Showing 3001 words to 6000 words out of 78127 words

Chapter 2 - BIYAYYA Book Complete Hausa Novels by HAERMERBRAERH.txt

17 Oct 2025

1449

ya kaimu safiyar...mu kwana lafiya sai da safe"

Takalman qafar sa taga ya cire ya d'ale gadon ya janye abin rufar ajikin ta ya kwanta ya rufuda shi shi kaɗai ba tare da ya kula da abinda ya yi ba, a hankali shima yace mata

" Sai da safe,"

Zare ido ta yi a hankali ta furta,

"Anan zaka kwana Daddy?"

'Did she just call me Daddy? Oh my God noo,'

Alhaji Abdullahi ya ayyana hakan a cikin zuciyar shi ya, tashi ya Yi ya juya ya d'an kalle ta sannan ya ce,

"Me kika kira ni da shi?," 

A hankali ta furta,

" Daddy,"

"No pls don't call me Daddy, i am ur husband not ur Daddy, call me with any sweet name.... like honey, sweetheart, baby and so on,"

Sake zare ido ta yi ta kame baki tana mamakin wannan tsoho mai budurwar zuciya, dan haka d'aga masa kai kawai ta yi, dan bata son komai ya yi nisa a tsakanin su, ledar dake hannun ta ya Karb'a ya jawo ta jikin shi ya zaunar zumbur ta yi ta miqe ya hannu ya sake maida ita jikin shi yace,

" Ammaan ki da Daddyn ki basu ce maki banda yima miji musu ko gardama ba?"

D'aga masa kai tayi, alamar sun fada mata banda yi wa miji gardama,sai Alhaji yace da Eamaan,

"Oya zauna na baki abinci naji qarar da cikin ki ke yi irin na masu jin yunwa, ni gidana bana son ana zama da yunwa kin gane?,"

Sake  d'aga kai ta yi bakin ta na rawa jikin ta ma nayi, a baki ya dinga bata kazar tana ci da kyar a haka ya ciyar da ita ta qoshi ya bata fresh milk, sannan ta miqe taje ta yi brush ta dawo, shima hannun shi ya wanko ya koma gado ya kwanta, can qarshe taje ta takure saboda bata yi zaton zai kwana anan ba duba da cewa akwai wasu d'akunan a sashen nata, murmushi ya yi daya ga tayi haka, sai ya hau gadon ya jawo ta jikin shi yace,

"Ba abinda zan yi miki bacci zamu yi,dan d'azu dana d'auke ki sai naji alamar baki sallah ko?"

D'aga kai ta yi da sauri, dariya yayi mara sauti yace,

" To yanzu yaushe zaki gama?"

  Nuni ta mai da hannu alamar kwana biyar,

" OK ba damuwa Allah ya kaimu, mu yi bacci kenan yanzu ba? naga kin gaji kema,"

Nan ma d'aga masa kai ta yi kawai, gani ta yi kawai ya rufe ido zai bacci ba addu'a ,se ta miqe ta fara addu'a a tafin hannun ta, tana gamawa ta fara shafawa, binta ya yi da kallon sha'awa dan gaba daya yanda take shafawar ya tafi da shi, ita kuma sam bada niyyar tada Masa sha'awa take yi ba,

"Ni ma ko zaki min addu'ar ne,"

'Daga masa kai ta Yi ta fara karantowa , tana gamawa ta hura masa iskar bakin ta,

Cike da kasala ya ce

" A'a ni kenan ba za a shafa min ba?"

Kauda kai ta Yi cike da kunya ta koma makwancin da taiwa kan ta ta rufa, murmushi ya yi, ya matsa jikin ta ya ja ta na shi ya rungume ta yace,

"Haka zamuna bacci bana son kina nisa dani kin ji ko?,"

D'aga kai ta yi cike da tsoro a ran ta sai wurga ido take yi kamar mara gaskiya, ga bacci tana ji gashi kuma ta kasa yi, hawaye ne ke zuba mata daga idanun ta zuwa kuncin ta, yana jin haka ya sake ta ya juya baya dan ya kula ya takura ta da yawa, yana juyawa ta sa pillo tsakanin su ta koma can qarshen gadon ta takure kanta, da jin haka sai Alhaji ya yi murmushi, a haka suka kwanta har bacci ya ɗauke su.

