Showing 54001 words to 57000 words out of 78127 words

Chapter 19 - BIYAYYA Book Complete Hausa Novels by HAERMERBRAERH.txt

17 Oct 2025

1460

fara'a a fuskar su, dan suna matuqar son Anwar sosai,Anwar  akwai mutunci ga kamala, da kyautata wa, yana yawan zuwa wajen siyan abincin shi da na Mai gadin gidan shi da Mai masa share share, in ya zo su na Shan hira kala-kala kan ya tafi,hirar siyasa ne ta ilimi ne da kuma hira akan yanda samari da 'yammata ke gudanar da soyayya a wannan zamanin saboda kasancewar wajen wajen saida kayan kwalam suna ganin abubuwa kala-kala dake faruwa.

Tin da yake zuwa wajen basu tab'a ganin ya je da budurwa ba, ko Kuma su ga ya tsayar da budurwa a wajen, dik da cewa waje ne da matasa maza da mata ke zuwa siyan snacks da sauran su.

Kwatsam sai su ka ji ya na musu tambayar da ta sa su kallon juna fuskokin su dauke da fara'a da alama bana Anwar ya samu wadda ta sace zuciyar shi, shi ma d'an murmushi ya yi ya gyara tsayiwar shi sannan yace,

"Tabbas akwai abinda baku sani ba game da rayuwa ta, wannan da kuka ji ina tambaya itace rayuwata,itace firsr love d'ina, wadda nake sa ran ta zama last, dan in ba ita na aura ba ba zan tab'a samun kwanciyar hankali ba ko soyayyar gaskiya,nan na ga ta shigo d'azu da safe kafin na wuce asibiti, ta na sanye da hijabi kalar pink dogo har qasa, fara ce me matsakaicin tsaho, ta na da kyau Mai d'aukan hankalin me kallon ta,tana da siririyar murya Mai sanyi da zaqin sauraro, girar ta na da cika sannan..."

Cikin tausasawa murya d'aya daga cikin securities na wajen  yace,

"Ranka ya dade ina roqon Allah daya mallaka maka ita Allah ya sa rabon ka ce, ba sai ka qarasa kwatancen ta ba ma na gane ta, tabbas na ga shigar baiwar Allahn Kuma na ga sanda ta b'uya a can wajen cike da tsoro, da Wani irin yanayi a tattare da ita, sanda ka shigo Ina gaishe ka baka ji ni ba ai, se na ga kana dube dube ka fita cikin damuwa, tafiyar ka ke da wuya baiwar Allahn ta fito ta sai bread ta tafi cikin hanzari, ranka ya dad'e gaskiya ban mata sani na musamman ba amman yan da ka kwatanta ta dai tabbas sun tab'a zuwa nan sau  biyu  su biyu mata da Kuma  namiji  d'aya sai qaramar yarinya sun siyi pizza ranar Sunday da ta gabata,inaga yanda za a yi yanzu shine tinda Ina da lambar ka da na ga  sunzo zan faɗa maka sai ka zo ka riske ta"

Cikin rawar hannu Anwar ya miqa masa hannu suka qara gaisawa, ya shiga godiya kamar har ma an had'a shi da Eamaan d'in shi,ya yi masu alherin da ya saba ya tafi gida cike da addu'ar Allah ya sa a kira shi da wuri idan an ganta, zuwa ya yi gida ya yi wanka ya wuce masallacin Juma'a aka yi sallah da shi,ya na dawowa gida sai ya ja qur'anin shi ya karanta suratul Kahfi bayan ya idar ya hau yiwa Annabi salati ,yana cikin yi ne bacci ya dauke shi.

'Baby  pls ka bari, ni bana soooo'

'kina mana so Sweety,to tsaya idan baki son wancan bari na maki wannan'

Sai ya fara tickling d'in ta ita Kuma ta na ta dariya, d'an tsaya wa ya yi kad'an ita kuma ta rungume shi,zata kai bakin ta nashi kenan ya ji an jijjiga shi, cike da jin haushi ya miqe tare da addu'ar tashi a bacci.

