Showing 69001 words to 72000 words out of 78127 words

Chapter 24 - BIYAYYA Book Complete Hausa Novels by HAERMERBRAERH.txt

17 Oct 2025

1440

masu tinanin su ta hanyar cewa,

"Kun San yanzu fa aure ne za a yi na soyayya, aure ne za a yi Wanda tin fil azal dangi shi suka zaci zai faru, duba da cewar kowa ya San soyayyar dake tsakanin Eamaan da Anwar d'in to kuma qaddara ta riga fata, dole kuwa yanzu ku ga dangi ko ta Ina"

Su Kan su su Ammaah da Maman sun yi mamakin cikar dangin nasu, saboda ba su yi gayyata ba, sun dai Sanar da daurin auren Eamaan da Anwar d'in, saboda dangi su sani, se Kuma suka basu mamaki da zuwa, 'yan uwan Mama sun ce dole ne a yi yinin biki, ba ruwan su da Wani auren bazawara ne, mijin ta ai saurayi ne.

Shagalin biki kuwa ya kankama, Eamaan ta yi mamakin ganin uban lefen da aka kawo Daga gidan su Anwar, se Daga baya ta yi murmushi ta tabbata Anwar be tab'a cire ran zai aure ta ba, maqota da abokan arziqi an tsattsaya ganin lefen da ya ba wa kowa mamaki, akwati seti d'aya da rabi kowanne kalar shi daban, Goggon Anwar ce ke musu bayani, seti d'aya ango ne ya yi abun shi tin da jimawa ya aje, Rabin setin kuwa uwar ango ce ta yi shi, kowa ka kalla fuskar shi d'auke take da annashuwa da annuri.

Bayan su Eamaan sun huce gajiyar su ne su Kai shiri da yamma dan zuwa gidan Iya,Eamaan Hafsat Yayah da  Fatee ne zaune a mota Yayah na tuqa su, sai da suka tsaya a Wani shago Eamaan ta yi musu tsaraba, duk Wani abu da Iya ke so se da ta siya mata dai-dai misali, sannan ta qara da d'an abubuwan ci da sha suka ci gaba da tafiya,da kwatance da tambaya aka kaisu  har gidan Iya, tana kwance jikin nata ya motsa, maganin ta na hawan jini ya qare, ga ba kud'in siya ko da da kud'in ma wa zai siyo mata sahabee baya nan? Duk tayi kashi da fitsari  a inda take kwancen a tsakar gidan, jikin ta ya yamushe ta rame kamar ba ita ba, cikin ta sai qara yake saboda yunwa Dake addabar ta,kwance kawai take bata san ina kan ta yake ba.

Ko da suka yi ta doka sallama suka ji shiru sun so su juya, a tinanin su ko wrong address ne aka basu,wata yarinya ce data nuna musu gidan ta basu tabbacin nan ne gidan, tsohuwar gidan na ciki yau kwata-kwata basu ga ta fito bara ba.

"Bara Kuma? Wanne irin bara, Iyan ce ke bara Kuma Ina Sahabeen?"

Inji Eamaan da kalmar barar ta gigita ta.

"Ai 'yan sanda sun kama shege, ya ishi kowa a unguwar nan da neman matan tsiya, matar shi kuwa bata da mutunci kwata-kwata bata raga wa kowa, to qarshe ma na ji ana cewa ta gudu ta bar shi, shi Kuma 'yan sanda sun tafi da shi shekaran jiya"

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un,"

Tini hawaye ya fara zarya da rige rige a kuncin Eamaan a hanzarce ta afka gidan, ganin Iya a yashe a qasa cikin Wani mawuyacin hali ne ya Sanya ta qarasawa a guje ta tallabi Kan Iyar ta Dora a cinyar ta ta na kuka ta na Kiran sunan ta, Iya da ke kwance magashiyan bata San wake Kan ta ba, sai qoqarin bude ido take amma ta kasa,  haka dai Yayah da Eamaan suka d'agata daga qasan, Eamaan tana kuka sosai ta ke gyara mata jikin ta, jallabiyar ta data dora akan atampar ta ta cire ta nade Iya a ciki, ta ce ma Hafsar ta taimaka ta siyo mata pure water ,domin kuwa Eamaan ta kula farkon abinda ya Kamata su fara yi wa Iyar maganin shi a wannan lokacin shi ne yunwa, dan yanda cikin ta ke kukan yunwa abun ya ba su matuqar tausayi,yau ko me Sahabee ya yi a ganin Eamaan ya Kamata 'yan sandan da suka kama shi  su tausaya musu, Hafsat na tsaye ta na jinjina irin tausayi na Eamaan.

