Showing 6001 words to 9000 words out of 78127 words

Chapter 3 - BIYAYYA Book Complete Hausa Novels by HAERMERBRAERH.txt

17 Oct 2025

1447

gaji da jin faɗan da ba gane inda aka dosa suke yi ba suka katse iya da faɗin,

"Mum kin ga kan mu,"

cike da murna suka haɗa baki suka fada,

" Wow kun yi kyau,waya kai ku saloon ba a faɗan ba na bada kud'in gyarn kai?"

"Mum ba saloon bane ba fa, Aunty Eamaan ce ta yi mana,"

Tin daga wannan lokacin Eamaan ta samu matsayi a zuciyar Hajiya Rabi, amma a wajen Iya kuwa cewa ta yi na neman gindin zama ne, sam ba a yi mata gwaninta ita, ko kwanta mata za ka yi tabi ta kai ta wuce sai ta kushe maka.

A haka Eamaan ta yi kwana shidda a gidan, a cikin waɗannan kwanaki Eamaan ta ga halayen mutanen gidan kala-kala, yau ne kwana na bakwai da kawo ta wanda daga shine Alhaji zai tattara ya tafi wajen Uwargida wato Hajiya Babbah.

Idar da sallahr ta  kenan ta cire doguwar riga da hijab ɗin ta na sallah tana ninkewa sai ta mayar inda take ajiye su, ta dauki qur'anin ta da littafin addu'o'in ta tana dubawa,daga qarshe sai ta d'akko wayarta ta kunna data suka hau chatting da Aunty Fa'iza dake qasar waje, sunje shaqatawa ne da Alhajin ta,shawarwarin yanda zata zauna da mijin ta da surukar ta har da kishiyoyin ta lafiya take ta bata, hakan kuwa yasanya mata mutuwar jiki sosai ashe aiki ne babba a gaban ta bata sani ba wanda take ganin anya zata iya kuwa? In ko haka za ta yi ba qaramar wuya zata sha ba kenan a gidan?

Suna cikin hira taji shigowar shi gidan ,a ranta ta qudiri niyyar yin dukkan abubuwan da Auntyn ta ta faɗa mata dan samun zaman lafiyar zuciyar ta da gangar jikin ta ko da ran ta baya son Alhajin, wannan dalilin ne yasa ta miqe duk da dukan da zuciyar ta ke yi ta je gare shi dan tarbon shi, amsar kayan hannun shi ta yi,wanda ta kula kitchen ya Kamata ta yi da su dika,godiya ta yi masa tare da sannu da zuwa,shi kuwa cikin kashe murya kamar ba dattijo ba yace,

" Godiyar me kike yi min daga dawowa ta kuma? Ki jira mana anjima idan na yi maki babbar kyauta kin yi min godiyar ko?"

Murmushi ta yi kawai ta wuce dan ba ta gane abinda yake nufi ba, tana tafe take faɗin,

" Ai dole mace ta zama mai yiwa mijin ta godiya a kullum ko dan saka ta a cikin sutura da killace ta da yayi ya bata wajen kwana, balle kuma ya bata abinda zata ci ta sha ina ga ya gama mata komai,"

Murmusawa ya yi har saida haqoran shi suka bayyana, lallai yarinyar nan ta tarbiyyantu wajen iyayen ta,

" Ba komai Eamaan dolena ne biya maki dukkan buqatun ki, indai ina da hali da iko,"

Godiyar ta sake yi mai da fatan Allah ya bashi ikon yin adalci a tsakanin ta da matan shi, kitchen taje ta cire komai ta mai mahallin da ya dace sannan ta fito,zaune ta gan shi a saman kijera sai ta duqa ta cire masa takalmi da safa, Alhaji kuwa sai ya bi qirjin ta da kallo, wani yawu ya hadiya, hula da agogon shi ta cire ta yi d'aki ta ajiye ta dawo.

