Showing 45001 words to 48000 words out of 78127 words
Chapter 16 - BIYAYYA Book Complete Hausa Novels by HAERMERBRAERH.txt
gidannan da abinda ke cikin shi zai zama mallakin wani ba, ruwan ku ne ku samu wani wajen fakewar kuma ruwan ku ne ku zauna har masu siyan gidan su zo su fidda ku,"
Tana kaiwa nan ta sa kai ta fice, gaba d'ayan su baki suka buɗe suna kallon ta har ta b'ace wa ganin su,nan take wani irin fargaba da tsoro suka shige su yanzu ina za su je? lallai lamarin Eamaan a bin tsoro da firgitarwa ne, to yanzu ya zasu yi?shin me ma ya sake samun d'an nata, sai a yanzu wannann tinanin ya zo mata,cikin hanzari kuwa ta yinqura ta tashi tana dingisa qafar ta da ta ke ciwo zata fita,Sahabee ne ya kalle ta yace,
" Iya ina zaki je kuma bayan ta gama fad'a mana saqon rashin mutuncin data ga dama ta tafi?"
"Kai da Allah ja can, daga dikkan alama Audu bai da lafiya sosai, shine dalilin da yasa za ta saida gidan a yi masa magani da kud'in ,ko kuma so take yi ta cinye kud'in gidan dan taga bai da lafiya bai san ina kan shi yake ba,"
Tana fita ta tarar da Eamaan da wasu mutane tsaye suna magana har da drivern Alhaji,shi kan shi drivern haushin su Iya ya ke ji, yana ganin Iyar ya d'auke kai gefe ya haɗe rai sosai, buɗe sauran bangaren su Hajiya Babba da Qarama su Eamaan ke yi, komai na nan kamar yanda suka bar shi, sai da suka bud'e ne ma suka ga akwai sarqoqi da wasu abubuwan masu amfani har da kuɗi a sashen Hajiya Qarama, d'iba Eamaan ta yi ta damqa a hannun drivern tace yaje ya siyar ya dawo, duk da ta San ta yi a kasada amma gwanda shi ya nuna damuwar shi akan mijin ta sama da mahaifiyar shi da ɗan uwan shi da ya wahaltawa a rayuwa.
Masu siyan gidan sun shiga ko ina sun gani, gida yayi musu fiye ma da yanda suke so kuma yayi musu za su siya, sun tsaida magana akan za su fara bayarda rabin kud'in zuwa wata uku masu zuwa su cike sauran,Eamaan kuwa ta yi na'am da hakan, dan haka Kiran lauyan Alhaji ta yi aka yi komai a gaban shi.
Driver kuwa direct wajen saida gwala-gwalai ya nufa ya siyar ya dawo mata da kud'ad'en ta cass ko sisi bai rage ba,ko da ta duba sai taga ta samu kimanin million biyu da rabi, nan take ta wari dubu d'ari ta baiwa driver, qin karb'a ya yi ya na hawaye yace mata a qara a maganin Alhaji baida komai da zai taimaka da shi dan haka ba zai karb'i ko sisi ba,cikin kukan tausayin su ta yi masa godiya amma ta bashi 20k ta matsa masa dole ya karba.
Shiryawa ta yi ta koma asibiti wajen mijin ta dan ta ga ya jikin nashi yake, a daren masu siyan gidan suka dawo dan nuna wa ma'aikatan da suka d'akko inda za a yi musu gyare-gyare,Iya ta rasa ya zata yi da ranta dangane da lamarin saida gida da son jin ya lafiyar ɗan ta take,Eamaan kuwa sam taqi kula ta balle tayi mata bayanin halin da ake ciki.
A cikin satin aka gama had'a masu komai na tafiya qasar India domin duba lafiyar shi wanda har likitan da zai duba ta ya san da zuwan su an gama arranging komai su kawai ake jira,tafiyar tasu ta zamto babu namiji a ciki daga ita sai Hafsat da Fatee.