" Kai dalla can galahore kawai, meye haka zaka zo ka tada ni ina bacci na me dad'i,"

Dariya abokin shi Jamal ya yi yana kallon yanda Anwar yake fushin da bai san shi da shi ba, kwata kwata fushin ma be dace da shi ba tinda ba halin shi bane.

" Haba namijin duniya,meye zai d'aga hankalin ka a mafarki haka? To koma mene ne alkhairi ne da yardar Allah success is urs man, Allah zai kare ka daga dikkan Sharrin da mafarkin ya qunsa ya kuma haɗa ka da alkhairin shi, dan haka ka miqe lokacin fara addu'o'i ya yi, tin da ka san dai ba wai mun san sa'ar da aka ce in mutum ya dace da ita a ranar juma'a ya yi addu'a Allah zai amsa bane lalube muke a duhu, Allah ya datar da mu"

A hankali ya tashi dik jikin shi a mace ya shiga wanka sannan ya d'aura alwala, sai da suka yi la'asar ya ci abinci sannan ya koma ya ja qur'anin shi suka hau karatun qur'ani, bayan sun idar Kuma kowa ya kama yi wa Annabi Muhammad salati, sannan daga baya naga suna ta addu'o'i wanda na san Anwar kam dole sai ya yi addu'a akan Allah ya had'a shi da  Eamaan,suna idarwa magrib ta yi suka fita masjid, sai da akai isha'i abokin shi ya ce suje suci abinci daga nan ya wuce gida,wajen cin abinci suka je suka ci suka sha,bayan sun gama ne Anwar ya tafi gida shi kuma abokin shi ya tafi nasu gidan, yana isa gida ya gaida Baba Mai gadin shi da  me masa d'an aikace-aikacen gida,ya miqa masu nasu daya taho masu da shi,sannan ya shige cikin gidan wanka ya yi sannan ya sa kayan baccin shi ya kunna karatu a wayar shi ya kwanta, a hankali ya tara hannayen shi a bakin shi ya karanta addu'ar bacci ya shafe jikin shi ya sake kwantawa cike da tinanin ta, sai juyi yake baccin yaqi daukar shi, ya kai wajen qarfe biyun dare a haka yana fatan Allah yasa ranar sunday ya ganta,ganin ya kasa bacci sai ya sakko daga gado yayi alwala, ya tada sallah yana roqon Allah in Eamaan alkairin rayuwar shi ce Allah ya bashi ita, kar ya zo ya yi ta wahala akan ta wannan karon ma ta samu wani, yana gama fad'an haka a addu'ar shi ya kuma tabbatar da me yace a addu'ar ta shi ya zaro ido waje, lallai in Eamaan ta bar shi a karo na biyu ya kad'e, tini ya fara roqon Allah akan ya mallaka masa ita in alkairi ce a gare shi,in ba alkairi duk da dad'in da son ta ya ke yi masa a ran shi da sabon da ya yi da son ta Allah ya yaye masa,a haka ya kai har 3am ya na addu'a kafin ya  miqe ya hau gado, nan da nan bacci mai nauyi kuwa ya yi awon  gaba da shi, 5:35am ya tashi ya ci gaba da ibada.

Haka rayuwar Anwar take gudana kullum, daga yaje wajen aiki, sai yayi ibada ya ci abinci ya nemi waje ya kwanta,sam baya daga cikin samari masu shiriritar neman matan banza ko shashancin shaye-shayen zamani, yana matukar k'ok'ari wajen kiyaye hakkin Allah da ya rataya a kan shi.

Yau sunday tin safe Anwar bakin shi yaqi rufuwa saboda murna da fatan sake ganin Eamaan, domin rage wa kan shi lokaci sai kawai ya yi ta aikace-aikace,dare na yi kuwa ya gabatar da sallahr  isha'i  a masallaci ya dawo ya yi  wanka, gayu ya yi na d'aukan magana shi Kan shi ya yaba da kyawun da ya yi, ya yi shiga cikin doguwar rigar shadda fara sol kamar wanda ke da yaƙini akan zai ga Eamaan a daren ranar haka Anwar ya sha tiraruka sai qamshi yake zabgawa,agogon shi da takalmin shi masu ruwan hanta daya saka kalar aikin kayan shi da hular shi.