Kitchen taje ta d'ebo masa drinks data haɗa da kanta na pineapple da ginger da lemon, sai flavor da sugar data saka dan d'and'ano, yana sha ya lumshe idanun sa saboda yanda  dad'in abun ke ratsa shi ,nan da nan kuwa ya shanye,ita kuwa sai ta qara masa wani, ya qara shanyewa, cikin dakewa da fad'uwar gaba ta fara qoqarin gwada abinda Auntyn ta ta koya mata,

" Sweet kar ka sha ka kasa cin komai,na yi girki me dad'i saboda kai gashi can ajiye a saman dining table kai kaɗai yake jira"

Sai da ya kusa k'warewa saboda yanda ya ji kalmar Sweet a bakin ta babu zato babu tsammani, tabbas a kunyace take itama amma tana son ta gwada abubuwan da aka koya mata,domin ba zata manta dalilin da ya sa aka aura mata shi ba dan haka zata yi iya bakin qoqarin ta dan ganin ta samu wannan ladan na tsamo shi daga halakar da ya jefa kan shi ciki ta neman matan banza, cike da jin daɗin maganar ta ya ajiye glass cup d'in ya fuskance ta yace,

" Eamaan me kika kirani da shi? Please kirani da sunan again,i want to hear it from your beautiful voice,"

Murmushi ta yi cike da jin kunya ta rufe fuskar ta, hakan da ta yi sai ya qara jefa shi cikin qaunar ta,murmushin ta kaɗai ya tashi kanshi ya jefa shi a wani hali, cike da jin kunya ta sake maimaitawa tace,

" Cewa na yi Sweet kar ka sha ka cika cikin ka..."

Wata dariya Alhaji ya b'arke da ita ta Jin dad'i, a kunyace ta miqe tana tafiya ta daukar magana ta wuce dining table,tabbas ta san ta tarowa kan ta babban aiki ,amma ba damuwa indai kwalliya zata biya kud'in sabulu akan BIYAYYAHr iyaye ba abinda ba za tai ba se dai idan abun ya sab'awa Allah ne dole zata guje shi, abincin taje ta d'akko ta jere a gaban shi, sannan ta d'akko qaramin carpet ta shimfid'a,dan ta kula a gidan sun fi son cin abinci a qasa, tana bud'ewa Alhaji ya yi karo da alkubus ɗin flour da ta haɗa da alkama tayi masa miyar gyad'a wadda ta sha naman qaramar dabba, yaji kayan qamshi ba kadan ba sai tashin qamshi miyar take yi, gefe kuma ga kunun aya mai had'in dabino, kayan qamshi, da sugar sai zuma kaɗan da ta saka dan ya qara gard'i a baki da amfani a jiki, gefe kuma farfesun kan rago ne, daya umarci ayi mishi kan ya fita,baje ciki ya yi ya kwashi girkin nan da kyau,dan kuwa tin da ya fara ci ya kasa yin magana, tinani yake yi wannan girkin ko a hotels ɗin da ya sha zuwa Abuja da sauran wuraren 'yan gayu bai taɓa cin irin shi ba, wa yayi girkin nan ne? Daɗi da santi ya sanya ya kasa tambaya, zurawa kawai yake yi, ganin ya ci har ya wuce geji ne yasa ta saka hannu ta riqe hannun shi tace,

" Ka yi hakuri ka bar abincin nan haka,in  ka ci da yawa ka qoshi bacci zai gagare ka mai dad'i yau ,ka San Annabi ya ce a raba ciki gida uku, Ɗaya na abincin, Ɗaya na ruwa, Ɗaya kuma na iska, da alama ka cika dika gurbin baka bar komai ba,"

Cike da jin daɗin kalaman ta masu yanga a ciki ya tashi tsaye bayan ya wanke hannu a robar data zubo ruwan wanke hannun,

"A gaskiya duk wadda tai girkin nan sai na bata kyauta mai tsoka,sai abinda ta zaba zan bata,"

Murmushi ta yi tace,

"Ni ce na dafa da kaina dan faranta maka,kuma albarkar ka kawai nake nema bana son komai bayan haka"

"In dai albarka ta ki ke nema kin samu, Allah ya albarkace ki, ya baki abinda kike so duniya da lahira,"

