Showing 57001 words to 60000 words out of 78127 words
Chapter 20 - BIYAYYA Book Complete Hausa Novels by HAERMERBRAERH.txt
ba sai na ci abinda ta dafa,"
Hafsat na faɗan haka ya kalli girkin gaban shi ya kalle ta, alama ta masa da Ido na eh Eamaan ce ta dafa,komawa ya yi ya tsiyayi juice din a cup, kurb'a ya yi tare da lumshe ido ya sosa kunne, sai da ya shanye ya yi godiya ya tafi,tana jin tafiyar shi ta bude qofar ta leqo tana sand'a , ji take kamar ta ce masa kar ya tafi, bayan shi ta bi da kallo, Anwar ba dai tsafta da Iya d'ora hula ba, murmushi ne ya kwace mata, ta na tsaye ta na yaba takun shi da yanda ya riqe hannun Fateema ya na mata hira ta Jiyo taku alamun ana fitowa daga kitchen, Hafsat ta gani ta nufo ta fuska ba walwala, ai kuwa ta juya a guje ta koma ɗakin ta ta danna qofar tana dariya,
"Da ki bari na kama ki mana, yar rainin hankali kawai, ai kina sane da cewar dan ke yazo amma kika bar ni da bayani da surutu ko, zan kama ki ne ai, munafuka ana so ana kaiwa kasuwa, kar ki kuskura ki ce Zaki tsaya Wani abu wai shi Jan aji in ganganci ya sa ki ka tsaya shirmen nan Zaki sha mamaki yarinya, wataqila ya samu wata ya aura, tinda zai tabbatar Baki son shi ne kawai,"
Wata iriyar fad'uwa gaban Eamaan ya yi, ta hau girgiza Kai, ta na Kiran sunan Allah, tare da fatan Allah ya sa kar ya juya mata baya.
Hafsat kuwa koma wa parlour ta yi suka je suka fara cin naman kazar ita da mijin ta tace,
"Mu cinye gobe ta gasa wani, Dan na tabbata yau ba zata Iya cin komai ba, ko Kuma in mun gama ka siyo mata pizza din ta ci in ta ji yunwa tinda dama pizza ta fi so, ka San Allah Habibi yau Eamaan ta ban haushi,"
"Mene na Jin haushin ta? Ni Kuma ta min dai-dai, so kike daga zuwan shi bai fito yayi jawabi ba sai ta miqa kai? Ai ba haka ake yi ba, ku mata masu aji ne fa, so kk ya ga tayi arha da yawa?"
Gyad'a kai ta yi cikin fahimta,sannan tace,
"Kuma fa haka ne Habibi,amma ni a gani na ita da Anwar ai ba wannan a tsakanin su, ka kuwa San yanda suka so junan su a baya? Na tabbata ko da aka aura mata Alhaji bata tab'a dena son shi ba, kawai BIYAYYAH ta yi ta hakura, saboda ita ta daban ce,"
"Kar ki damu, da yardar Allah wannan karon Eamaan ta Anwar ce"
"Allah ya yarda"
Abincin su suka ci suka sha lemon farar shinkafar su, sannan Hafsat ta ci gaba da bashi labarin soyayyar Eamaan da Anwar ya na jinjina biyayya irin ta Eamaan,a haka bacci ya fara d'aukar Hafsat, dama Fatee ta jima da yin baccin ta, dan haka sai ya ɗauki Fatee ya tashi Hafsat suka wuce d'aki.
Sai da Eamaan ta tabbata sun tafi ta fita parlour ta zauna ta nad'e qafa kan kujera ta kunna kallo,Kamal ne ya fito riqe da Key d'in mota dan ya je siyo mata pizza, kallon shi ta yi ta sunkuyar da Kai qasa ta na murmushi, shi ma murmushin ya yi ya wuce ta be ce komai ba.
