinda ya aikata.
Bayan kwana biyu likitoci suka basu shawarar kawai a maida shi gida a ci gaba da jinyar shi,idan yaso sai su dinga kawo shi gashi akai-akai, dan kuwa ciwon ba mai warkewar bane yanzu, kuma gashi kuɗin zaman asibitin ma yana neman ya gagare su, haka aka basu kujerar tura marasa lafiya da magunguna aka d'oro Alhaji suka dawo gida.
Duk ran girkin kowaccen su sai a tura shi akai shi bangaren ta,masu aiki kuwa Iya ta sa aka tara mata su dika ta basu hakuri ta sallame su, cikin kuka da fatan samun lafiyar Alhaji Abdullah suka bar gidan, tinda suke a gidan basu taba zama da yunwa ba haka ma yaran su dake gida kullum a qoshe suke,masu kirkin cikin su ma har maqotan su suke yi wa alkhairi,sutura kuwa sai dai su baiwa wasu saboda basu da talaucin ta ga albashin su mai tsoka suna Karb'a akan lokaci babu fashi ko yankewa, masifar Iya da Sahabee ce kawai dama ke sanya su jin sun gaji da zaman gidan watarana.
Bayan tafiyar masu aiki sai gidan ya zama shiru kamar babu mutane a cikin shi, a hankali Sahabee da Hajiya Babba suka dai na tausayawa Alhaji halin da ya shiga, har ta kai idan ya dawo ɓangaren Hajiya Babba ta dinga masifa kenan idan yayi fitsari a jikin shi ko ba haya, yawun shi kuwa ganin shi take yi kamar wata najasa idan ya zuba a qasan carpet ɗin ta ta dinga zuwa ruwa tana wankewa tana masifa kenan,qarshe dai idan baya nan tafi samun kwanciyar hankali ta yanda ita da Sahabee sai su kwana aikata masha'ar su a natse,a hankali suka buɗe sabuwar rayuwa ta jin daɗi babu kama hannun yaro, daga baya ma duk da sun kula Alhajin ya sani ba ya iya komai baya iya magana sai idon shi da zai ta zubar da hawaye ba su damu ba, harkar su kawai suke yi ko yana sashen Hajiya Babbar.
Iya kam kullum ta na kan abun sallah tana kai kukan ta ga Allah ya kawo musu sassauci ya baiwa Abdullahn ta lafiya,a kwana a tashi kula da Alhaji da komai nashi ya koma wajen Eamaan,ita ke kula da kashi da fitsarin shi, itace ke qoqarin d'aga shi duk nauyin shi ta wanke shi ta gyara shi, Ammaahn ta kullum kukan tausayin d'iyarta ta take yi game da halin da take ciki, haka ma Daddy da Mama suna tsananin tausaya mata, duk wanda yaji rayuwar da gidan Alhaji Abdullahi ta koma sai ya tausaya masu.
Yau Eamaan ta fita a girki Hajiya Babba zata ɗauka dan haka tin kafin lokacin komawar shi sashen Hajiya Babban yayi Eamaan ta bashi abinci yaci ya qoshi ta yi masa wanka ta gyara masa jikin shi sannan ta gangara shi zuwa sashen Hajiya Babba, koda taje sai ta k'wank'wasa qofar sashen Hajiya Babbar, ita kuwa tana zaune ta sha kwalliya sai zabga qamshi take yi tana taunar chewing gum kamar wata qaramar yarinya,cike da rashin mutunci ta buɗe qofar ta tsaya ta kalli Alhajin ta maida kallon ta kan Eamaan da ta rame tayi duhu saboda wahala sannan tace,
"Wai ni meye ne na wannan gangare-gangaren ne ? Ni ki je na yafe maki girkin nawa ki haɗa dika ki riqe,dan banga dalilin da zai sa ana kawo min aikin kashi da fitsari ba kullum, naji da nawa ma mana haba ! ke da kika ga zaki iya kije kiyi ta fama amma ni kam ba zan iya wankin kashin qato ko na ce tsoho kamar wannan ba, in kuma zancen auren ne sai ya sallamen na qara gaba dan bashi da wata mamora yanzu a waje na,"
Hannun Alhaji na dama dake motsawa kaɗan kaɗan ya d'aga yayi nuni da yatsun shi guda uku,nan take Eamaan ta durqusa a gaban shi tana ta cankar abubuwa amma yana kad'a mata yatsa alamar basu yake nufi ba, qarshe dai Hajiya Babba ce ta ce masa,
"Wai tsaya ko dai masakin mijin naki yana nufin ya sake ni saki uku ne?"