Fita ta yi ta siyo ruwan roba ta kawo ma Eamaan d'in, shayi Eamaan ta had'a mata da ruwan pure watern da Kuma kayan tea din da ta yo mata tsarabar su, Eamaan ta hau d'ura wa Iyan a hankali, Wani ya shige Wani ya dawo, a haka ya qare,sun Kai kusan minti biyar zaune kafin Iya ta fara bude ido, tana juya shi a hankali, Eamaan na zaune a qasa Kan Iya na cinyar ta, cike da tausayawa take kallon Iyar se take ganin Bata kyauta wa Alhaji ba da ta bar mahaifiyar shi a wulaqance haka, to amma ba laifin ta bane, Bata San haka abun yake ba da ta taimaka musu.

  Iya na fahimtar a saman cinyar wa take sai ta fashe da Wani irin kukan da ya sa Eamaan ma fashewa da kukan tausayin Iyan, ba komai ke sake Sanya ta kuka ba face ganin wai yau ace mahaifiyar Alhaji Abdullahi ce anan, kuma take  a haka cikin mawuyacin halin jinya da talauci,yanda ya rayu ya na gatan ta mahaifiyar shi da kula da ita, gashi yanzu qanin shi da be San darajar ta ba Yana wulaqanta ta, Allah ya wa Alhaji rahama ko Dan yanda ya rayu ya na kula da mahaifiyar shi.

Tun Eamaan na yi wa Alhaji addu'a a zuci har ta fito Fili  yayunta na amsawa da "Ameen" kafin Yayah ta dafa kafad'ar Eamaan d'in ta ce mata

"Kukan ya Isa haka dear ,ya kamata mu zo mu tafi dare nayi, mu miqata asibiti,dan wannan da gani ba  yunwa bace kad'ai matsalar ta har da rashin lafiya,in yaso bayan an gama walima goben mun je asan ya za ai da ita,ni na maki alqawarin zan sauya mata gida zan aje mata wadda zata kula da ita,Ina ga ai hakan yayi ko?"

Gaba d'ayan su sunyi na'am da shawarar ta, nan suka dauke ta suka ja qyauren gidan, suka tafi da ita asibiti suka damqa a hannun kwararrun likitoci Dan mijin Yayah sanannen d'an siyasa ne da ake damawa da shi, transfer na kud'in da za a kula da Iya ta yi wa asibitin suka fara Shirin komawa gida, Eamaan kuwa  zuciyar ta ta karaya ji take kamar kar ta tafi, zuwa ta yi wajen Dr. ta masa magana akan ya taimaka a ba wannan tsohuwar kulawa ta musamman, tabbaci ya bata akan kar su damu, za a kula da ita kamar yanda ya Kamata, a gaban ta ya kira wata nurse mai kamala ya damqa komai hannun ta sannan suka bar office din Dr. d'in, akan da safe zasu dawo.

Jaka Eamaan ta bude ta zaro kudi ta bawa Nurse d'in tace ta sai wa Iya kayan shayi, da Duk abinda zata buqata tana so a bata kulawa sosai, kar a barta da yunwa, ta dinga bata abinci ta ci ta qoshi, sauran canjin ta riqe, godiya ta mata sannan suka tafi, Yayah ce ta ke Jan motar ita ko Eamaan na gefe idon ta a rufe, tana ta tinani kala-kala ,a haka suka isa gida jikin ta ba kwari.