Se da ya siyo ya dawo ya miqa mata ne ya samu kujera me cin mutum d'aya ya zauna ya na fuskantar ta ya ce,
"Eamaan yau dai na ga Anwar d'in ki Kuma aboki na, danni dai a nan garin na San shi, ban ma San shine the same Anwar da ake ban labari ba,a iya d'an sanin da na yi masa na San Anwar mutumin kirki ne , Kuma gashi ya had'u ko ta ina, dan haka zan Baki shawara kar ki yi wasa da damar ki, ba safai ake samun irin soyayyar da Anwar yake miki ba a wajen maza, Anwar ya nuna shi masoyin ki ne na gaskiya, to ki daure ki zama masoyiyar shi ta gaskiya kema,Allah ya muku zab'in alkhairi, sai da safe"
"Ameen na gode"
Ta furta a hankali shi kuma ya shige d'aki ya barta ta na ci gaba da kallon ta, bayan tafiyar shi ne ta hau cin Pizza tare da korawa da lemon ta, can qasan ranta ta take hango murmushin Anwar da sautin muryar shi, zuciyar ta fari kwal kamar farar takadda.
Ta na gamawa ta kashe ta shige d'akin ta ta yi brush tayi alwalar da take yi kullum kafin ta kwanta bacci, addu'ar bacci tayi ta shafa a jikin ta sannan ta kwanta cike da tinanin shi a ranta.
Tin daga ranar nan Anwar ya samu wajen zuwa, ga tsaraba da yake yowa Fatee na ci da na wasa duk zai je gidan, a nan yakan ci abincin dare da ya bar gidan sai ya je ya saiwa me gadin shi da me sharar shi a wani wajen, tinda yake zuwa basu taba hira da ita ba, dan ba ta bari su zauna a inuwa ɗaya ,da ta jishi zata miqe ta gudu ko ta yi shiru taqi magana, abun na matuqar damun shi.
Dan haka yau dai ya yi alqawarin sai ya sakata tayi masa magana,ko tana so ko bata so, dan ya san tana son shi she is just playing hard to get.
Bayan ya parker motar shi a waje ne ya kalli Kan shi a gilashin motar ya tabbata ya had'u,murmushi ya wa Kan shi sannan ya bud'e gate din gidan ya shiga bakin shi d'auke da sallama, a bakin qofar shiga cikin parlour ya tsaya ya na kwankwasawa tare da sallama, Hafsat ce ta bud'e masa ya shiga, daga tsayen suka fara gaisawa, shi Kuma ya dauki Fateema ya na d'aga ta sama suna dariya, Fatee na ganin shi, ta fara murna ta na fad'in Daddy , Anwar d'in ne ya ce tana ce masa Daddy,dan kuwa yana son yarinyar sosai.
Sanda Eamaan ta ji ya na ce wa Fateema ta na Kiran shi Daddy ta ji dad'i amma Kuma ta ga rashin dacewar hakan, what if hasashen da suke be zama gaskiya ba,ai ai daga baya Yarinyar ta shiga damuwa.
Eamaan ce ta fito domin mayar da plate ɗin da ta sha fruits kitchen sai satar kallon su take yi, suna bata sha'awa in ta gan su a tare,kallon Fateema yayi ya ce,
" Babyna na zo yau zan maku sallama tin da Mummyn ki ba kula ni za ta yi ba ina ganin na hakura kawai, kar na takurawa zuciyar ta, duk abinda take so shi nake so, na hakura zani a daura auren nawa da waccan da aka zaba min shekara da shekaru Ina qi, a yan zu na San Eamaan ta dena so na, ni Kuma ba zan takura mata ba har abada"
Yanda yake maganar dole mutum ya zata da gaske yake yi, zaro ido Eamaan ta yi sai gata gaban shi kamar ta riqe shi take ji, cikin narkakkiyar murya kamar ta me son yin kuka ta ce,
"Please Anwar don't go, Kai ma ka San abinda ka ke fad'i ba haka bane, pls don't marry anyone while i am here beside you, Ina gudun kar na sake shiga halin da na shiga ne a baya akan soyayyar ka,bana so na saki jiki a raba mu."