Hafsat na ta bata kwarin guiwa akan zasu iya ba dole sai da namiji ba kar ta damu, tinda Sahabee ba namijin arziqi bane ba dole su za su yi komai, a asibitin NARAYANA HOSPITAL suka sauka, asibiti ne babba mai matuqar girma da d'aukaka a fadin qasar ta India dama wasu qasashen, domin asibiti ne daya had'ar da likitoci kala-kala masu aiki akan kowacce cuta,sai dai sunfi k'warewa wajen dashen zuciya da masu ciwo irin na Alhaji,ai ko cikin hikima ta ubangiji suna zuwa likitoci suka amshe su,babban doctor din su ne ya zo da kan shi ya duba shi, yana ganin yanda Alhaji yake ya san sai Wani hukunci na ubangiji zai tashi,amma dole zasu gwada su gani ko da abinda zasu iya yi akan shi, sun fi awa bakwai suna abu ɗaya akan Alhaji.
Eamaan idon ta ya yi baqi ta qasa alamar rashin hutu da bacci duk yanda Hafsat taso ta huta amma inaaa ta qi sam, hankalin ta a tashe yake wanne bacci za ta yi kuma, washe gari wajejen qarfe 12:36pm Dr. Maheer Shatty ya fito dauke da rigar shi a hannu, cike da rauni da tausayawa ya kalli su Hafsat ya wuce Office din shi ya jima a zaune kafin ya aika a yi masu iso wajen shi, suna shiga ya deb'o ruwa a cup ya tsiyaya ma Eamaan, da Hafsat a glass cup d'in shima ya sha, Eamaan ce ta tambaye shi cikin harshen turanci, take sanar da shi ya fada mata me ke faruwa dan ita ba ta ruwa take ba, kallon ta ya yi da tausayawa yace, mata sai dai su yi hakuri amma sun yi iya bakin qoqarin su amma sai da suka rasa Alhaji, qamewa ta yi a kujerar ta na fidda wani nunfashi mai zafi daga baki da hancin ta, yanda ta tsorata ya sa likitan tashi daga kujerar shi ya je gaban ta ya dafa kafad'ar ta ɗaya yace,
" Madam take it easy please,breath in and out everything will be ok"
" Everything will be ok? When my husband is dead? Everything will be ok when i don't have anyone to take care of my daughter? Don't tell me everything will be ok, u have no right to tell me everything will be ok,just take me to him, i want to see my husband, i wanto to talk to him, i know he is doing fine, u just don't want to tell me, pls take me to my husband,"
kuka take sosai wanda ya sa Dr. Da Hafsat kwalla ,Fatee ma kukan take kamar ta san me ke faruwa,a hankali ya miqe ya kai ta d'akin da gawar Alhaji ke kwance, kamar ba shine majinyacin da ya ke cikin jinya da wahala ba, kamar ba shine yake kashi awando magana ta gagare shi ba, fuskar shi cike take da annuri da murmuhi a saman ta, magana Eamaan ta fara yi masa kamar wanda yake jin ta,shi kuwa bai san tana yi ba saboda babu ruhi a jikin shi kwance kawai yake a miqe samb'al , Eamaan bata san ta shaqu da Alhaji ba sai a yau, ganin tane ya fara yi mata hazo a hankali ta yanke jiki ta faɗi a wajen.
Alhaji ya nuna mata so mara adadi, ya zama kamar raqumi da akala a wajen ta , ya daina munanan dabi'un shi ta dalilin son da yake yi mata da shawarwari da wa'azin da take yi masa, Alhaji ya zama wani bangare na jikin ta.
