Showing 63001 words to 66000 words out of 78127 words
Chapter 22 - BIYAYYA Book Complete Hausa Novels by HAERMERBRAERH.txt
ta ce,
"Wai ke albishir aka maki da makka ne kk ta murmushi haka? Kin ma qi taba abincin ki a bakin ki sai juya cokali kk, meke faruwa ban San da shi ba, ban labari na sha dear sis,"
Murmushin ta ne ya fad'ad'a,
"Ban san me ke damuna ba Hafsy, kawai ji na nake ina cike da nishadi, tinda na sa qafa na sauka a gado, da farko dai daren jiya cikin damuwar wani abun da ban san meye ba na kwana, amma yanzu zuciyata cike take da farin ciki kamar ance an mallaka min Anwar,"
Ta qarasa tare da dafe bakin ta lokacin da ta ji qarar takalmin Kamal na zuwa wajen su, qara gyara mayafin ta ta yi ta rufe jikin ta sosai, tana murmushi,
"Kin ji da gulmar ki an jima shi zaki ta yi wa wannan rashin kunyar taki ai,"
"Albishirin ku, ko dake Eamaan albishir, me zaki ban inna fad'a maki wannan kyakkyawan labarin,"
Zaro ido ta yi waje cikin wata iriyar murna kamar ta san me zai ce mata,
" Yah Kamal sai abinda kk so zan baka,"
" kin tabbata?"
" Eh na tabbata,"
"Ok dazu da misalin sha d'aya aka daura auren Anwar da Eamaannnnnn"
Ya qarasa maganar shi cikin d'aga murya yana farin ciki,sai kama hannun Hafsat yana juya ta yana kallon Eamaan suna dariya, Idon ta ya cika da hawaye murmushi ɗauke a fuskar ta,daga baya kawai se suka ga ta fashe da kuka ta miƙe zata bar wajen..........
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH. 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 25:
Kukan murna Eamaan ta yi sosai kan ta ɗago da idanun ta da suka sauya kala daga farare tas zuwa launin ja, haqoran ta farare wanda suke a jere ɗauke da siririyar hushirya sai haskawa suke, Hafsat da ta matsa kusa da ita tana shafa bayan ta da sigar lallashi ta kalla, itama murmushin ta sakar mata Fatee kuwa na ta kallon ta da mamakin dalilin kukan nata, Eamaan ce ta ce,
" Yah kamal me kake so a matsayin goron albishir d'in da ka min yanzu?"
" Ba abinda nake so illa kafin nan kafin ki tafi ki koya ma Hafsat duk girke-girke da kike yi mana masu dad'i, sannan kuma a bar mana Fatee har tsawon lokacin da kuka gama cin amarcin ku sannan ku karɓe ta, ke in ma Anwar ba zai d'auke ta ba ni nayi tayin riqe Fateema har abada a matsayin ta ƴata"
Farin ciki ne ya qara sanya ta kuka sosai mai cike da murmushi, lallai Yah Kamal na son Hafsat sosai, dan ta kula yana taya Hafsat son duk abin da take so, ko baya son abun nan indai ta na so to fa Shima abun nan ya zama abin son shi,lokuta da dama shi da Eamaan sukan zauna su yi ta gulmar Hafsat d'in, su Kan yi magana da Eamaan akan shi fa baya son kaza a da amma tinda ya kula Hafsat na so ya ji ya fara son abun.
" Yah Kamal kome kake so zan yi maka,kai daga yau ma zan fara inshaa Allah, game da Fatee kuma shi fa Anwar cewa ya yi da ita za mu tare duk sanda Allah ya sa muka yi aure, amma dole zan lallab'a shi mu barta ko wata biyu muka yi an maida ta yanda dai ya amince,"
Kamal ne ya kalli Hafsat da farin ciki ya bayyana a fuskar ta ya matsa jikin ta ya dora kan ta a gefen jikin shi dan itan tana zaune a hannun kujera ne kusa da Eamaan da ke kukan farin ciki sannan yayi kissing goshin ta, a tare suka yiwa Eamaan godiya tare da fatan Allah yasa Anwar ya bar musu Fateema su riƙe ta na tsawon lokaci.