Nan take Alhaji yayi saurin daga yatsan shi qarami alamar eh,salati Eamaan ta sanya tace,
"Ah ah ba haka yake nufi ba,ai kin ga bashi da lafiya ma be san me yake faɗa ba,"
A rikice Eamaan take yin maganar saboda bata so ta gasgata abinda Alhajin yayi,ita kuwa Hajiya Babba shewa ta sanya ta buga cinya tace,
"Tafi nono haske Abdullahi,me zan ci gaba da zama nayi a cikin wannan qaddararren aure dama ni? ko da can ba zaman ka kai kada'i nake yi ba a gidannan zaman qanin ka da dukiyar ka nake yi, shi yasa kaga na kafe har ina jin tsoron kar asirin mu ya tonu, na godewa Allah da bana haihuwa da tini ka samu abinda zaka sarqafe ni na zauna da kai dan dole a wannan halin babun da ya same ka,shi kanshi wanda nake zaune domin shi yanzu ya zama lagwani, ba sosai yake iya min aikin danake so ba,dan haka sai dai nace Allah qara sauqi,"
Ta kad'a jikin ta ta shige bangaren nata, akwatunan ta ta d'akko ta loda kayayyakin ta sannan ta ɗauki dik wani abu da ta san yana da daraja a sashen nata,sai da ta gama tana qoqarin fitowa sanye da mayafi ta tarar da Eamaan a bakin qofar ta tsaye cikin ɓacin rai tace mata,
" kin san Allah kika kuskura kika ce zaki deb'i wani abu ki bar gidannan da shi sai kin fita a nakashe kema, in kuma kin musa abinda zan iya aikatawa bismillah saboda in zan iya tinawa randa Hajiya Qarama zata bar gidannan bata ɗauki komai ba Itama har murna kika dinga yi a ranar,ina da labarin ke ɗin auren cushe aka yi masa dake kuma ya hakura ya zauna dake babu ko tsinken iyayen ki a siyan kayan d'aki, dan haka kama hanya ki fita kafin na nuna maki d'anyen aikin da zan iya aikatawa,"
Hajiya Babba tayi matuqar tsorata da yanda Eamaan ta canja cikin qanqanin lokaci ta koma kamar wata mahaukaciya sabon kamu.
" To ai dai a barni na ɗauki jakar hannu ko,"
Hajiya Babba ta faɗi hakan cike da tsoro da fargabar abinda Eamaan zata yi mata, Eamaan hanya kawai ta nuna mata ta na bin ta da gigitaccen kallon nan nata mai rikitarwa, sumi-sumi Hajiya Babba ta rab'e ta ta fice tana maganganu qasa-qasa kamar wata qaramar yarinya,sai da taje bakin gate din fita kuma ido ya raina fata, gaba ɗaya tinanin rayuwar su ta baya ya dawo cikin kanta kamar a film ta hau tina farkon haduwar ta da Alhaji har ta sanar da mahaifiyar ta tana son shi aka sanya Iya a tsakanin magana ta bashi umarni ya aure ta, ita ce matar shi tin ta saurayi da budurwa,nan take ta hau tina irin jin dad'i da gatanta ta da yayi.
kuka ne ya zo mata mai d'aci a wuyan ta da bakin ta, kuka ne irin na nadama da tunanin yanzu gashi ta tsufa ta girma amma zata koma zaman gaban iyayen ta,gashi ba wani arziqi gare su ba,Alhajin ne dama ke taimaka masu duk wata.
