Showing 18001 words to 21000 words out of 78127 words
Chapter 7 - BIYAYYA Book Complete Hausa Novels by HAERMERBRAERH.txt
bace yar iska,Sahabee kuka yake yi sosai na baqin cikin ganin shi qasqance gaban yarinya qarama kamar Eamaan ta na yanka masa gargad'i bayan ya yi masa duka,qasan ran shi kuma yana kukan takaicin rasa babbar damar kashe qishin ruwan shi akan Eamaan, gefen idon shi ya yi jawur inda turaren yayi nasarar shiga ciki, umartar shi ta yi daya fice maya daga waje kafin ta sake sanya masa turaren a idanun shi,ai kuwa da gudu-gudu ya miqe zai fice daga sashen nata, Eamaan ta daka masa tsawa ya dakata tace,
"Wannann jakar taka da takalmin ka d'aya da ka bar min anan uban wa zai ɗaukar maka,"
"Bbbaaaabaaa kowwaaa, niiii zannnn d'auuuke abu na"
Wurga masa ta yi ya ɗebe su da hanzari ita Kuma ta danna qofar ta rufe da makulli, kuka ta zauna a wajen tana yi sosai,zuciyarta ta yi mata kunci, wannan shine babban misalin in kayi zina da 'yar wani ko matar wani ko qanwar wani ko mahaifiyar wani kaima za a yi da naka,ficewar motar Alhaji da taji ne ya sanya ta je ta dakko Ice cream ta sha ko ranta zai yi sanyi amma ina bata samu abinda take so ba, nan take taje ta dauki qur'aninta ta fara karantawa ko zai ɗauke mata damuwar dake ran ta, ta fara kenan ta ji shigowar mutum ashe qanin mijin ta ne,ajiyar zuciya ta yi ta goge hancin ta dake d'igar da hawaye da majina,ta tabbata Alhajin na su sai gobe a ganshi tinda ya tafi wajen matan banzan shi, kuka ta ci gaba da yi sosai zuciyar ta kamar ta fito waje dan qunci, wannan wace irin rayuwa ce,Allah ya sani a rayuwar ta bata tab'a hango ta zaune da kishiya ba ita da Anwar d'in ta sai gata a gidan me mata biyu ya qara masu da wasu matan banzan a waje lallai bahaushe ya yi gaskiya da yace qaddara ta riga fata,a yanzu Allah kaɗai yasan iya adadin matan da Alhaji ke bi da wanda ya lalata ba tare da amincewar su ba, cikin kukan da take yi ta kalli sama tace,
" Yah Allah ka qaramin hakuri da juriya, Allah ka sani daga bayin ka masu godiya,"
Sai ta miqe ta share hawayen ta duk ta hada zufa sosai kamar wadda ta yi dambe, ko yake ai qanin damben tayi ma, wanka ta dad'a shiga ta yo tare da d'aura alwala ta zo ta saka doguwar riga, tirarukan ta masu sanyin qamshi ta fesa,ta zira dogon hijabin ta a saman kayan ta sannan ta fara nawafil, ba ta San iya adadin raka'a nawa ta gabatar ba saboda yawan sallolin da ta yi,lokacin da taji ta gaji sai ta sallame ta zauna ta ta fara karanta 'Qur'ani tana idarwa, ta yi addu'o'i ta shafa, tasha kuka a wajen addu'ar sosai, kanta jingine da jikin gado bacci mai daɗi da nauyi ya ɗauke ta.