**************************
Anwar na qara murmurewa ya sa aka je gidan shi sabo aka gyara shi fes, dan ba abinda bai zuba ba na more rayuwa dai-dai qarfin shi, komai yayi masa yanda yake son shi, gidan na ɗauke da d'aki hud'u ne sai palour biyu, dinning area ɗaya, kowanne d'aki da toilet ɗin shi, sai Kuma toilet guda d'aya a harabar gidan, gidan ya na da farfajiya mai girman da zata Iya d'aukan a qalla mota uku, a can bayan gidan Kuma ya yi dan garden me d'auke da kayan wasa na yara wanda manya ma zasu iya hawa lillunan wajen, gidan yayi matuƙar haɗuwa gwanin sha'awa,yana tafe ya na kallon yanda aka tsara gidan ne ya ji qarar saqo a wayar shi, daya duba sai yaga No Kamal ne ta turo mai wata Number waya a qasa an rubuta *Ur sweetheart No* wani dad'i ne ya kama shi, dan dama yana son ya aika kuɗi yace kamal ya sai mata waya mai kyau amma da alama Kamal d'in ya riga shi, shi kuwa me zai yi ya biya Kamal kyautatawar da yake yi masa, saving ya yi da 'My one' ai ko yana gamawa ya shiga ɗaya daga cikin palourn ya qame a kujera ya danna kiran layin na ta, Eamaan na can na ta faman koyawa Hafsat girki ta ji wayar ta na ringing wanke hannun ta tayi ta d'aga tare da yin sallama a zuciyar ta tana mamakin waye wannan da ya samu No ta sabuwa haka? Iya sanin ta ba kowa ne yasan tana da waya ba.
Ajiyar zuciyar da ya sauke ne da ƙarfi ya sanya ta dafe jikin cabinet na kitchen ɗin ta jingina dashi tana murmushi mai sauti, Hafsat na ganin haka ta daki kafadar ta ta ce,
"Sarakan soyayya bari na kwab'a na yau na tara a gaba, na San yanzu ko wuqa zan caka maki ba ji Zaki yi ba,"
Fita ta yi ma daga kitchen d'in kwatakwata ta tafi d'aki ta kwanta a gado ta mimmiqe ta na sauraron muryar Anwar d'in da ke ratsa dik wata kafa ta jikin ta.
"Kin san me?"
" A'a sai ka fada"
" Ina gidan mu yanzu haka,inda zamu zauna ni da ke da Fateema nake nufi,ina kan doguwar kujera a kwance nace bari na kira ki naji muryar ki,yanzu iwar haka inshaa Allah wani satin kina gefe na a kwance muna hira ko?"
Cike da jin kunya kamar yana ganin ta ta rufe idon ta,
" Kaii Daddan Fatee, ni dai ba ruwa na, babyn ka na jin ka, gata a kwance tana bacci"
Dariya ya yi dan ya san wayon ta,gani yake kamar kunyar ta tama qaru ne akan tada da take budurwa, anya zasu sha amarcin da yake hango masu kuwa da wannan kunyar tata?
"Ita ma Fateeman ai ta shaida Daddyn ta na son Mummyn ta sosai, dan in ba ita ba zai iya rayuwa ba, sauran qiris na mutu Abbana ya taimaka ya yi ma Daddyn ku magana aka daura auren mu,"
Nan ya kwashe komai ya sanar da ita har halin da suke ciki shi da Hajiyan shi,
" Allah ya qara maka lafiya Daddan Fatee, amma gaskiya banji dad'in yanda ka yi wa Hajiya magana ba, waya faɗa maka ana jayayya da iyaye ta yanda ka yi? Ko kuma kai fushi da su? Kar ka manta fa dik BIYAYYAHr da na yi wa iyaye na Kai ne sila, tarbiyyar da ka dinga d'ora ni a Kai ta yin BIYAYYAH wa iyaye ita ta Kai ni ga auren Alhaji, gashi yanzu alhamdulillah naga ribar BIYAYYAH Anwar, ko kasan sanadin BIYAYYAH ne yanzu zamu yi aure? So kake in mun samu yara muma in mun musu fada suna fushi da mu? idan baka son haka ta kasance damu ka baiwa Hajya hakuri ka daina mata yanda kake yi mata kaji nawan,"
duk abinda take fada yana yi yana bata amsa da A'a da eh ne tare da d'aga kai kamar tana ganin shi,
"Inshaa Allah yanzu dana koma zan bata hakuri na gode sosai, kuma ki fara shiri nan da sati zaki tare, me kike gani zamu yi na bikin, dinner ko walima?"