"Yanzu ina ji ina gani zan bar wannan gidan na koma na qasa na barwa wannan yarinyar ita kaɗai,"
Hawaye ne ya dinga zubowa a idanun ta babu qaqqautawa, ba dan ta so ba dole ta fara takawa ta bar gidan tana waiwayen shi,ta sha tafiyar qafa kafin ta fita daga unguwar ta samu abun hawa ta yi gidan su, ba qaramar zufa ta had'a ba saboda rashin sabo da tafiyar qasa da tayi, a baya kuwa dik inda zata je komai rashin nisan shi sai dai driver ya kai ta,yanzu gata itace zaune a adaidaita sahu.
Ta na isa gidan nasu ta sauka ta ce wa me adaidaitan ya Jira ta karɓo Masa kud'in shi, da kyar ta samu a wajen qanin ta takai masa, labarin abinda ya faru na rasa dukiyar Alhaji ya riski kunnen mutanen gidan nasu baki ɗaya,dan haka qannen ta da a baya ita ke taimaka masu suka fara fatan kar shegen son abin duniyar ta da kowa ya santa da shi ya rabo ta daga gidan mijin ta da suka yi shekaru sama da ashirin a tare, idan ko ta kuskura tayi hakan ba qaramin takura musu za ta yi ba, zawarawan ai se su yi yawa a gidan nasu, sai dai cikin rashin nasarar amsa roqon su Hajiya Babba ta kaso auren ta gotai-gotai da ita ta dawo gida .
Lokacin da Sahabee ya dawo aka sanar da shi abinda ya faru ba qaramin baqin ciki ya yi da faruwar hakan ba, haushin yayan nashi ne ya kama shi sosai saboda sakin Hajiya Babba da yayi, ba qaramin dad'in mu'amala da Hajiya Babban yake ji ba a gidan, d'aki ya shige ya na masifa kamar wanda ya biya sadakin auren ta,
"Mutum ba lafiyar ma ba zai hutawa ran shi da shegen sake-saken mata ba, da tana nan yanzu da baka huta da wasu abubuwan ba Kai bawa? Ka kama ka saki mace saki uku da tsufan ta da komai ai sai ka zauna da wannan afiruwar ku qarata can,"
Iya binshi kawai take yi da kallo dan ganin yanda yake ta faɗa kamar shine babba ba Alhaji Abdullah ba, nan take ta hau zargin shin ko dai Sahabee ne wanda Hajiya Babba ke magana akai? gaban ta ne yayi wata iriyar faɗuwa data tina wasu abubuwan dake faruwa a tsakanin su wanda a baya bata kawo komai ba ta zaci tsananin shaquwa ce kawai ta matar wa da qanin miji, lallai kuwa biri yayi kama da mutum ashe dai an jima ana cin amanar d'an nata a cikin gidan shi? Kuka ne mai qarfi ya k'wace mata, nan take nadamar irin mummunar tarbiyyar da ta baiwa yaran nata ta baibaye ta.
Daga qarshe da ta ga kukan ba zai kaita ko ina ba sai dai ma ya tada mata da ciwon da bata da maganin shi a yanzu sai kawai ta fara addu'a tana nemawa d'an nata gafarar Allah akan zunuban da ya kwasa na zina, ga illar da zina ta janyo masu a rayuwa, dan kuwa dik halin da suke ciki ta tabbata sakamakon zinace-zinacen da yaran nata suka aikata ne.