Sahabee kuwa yana fita ya hau waige-waige baiga kowa ba sai da yaje dab zai shiga bangaren su mai gadi ya fito daga d'akin shi ya gan shi, Hajiya Qarama da ta ji motsi ce ta leqa tace waye nan, muryar shi na rawa yace,
" Ni ne Sahabee,"
Sake labulen ta yi tare da sake tsakin ta koma,me gadi ne ya dalle shi da fitila, yana ganin shine ya sauke ya fad'a d'akin shi, dan ya san rashin mutuncin Sahabee kala-kala tinda ya sha yi masa, dan haka ya na iya masa rashin mutunci akan haska shin da ya yi da safe,shi kuwa Sahabee yau ba wannan ne a gaban shi ba, tinani yake yi kala-kala ga wani mugun tsoron Eamaan da ya ke ji na qara shigar shi a duk sanda ta faɗo masa a rai, bud'ewa ya yi ya shige sashen Iya direct d'akin shi ya je ya aje jakar shi ya faɗa toilet, wanka ya yi ya fito ya wanke kayan da ta fesawa tirare a jiki, dan gaba daya qamshi yake yi irin na Eamaan ɗin,a cikin toilet ɗin ya shanya su ya fito d'aure da towel,kallon kanshi ya yi a mirror yaga irin kyaun qirar da yake da ita 'yammata na mutuwa akan ya kwanta da su amma Eamaan ta yi masa wannan gagarumin wulaqancin da tozarcin,duk kyawun jiki da kyawun fuskar shi amma matar tsoho ke gudun shi take wulaqanta shi.
Murmushi ya yi ya tabbatar wa kan shi lallai bahaushe ya yi gaskiya da yace abincin wani gubar wani, ashe ba kowacce mace bace zata zauna ta ci amanar mijin ta da wani a wannan zamanin kamar yanda yayi zato? Sannan ba kowacce mace bace ballagaza mara kamun kai,ashe akwai sauran matan kirki da ke kare daraja da qimar aure komai kyau da kud'in namiji ba za su bishi ba? Matan dake jiran sakamakon su na alkairi a wajen Allah, yau ya tabbatar da cewa komai rashin samun yanda mace take so a wajen mijin ta akwai na k'warai da suke jiran ladan su na haƙuri a wajen Allah ba su kaucewa hanyar gaskiya saboda bin son zuciyar su, rigar shi ya ɗauka a wardrobe ɗin shi ya saka ya haye gado, sai dai Sahabee ya kasa bacci sam, a kowanne second qara ganin girman Eamaan yake, sannan wani irin kwarjinin ta na cika qirjin shi, Hajiya Babba ya tina da ta ke yi mai waya a koda yaushe sannan take manne masa akan tana so ya dinga neman ta, rintse ido ya yi ya toshe kunnen shi, dan kuwa wata iriyar nadama yake jin tana son shigar shi wadda be shirya mata ba a yanzu sam,gani yake yi kamar akwai sauran nasara ko ta ɓangaren Hajiya Babba zaina ci gaba da rage zafi, tinda in yana nan ba ya zuwa wani waje sosai saboda Iya tafi son ganin shi a gida.
Tun da asubar fari Eamaan ta farka daga bacci duk jikin ta na yi mata ciwo,bayan ta yi sallah ta kammala duk wata ibada da ta saba yi bayan sallar asuba sai shirya ta fito zuwa wajen Iya,a hanyarta ne taga motar Alhaji na shigowa gidan,sai ta tsaya ta ɗan kalle shi fuskar ta tayi kicin-kicin saboda tsabar ɓacin rai, sai da idon shi ya shiga nata ta sa kai ta yi gaba, gaba ɗaya ta zare masa laka da kallon da ta watsa masa,dan haka da kyar ya qarasa shigowa, ya fita ya yi bangaren Hajiya Qarama, wadda ya tarar itama ta yi kicin-kicin da rai,ko kula ta bai yi ba ya wuce d'aki ya yi wankan tsarki, ya fito sanye da towel iya qugun shi, Hajiya Qarama ce ta hau bin shi da kallon buqatar mijin nata amma kuma wata zuciyar na qissima mata Jin haushin shi.
Bayan ta manta itama ta na da nata laifin wajen fitar shi yawon banzan, saboda qazantar ta da rashin kula da miji.