Eamaan ta qarasa maganar ta cike da zubda hawaye, Anwar ji ya yi kamar Allah ya gama amsa masa addu'o'in shi gaba d'aya dan kuwa Yana da yaqinin Eamaan na son shi , amma sai ya saka fuskar tausayi ya ce,
"To Eamaan me yasa kika ƙi kula ni all this while, baki ma son ganina, na zama kamar dodo a gare ki,"
Kwalla ce ta taru a cikin idanun shi,Hafsat na ganin haka ta ja hannun mijin ta suka shige ciki,suna shiga ya k'wace hannun shi yace,
"Ke malama da kin bar mu mun ga soyayya, "
"Zo na baka soyayya bar su su yi tasu ta yaushe gamo"
Kama qugun ta ya yi suka haye gado suna dariya.
Eamaan da hawaye ya wanke wa fuska ce tace,
"Na qi kula ka ne sabida bana son karya zuciyoyin mu a karo na biyu, ka sani zai wahala Hajiya ta bari ka aure ni, tinda tin fil'azal ita ɗaya ce bata son tarayyar mu a baya, hakan ne ya bawa Daddy kwarin guiwar aura min Alhaji ko ka manta ne? Ina sane da yanda ta dinga murna ta nuna Maka illar soyayya da ni,na samu labarai kala-kala akan yanda ta so ka yi aure Kai Kuma ka qi, ka na ganin yanzu zata amince ka aure ni ne?"
Kad'a kai ya yi alamar bai manta ba,
" To ka gani, so ka ke sai munje mun shaqu fiye da da muzo rabuwa ta mana wahala? Wannan shi ne dalilin qin kula ka da bana yi, amma ni ba dan bana son ka bane,"
Ta Kai qarshen maganar ta cike da jin nauyin Kalaman ta, zaunawa suka yi a tare suna ta tattauna matsalar da suke hasashe da yanda zasu yi maganin ta, ba tare da sun kula da lokaci ya ja ba, Kamal ne ya fito ya na hamma ya ce,
"Akaramakallahu yau ko a rufe qofar da Kai ne?"
Kallon agogon bango suka yi a tare sha biyu saura tayi, da sauri Anwar ya miqe yayi musu sallama ya tafi gida da alqawarin zai dawo washegari su qarasa magana.
Raka shi Kamal ya yi daga nan ya rufe gidan ya dawo sai ya tarar ba kowa a parlour, yau Fateema da Eamaan zata kwana, dan dama ita tana ganin yarinyar na takura musu, su kuwa tsabar yanda suke son ta ne ya sa suke kwana da ita.
A daren ranar Eamaan da Anwar sun yi bacci Mai dad'i cike da mafarkai kala kala.
washe gari.............
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH. 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 23:
Da sassafe ya shirya dan zuwa kano, ya matsu ya ga manyan shi dan su shiga maganar auren su da Eamaan, a bari ya huce shi ke kawo rabon Wani in ji bahaushe, sanyin jiki da Jan jikin shi na daga abinda ya ja masa rasa Eamaan a baya,wannan karon kuwa ba zai yi qasa a guiwa ba wajen gabatar da Kan shi da wuri.
Bayan ya gama shirin tafiyar shine tsaf, ya dakko jakar shi da zai tafiya da ita ya saka a mota, ya na so ya fara biya wa ta asibiti ya duba marasa lafiyan da ya yi wa aiki shekaran jiya ka fin ya wuce,asibitin shi na da kwararrun likitocin da ko baya nan za su kula da komai magana ya yi ma Baba mai gadi da mai share share akan su kula da gida, ya musu sallama tare da damqa masu kud'i a hannun su ko da zasu buqaci Wani abun baya nan, Anwar mutum ne Mai tausayi da kyautayi, ba ruwan shi da Yana biyan su albashi kullum cikin kulawa da su yake baya gajiya.