Qarfe 3:30am nayi ta farka tai addu'ar tashi daga bacci, kallon shi ta yi ta ganshi shame-shame yana ta kwasar bacci,miqewa ta yi taje tai alwala ta fara karanta qur'ani da ka saboda mahaddaciya ce ita, daga qarshe ta kai kukan ta wajen Allah, lokacin sallar subh nayi ta kalle shi duk kiran sallar da ake a masallacin gidan bata ga ya motsa ba sam, sai da aka idar ne ma taga yai wani juyi tare da munshari ya qara jan bargo abun shi, tana so ta tada shi dan ya yi sallah amma tana tsoro, a haka tai shahada taje ta tada shi,ai kuwa haka ya juyo fuskar nan kamar jar wuta babu walwala a cikin ta,ita kuwa gata tsaye zulum a hijab, cikin wata iriyar murya yace mata,

" Ko dayake ke baquwa ce a gidannan baki san qa'idoji na da dokoki na ba,amma idan ina bacci ba a tada ni daga yau ki sani kuma ki kiyaye,"

Juyawa zai ya kwanta yaji tace masa,

" Wayyo ban sani ba ka yi hakuri inshaa Allahu zan kiyaye, wai dama na jiye maka tsoron fitar lokaci ne, tinda Allah yace azaba ta tabbata ga waɗanda basa sallah akan lokaci, naga in kai sallar zaka iya kwanciyar ka ka huta,amma tinda haka ne zan kiyaye daga yau,"

Duk bayanan da take yi masa sun dira a kunne da zuciyar shi, tsaki yaja ya miqe tsaye ya shige toilet,saida yai brush sannan ya yi alwala ya fito, Sallah ya tada ya burbura ta ya sallame ya haye gado ya koma baccin shi, mamaki ne fal cikin ta, dama haka masu kuɗi suke ko dai shi ke hakan?

Kafin ya tashi da safe ta yi wanka gudu-gudu sauri -sauri a ɗayan d'akin, dan bata son ya tadda ita tana wanka, tana gamawa sai ta sanya sabbin kayan da ta tafi da su d'akin, ta yi kwalliya sassauqa mai kyau, sannan ta koma d'akin nasu ,zaune ta tadda shi ya dafe kai yana murzawa a hankali,durqusawa ta yi ta gaida shi, ya amsa cikin ɗan sakin fuska, kallo ya bita da shi kamar zau had'iye ta, dan kuwa ba qaramin sha'awar yarinyar yake ba, dalilin da ya sa ya aure ta kenan, ba wai dan yana son ta ba, a hankali ya miqe ya shiga toilet yana saqa abubuwa da dama akan ta, wanka shima ya yi ya shirya sannan ya kama hannun ta suka fita dan zuwa sashen mahaifiyar shi, tana ganin sunyi hanyar waje tace,

"Bari na d'akko hijab,"

kallo ya bita da shi, sannan yace

"A cikin gidan ma sai kin saka hijab?"

"Dama naga kamar sai munbi ta wajen masu aiki ne, kar na haɗu da wani daga cikin masu aikin ba mayafi jikina kuma shi yasa,"

kad'a kai ya yi ya jingine yana jiran ta, koda ta dawo sai ya bita da kallo,dan kuwa da ta saka hijab din ma ba qaramin kyau yaga ta qara yiba a idon shi,

"Lallai Eamaan komai naki mai kyau ne,"

Murmushi ta yi tace Masa

" Na gode,"

Hajiya A'i dake tsaye jikin window ce ta hango su suna murmushi sai taji zuciyar ta kamar ta fito waje saboda kishi,

"Dubi dan Allah dan tsabar ya siya  mana raini ya rasa wadda zai auro sai d'iyar cikin mu,hmmm ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta, dan wannan irin su auren kuɗi ke kawo su, Allah ka azurtani da tsayyen d'an da nima za a dama da ni a cikin gidan nan,"

Sakin labulen ta yi taje d'aki ta saka d'ankwali, dan ita ba mace ce mai son d'aura d'ankwali ba a koda yaushe,tana gamawa sai ta fito tana takun qasaita, a babban parlour ta tadda Hajiya Rabi da yaran ta Sabeerah da Ilham suna ta shagwab'a a jikin Daddyn su, Eamaan ce ta shafa kan Ilham tace,

"Meye sunan ki?"

