Showing 66001 words to 69000 words out of 78127 words
Chapter 23 - BIYAYYA Book Complete Hausa Novels by HAERMERBRAERH.txt
na muke zaune a wannan akurkin, domin rufin asirin ka shine nawa,se yanzu na gane duk Kalaman ka a gare ni qanzon kurege ne,tin yanzu gashi ka fara karya alƙawarin ka na bani kud'in anko a duk sanda na buƙata,to ka buɗe kunnen ka da kyau kaji ni,wannan ankon da na ciyo bashi se ka biya ba zaka sa na ji kunya ba,dubun nan talatin da bakwai cassss se ka kawo su,sannan ga kudin ɗinki dubu biyar da aka yo min,dole ne ka biya kud'in takalmi da jaka da mayafi da na sa qanina ya amso bashi a shagon abokin shi, ba zaka sa na ji kunyar qanne na ba a dinga raina ni ana zagin miji na ana kiran ka talaka,sarqa da dan kunne da abun hannu da zan yi amfani dasu Kuma ka siya daga baya kafin ranar bikin tazo.
Kai dama zaka godewa Allah na samu bashin? Yanzu a wannan zamanin bashin ma ai se ka yi da gaske zaka same shi, ni yanzu na gama gane inda ka dosa dik ƙarya ka zuba min lokacin neman aure na,gashi yanzu ka gaza a kula da ni, dama ko a gadon ma hakuri nake da Kai yanzu,"
fashe wa ta yi da kuka har da shessheƙa kamar shine ya gama yi mata rashin mutunci ba ita ba, duk maganganun da take yi sun shiga kunnen Iya sun zauna a zuciyar ta daram, kad'a kai Iya ta yi alamar muje zuwa yanzu aka fara tinda na hana ka auren ta ka kafe, to ga irin ta nan ai.
Sahabee kuwa duqawa ya yi a gaban ta ya na bata hakuri da tabbatar mata ze biya kud'in ko nawa ne, murmushi ta fara yi masa ta na wani kakkama shi, Sahabee na ganin ta sakko ya tallabe kan ta zai yi mata kiss, cikin nuna qyanqyamin shi ta janye jikin ta tace,
"Haba my baby ki yi hakuri mana na ce maki inna samu zan baki, kinga a wajen aikin mu ni ke ajiyar kud'i, inna je zan ranta na baki, a albashina sun dinga d'auka a hankali har na gama biya, ba dai dubu tamanin bane dika kud'in? kar ki damu zan baki ni dai ki min murmushin ki me kyau na gani ko naji dad'i a raina"
Murmushin ta masa ta rungume shi tana boye fuskar ta a bayan shi tare da murgud'a masa baki da harar shi, shafata ya soma yi cikin b'ata rai ta ture shi tace,
"A'a gaskiya ciki na babu komai me zan iya yi maka yanzu? ni yunwa na ke ji kamar banci komai ba nake jina, gaskiya ka samo mana yar kaza yau mu d'an ci a gidan nan mu maida mugun yawu, kaima kasan kullum sai na ci kaji bama kaza ba sanda Ina gidan mu,amma ka duba ka gani sai na yi sati ko kwana hudu ban ganta ba anan gidan."
Hawayen munafurci ta share ta fyace majina ita a dole zaman haƙuri take yi a gidan Sahabee, jikin shi na rawa ya fita ya amso bashin qatuwar kaza guda d'aya,wanda da kyar ma aka bashi bashin kazar saboda dama can akwai tsohon bashin kusan dubu bakwai da Mai kajin ke bin shi, yau d'in ma dan ya gilla qaryar a gobe zai kawo masa har na baya ne sannan ya yarda ya bashi, Sahabee ya qudurta a ran shi gobe zai je wajen aikin nasu ya d'akko kud'in ba Wanda ya sani tinda a office ɗin shi suke.