Washe gari da sassafe ta je kitchen da kan ta, ta haɗawa Iya kunun gyaɗar da ta saba haɗa mata a da, abokan wasan ta na ta mata tsiya, murmushi kawai take ba ta iya mayar musu,ta na gama kunun  ta mata ferfesun kaza ya ji kayan qamshi ya nuna sosai ya yi luguf ,ta dora mata da bread mai laushi, ta saka a food  flask, se da ta ga ta kammala komai sannan ta shiga wanka ta hau Shirin fita, ta gama shirin tafiya kenan Ammaah ta shigo,

"Ni kuwa Baki fad'an ya kuka samu su Iya ba jiya, Kun dawo Ina tare da mutane ban samu na tambaye ku ba"

Kwalla ce ta taru a idon Eamaan ta samu waje ta  zauna a gefen gado, Ammaahn ma zama ta yi a gefen gadon tana bin Eamaan da kallon son Jin me ya faru a jiyan.

Cikin sharar kwalla ta fad'a mata abinda ya sami Iya, da inda suka  kaita a jiyan, shine yanzu take son ta je ta gan ta, Ammaah ta jinjina wa d'iyarta ta da zuciyar tausayi,rungume ta kawai ta yi da fari bata San ma me zata ce ba kawai se ta hau shafa bayan ta, sun dan jima a haka kafin ta samu bakin magana,

" Allah yayi miki albarka Eamaan,ni dai a wannan lamarin zan iya qaryata bahaushe da ke cewa albasa batai halin ruwa ba, dan kuwa ni dai tawa albasar tayi halin ruwa a nan har ma ta fi yanda ake zaton ta,ana fad'in kyawawan halaye na Ina ganin anya haka nake? To Eamaan ke har  kin fini kyawawan halaye ma, Allah ya qara maki imani, da tsoron shi, ina son ki Eamaan,Allah ya miki albarka da ke da zuri'ar ki da sauran yaran musulmi dika"

" Ameen Ammaahna nima ina son ki da yawa,"

Murmushi suka yi a tare sannan Ammaah ta share wa Eamaan hawayen ta,tare da miqa mata hijab din ta, Eamaan komawa kitchen ta yi ta dauki food flask da Kuma flask din ruwan zafi da ta zuba kunun ta zuba su a Wani basket na d'aukan abinci, sannan ta koma dakin su ta zauna tana jiran Hafsat ta dawo daga dakin Mama, dan da ta shiga nan toilet din nasu Dan wanka se  ita da Fatee suka tafi na Mama,kafin su zo ta kira Anwar ta labarta masa komai, sannan ta bashi hakuri jiya ta fita ba da izinin shi ba, gashi yau ma suna Shirin komawa asibitin, nuna mata ya yi Babu komai, in da abinda take buqata ma ta Sanar da shi, in Kuma ya zo ya Kai su ne ma Duk se ya fito, da sauri ta dakatar da shi Dan Bata son abinda za a ga rashin kunyar ta Kuma, ta na zaune bayan ta gama wayar ne su Hafsat suka  shiga suma sun kammala shirya wa se kawai suka fita mota suka wuce asibiti.

Suna isa suka tarar da Iya sai kuka take tana ba ma'aikaciyar da Eamaan ta sa ta kula da ita labarin Ƴan sanda sun tafi da Sahabee, jiya wasu suka je gidan ta suka mata wanka, bata san ko su waye ba, da sauri Eamaan taje ta kama hannun ta dika da take ta wurgawa a iska tana bayani,

" Iya nice Eamaan kin manta ne jiyan har ki ka kalle ni ki ke kuka, Iya ni ce Eamaaniin ki, ga Fateema ta zo ta gan ki Iya, jiya ita muka je kai miki amma se muka tarar da ke a cikin mawuyacin hali,se muka kawo ki nan,"

Qanqame hannun Eamaan Iya ta yi, ta fashe da kuka, ta kasa magana sai kuka,hakuri ta dinga bawa Eamaan, Eamaan ta nuna mata ba komai, komai ya wuce, labarin rayuwar da sukai da Sahabee da matar shi Iya ta ba wa Eamaan, da kuma yanda ta na zaune 'yan sanda su ka zo suka tafi da Sahabeen ta,ita kuma tana zuba mata abincin ta na sauraron ta tare da jimanta lamarin,sosai Eamaan ta tausaya wa Iya rayuwar da ta yi ,Sahabee kuwa can ta matse masa ai shi ya ja wa Kan shi rayuwar wahala to se ya ci wahalar shi shi kad'ai d'auke Iya za ta yi Daga wajen shi.