Goge jikin sa yayi ya shafa mai da tiraruka ya zira jallabiya da dogon wandon ta ya nufi ɓangaren Iya, a kitchen ya Jiyo motsin Eamaan,ita kuwa tana can tana so ta markad'a waken da tasa tin jiya mai aiki ta sirfa mata dan ta yi qosai da safe da shi,sai ta sake wankewa albasa da attaruhu ta saka ta markad'e sannan ta juye markad'add'en waken a wani bowl mai fad'i, ta saka zallan gishiri sai dan farin maggi kaɗan da onga green ɗin, saboda in ta saka maggi dunqule yana watsewa a mai, baya haɗe jikin shi ya tashi yanda take so,bugawa ta hau yi sosai kafin nan ta fara soyawa,tana yi ta na duba kunun gyad'an da ta ɗora, bayan ta gama ne ta zuba ma kunun nono irin asalin kindirmo ɗin nan, nan da nan kunun gyad'ar ya qara yin fari tass, ta zuba su a flask ta saka plate ɗaya cup ɗaya, dan bata son ta saka biyu a san ta san da dawowar Sahabee, tana jiyo Alhaji na gaida Iya suna hira sai ta ja ta tsaya dan kuwa bata son ganin shi sam.
Wani irin kyankyamin shi take ji yanzu, amma haka danne ɓacin ran ta ta ɗauka ta shiga da sallama, Iya na ganin ta yawun ta ya tsinke dan ta san zata ci mai daɗi ,amma dan mugun rai sai ta b'ata rai, Sahabee ne ya buɗe qofa zai fito daga d'akin shi saboda yunwar da yake ji,ya na Jin Eamaan a parlour ya yi maza ya koma d'akin shi ya danna lock ɗin qofar ya rufe yana haki,ba wanda ya san da yana ciki sai qarar danna qofar shi suka ji, bin hanyar su ka yi da kallo baki d'ayan su, Eamaan kuwa da ta San ko waye a dakin ba ta juya ba ajiye abincin ta yi zata bar wajen.
Iya kuwa umarni ta bawa Alhaji dan ya leqa yaga waye a d'akin Sahabee bayan Sahabee baya nan lokaci ɗaya kuma tana dagawa Eamaan hannu ta dakatar da ita, cike da tsoro Iya ke kallon wajen, Eamaan da taga hankalin su ya yi wajen, se kawai ta yi murmushi ta fice daga ɓangaren gaba ɗaya ba tare da ta bi ta kan umarnin Iya dake tsaida ita ba, sashen sauran matan ta je ta gaida su kamar yanda ta saba sannan ta wuce nata wajen.
Alhaji na leqawa ya ga Sahabee a tsaye sai wurga ido yake yi, a zaton shi Eamaan zuwa ta yi ta faɗa musu me ya faru tsakanin su a daren jiya,ko da ba qarar shi ta kai ba baya son su sake had'uwa da Eamaan idanun ta na rikita shi kwarai da gaske.
Eamaan na da wata baiwa da be tab'a had'uwa da mace kamar ta ba, kasa cewa komai ya yi da Alhaji ya nuna farin cikin ganin shi sai ya hau yashe haqora yana yaqe.
"Yaushe ka dawo?"
Qeya ya sosa kafin yace,
"Jiya da daddare na dawo na isko kowa ya yi bacci, kawai sai ban tada kowa ba nima na kwanta, ina kwana Yaya?"
Gaisawa suka yi sannan suka qarasa wajen Iya,tana ganin shi ta tashi tsaye tana washe baki murna a wajen ta kamar wanda ya b'ata aka ganshi, sosai ta ji dad'in dawowar tashi, waya ta ɗauka tace bari na kira Eamaan ta zo ta haɗa maka abin karyawa, wata sufa ya yi ya damqe wayar yana in ina yace ,
" Baattaa kawaiii zan ci ko me aka dafa maki, ni daga yanzu ma ana haɗa mana abinci kawai ba sai an yi wa kowa nashi daban ba,"
Daga jin yanda yake maganar kasan akwai wata a qasa duk zufa ta tsattsafo a goshin shi kamar wanda ya yi gudu,mamaki ne fal a cikin ran su bama ya Alhaji wanda ya san halin Sahabee na son takurawa Eamaan ɗin ,nan take ya d'iga wa Sahabee alamar tambaya, tabbas akwai wani abu a qasa, yana ganin irin kallon da Alhaji ke bin shi da shi sai ya hau yaqe yana faɗin,
"Ya naga duk kunyi shiru kuna kallo na? Na yi tunani ne saboda rashin lafiyar Iya na daina duk wani rashin da'a ko BIYAYYAH danake yi a baya,daga yanzu na dena qasqantar da na qasa dani,"
Murna ce ta cika zuciyar Iya a lokacin da ta ji kalaman autan nata, abinci Iya tai ta d'ura masa, shiko sai kwashewa yake yana ci dan kuwa ya yi kewar abincin Eamaan sosai.