Koda ya dawo sai ya baje mata kazar a gaban ta yana murmushi, zama tayi kamar mayya tana washe baki, a tare suka hau cin kaza tana zuba surutu kamar tsohuwar redio, yawun Iya gaba ɗaya ya gama tsinkewa saboda tana jin dik abinda ke faruwa,hawaye take zubarwa tsabar kwad'ayin da ya addabe ta, tinanin gidan Alhaji Abdullah kuwa ya zame mata ibada dan kuwa kullum sai tayi,yanzu da acan ne ko kaji nawa take so se ta sa a gasa mata ta ci,a rayuwar nan dama dik wanda yasaba cin dad'i tofa shi yafi begen dad'in, haka suka gama tass suka sha ruwa basu sammata koda fuffuke ba, da kyar Sahabee ya samu had'in kan ta ya sauke buƙatar shi dik da faranta mata da yake ƙoƙarin yi a kullum.
Washe gari da sassafe ya shirya bayan ya gama yi mata aikace-aikacen gidan da ya saba,sai ya leqa Iya ya mata sallama, bai ji ta amsa ba ya wuce dan bai damu daya ga lafiya take ba ko akasin hakan, yana fitowa ya sa kai ya tafi.
Lokacin da ya isa office bai tarar da mutane ba sosai sai ya zauna ya gaggaisa da mutanen da ya tarar,sannan ya tashi zai shiga office ɗin shi d'auke da jakar shi a hannu,sauran ma'aikatan kuwa yana tashi suka hau qulmar shi suna cewa tin da ya yi aure ya rame kuma yake makara,ko kuma ma ya yi fashi gaba d'aya yaƙi zuwa,yana ji bai kula su ba ya wuce, sai da qafa ta d'auke lokacin cin abincin rana ya yi ya buɗe wajen da ake aje kud'in ya kwasa,da har ya dauki dubu d'ari ya rufe, daga baya kawai yace bari ya ɗauki dari biyu zasu masa amfani a gaba, sun dinga zara a albashin sa a hankali har ya gama biya, yana gama d'iba ya rufe ko ina ya tafi gida hankalin shi kwance, yana zuwa gida ya zaro dika kud'in ya zube a gaban ta tin kafin ya cire kaya ya huta, amarya kuwa na ganin wannan uban kud'in sai rawar kai ta tashi, tana ta yi maaa sannu da zuwa harda tashi ta ɗora girki tana faɗin ya gaji ya zauna ya huta zata yi musu abincin.
Bayan sun ci abinci sun gama ne ya shiga wanka ya fito yayi alwala saboda gabatowar sallar magariba, koda ya je masallaci yayi sallah ya dawo da isha'i Amarya ta maqale masa,ranar Sahabee ya samu kulawa ta musamman a wajen matar shi har bai san sanda dare yayi nisa ba,bata barshi ba har sai da taga bashi da sauran qarfi a jikin shi, tana ganin ya yi bacci ta ɗauki wayar ta ta kira qawar ta tace mata,
"ke shegiyar ga fa kayan ki nan zan dawo maki da su, ni kam na samu kudin da na dan samu zan qara gaba, na gaji da qaddararren auren nan, dama ace yana d'an samu ne kuma yana da qarfi sosai a gado to da na hakura, amma ba komai daga sama har qasa komai a bushe me zai zaunar da ni? Ina nan tafe yanzu ki saurare ni nan da awa ɗaya, dan haka ki fito bakin hanya na baki kayan ki na ƙara gaba."
Dariya kawai waccan take kwasa tana ta hura mata kai, tana ziga ta,cikin shewa tace,
"To muguwar sai kinzo, ai ita bariki haka take dama, wanda bai zo bama jiran shi take gashi ya faɗa hannun ki kin kwashi rabon ki zaki arce,ina nan ina jiran ki sai kin zo."