Ko sisin ta ba zata saka dan fidda shi ba, in ya dawo yana buqatar tsohuwar shi ga ta nan, amma ita da shi ko a hanya ba ragowa, shida ko mutuncin kanshi bai sani ba balle na wani? baiwa Iya kunu ta fara yi,Iya kuwa cikin sauri ta shanye cup ɗaya, tausayin ta ne ya qara kama Eamaan,  Hafsat kuwa dariya ce ta kama ta ta kauda kai tare da shanye dariyar, naman Eamaan ta dakko ta yi  ta zare mata qashi tana bata a Baki,sai da ta ga Iya ta qoshi ta Kai geji sannan ta kyale ta.

Iya da ta ji cikin ta ya d'auka ta kalli Hafsat da ke d'auke da Fatee ta ce,

" wannan itace jikallen tawa?  Taho wajen kakar ki Fadhimatu kin ji"

Maqale kafad'a Fatee ta yi, Eamaan ta dauke ta zata miqa ma Iya ita ta tsanyara kuka tana kiran Daddyn ta,mamakin ta ne ya kama Eamaan da Hafsat wannan shi ake Kira da sabon salo, sarai sun gane wa take nufi (Anwar)

Iya ce ta share kwalla tace,

" ku kyale ta banga laifin ta ba, laifin mu ne da tun da bamu neme ta ba, dan yanzu ta qini ba laifi bane,"

Eamaan ce ta ji tausayin Iya ya ratsa ta,

" Iya dan Allah ki dena tuna baya komai ya wuce, sannan ina so in Sanar da ke yanzu in sun sallame ki zamu tafi dake gidan mu, na sake yin aure cikin satin nan, yau ne walima in Allah ya kaimu anjima da yamma da dare Kuma zan tare, in an kwan biyu kuma zamu koma bauchi da zama ni da mijina, ko da ace har aka sallame ki baki qara gani na ba,Iyayena da Yayah Babba zasu kula da ke, dan kuwa ko ba komai ni da Alhaji mun zama d'aya,Kuma mutuwa ce ta raba mu ba Wani tashin hankali ba, sannan kuma ke kakar Fatee ce dole mu girmama ki mu kula da ke"

Iya kam kunya ta gama baibaye ta, ta yi kukan har ta gaji, Hafsat ce ta fada ma Eamaan cikin harshen turanci akan taje ta ga likita ta ji ko za a iya Basu sallama a yau d'in se su tafi da ita kawai,haka akai kuwa, aka rubutawa Iya sallama da magunguna na hawan jinin ta suka tafi.

*****************************

Sahabee kuwa na can wajen 'yan sanda sun bar shi a cell ba a miƙa shi kotu ba ƴan duniya suna casa shi kamar masara a turmi,ihu kawai yake yana faɗin,

"Waaaayyoooo officer dan Allah ku ma wannan qaton magana ya daina kirbata kamar ya samu kub'ewa, wayyo Allah, na wayyoo Allah na,"

"Ba zaka rufe min baki ba,nace  za kai shiru ko sai ka ci uwar ka, ai dama na gaya maka tin a alaba rago zamu had'e ne watarana, ga shi mun had'u, ka manta yanda kai kutun-kutun ka rabani da dadiro na sannan ka dawo ka aure min yarinyar da na yi niyyar aura, ka min asara Kai ma ai ga shi yanzu ta gudu ta barka kana cin kwakwa,"