Bayan sun samu ta farfado ne Hafsat ta sauke ajiyar zuciya tana godewa Allah,ita kuwa kwance take a gado bata imm bata umm umm, sai dai hawaye da yake zuba ta gefen idon ta kawai, shirye-shiryen komawar su Hafsat ta hau yi, a wannann lokacin dole akaiwa Fatee yayen dole, dan ko ruwan nonon babu ma a tattare da ita ya ɗauke kan shi,saboda rabon ta da abinci tun a jirgi da za su zo, in an zaunar da ita sai dai ta qurawa waje ido,in ta dad'e a haka daga baya sai ta fashe da kuka,a haka suka dawo Nigeria d'auke da gawar Alhaji, drivern sune yaje ɗaukan du wanda direct gidan su Eamaan ya yi da su, don yanzu Iya da Sahabee sun canja unguwa wanda suka sayi gidan su sun tashe su,tinda suka je gidan Eamaan bata ce komai ba sai da taga kowa ya hallara sannan tace,
"Duk wanda ya sanar da su Iya mutuwar Alhaji kan akai shi bai kyauta min ba, ya ci amanar tarayyata da shi ko wanene,"
Tana gama faɗin haka ta shige dakin su na da ta kife a gado ta yi ta kuka tana nemawa Alhaji gafarar Allah tare da rahamar shi da kuma sauqin kwanciyar qabari, daga wannan addu'o'in da take masa ta samu nutsuwa ta rage kuka,a haka aka haɗa ruwan wankan da za a yi masa aka kira ta, dan kuwa ta ce ita za ta yi masa, d'akin da zata yi masa wankan Ammaah ta raka ta ta shiga sai ta ja mata qofar ta rufe,tsarki ta fara sannan ta yi masa alwala ta soma yi masa wankan tana yi tana hawaye tare da yi masa addu'a, qamshi ne kawai ke tashi a ɗakin saboda turarukan da tayi masa amfani dasu, har a wannan lokacin murmushin dake saman fuskar shi bai gushe ba, a haka ta gama ta yi masa addu'a sosai sannan ta buɗe ta fita daga ɗakin, qarasa hada shi aka yi , sannan aka dauke shi sai gidan shi na gaskiya gidan da kowa zai je, gidan da ke jiran wanda ba a haifa ba ma, gidan da ba ruwan shi da matsayin ka ko na iyayen ka, kawai kaje masa da aiki mai kyau kaji daɗin kwanciya a cikin shi,kaje da mummuna kuma zaman ka ya munana.
( Kun taɓa aikata zina a rayuwar ku? Tuba kawai zaku yi tuba na gaskiya sai Allah ya karb'i tuban ku ya kyautata qarshen ku,idan kuma mutum bai yi tuba na gaskiya ba, to fa tabbas yana cikin tashin hankali nan duniya da qiyama, Allah ka tsare mu da dikkan musulmi daga aikata zina da abinda ya dangance ta,)
Dik da cewar Eamaan bata zamo daga cikin mutane masu yawan surutu ba tin farkon rayuwar ta, sai mutuwar Alhaji ta sa ta sake zama shiru-shiru,a koda yaushe cikin yi wa Alhaji addu'a take yi da kuma neman itama Allah yayi mata kyakkyawan qarshe, dan kuwa mutuwar Alhaji babbar aya ce da Allah ya saukar, tana nan kwance tana hawaye Ammaahn ta ta shiga ɗakin ta samu gefen gado ta zauna,hannun Eamaan ta kama tace,
"Eamaan na san kin yi hakuri tin daga farkon haɗa auren ki da Alhaji har zamantakewar auren ku da shi, sannan na san irin hakurin da kike yi a yanzu da ya rasu, amma dik da haka ina mai qara baki hakuri tare da yi maki nasiha akan ki ci gaba da hakuri, Allah ya jiqan shi ya sada shi da rahamar shi, ki taso muje palour kin yi baqi, amma ina son ki tausasa zuciyar ki ki sanyawa kan ki hakurin nan da na san ki dashi"
D'aga mata kai kawai Eamaan ta yi, ta sa hannu ta share hawayen ta sannan ta zira hijab ɗin ta dogo har qasa suka fita,ba ta tab'a tsammanin ganin su yanzu ba dan haka ganin su zaune sai ya sanya ta jin kamar ta koma d'aki amma haka ta daure ta qarasa cikin parlourn....