"Ni gaskiya bana son yin wani bidi'a na fi son auren mu ya yi albarka,domin kuwa auren da aka yi cikin ƙanƙanin kashe kuɗi yafi albarka,sannan auren da ba a sab'awa Allah ba wajen nuna murna Shima ya fi albarka, dinner din yanzu da ake Banda nuna tsiraicin amarya, se rashin kunya da fitsara da ake yi, ga kad'e-,kad'e na mutanen da ba addinin mu d'aya da su ba, ga Raye-Raye da zaka ga mata da maza ana yi, dan haka mu yi walima a cikin gida kawai, yan uwan mu da abokan arziqi su hadu aci a sha kowa ya sa mana albarka shikenan, ko ya kace?"
Yaji daɗin maganganun ta sosai dan ta nuna mai tana aiki da ilimi, shiko zai bata mamaki wajen sata ta ji dad'i a rayuwar ta,
"Shikenan yanda kk ce haka za ai gimbiya ta, jibi ina hanya,"
"Ko kazo ba zaka ganni ba,dan kuwa ba zan fito ba, sai sanda aka kaini za ka ganni,"
Yana kwance ya d'ago ya zaro ido,
" lallai da kin azabtar da mu kuwa, habaa ke kuwa kar mu yi haka da ke manaaa,"
Dariya ta yi ta masa ta jaddada masa ba fa zai gan ta ba,haka ya hakura yace to kuwa ba zai dawo ba, har sai an kai masa ita, haka suka yi ta soyayyar su ta waya, suka ci gaba da tsara yanda zasu yi zaman su in Allah ya kaisu ranar da zasu kammala mallakar junan su.
Amarya ta sha gyara sosai, da kan ta take gyararrakin jikin ta, wanda da dama da kayan da muke dasu ne na cikin gida take amfani dasu irin su fruits, madara, baking soda, da sugar gishiri da sauran su( ku duba novel dina na baya 'YAN ABUJA, WATA UWAR,DA KAINE JARUMI, 'YAR RAWA zaku samu kayan gyaran jiki inshaa Allah, ko kuma ku sayi littafin MAIDA TSOHUWA YARINYA za ku ga yanda ake gyaran jiki da natural abubuwan da muke dasu a tare damu 09031416423)
Eamaan ta yi kyau sosai, ba kad'an ba, Kamal kullum sai ya tsokani Anwar ta waya akan irin kyan da yaga Eamaan tayi, shi kuma ya yi ta jin kamar ya yi tsunstu ya zo ya ɗauke ta, wataran in ya ji yabon ya yi yawa, yakan ce masa,
"Malam she is my wife oo,ya kamata a dena kallon ta da yawa haka,"
Kamal ya kan yi dariya sosai sannan sai ya bashi amsa da
"Ni da nake da Hafsat me zan da Eamaan?"
Anwar da kamal sun zama manyan abokai fiye da yanda sukw a baya,a dik sanda Anwar zai ga kiran kamal to fa zai ɗauka cikin sauri da gaggawa dan yaji yanda Eamaan ɗin shi take.
*************************
Wanka Sahabee da amaryar shi suka fito a tare, daure take da towel iya guiwa duk qafar ta da tasha man bleaching ta yi kala biyu nan baqi can fari, sai gwaguis ɗin gashin ta da ya sha relaxer qeyar duk ta cinye, sai kad'a jikin ta da yake a sake shakaf take faman yi ita a dole ga wayayyiya ƴar bariki, sai buɗe gajeren hancin ta mai faɗi take yi kamar salansar babur.