Eamaan na isa sashen ta ta rufe bangaren ta ta fara gyara gidan, ta goge shi tsaf, sannan ta haɗawa kanta oatmeal dan ta sha,zaune take saman dinning table ta na wasa da spoon ɗin a cikin qaramin bowl ɗin da ta had'a oatmeal, wani tunani ya faɗo mata a rai, yau mijin ta ya je neman mata ya ci nasara a neman matan nashi,ita kuma qanin shi ya je neman ta Allah ya tsare ta wanda hakan baya rasa nasaba da kullum cikin sallolin ta na farillah da nafila tana neman tsarin Allah akan zina da dik abinda zai kusantar da ita wajen aikata zinar, musamman ma a wannan zamanin da zinar ta yi katutu a zuqatan mutane, ya zata yi a lokacin da jarabawa ta afka mata qanin shi ya ci nasara akan ta?
kwallar ta ta share sannan ta kawar da wannan tunanin a ranta da addu'ar Allah ya ci gaba da bata kariya, sannan ta qarasa abincin ta ta wanke bowl din ta ajiye a inda ya dace ta fita daga kitchen ɗin, d'aki ta shiga ta fad'a bathroom ta yi wanka ko mai bata tsaya shafawa ba balle wata kwalliya ta zira riga ta kwanta baccin safe, nan take kuwa wani bacci mai dad'i ya ɗauke ta, Alhaji yazo ya yi ta bugun qofar ta shiru ba ta bud'e ba, gashi ya San ba ta saba rufewa ba, kad'a kan shi yayi ya koma ɓangaren Hajiya qarama, wadda har a lokacin bata yi wanka ba, d'aki ya nufa shima ya rufe ya kwanta, wayar shi ya duba yaga missed calls din Eamaan a jiyan nan da nan yaji tashin hankali da damuwa sun mamaye shi, dan ya tabbata hakan ne ya sata fushi har ta qi buɗe masa qofa,ya qudurta kome zai faru zai shawo babyn shi tinda shi yayi mata laifi, kuma zai qoqarin daina bin mata kamar yanda take buri.
Alhaji ya samu nasarar shawo Kan Eamaan ta hanyar yi mata alqawarin dena bin matan banza a waje, ita kuwa sai ta sanya shi ya yi alqawari tsakanin shi da Allah ta nuna masa cewar Allah yake sab'awa ba ita ba,sannan ba Iya ba ba matan sa ba, Allah shi ke da wuta ya ke da aljannah, idan ya tuba ya dena cikin Rahamar Allah sai ya Sanya shi a aljannah, idan ya qi tuba ya ci gaba da aikata zina se ubangiji ya azabtar da shi da wutar shi, kar ya manta wutar duniya ma ba ya iyawa da ita balle ta lahira, da wannan nasihar Eamaan ta samu nasarar hana Alhaji Abdullahi yawon dare, ya kame kan shi ya ke qoqari wajen danne buqatar shi ta bin matan banza a duk sanda be samu yanda yake so ba a wajen sauran matan nashi,a haka yake hakuri ya Jira har ranar girkin Eamaan ɗin ya zagayo ko girkin Hajiya Babba, ita Kuma Eamaan sai take hakuri da danne duk Wani rashin so da qin kusantar ta da yake ta na nuna masa ta na so, Kuma ta na Jin dad'in kasancewar su tare a koda yaushe.