Jin hakan da ya fad'a sai da gaban ta ya faɗi dan kuwa Anwar ne zaɓin ran ta, shine abun son ta, yana yi mata wannan addu'ar shi ne ya gilma a idanun ta, dakewa ta yi ta miqe ta shige kitchen da kayyakin da ta kwashe bayan ya gama, zuciyar ta na saqa mata abubuwa da dama, tabbas bata jin son shi a ranta, a can cikin qasan ran ta a akwai Wanda take so, amma ba amfanin riqo da wannan soyayyar har ta b'ata rayuwar da Allah ne kad'ai ya San qarshen ta,dole ne ta yi hakuri, dole ne ta Yi BIYAYYAH, dole ne ta danne komai ta binne shi a qasan ran nata, dan ta samu farin ciki a gidan auren ta,takun da take yi ne dan zuwa d'aki ya sanya Alhaji Abdullah bin bayan ta ba tare da ya San ma ya na biye da itan ba........

Anya kuwa wannan BIYAYYAHr taki zata haifar maki da d'a mai ido kuwa Eamaan sai na ji ra'ayoyin ku makaranta?
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼  BIYAYYAH  💅🏼








  RUBUTAWA :HAERMEEBRAERH







Page 4:






Suna shiga ciki Eamaan taji alamar yana biye da ita a baya, nan take zuciyarta kama rawa tana tsalle dan tsoro kamar zata fito waje,duk da cewa tasan yau ta ta qare, hawaye taji na son zubo mata amma ta yi saurin maida shi ciki, yaqe ta yi ta juyo shi kuma ya yi mata murmushi,juyawa ta yi da nufin shiga bathroom,hannun ta ya kama ya na bin ta da kallon tuhumar Ina zata je? Cikin yaqe dan kuwa murmushin be kai har zuci ba tace masa,

"Ruwa zan ɗan watsa, yanzun nan zan fito"

A qa'ida yanzu kam ai ba wani wanka da ze yi shi kam kawai baccin shi zai yi, amma da alama Shima yau ze gwada yin wankan daren, kafin ya gama tinanin da ya ke yi ya ji rufe qofar ta, fad'awa ta yi ciki da sauri ta rufe gam ta fara wanka, tana gamawa ta yi brush tai alwala, samun brush din shi ta yi ta saka masa toothpast a jiki ta ajiye sannan ta fito, ta yi masa nuni da toilet din tana murmushi mai cike da jin nauyin sa, shima cire kaya ya yi a gaban ta ko kunya baya ji, Eamaan kuwa da sauri ta ɗauke idon ta ta kalli gefe, cikin ranta tace,

'shifa wannan tsohon sam naga kamar bai san kunya ba, ko dan yaga ina mai haka ne? Shi bai san daurewa nake yi bane? Haka kawai yau yanda ya wuni baya gida zan barshi ya hau min gado ba wanka,ai bazan iya bacci ba,gashi ya ci abinci kuma be yi brush ba zai kwanta,aiko yau dana shiga uku in yayi min irin abun d'azu da safe kafin ya fita,amai zan yi na tabbata'

Tana maganar zuci take gyara jikin ta,wata rigar bacci ta saka mai ɗan kauri kuma ba wata mai nuna jiki ba, amma duk da haka ta yi mata kyau,rigar fara ce sol, sai ta hannu da wuyan ne aka yi musu ratsin blue me haske, zani ta daura a saman kayan ta ɗora hijab, ta shimfid'a masu sallaya ta zauna zaman jiran shi, sai tashin qamshi take yi, yana fitowa ya gan ta a zaune a sallaya sai ya kauda kai, ya shirya cikin kayan bacci riga da wando kalar fari shima, kallon ta ya sake yi yaga abun salla biyu ta shimfid'a, sai yace mata,

"Me zaki yi ne na gan ki anan a zaune? daman baki yi salla bane?"