Amaryar Sahabee ba kyakkyawa bace, sannan ba za a kira ta da mummuna ba a tashin farko,shi kuwa a wajen shi babu macen da ta kai ta kyau a idanun shi dan haka duƙawa yayi ya dakko bokitin wankan da kwandon wanka ya biyo bayan ta, Iya na ciki bata San ma sun shiga wanka tare ba, zafi dik ya ishe ta ga warin kashin kaji be gama sakin d'akin ba,dan haka sai kawai ta ɗauko tabarma da matashin Kai ta fito ta shinfida a tsakar gidan dan ta shaƙi iskar ƴanci.
Tafe suke Amarya na gaba angon ta na biye da ita riqe da bokoti da kwandon wanka a hannu,tana ganin Iya a tsakar gidan kwance sai ta koma da baya ta rungumo shi tana wani shafa qirjin shi, Iya da ke kwance ce miƙe zaune ta hau tari babu qaqqautawa, amarya kuwa ƙin sakin Sahabee tayi dik da ƙoƙarin da yake na son zuwa wajen Iya,cikin takaici Amarya tace,
"Baby meye haka kuma ina zaka je? Ko kana nufin ba zata yi tari ba saboda gata yayi mata yawa? Wuce mu je ka shafa min mai ni kar na bushe."
Gaba suka yi abin su suna shiga ta ɗakko mai ta bashi ya shafa mata sannan ya sanya mata kaya, daga karshe sai ta hau yi masa magana cike da kirsa da shagwab'a tana faɗin taso yin wanki gashi ta yi wanka bata so ta b'ata jikin ta,
"Kar ki damu zan wanke maki mene a ciki, ai duk a cikin soyayya ne,"
Tulo masa kayan ta masu datti ta yi dan tinda aka yi auren su ko tsinke bata taɓa wankewa ba,dan haka kayan wanki gare ta masu yawa, aiko ya na ganin su ya zaro ido yana ayyana anya wannan ba tin daga gidan su tazo masa da masu datti ba? Kan dole babu yanda zai yi ya d'ebi kayan ya je yayi ta wankew.
Ita kuwa zaman yin kwalliya tayi a d'akin ,bayan ta gama ta fita tsakar gidan ta dasa kujera ta zauna a gefen shi tana yi masa fari da sun haɗa ido,hannun ta riƙe da mafici tana firfita fuskar ta da ta dame da powder da zufa, data ga alamar ya gaji zata zaro zancen batsa ta watsa masa,nan da nan zai qara qaim wajen yin wankin yana washe baki,Iya da ta ga abun na neman fin ƙarfin ta sai ta tattare shimfidar ta koma ɗakin ta,tana shiga d'akin ta zauna a bakin katifa tai ta kukan baƙin ciki da dana-sanin rashin tarbiyyar da bata baiwa yaran ta ba musamman sahabee, nan take zuciyar ta ta tuno mata Eamaan baiwar Allah da irin muzgunawar da ta dinga yi mata dik tsananin biyayyar da ta dinga yi mata.
A ɓangaren amarya Eamaan kuwa........
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 26:
A hankali Amarya ta maida Sahabee tamkar wani bawan ta, domin kuwa dik wani aiki da ya kamata a ce itace take yin shi sai ta mayar masa da shi aikin shi,shine shara, wanke-wanke,girki, d'iban ruwa da wankin kayan su,a dik sanda yayi girki taci taji bai yi mata daɗi ba yanda take so sai ta sa shi ya siyo a waje.
Yana matuƙar wahala wata yazo ya wuce bata je biki ba, babban abinda yafi ƙayatar da ita a zuwa biki shine ɗinka anko,wannan shine babban dalilin da yasa ta ƙware wajen yawan roqon kud'i,abinda dik ya bata da shi zata sayi anko tayi ɗinki idan ya ragu ta kaiwa bokan ta ya qara kafe mata shi ta yanda sai abinda tace yayi kawai zai yi, dik kuma abinda bata so to fa bai isa ya aikata shi ba.