Tana mata murmushin dake nuna tsananin shiga ranta da yaran suka yi,Ilham tace,

" Suna na Ilham, amma Sabeerah na kirana da Elly, ni kuma ina kiran ta Saby,"

murmushi ta yi tace,

"Oh kenan wannan itace Sabeerah? Can i call u saby ?"

" Yeh u can, and let me tell you u a scret,"

Sai ta kai bakin ta dai-dai kunnen Eamaan tace mata,

" I like u, don't tell anyone,"

D'aga mata kai Eamaan ta yi cike da jin dariya,itama ta kai bakin ta kunnen Sabeeran tace mata,

"I like u too, u ar beautiful Maa shaa Allah,"

wani fari ta yi sosai tai tsallen murna, Daddyn su da Hajiya Rabi ba qaramin burge su Eamaan tai ba, Ilham ce ta b'ata rai,Eamaan na ganin haka sai ta kama hannun ta tace,

" Elly me ya faru,"

"Ba ku bane kuke gulmata,"

Daddyn ne ya fara dariya sannan Hajiya Rabi,

"Ba qulmar ki muka yi ba zo kiji wata magana kema,"

sanar da ita tai itama tana son ta, yaran sukai ta murna, suka rungume ta .

" Mtsssss aikin banza da asubar fari za a cika ma na kunnuwa, sai kace ku kad'ai ne yara a unguwar nan,"

"A'a fa Hajiya Babba, ba zai yu kawai ke baki so yarana ba Allah ya kawo mai son su kuma suma suna son ta ki zo ki kina qananan maganganun da kika saba, "

Habaaa ai akamar Jira Hajiya Babba take yi sai suka kacame da zage-zage sukai ta faɗa da junan su,nan da nan idon Eamaan ya kawo hawaye dan kuwa ita bata saba ganin wannan ba a gidan su, dik da cewa kuwa itama gidan su mata biyu ne.

"To kaji kun fara ko? kut kut kut kut, ga hatsi to kuzo ku tsattsaga, jarababbu, baku da aiki sai jaraba akan miji da 'ya'ya, ke wani ya hana ki yi  cikin ki haifi naki? Ke kuma da kike jaraba akan yara naga dai yaran ba naki bane ke ɗaya, da anyi magana sai iko akan yara, wannan kuma yar afiruwar wace ce ita take zaune kuturinta dana Audu waje  d'aya?"

Hajiya Iya kenan wato mahaifiyar Alhaji Abdullahi ke wannan maganganun tana kanne idanu tana nuni da yatsun ta da suka sha jan lalle irin na tsofaffi.......

*Iya jaraba kamar yanda Su Saby ke kiran ta ta fito fa*😱
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼  BIYAYYAH  💅🏼








  RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH







Page 3:






Cike da ladabi Eamaan ta zube a gaban Iya sannan ta ce,

" Barka da safiya Iya,"

Cikin isa da ɗauke kai ta amsa da,

" Lafiya ! baku ban amsa ta ba ai kan a kai ga gaishe-gaishen,"

Alhaji ne ya duqar da kai cike da biyayya yace,

" Iya amarya ta ce mai suna Eamaan, jiya ban shigo gida ba sai wajen 12am, shiyasa ban kawo maku ita ba ta gaishe ku,sannan nayi zaton ko dangin ta da suka kawo ta jiya sun kawo maki ita ta gaishe ki,"

" Eh sun kai ta, amma ai a qunshe ta ke waya gan ta? Miqe ka zauna abun ka,"

Miqewa yayi ya zauna kowa ya yi shiru,amma Hajiya A'i da Hajiya Rabi sai harare-hararen juna suke yi, Ilham ce ta gaida kakar tasu, cike da fara'a ta amsa mata, sannan Sabeerah ta gaida ta itama, amsawa tai sannan tace,

"Shin yau babu mai bamu abinci ne a gidan sai mun roqa?"