Sallama suka yi ta aje yar rakani kashin ta ta fara haɗa kayan ta a hankali,sahabee kuwa na nan washarere jiki a bude dik ya gaji, ta kalle shi ta tofar da yawu a gefe tace,
" Allah ya kiyaye na ci gaba da zama da wannan lagwanin, ba kuɗi ba biyan buƙata, ga mazaje can a waje na jira na a biya min buƙata kuma a bani kuɗi amma ina nan a rakub'e kamar ƴar karo? dama ai dan na zaci har lokacin yana tare da wannan yayan nashi ne mai kuɗin da yake kashe min a baya,wanda shima na ji ana ta rad'e rad'in d'an hannu ne,(Matsalar zina kenan yan uwa, Alhaji dai ya mutu amma ga wata tana tino da labarin shi kuma tana maimaita ai dan hannu ne, wanda ana so in za a tina ka a tina ka da aikin alkairi, Allah ya kyauta ya samu aikata dai-dai, ya yafe mana a inda muka yi kuskure, Allah ya shiryar damu da zuriar mu) tana gama mitar ta ta kwashe kud'in ta d'ure a jaka ta sa kai ta bar gidan, d'akin Iya ta leqa taga yanda ta barta tin safe tana nan kwance a haka har a wannan lokacin, sakin labulen ta yi ta kyab'e baki tai gaba tana mitar sai shegen son jiki kawai tsohuwar ta sani da sa ido, tana fita gidan qawar ta ta nufa ta miqa mata kayan da dubu biyu kamar yanda suka yi alqawari tai gaba.
Sahabee kuwa sai da ya kai awa d'aya bayan fitar ta ya na bacci kafin ya farka, kallon d'akin ya yi yaga kamar anyi yasa, shiru ya yi ya ɗauki gajeran wandon shi irin na ƴan ball ya saka,neman ta ya fara yi amma babu ita babu dalilin ta, ɗan murmusawa ya yi sannan ya ce,
"Wataqila tana can tana gasa kan ta, dan yau na more ta sosai ba kad'an ba , yaushe rabon da ta barni nayi irin na yau? Muguwar ai haka zan nayi mata kuwa daga yau."
Yana nan har aka kira la'asar yaji shiru bata dawo d'aki ba,sai ya tashi ya leqa band'aki dan yaga me take yi haka, yana shiga yaga wayam, hankalin shi ne ya fara tashi cikin sauri ya koma d'akin ya hau bincike, nan fa yaga babu kud'i babu dalilin su Kuma ba kayan ta na sawa,sai wata dubu buyu da ya gani da takarda a aje an dora kwalbar Mai akai.
Buɗewa yayi ya ci karo da mummunan bayanin da ya sanya shi yin zaman ƴan bori a ƙasa,wasu zafafan hawaye ne suka fara tsartuw daga idanun shi,a guje ya fita zuwa d'akin Iya dan sanar da ita mummunan abinda ya same shi,yana zuwa sai ya ganta kwance yanda ya barta tin safe da zai fita aiki.
A hankali cikin rawar jiki ya qarasa shiga cikin d'akin ya sa hannu ya taɓa ta ya ji shiru bata motsa ba kuma bata ce komai ba,hannu biyu ya sa ya juyo da ita sai yaga bata motsi,da gudu ya fita tsakar gida ya samo ruwa ya hau yayyafa mata amma shiru Iya bata farka ba.
Ɗaukar ta yayi da kyar ya yi waje da ita ya ajiye ta a dakalin ƙofar gidan su ko riga babu a jikin shi, se da ya wahala kafin ya samu abun hawan da zai Kai su asibiti, dubu d'aya me adaidaita ya caje shi, ya ce su je ba komai ze biya, ko da suka Isa asibiti Sahabee kuka ya sa ya na neman a taimaka masa, ganin yanayin da yaje asibitin dashi ne daga shi sai gajeran wando ga Iya a kwance rai kwakwai mutu kwakwai ne yasa likita ya ce a shigar da ita ya duba ta sun kawo kuɗin daga baya.
Da kyar aka samu Iya ta farfad'o daga doguwar sumar da ta yi, takarda likita ya bashi me d'auke da magungunan da za a siya wa Iya, likita ya ce daga baya za a yi maganar bill na asibiti Kuma.