Dariya suka d'auka gaba d'aya 'yan wajen, dan yanzu sun fahimci me yasa ogan nasu da suke Kira da Mugu ke ta jibgar shi tin da aka kawo shi dukan safe daban na dare daban, su kuwa ma'aikatan wajen dama suna tsoron mugu, dan costomer ne an Saba kawo shi, duk jikin Sahabee ba inda baya ciwo ya yi tsami sosai, ga targad'e da ya samu a hannu, ya daku iya dakuwa,Duk  ya Wani bushe ya  qara qobarewa, in an kawo wa mutanen wajen abinci cinyewa suke ba me sammasa,da fari har ya amsa laifin shi da bakin shi, da Jin an ce ya biya kud'in ya dawo ya ce ba shi bane, an kad'a an raya ya ce ba shi bane, a tunanin shi in yace bashi bane za su hakura su kyale shi, in kuwa suka ce ya biya da shekarun shi ze biya? Me ya ajiye ? Wannan ne dalilin da ya sa suka ki miqa shi kotu suka aje shi anan, in ya wahala ze amsa laifin shi,ma'aikatan wajen ba Wani abincin kirki suke bashi ba, in ma an bashi ya na fara ci Oga Mugu da yaran shi ke  amshewa  su cinye,ya yi kuka har ya gajia ya daina, in ya roqa su bashi ya ci, sai su saka masa a qasa su danna kan shi suce ya ci yana haushin kare a haka zai ci yana yi yana kuka, in ruwa ne a gwangwanin da suke kama ruwa suke juye masa ya kafa kai su dangwara kan a ciki haka zai sha ya na hawaye, rayuwa a yan kwanakin nan kawai ta mai qunci, Allah Allah yake a miqa shi kotu, wata qila azabar ta ragu,su kuwa sun gaji da tambayar shi ya amsa laifin shi sun zuba masa ido.

******************************

A gidan su Eamaan kuwa suna nan suna ta shan walima, abinci gashi nan ba a magana kamar an riga da an tsara taron,  Amarya ta sha gayu na daukar magana, ango na can da abokan shi, Kamal, Jamal  da wasu Daga cikin ma'aikatan asibitin Anwar d'in suna tasu walimar,sai kusan magrib aka tashi .

Dangi na kusa daga wajen walimar gidajen su suka wuce, 'Yan Kai amarya na nan an yi dandazo ana jiran motocin Kai amarya, ai kuwa ana fara jera motoci a qofar gidan mata sukai ta shigewa ana ta diban su  zuwa gidan amarya, Yayah ce akan komai ita da qawayen ta, kowa ya je ya ga gidan sai ya yaba matuqa Dan kuwa Anwar kusan ba abinda be zuba ba, dik da ba Wani zama za su na yi sosai ana d'in ba.

Da misalin goma na dare Yayah da qawayen ta suka dawo gida, ango yazo a motar shi daban, sai abokan shi da suka rako shi, daga nan su wuce shi kuma ya dau matar shi su tafi gidan su, wannan tsarin Hajiya Yaya da qanin ta Anwar ne, shine dalilin tsayawar ta a gama hayaniyar da ganin gidan ya d'au matar shi su je su huta.

A qofar gidan suka yi parking motocin su suka firfito, ciki suka dunguma,Daddy ya sa aka fito da Eamaan dake kuka, kamar wadda za aiwa auren dole, kukan nan na matuqar taba zuciyar Anwar, ji yake kamar yaje ya lallashe ta, amma haka ya duqar da kai yana sauraron ajiyar zuciyar da take saukewa, qarasowa ta yi gaban daddy, Daddy ya bud'e mata hannayen shi ta je ta fad'a tana buɗe sabon babin kuka, shima share hawayen shi ya yi,ya kira Anwar ya kama hannun shi ya damqa masa hannun Eamaan,kansu aduqe Daddy yayi masu addu'ar zaman lafiya, sannan ya gyara murya ya ce

" Anwar ga amanar princess d'ina nan na damqa maka, bar gani na tsoho, if u ever make her cry zaka gamu da ni, in dai ba kuka ne na farin ciki ba, ina fatan ka gane,Allah ya muku albarka ya baku zaman lafiya da zaman hakuri da juna,Ina so ku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login