A kwana a tashi Eamaan da Alhaji suna ta samun kusanci da junan sj da shaquwa,sai dai har yanzu babu wata soyayyar shi a ran ta sai girmamawa, komai nashi ta sani Kuma yana yin shawara da ita sosai.
kwatsam watarana Alhaji Abdullah ya tashi da ciwon baya se yake sanar da ita, Eamaan tayi masa sannu sannan ta bashi maganin ciwon jiki ya sha, abu kamar wasa ciwo kullum na gaba har dai watarana suka shirya dan zuwa ganin likita game da ciwon bayan nashi fatan ta Allah ya sa ba wata mummunar cuta bace ta kama Alhajin nata.........
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 9:
Gaba ɗaya rayuwar Alhaji ta zama sai a hankali saboda yawan jin kasala a jikin shi da yake fama da ita,haka tafukan hannayen shi da qafafun shi suke kumbura,kai hatta da fuskar shi ma ta hau ta yi haske, uwa uba yawan jin qaiqayi da yake a jikin shi duk yafi damun shi saboda yawan susa da yake yi ba ya jin sauqin qaiqayin, sai dai ma da ya gama susar wasu quraje ne suke fito masa qanana a jikin shi,idan kuwa ya je yin fitsari to fa da kyar yake iya yi, rabon shi da Kashi kuwa ya kwana biyu, abubuwa dai sun taru sun yi mai yawa.
Randa zasu je asibitin ya kama ranar girkin Hajiya Babba ne, ta sha kwalliyar ta kamar yanda ta saba suka shiga mota ita da Alhaji suka zauna a baya Sahabee da driver kuma na zaune a gaba, suna zuwa aka bashi gado, likita ya rubuta wa Alhajin gwaje-gwajen da ya Kamata a masa dan danin makamar ta inda za a yi masa magani, dik da cewa already akwai ciwon da yake zargi shi ke damun Alhajin duba da symptoms ɗin da suka bayyana a jikin shi.
Ai kuwa gwajin farko suka gano gaba ɗaya qodar shi sun samu matsala, d'aya ce kawai me ɗan sauqi-sauqi, akwai yiwuwar in ya sha magunguna aka wanke masa ita zai iya samun sauqi, hankalin Hajiya Babba da Sahabee ba qaramin tashi ya yi ba da jin wannan mummunan labarin,sanda suka yi waya suka sanar a gida kuwa kowa ya shiga damuwa, a haka likitan ya bashi duk wata kulawa da ya Kamata a bawa mai irin ciwon.
Iyalan Alhaji Abdullahi su na iya bakin qoqarin su dan bashi magani akan lokaci da bashi kulawar da likita ya umarta a bashi, duk da sun so matuqa a fita waje da shi amma likitan ya musu alqawarin za su bashi kulawa kamar ya na qasar waje,abokan shi na siyasa sun shiga damuwa Suma duba cewa kusan shi ne jigon jam'iyyar tasu, gashi mutane na son shi da girmama shi, addu'a suke tayi da fatan Allah ya tashi kafad'un shi.
Matan Alhaji kuwa shifting ɗin zama a wajen shi suka fara yi kamar ma'aikatan gwamnati, in girkin wannan ya fita wannan ta zo, duk ranar da ta kasance ranar girkin Eamaan ne tofa ranar sahabee ba shi a zuwa asibiti, dan tinda abunnan ya faru yake toshe duk wata kafa da zata had'a su a waje guda.
Wata rana Iya ta kira Eamaan sashen ta, duk da cewar washe gari ne zata karbi girki, kimtsawa ta yi ta saka hijab din ta ta fita zuwa wajen Iya, tana zuwa ta tadda ta da himilin rake a gaban ta,Eamaan zama ta yi ta tankwashe qafa a gaban Iya ta gaida Iyar,cikin tsuke fuska Iya tace wa Eamaan.
" Ni ba gaishe-gaishe ne ya sa na kira ki nan wajen ba, ammmm kina jina ko wannan raken nake son ki samu ki markad'en shi ki tacen ruwan sa kamar yanda na ji ki a waya rannan kina gayawa wata,jarababbiya kamar ki wai har kin san hada maganin mata da rake, to ni na lafiya zaki haɗawa d'ana yanzu ba na kayan jarabar taki ba, dan