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 19:
Sahabee ne da Iya zaune suke ta zabga kukan rashin Alhaji Abdullahi da aka yi, gaba d'aya parlourn kallon su kawai ake yi babu wanda ya tausaya masu sai ma haushin su da kowa ke ji a wajen, amma saboda karamci irin na su Ammaah ko a fuska ba su nuna masu ba, daga Daddy har mama kowa ya gaishe da Iya yayi mata ta'aziyyar rashin ɗan ta da tayi,Eamaan na ganin su wani tuquqin baqin ciki ya taso mata, kawai sai ta nemi waje ta zauna tana bin su da kallo, dan kuwa ita gani take yi ta sanadin abinda Sahabee yayi ne ta rasa mijin ta,Iya kawai ta gaida saboda kasancewar ta mahaifiya ga Alhajin ba dan haka ba ko kallo bata ishe ta ba,
" Ina wuni,"
Ta furta tare da komawa gefe ta zauna a kujera idon ta rufe dan ko ganin su ba ta son yi, amsawa Iya ta yi tana ta zuba tana fad'an a inda suka ji rasuwar,shiru wajen ya ɗauka babu wanda ya ce mata ci kan ki,kalma ɗaya kowa ke amsa masu da Ameeen idan suka furta Allah ya jiqan Alhaji.
Eamaan kam ma ko kula su bata yi ba balle ta amsa Ameen ɗin ,tana kyautata wa Allah zato ya gafarta wa Alhaji kuma zai yi masa rahama da yalwatacciyar rahamar shi,suna nan zaune banda maganganu da kukan Iya dake tashi baka jin komai a haka aka kawo Fatee tana ta kuka, Eamaan ce ta karɓe ta tana ta jijjiga ta a hankali ta samu ta yi shiru, Ammaah ce ta kawo mata abinci ta ɗauke ta tana bata, can a cikin surutan Sahabee su ka ji yana fad'in
" Allah ya jiqan Yayah, tin da abubuwa sun zo a haka kuma Fatee ita kad'ai ta rage mana a dangi da zamu kalla muji dad'i, sai a had'a mana kayan ta mu tafi da ita,"
Cikin sauri Ammaah ta ajiye Fateema a cinyar Mama ta yi kan Eamaan ta riqe ta tana yi mata magana cikin sanyin murya,Ammaah ta tsorata da yanayin da taga 'yarta ta ta shiga cikin qanqanin lokaci, yanayi ne da tinda ta haife ta bata taɓa gani a tattare da ita ba, jikin ta sai rawa yake yi, idonta kuwa ya yi jawur kamar jan yadi, tashi tayi tsaye Ammaah na riqe da ita ta fara takawa tana bin Sahabee da wannan deadly look din nata, cikin sauri Sahabee ya ja gefe kusa da Iyaa yana zaro idanu, bata ce wa kowa komai ba ta shiga ɗakin ta, Ammaah ce ta basu hakuri tana qoqarin bin bayan Eamaan ɗin sai gata ta fito ɗauke da leda a hannun ta ta wurga ta a fuskar Sahabee, abinda ke cikin ledar ne ya leqo,nan fa sahabee yayi arba da kuɗi sai ya hau zare ido yana washe baki,
" ku tashi ku fita da ragowar abinda ya yi saura na ɗan uwan ku a wajena, na yafe gadon shi bana so ku haɗe ku cinye dika dan shine dama ya fiye maku ɗan ku, d'iyata in ta girma kun bata nata a hannun ta in kuma kun cinye kun bata a lahira,ni ba zan karb'i gadon ta ba ba kuma za ku bar shi a hannun dangina ba, marasa hankali da imani kawai, kutashi ku fice nace !!!!"