Kallon kallo suka fara yi a tsakanin su domin kowaccen su tana qyashin ace ita ce zatai directing masu aiki suyi girki bayan mijin na wajen amaryar shi, Hajiya Qarama ce wato Hajiya Rabi ta miqe ta fice hanyar da zata sada mutum da kitchen ɗin gidan,ma'aikata sun yi abinci kala-kala suna jira a kitchen ɗin suna zazzaune suna jiran me zai je ya zo tinda ba a basu umarnin kaiwa ba, tsoron masifar Iya kuma ya sa sun kasa yi wa kowa magana, a tsaye cirko-cirko kamar wasu zakaru ta iske su, dan kusan suna jiyo tashin muryar ta koda basu fahimtar komai sin san masifar take saukewa, umarnin kawo abubuwan da suka dafa ta yi masu, suka ko biyo bayan ta da abincin kala-kala suka ajiye suka yi waje, a qaton carpet d'in  da suke haɗuwa kowa yaci abincin  suka baje, dan Iya bata son hawa dining table,dan haka dole kowa nan qaa zai zube in dai tare za a ci da ita, kowa na zaune yana kwasar girki banzda Eamaan, jita take yi duk a takure,saboda bata saba da su ba,Iyace ta kalle ta a yatsine cikin masifa tace,

" Malama idan za kici abinci ki kama ki ci,kina wani sunne kai kamar ta kwarai,"

Cike da jin tsoron Iya ta fara cin abincin, Alhaji kuma sai ya ji tausayin ta ya kama shi saboda ba haka ya san jikin ta ba duk ta rame, sai ya ji kamar ya bata a baki, gaba ɗaya ya kula a tsorace take da Iyan tashi, a haka aka ci aka gama, kowa ya tashi ya nufi sashen shi masu aiki suka ɗauke komai suka gyara wajen.

A hanyar su ta komawa sashen nata ne Alhaji ya kula da damuwar da ke tattare da Eamaan din, kafin ya gama nazarin ta ya ji ta na yi masa tambaya cike da damuwa.

" Alhaji kullum a babban parlor zamu dinga cin abinci?"

" A'a na yau ne kawai dama ina so ne na haɗa ki da sauran abokan zaman ki ku ga juna, to na zata Iya zata yi mana nasiha ne, amma na ga yau faɗan ta kamar yafi na kullum zan je na ji me ke damun ta yau ɗin, sannan kuma zamu haɗu a bangaren Hajiya Babba mu yi magana zuwa Wani lokacin,"

D'aga masa kai ta yi alamar gamsuwa da bayanan shi ,dan kuwa bata fatan sake zuwa wajen wannan tsohuwa mai faɗan tsiya.

Suna shiga d'aki ta cire hijabin ta ta ninke shi ta zauna waje d'aya a gefen gadon ta, kallo ya bita da shi yaga kamar har wannan lokacin a tsorace take, jan ta ya yi jikin shi ya fara lallashin ta,yanayin yanda yake yi mata ne ya sanya ta mamakin shi, da alama dai Alhaji baya tunawa da shekarun shi idan yana wasu abubuwan, luf ta yi a jikin shi tana zubar da hawaye a hankali dan bata son ya gane kuka take yi,sai kawai ta ja baya ta gyara kwanciyar ta kamar wadda ke yin bacci, murmushi ya yi dan a zaton shi wasannin da yayi mata ne suka sa mata kasala har ta yi bacci, miqewa ya yi yaje ya yi wanka ya fito tare da sanya kaya masu kyau, sannan ya dauki key na motar shi ya fice ya bar gidan dan zuwa wajen shaqatawar shi, wanda da fari ya zaci zai iya hakuri da ci gaba da neman matan banza, amma zuwan Eamaan da lamarin da ta zo da shi na baƙon wata na mata ba zai iya jurewa har ya jira ta gama ba,tana kallon shi ya gama duk abinda zai yi amma bata motsa ba, sai da ya fita ne taje ta rufe qofar ta jingina da murfin qofar ta hau kuka da qarfi, tabbas bata qaunar bawan Allah'n nan, gaba daya ba sa'an yin rayuwar auren ta bane, a ganin ta ko da cikin tsarki take yazo mata ai ganin shi zata yi kamar Daddyn ta, babban mutum haka ya dinga sauke buqatar shi akan ta da qananun shekarun ta? kaiii akwai takura sosai da jin nauyi gaskiya.