Kad'a ido ta yi ta kifkifta su sannan tace,

" A'a na zaci zaka ce muyi nafila ne irin na sabon aure da na ji ana yi tinda na ga ba mu yi  ba mu,bana son sai ka fito ne sannan kace na shinfida abun sallah, nafi son na dinga yin abu mai kyau kafin ka bada umarnin yin shi,"

shi dai bai ce komai ba ya nufi inda take zaune,amma shi bai san wata sallar sabon aure ba, abinda ya sani baya wuce kawai akai masa mata ya kwanta bacci ya biya buqata ya miqe shikenan,

"To miqe muyi sallar raka'a nawa zamu yi babyn Alhaji?"

Sanar da shi tayi komai tayi a lokaci ɗaya dan ta yi saving kanta da tambaye-tambayen da zai ta yi mata, sallar suka yi,bayan sun idar ne yayi mata addu'a yanda ta koyar da shi da Hausa,dan ta kula se su kwana be riqe larabcin ba,sannan suka miqe suka hau gado, kashe fitila za ta yi,yace sam bai san zance ba, tsoron duhu yake yi, dariya tayi ta masa yanda ya nuna da gaske tsoron duhun yake, dama tin da ta zo sai sun yi wannan dramar kashe fitilar da dare, komawa ta yi ta kwanta ya matsa ya dauke ta cak ya dora a jikin shi, daga haka Alhaji Audu ya sauya salon tsokanar da Eamaan ke yi masa......

Kafin ya gama abinda yake yi idon ta da zuciyar ta sun kumbura kamar su fashe ,ba dan komai ba sai dan kukan zahiri da badini da take yi, ga kunya da ke addabar zuciyar ta da wanne ido zata kalle shi da safe kuma? Mutumin nan fa sa'an Daddyn tane,amma ya zauna ya baje basirar shi a kan ta.

wayyooo ina zata sa kanta da wannan lamari yau? Alhaji Audu kuwa lallashin ta yake tayi sosai, tare da mata alqawurran jin daɗin rayuwa kala-kala, shi a zaton shi kayan more rayuwa sune a gaban kowacce mace, bata ce masa komai ba, ta miqe da kyar ta yi bayi,ruwa mai d'umi ta shiga ta zauna,sai da ta ji jikin ta ya yi mata dai-dai sannan ta bari, tai wankan tsarki ta fito d'aure da alwala,lokacin qarfe 2 na dare ne, nawafil tai tayi tana kumawa, a sujjadar qarshe ta samu tai addu'a akan neman zaman lafiyar su, da roqon Allah ya bata jimirin yi mai biyayya,sannan ya yaye mata soyayyar Anwar a ranta ko za ta ji dad'in zaman gidan mijin ta, tana haka taji ya saki wani wawan minshari, addu'a ta ci gaba da yi ta na kuka a cikin sujjadar ta, ta sauke babban nauyin da Auntyn ta take ta mata nuni akai d'azu, ta tabbata a yanzu Anwar yayi mata nisa,dan haka dole ne ta yi hakuri ta rungumi mijin ta da auren ta tin kafin lokaci ya qure mata, Wani shiga damuwa da tashin hankali ba nata bane,a hankali ta miqe ta haye gado ta kwanta ta rintse ido da fatan bacci ya ɗauke ta dena jin rad'ad'in da zuciyar ta ke yi mata.

Asubar fari ta tashi tai sallah amma Alhaji Abdullah yana nan kwance yana bacci, dabara ce ta faɗo mata a ran ta,wayar ta ta sa ta kunna karatu ta ajiye a gefen kan shi, karatun ne ya tada shi,nan take kuwa ya buɗe ido yana guntun tsaki, ita ya gani kusa da shi tana yi masa murmushi tare da sunne kai qasa alamar jin nauyin shi, nan da nan abinda ya faru a daren jiya ya bijiro wa ƙwaƙwalwar shi, shima murmushi ya saki wanda be shirya wa, a can qasan ranta kuwa tana jin haushin shi saboda barin ta da ya yi tayi jinyar kan ta, shi Kuma ya baza ciki da baki yana bacci, sake murmusawa ta yi ta sunne kai qasa sosai, cikin murya cike da shagwab'a tace,