Wajen shaye-shayen magungunan mata kuwa an bata lambar yabo dan kuwa ƙwararriya ce a wannan fannin tinda ta gama gano lagon sa,indai zai samu biyan buƙatarsa to fa komai zata yi masa baya gani,kan kuce me Sahabee ya tashi daga d'an gaye ya koma Wani iri da shi kamar d'an aikin gidan dama can shi ba me kaurin jiki bane se ya sake jemewa ya rame sai uban tsawo kamar igiya,gaba ɗaya ya zama wani abin tausayi da shi.
Tsakanin uwa da ɗa sai Allah,ganin halin da ya shiga ne ya sanya ciwon Iya yake yawan tashi, Sahabee bai ma san tana yi ba balle ya sai mata magani, watarana har kasa tashi take yi ta fita koda yin alwala ne.
Idan abun ya yawaita ne yaga be ga gilmawar ta ba na kwanaki sai ya ɗaga labule daga bakin ƙofa zai yi mata sannu sannan ya kama gaban shi ya shiga sabgogin shi kamar bai ga halin da take ciki ba,matar shi kuwa sai suyi kwanaki bata leqa ta ba balle ta duba ya jikin ta yake, lokacin da ta ga damar gaishe ta kuwa to daga bakin qofa take d'age dan buhun labulen itama ta ce mata sannu ta yi gaba abunta,a cewar ta ai uwar miji ba uwar ta bace.
Babban abinda yafi baƙantawa Iya rai bai wuce yanda matar nan zata kalli idanun Iya ta dinga kiran ta da ƙazama wadda bata share ɗakin ta balle tayi wanka taji dad'in jikin ta,Iya ta yi nadamar abubuwan data dinga yiwa Eamaan a baya, gefe ɗaya kuma ta yi nadamar yanda ta dinga yiwa Alhaji Abdullah da yake tsananin tausaya mata da taimaka mata tare da yi mata ladabi da BIYAYYAH,a kullum ba shi da burin da ya wuce na ya ganta cikin walwala da farin ciki, duk dan kar ran ta ya baci da girman shi haka zata sa shi a gaba da fad'a kamar yaro qarami, ga masu aiki wajen uku ya zuba mata ita kaɗai a sashen ta dan su kula da dikkan buƙatun ta, amma dik da haka ta takurawa matar shi mai tsananin BIYAYYAH dik da cewa ba auren soyayya suka yi ba, idan tace masu abu fari ne komai baqin shi basa yi mata musa haka zasu yarda da abinda tace ɗin.kuka shine ya dawo abincin Iya Kuma ya zamto abin Shanta.
Idan ana girki a gidan haka hayaƙin zai shiga ta ɗan ƙaramin windown nata tai ta tari tana neman iskar shaƙa mai kyau, dik randa tayi gigin fita dan ta shaƙi iska amaryar sahabee sai ta nuna mata bariki ta hau taɓa shi a gaban idanun ta shi kuwa yana biye mata,tsananin da Iya ke ciki yayi tsanani har ya kai ga yanzu bata gani sosai saboda hawan jini da yayi mata yawa da kuma hayaƙi dake addabar ta kullum.
Muryar Amaryar Sahabee ke tashi kamar wata gardi a cikin gidan cikin ɓacin rai take magana.
" Yanzu honey kana nufin bashin da na ciwo saboda ankon bikin qawata ba za ka samu biya ba? kai fa ka yi min alqawari kafin auren mu ba zan tab'a neman abu na rasa ba kace min babu ni babu wahala aikin gida da komai ba nawa bane naka ne, sannan ka jaddada min kar na damu da maganar kud'i ko nawa ne baka da matsala akan su zaka dinga bani,ni ba ma abinda ya fi min ciwo ma sama da alqawarin zama a qaton gida bayan d'aura mana aure sai na ga an kawo ni nan, hakuri kawai na yi na rufa Maka asiri wajen dangi na da qawaye