Direct gidan su Hafsat yaje ya tsaya a waje ya yi ma Kamal waya,ya sanar da shi abinda yake shirin yi, Kamal kuwa sai ya bashi goyon baya d'ari bisa d'ari,tare da qarfafa masa guiwa, sannan yace ya shigo su gaisa da Eamaan mana kafin ya wuce, shiga cikin gidan yayi ya jira Kamal ya bud'e masa qofar parlour ya shiga da sallama.
Hafsat ce ta fito sanye da babban Hijab, dan cikin ta ya fara girma ba laifi, gaisawa suka yi ta wuce dakin Eamaan dan Kiran ta, karo suka yi a hanya ta miqe hannayen ta ta na miqa, dan ta gama sakankancewa Kamal ya fita tinda takwas ta gota, Anwar dake hango Eamaan da ke miqa wani yawu ya hadiya ya kyafta kyafta idanu, da saurin ya dauke idon shi saboda rashin ganin dacewar qura mata Ido da ya yi, a zuciyar shi ya hau istighfar, can shaid'an ya sake bijiro masa da kyawun surar ta, numfashi ya ja ya na tunanin wa zai ga wannan yace ta taba aure ballantana ma a ce har ta Kai ga haihu? Allah mai halitta kenan ,hannu ta d'aga ta daure gashin ta tana kallon Hafsat dake Jan hannun ta dan su koma ciki, ja ta yi ta tsaya sannan ta ce,
"ke malama, kamal bai tafi ba fa har yanzu, yau ya makara kin dai gane ai, kuma Anwar ma na palour ya na jiran ki, Allah ya taimake ki kamal na d'aki be gan ki ba, amma dai wataqila Anwar ya ga amaryar shi cikin night wear kafin aureeee"
Turo baki ta yi cike da shagwab'a tace,
"Me yasa ba ki faɗan duk waɗannan bayanan ba ki na hango ni se da na gama dik Wani shirme ya ganni, sannan shi mijin naki me ya hana shi tafiya Office da wuri yau, kuma shi Anwar d'in me ya kawo shi da wuri qarfe takwas gidan mutane?"
Dariya sosai Hafsat ta yi ta tura Eamaan toilet dan bata da lokacin amsa tambayoyin ta dika, ta dakko mata kayan da zata saka kan ta fito,Jiranta ta yi dan ta taya ta shiryawa da hanzari, nan tana fitowa kuwa ta saka kayan ta Hafsat ta gyara mata gashin ta tayi kyau sosai, sai tashin sassanyan qamshi take in ba ka matsa kusa sosai da ita oba ba zaka ji ba,( Saboda har yanzu shi din ba muharramin ta bane, dan haka ba zata sake ta saka tirare mai qamshi sosai da zai ja masu fitina ba, musamman yanda suke son juna tirare zai Iya kunna masu wutar fitina a tsakanin su, gare ku mata masu zuwa zance wajen masoya a ci turare Eamaan na magana) yana ganin ta a zuciyar shi yace,
' Yah Allah she is so beuatiful, ko wace shiga ta yi kyau take yi mata'
Sai da ta sake maimaita sallamar ta da qarfi tare da dan dukan table ɗin gaban shi sannan ya dawo daga kallon ta, ɗan murguda baki ta yi kaɗan ta ce,
" kallon fa?" Shi Kuma ya ce,
" kyawun fa?"
Dariya suka yi a tare, sannan ya zama serious ya ce,
"Da gaske nake kyawun ki ne ya sa na kasa sanin kin iso gare ni har na shagala da kallon ki,"
kunya ce ta kama ta, ta dan yi murmushi ta ce,
"To naji sarkin tsokana kana nan da halin ka ko? Me ke faruwa ne na gan ka da sassafe haka?"
Gyara zaman shi yayi sannan yace,
" Babu tsokana a tsakanin mu indai ta wajen fad'an gaskiya ne, Eamaan ke me kyau ce, kyan ki na d'aukan Ido Kuma ya na sanyaya zuciya, Allah ya qara kyautata halayen ki su ninka kyawun fuska da jikin ki."