Likita ya shawarce shi akan ya samo mata abu me ruwa-ruwa da zata sha in ta farka saboda akwai yunwa a tattare da ita sosai, Sahabee tsugunnawa ya yi a wajen yayi tsuruu yana tunanin inda zai samo kud'ad'en da zai yi wannan hidimar da su.
Kamar wanda aka mintsina haka ya miƙe cikin hanzari ya nausa ya nufi ma'aikatar su,dan kuwa ya tabbata yanzu ba kowa dik an tafi gida, zai yi amfani da wannan damar dan ya samo wasu kud'ad'en a can,a guje yake tafiya yana haki duk inda ya wuce mutane sai sun bishi da kallo sai kace wani kwarto,a rayuwar shi kaf bai tab'a tinanin zai shiga damuwa irin haka ba,a yau ya gane ashe uwa uwace,dik duniya bayan Allah da manzon sa baka da kamar ta.
Kamar yanda ya zata kuwa ya na zuwa ya tarar da wajen a rufe ba kowa dik an tafi gida sai Mai gadi, zagayawa ya yi ya haura Katanga ya shige ya balle makullin cikin dabara da kwarewa irin ta tsoffin 'yan bariki, (Kun San Wanda ke bariki ba a raba shi da sata) dubu dari da hamsin ya qirga casss, ya zamana ya saci dubu dari uku da hamsin kenan, yana gamawa sai ya barbaza kayan wajen ya koma ya haura Katanga ya koma asibitin,yana zuwa ya biya komai da ya Kamata ya biya har ya samu na abinci da zasu ci, gida ya koma dan ya yi wanka ya d'an huta Kuma tinda Iya bacci take, ko da ya kammala duk abinda zai yi se ya kashingid'a da niyyar zuwa bayan isha'i se ya koma asibitin,bacci ne mai nauyi ya ɗauke shi ba shi ya farka ba se subahi tsabar gajiyar da ya kwasa.
Kwanan Iya biyar a asibiti jiki yayi sauƙi ta murmure, dan haka likita yace musu a yau zai sallame su, Iya na Jin maganar Sallama ta hau kuka ta na fad'in ita su bar ta a wajen su kawai kar a bari Sahabee ya Maida ta gida, kowa a wajen ya tausaya mata sosai dik da cewar basu san menene tsakanin su ba, ba yanda za su yi dole hakuri suka bata Sahabee yazo da yamma suka koma gida.
Tinda suka koma gida sai ya rage mugun hali ya ɗan fara kulawa da ita,dan kuwa watarana har yakan sai mata madara ta leda guda d'aya da bread yankan nera ɗari, sai ya dafa mata ruwan lipton ya sa mata sigan ashirin a ciki, shi kuwa kafin ya wuce aiki zai je wajen mai shayi ayi masa had'in kauri yaci ya sha ya ƙoshi.
A haka rayuwar Iya da Sahabee ta ci gaba har kud'in ya tasamma qarewa, a wajen aikin shi kuwa da fari sun zaci shiga aka yi akai sata, saboda samun wajen da suka yi a b'alle,sai da bincike yayi bincike suka gane cewar Sahabee ne ya yi satar.
Wata ranar talata suna zaune shi da Iya yana ta mata masifar ta yi fitsari a zaune, dan kawai bata jin dad'i ba zata qwarara jikin ta ba ta isa bayi sai ta saki fitsari a zaune? da anyi mata magana kuma tace qafa ke matsa mata,waye qafarshi bata ciwo amma haka yake tafiya bayi sai ita? Hawaye kawai take zubarwa tana jin kamar ta hadiyi zuciya ta mutu dan baƙin cikin sahabee ya ishe ta,yana nan yana sababi aka hau k'wank'wasa ƙofar gidan nasu, Sahabee ne ya miqe dan zuwa ya ga waye yake musu bugu kamar ya basu ajiya, dan shi ya riga ya cire ran waccan gantalalliyar zata dawo gare shi ma shi yasa ko neman ta baiyi ba, shi se yanzu ma yake danasanin auren ta da yayi dama haɗuwar bariki ta gaji haka,tafe yake ya na ci gaba da masifa har ya isa qofar gidan, a jingine da qofa yaga shugaban wajen aikin su da ƴan sanda biyu,wani tsallen bad'ake ya yi zai juya ciki a guje suka ko yi ram da shi, ihu yake yana fad'in,
"Ku yi min rai sharrin talauci ne ya sa na tab'a maku kuɗi amma zan biya ku ba sata nayi ba aro ne, kunga mahaifiyata ita ce ba lafiya na deb'o na ke mata magani dasu."