( yan uwa mu sani zina babbar musiba ce ta kowacce fanni a rayuwar me aikata ta,zina na wakana a wannan lokaci da zamani namu ta hanyoyi kala kala, a kullum sabon salo ake fitowa da shi Wanda yake qara qawata wa masu yin ta ita, yake Kuma sauqaqa wa masu yin ta ita, a komai da muke na yau da gobe an qawata ta kuma an kutsa ta cikin shi ta yanda ko ka sani ko baka da masaniya kana aikata Wani sashe na zinar, misali kallon tsiraicin mata da maza a waya ko films da muke ganin ai kallo muke yi ba wani abu ake yi ba mara kyau, to shi kallon tsiraicin fa me za a kirawo shi? Ka zauna kana kallon gashin Kan macen da ba muharramar ka ba har ka yi sha'awa, ke kuma kin qurawa qirjin namijin da ba muharramin ki ba ko cinyoyin shi har ki yi sha'awa, ko sauraron muryar Wanda ba muharramin ki/ka ba har sha'awar muryar ta gifta ma mutum a zuciya,sai wanda yai tsantsar nazari ya fuskance ta kuma Allah ya kare shi shine zai fahimci ta Ina ta kutsa masa/ta a daqile ta,dan haka mu zama masu kula,da yawaita istighfar dan musibun zina ba su da iyaka,ba kuma su da adadi, Allah ya kare mu daga sharrin zina da dikkan dangogin ta).
Gidan Alhaji Abdullah ya koma abun tausayi saboda yanda iyalan shi ke cikin halin ni 'yasu,lokuta da dama haka za su tashi basu da ƙwayar hatsi a gidan,gashi babu wasu kuɗi da suka rage da Eamaan zata yi amfani da shi koda kuwa ta fannin samun wata guntuwar sana'ar ne da zata riqe su,qarshe dai aikin da Alhaji ya samarwa Sahabee ada ya raina shi ya koma yi dole wanda da kyar suka karɓe shi, albashin nashi kuma qarshe dai rabi mata ke cinyewa rabi ya sammasu ba wani isa yake yi ba, ba laifi yanzu Alhaji tinda yana ganin likitoci ana ba shi kulawar data dace ya fara magana saidai ba ta fita sosai,sannan yana samu ya d'aga hannun shi na dama sosai, bangaren hagun shi kuwa yana ta lallab'awa da qoqarin motsa shi.
Motocin da suka rage musu guda biyu a gidan ne Iya ta bada shawarar a bada ɗaya haya sai ana kawo masu kuɗin a kullum suna samun na cefane ɗaya kuma su barta dan ci gaba da amfani da ita a gidan,haka ko aka yi sai suka kirawo asalin drivern su na da suka yi masa bayanin komai ya amince zai yi aikin dama tinda ya bar gidan bai samu wani aikin ba.
Tinda ya fara kuwa kullum yana kawo masu balance din dubu biyu wanda ba ta kai su ko ina,hakan ta faru ne sakamakon sabo da kashe kuɗi da suka yi a baya, Eamaan kuwa ta yi alqawarin ba zata ɗauki matsalar gidan ta ta kai wa iyayen ta ba zata yi dik iya qoqarin da zata yi dan taga ta wadata su da abincin da za su ci da sauran buqatun su.
****************************
Zaune suke a saman dinning table zasu karya Ammaah ta hau yiwa Daddy kukan ya taimaka wa Eamaan da iyalan ta dan kuwa ta tabbata suna cikin matsin rayuwa duba da abubuwan da suka faru da su,tana so ita dai ya barta ta je ta ga d'iyarta ta, Daddy kuwa yace sam ba zata je ba saboda idan taje ma d'agawa Eamaan hankali zata yi su yi ta koke-koke Mama ma ta sanya baki amma yaqi amincewa sam, suna cikin maganar ne Eamaan ta yi Sallama ta shiga parlourn nasu goye da Fatee.........
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 17 :
D'aga kai suka Yi gaba d'ayan su suka kai duban su kan Eamaan da ke shiga parlourn nasu, Ammaah ce ta yi saurin goge hawayen ta ta miqe ta nufi Eamaan da sauri ta rungumeta,Eamaan cikin fara'a ta sakko mata da Fatee dake ta kuka, baya Ammaah ta ja