"My Sweet yau ma zaka makara sallah fa, ni bana son kowa na samun lada ana wuce mijina gaskiya,"

Sai juya baya irin na shagwab'ab'b'un nan, bacci ne fal idon shi amma baya Jin zai iya jure wannan salon nata, ga wata iriyar shagwab'a da juya jiki da take yi wanda be saba ganin hakan ba a wajen matan shi da sauran karuwan da yake mu'amala da su saboda ya gama yarda Eamaan ta daban ce a cikin mata, tashi ya yi bai kula ta ba ya shige bathroom ya yi  wanka sannan ya zo ya yi sallah,ko addu'a be tsaya yi ba  ya koma gado abin shi tare da Janta jikin shi dan su koma bacci,shafa fuskar ta ya yi a hankali sannan yace ,

"To na yi sallah lada be wuce mijin ki ba , mu koma bacci dan ni bacci nake ji,"

Ba tare da ta musa masa ba kuwa suka koma baccin su.

Tin daga ranar Eamaan ta zama kwararriya wajen yi ma Alhaji wayo na sa shi yin duk wani abun da ba yayi a da musamman ta bangaren ibada, wajen wanka da brush ɗin dare dana asuba kuwa yanzu shi da kan shi in bai yiba ma zai ji ba daɗi, matan shi ma sun ga sauyi sosai a tattare da shi, Iya ma uwar sa ido sai da ta ga ɗan nata gaba ɗaya ya sauya, har masjid yana fita yanzu, amma taurin kai na tsohuwar nan ba abinda ke haɗa su kuma ya raba su da Eamaan sai zagi, da kyara,ita ko bata nuna mata wata alamar ta ji haushi dangane da yanda take mata a gidan, iyaka in ta mata abinda ya mata zafi sosai,sai ta dawo sashenta ta sha kukanta ta bawa Kan ta hakuri, sannan ta Kuma tina wa Kanta cewar dama zaman BIYAYYAH take yi a gidan ba zaman soyayya ba,Dan haka zata jure komai watarana sai labari.

Babban abin da ke damun ta yanzu be wuce matsalar neman matan shi ba da ya dawo da shi, dan kuwa har yanzu bai dena ba, tana yawan ganin condom a kayan shi, rannan ma da yaje Abuja girki ya fad'o ta wajen ta used condom ta gani a aljihun sa na babbar riga,abun na matuqar bata mamaki wai shin wannan jaraba har ina, kuka take yi sosai in ta ga hakan, ace mata har uku amma ba zaka daina neman mata ba? ta qudurta indai ita mace ce da yardar Allah sai ya daina bin matan banza.

A cikin wata na uku da auren su Eamaan bata taɓa zuwa gida ba dan ganin iyayen ta da ta yi kewa sosai, dan haka yau ta roqi Alhaji da ya barta taje ganin Ammaahn ta, kullum sai dai su yi waya ta gaji da hakurin rashin ganin mahaifiyar ta,Mama Kareema ma ta matsu ta gan ta tana son zuwa amma basa shiri yanzu da matan Alhaji shi yasa bata zo ba,sunce da munafurcin ta aka haɗa baki aka yi masu kishiya da d'iyar su, da kyar ya yarda dan Alhaji ba dai kulle ba.

To fa dama kunsan mai aikata zina ko wani mugun hali, kullum tsoron shi kar nashi su fita ayi da su, bai san in dai kana yi ba sai an yi da naka komai kullen ka, sai dai in ka tuba ka bi Allah, Allah ya yafe maka ya kuma kare zuri'ar ka.

Gaye tasha sosai na zuwa gida tana gamawa ta rufe wajen ta ta bi wajen Iya dan yi mata sallama, bayan ta gaida ta ne ta sanar da ita cewar Alhaji ya bata izinin zuwa gaida Ammaahn ta.

"To in ya baki izini ni ban bayar ba ba zaki je ba,kina ganin ai gidana ya yi datti amma ba zaki taya a gyara ba, maza jeki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login