Cike da wata gigitacciyar tsawar da ko iyayen ta basu taba jin ta yi irin ta ba ta qarasa maganar ta,ai kuwa tayi matuqar kid'ima kowa a wajen, ba shiri Sahabee ya tattare kud'ad'en ya mayar ledar ya kama Iya suka bar gidan hankalin su a tashe, daf zasu fita ne ya juyo yace,
"ko ba jima ko ba dad'e sai Fatee ta dawo hannun mu,"
"Naga dan iskan da zai ɗaukar min yarinya ya kaita gidan tsohuwar da bata san ya zata baiwa kanta tarbiyya ba balle yaran ta su tashi cikin son junan su ɗaya bai yi sanadin rasuwar ɗaya ba, har ta samu damar yi wa jikar ta tarbiyya ta zama yarinyar kirki bata sanya ta zama karuwa ba kamar yaran ta,"
A kunyace Iya ta sa kai tsakar gida ta ja hannun Sahabee dan su bar gidan,shiru gidan ya ɗauka dan kuwa babu mai bakin magana Eamaan ta baiwa iyayen ta da suka haife ta suka raine ta mamaki ma balle kuma wanda suka same ta da girman ta, shi yasa bahaushe ke cewa a kiyayi fushin mai hakuri.
Direct gidan hayan da suka kama a cikin gari suka nufa dikkannin su babu mai cewa kowa komai a hanya,bayan tafiyar su kuwa Eamaan ta zauna dab'as a qasa tana ta kuka,cikin kuka ta ke faɗin,
"Na rantse ba wanda ya isa ya ɗauki Yarinyar nan a cikin azzaluman can, Ammaah dan Allah ku yi min alqawarin ko me zai faru ba zaku bada Fatee ga wad'ancan marasa Imanin ba, gwanda akai ta gidan marayu wasu su ɗauka su raine ta dana basu ita, Ammaah baku san halin mutanen nan bane,Sahabee shine ya yi sanadin da ciwon Alhaji ya tashi har ya kai shi ga mutuwa, a gaban Alhaji ya so keta min haddi Allah ya bani iko na yi masa duka da muciya,Sahabeen nan da kuke gani shine ke neman matar alhaji tin da ran shi, Iya ta sani amma bata d'auki mataki ba,Iya ta san Alhaji bashi da lafiya amma ko ta nuna damuwar ta akai, kaiiii wadannan ba mutane bane, they are monsters, they don't deserve to be called humans, ba su da humanity kwata-kwata a tare dasu Ammaaaaah,"
kuka take yi tin qarfin ta tana wata iriyar jijjiga,Ammaahn ta na gefe tana share hawayen ta itama,Mama ce ta zo ta rungume ta ta d'aga ta a wajen ta kaita d'aki ta kwantar da ita tana shafa kan ta a hankali da sigar lallashi,tana nan zaune da Eamaan har Eamaan tai bacci, Fatee ma dake kuka ma ta yi nata baccin Ammaah ta shiga ta kwantar da ita a gefen mahaifiyar ta da ke sauke ajiyar zuciya,ta ja masu qofar suka fita.
Parlour suka koma dukkan su suka zauna jigum-jigum suna jimanta abinda ya faru a zuciyoyin su, Daddy dake zaune bai ce qala ba tinda su Iya suka zo ya sake dafe kan shi dake sara masa ya fashe da wani matsanancin kuka,kukane na dana sani da nadamar sanya 'yar shi cikin damuwa da rud'anin rayuwa, ashe haka d'iyar shi ta qunshi baqin ciki kala-kala a gidan da yayi zaton tana zaune cikin farin ciki? Yayi zaton labarin kulawar da Alhaji ke baiwa Eamaan da yaji a wajen Hafsat shine asalin labarin rayuwar da 'yar shi ke fuskanta a gidan auren ta, ashe akwai wani qullalen qulli da take fuskanta wanda tsananin Biyayyar ta ya sanya bata taɓa kokawa ba, tabbas bai wa d'iyar shi adalcin haɗa ta aure da Alhaji ba,farin cikin shi ɗaya yanda abokin nashi ya daina neman mata kafin rasuwar shi, yasan inshaa Allah ya samu rahamar Allah, amma ta wani ɓangaren yayi sanadin samun tabo a zuciyar 'yar shi mai wuyar warkewa, dole ne ya bata hakuri ya nemi gafarar ta kada haqqin ta ya kama shi.
Ammaah da Mama ne suka zauna a kusa da shi suka dafa