Ta ji dad'in Kalaman shi sosai, murmushi kawai tayi bata ce komai ba ya ci gaba da magana,
"Ammm abu na gaba shine dama na zo na ne na shaida maki zani Kano dan sanar da magabatan mu batun sake qulla alaqar soyayya a tsakanin mu, Wanda muke fatan ya Kai mu ga aure, tinda kin ga yanzu mu ba yara bane,mun mallaki hankalin mu, kar mu yi shiriritar jinkiri Wani abu ya gifta a tsakani, kar mu zo ina baya-baya wani ya shigen a sake maimaita abinda ya faru ao baya, a toh dan wannan karon sai dai ai yaqin duniya na uku ba yarda zan yi ba ehe,"
Ya fada cike da abun dariya, sai kace qaramin yaro, dariya ta yi sosai tace,
"kai ko, Allah ya bada sa'a ya san ya mana albarka a tarayyar mu,"
cikin murna yace,
"kin amince kenan na je neman auren ki da yawun ki? "
" sosai ma,na amince"
Ta fada tana rufe fuska, miqewa yayi dai-dai Hafsat ta fito dauke da plate da kayan karyawa akai,
" A'aa ina kuma zaka je baka karya ba,"
"Inaaa ai ni yanzu na ma fasa biyawa asibitin waya zan kawai su duban mara lafiyar nan, ba zan zame ko Ina ba Daga nan sai Kano, an ban damar zuwa neman aure ai ban ga ta zama ba,"
Eamaan ce ta miqe ta je kusa da shi ta dan shagwab'e fuska ta ce,
"Yanzu tafiya za ka yi bamu ci abinci ba, da ni fa zamu karya ko baka son cin abinci da ni?"
Ta qarasa maganar ta tana kallon shi, ai bai san sanda ya zauna ba ya karb'i babban tray din hannun Hafsat ya na mata godiya ya dire a gaban Eamaan ya na bin ta da kallo fuskar shi cike da annuri, bude plate din gaban shi ya yi, soyayyan kwai ne da chips, sai miyar hanta, da taji kayan lambu, ga tea a flask mai kayan qamshi, zuba masa tea Eamaan ta yi tace ya fara ci bari ta had'o nata Tea din, dan bata shan wannan irin me Madara, in ta dawo bai fara ba ta fasa ci da shi, yana jin haka ya gane so take yaci kawai, amma dama ba tare zasu ci ba, nan take ya yi murmushi dan a koda yaushe yana alfahari da Eamaan din shi, sai da ya gama tass ta dawo,zata kwanukan yace mata,
" Ina Fatee na? Ko bacci take ne,"
"Ban sani ba gaskiya, dan ba dani take kwana ba,"
Kamal ne ya fito cikin shirin fita shima dauke da Fatee a hannun shi ko nauyin ta baya ji, Hafsat Kuma na ɗauke da jakar shi kamar kullum, tana ganin Anwar ta hau tsalle-tsalle a jikin Kamal tana faɗin,
" Daddy, Daddy oyoyoooo,"
Tana ta dariya shima cikin so da qaunar yarinyar ya isa ya karɓe ta, an mata wanka sai qamshi take yi, wannan aikin Kamal ne wato feshe ta da turare, da an mata wanka an shirya ta in zai saka tirare itama sai ya feshe ta da shi, har waje suka kai su, Kamal ya bawa Hafsat kiss kad'an a lips d'in ta, Anwar na gani ya radawa Eamaan a kunne,
"Kinga gani ko, kin ga yanda ake yi in miji zai fita ko? Haka za mu dinga yi bayan mun yi aure, ni fa su Hafsat na bala'in burge ni,ko dayake muma nan da wasu 'yan watanni zamu fara irin nasu, ko dake namu ma sai yafi nasu ko,"
Kallon shi ta yi tare da qanqance ido,fuskar ta kuma na dauke da murmushi, dauke kai ya yi alamar yaji tsoron wannan kallon ya miqa mata Fatee wadda ta fara kuka saboda bata son su rabu, lallashin ta