Ba wanda ya kula shi suka tasa ƙeyar shi gaba suka saka a mota, Iya na kuka shima yana yi, hakuri suka bata dan ba zasu iya yafe masa ba,bayan tafiyar su kuwa Iya ta sha kuka kamar babu gobe, ko ba komai mutum rahama ne, sannan hannun ka baya taɓa rub'ewa ka yanke ka yar in ji bahaushe. Kan dole ta hakura ta yi shiru, ga shi ita bata taɓa ma shiga maƙotan ta ba balle su san da zaman ta su taimaka mata, matar Sahabee duk ta gama sawa an tsani gidan nasu ba mai son su a unguwar kaff, haka Iya ta koma rayuwa ita d'aya da safe ta ja jiki ta yi bara a qofar gida har ta samu na siyan abinci, da yamma ma ta fita qofar gida ta zauna, in duhu ya fara ta ja jiki ta kulle gidan ta ci abinda ta samo ta yi sallah ta shige daki se Kuma wata safiyar.
***************************
Sauran kwana biyu a kai Amarya Eamaan d'akin ta, wasu daga cikin ƙawayen ta da suka yi makaranta a baya tare ne suka shirya dan zuwa bauchi, ciki har da babbar ƙawar ta Aisha,Yayah ma ta samu zuwa bauchi dan kuwa tace wannan karon ba zata yi missing bikin Eamaan ba.
Eamaan tayi wani irin kyau na musamman fatar ta har wani santsi da sheƙi take yi kamar wadda aka wanke da inji, ga wani irin mayen qamshi me kama jiki da take yi, gashin ta kuwa ya sake cika da tsaho kamar wanda ake bawa taki,Eamaan ta maida kayan fruits abincin ta,madarar shanu, zuma,da sauran kayayyaki masu gina jiki,in zata yi wanka sai an saka ruwan lalle a ruwan wankan nata da madarar turare.
Ranar kai amarya kuwa Hafsat Yayah da ƙawayen amarya sun shirya angwaye kawai suke jira dan su rankaya garin kano kai amarya ........
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 27:
Yayun amarya da qawar ta Aysha sun gama shirin su tsaf dan dawowa da amarya garin kano ta dabo tumbin giwa,tafiyar awanni hud'u da minti arba'in ne ta iso da su har qofar gidan su Eamaan d'in, Wanda ta kula da shige da ficen mutane a gidan nasu,har hakan ya tuna mata da lokacin auren ta na fari, a wancan lokacin ma haka aka yi taron mutane sosai a gidan nasu, wannan karon bata zaci zata ga kowa ba duba da yanda auren nata ya zo da Kuma cewar ita fa yanzu bazawara ce ba budurwa ba, wanne taron mutane Kuma za a yi?
Anwar bai san da dawowar su ba, da ace ya sani to fa ba makawa sai ta ganshi a ƙofar gidan nasu,direct d'akin su suka nufa suka yada zango dan huce gajiyar da suka kwaso, sanin cewa amaren na tafe ne ya sa aka tanadar masu abinci da abin sha, Hafsat da ke Jin yunwa ce ta zuba masu ita da Fatee suka fara ci, a can tsakar gidan kuwa cike yake da 'yan biki mata, gaba d'ayan su mamakin taruwar mutane da yawa suka dinga yi, Yaya ce ta katse