A haka tana kuka taje toilet dan ta gyara jikin ta, yatsina fuska ta yi ta cire rigar ta ta aje ta a cikin washing machine ta kunna ya shiga wankewa, saida ta gama wanka sannan ta fita ta shirya cikin shadda mai matuqar kyau kalar purple aikin jiki an yi shi da pink ɗin zare,ba qaramin kyau ta yi ba a cikin kayan,tirare gidan tai da tiraran wuta, sannann ta samu waje ta hau rera karatun qur'ani idanun ta lumshe, ta windown parlourn taji kamar ana motsi, aikuwa sai ta miqe a tsorace sannan bata daina karatun da take yi ba, tana leqawa bayan ta kai qarshen aya ta ce

"Waye a nan,"

Juyawa su ka yi za su gudu, a dai-dai lokacin Eamaan ta leqa taga ashe yaran ne, ajiyar zuciya ta sauke da qarfi sannan ta kira su ciki, a hankali suka je kamar masu jin tsoron ta, buɗe masu qoqafar ta yi suka shiga ciki suka tsaya suna jiran su ji ko zata yi musu faɗa.

Ba tare da sun san cewa Eamaan taji dad'in zuwan su ba suka hau bata hakuri,ita kuwa murmushi tayi dan dama a cikin kaɗaici take, nan da nan ta rungume su ta hau yi musu wasa har suka saki jikin su da ita.

Kafin minti goma sun sake da ita sosai sai wasa suke yi abun su, kan su ta kalla taga gaba ɗaya ya tsufa har tsagar ta haɗe waje ɗaya baka banbancewa tsakanin kitso da tsaga,ga gashi har gashi amma duk a cukurkude yake, kayan su ta cire masu ta wanke masu kan su tass, ta samu bands ɗin ta da take amfani da shi ta gyara masu kan bayan ta yi drying gashin ta yi oiling ɗin shi yana sheqi,kan su ya yi matuqar yin kyau sai sheqi yake yi, cike da murna suka kwasa suka yi wajen maman su dan su nuna mata,a lokacin kuwa Iya tana wajen tana zazzaga mata masifa akan ita zata kula da abinci har Alhaji ya gama angwanci ya raba masu kwana, ranta a haɗe sai qunquni take yi suka shiga,Iya ce tace,

"In kika zagen kin zagi ta gida 'yar nema kawai masu abun kunya, gaku nan rid'a-rid'an mata amma kuna zaune miji na neman matan banza a waje, ga shinan ai kun ja an kawo maku yar cikin ku se ku zauna ku yi ta goga kishin da ita,"

" A'a fa Iya kar ki ɗora mana laifin da ba namu ba ah toh,neman matan shi ba laifin mu bane tinda ba mu muka haife shi ba balle mu bashi tarbiyya,"

Ta fada tana murguda baki,

" Iyyee to me kike nufi tijararriya? Wato ni ce ban bashi tarbiyya ba ko? To a cikin tarbiyyar dana ba shi ne lokacin har ake cewa na yi mai auren wuri, ganin yana bin matan kar ya lalace da yawa ne ya sa na yi masa auren, amma aka kawo ku aka zuba gaku nan kun zama kamar hoto a gidan, shashashai kawai, ita waccan ta yi wani d'irim da ita da anyi magana ta ce ita tayi ta gaji ba zata kashe kan ta ba, amma ai bata gaji da tatse masa arziqi ba ko? Ke kuma da na ke gani a waye kike ashe kallon kitse nake wa ro,......"  Yaran ne suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login