Yana nan zaune ya gaji da Jira ba a Kira shi an ce an ga gilmawar ko da me kama da Eamaan bace, dan haka rufe parlour ya yi ya dauki key d'in motar shi ya fita,masu aikin shi sake baki kawai suka yi suna kallon shi dan ganin irin kyan da yayi, ga mota ya sa an wanke masa sai daukan ido take fara qal, me gadi ne ya tsokane shi yace,

" Ranka ya dad'e ko za a je wajen surukar tawa ne irin wannan kyau haka?"

Dariya yayi sannan ya ce

"I hope zan had'u da surukar taka a daren yau Baba,ka taya ni da addu'ar samun nasarar farautar da zan je ko Allah zai sa na samu sa'a"

"Allah ya baka sa'a d'ana, kaje lafiya ka dawo lafiya cike da nasara,"

Cikin jin dad'i ya fice daga gidan, direct Sky crown ya je,ma'aikatan wajen na ganin shi suka hau gaida shi, suna ta yaba kyawun da ya yi,Anwar baya daga cikin maza masu tsananin kyau, za a iya sanya shi a layin matsakaitan mazaje wajen kyau, tsaftar shi da Iya gayun shi ke qara fidda kyan shi,domin ita tsafta da iya gayu na sa mummuna ma a ga kyawun shi, zuwa yayi ya samu wani table da babu kowa ya zauna ta yanda duk wanda ya shigo ko zai fita zai ganshi,kira yayi aka kawo masa coffee da sandwich wanda yaji vegetable a tsakiya da nama,  ko tab'a sandwich d'in bai yi ba dik da yunwar da yake ji zuciyar shi nata bugawa saboda ɗokin ganin Eamaan,shin wai ta ina zata shigo ne? coffeen kawai yake ta kurb'a kadan-kadan.

Anwar ya kai wajen minti talatin a wajen amma bai ga mai kama da Eamaan bama ta wuce, kallon hanyar shiga wajen ya sake yi, idon shi ya sauka Kan wani abokin shi Kamal ɗauke da yarinya a hannun shi, kafe yarinyar ya yi da ido ya na so ya tina inda ya tab'a ganin ta amma ya kasa tinawa, Eamaan da Hafsat ne biye a bayan Kamal mijin Hafsat ɗin.

Wata iriyar ajiyar zuciya Anwar ya sauke mai qarfi tare da yin hamdala a bayyane, yalwataccen murmushi ya saki wanda ya sake qawata fuskar shi, miqewa ya yi ya na bin Eamaan da ke tafiya kamar d'awisu, fuskar ta se sheqi take yi a cikin hasken ƙwan lantarkin dake wajen,gani yayi ta yi masa wani irin kyau kamar bata tab'a aure ba a rayuwar ta balle a ce ta haihu, Ido kawai ya zuba mata ta baya ya na aje qafa a duk inda ta d'auke ta ta, ya ma manta da ya ga Kamal gaba d'aya ya tattara hankalin shi ya ɗora shi a Kan Eamaan din shi.

Qamshin turaren shi ne ya yi wa Eamaan dad'i a hancin ta,nan take ta tina yanda Anwar ke son irin turaren, tsayawa ta yi cak, kamar wadda aka dannawa remote control,lokaci daya ta juya , iskar da take shaqa ce ta ji ta na neman yi mata kad'an sakamakon idanun ta da ta sanya a cikin na Anwar.

Kallon ta yake yi baya ko qifta wa saboda ji yake yi kamar in ya qifta zata bace masa, ma'aikatan wajen sun kula da yanda gaba d'ayan su suka qame qam suna aikawa junan su kallo na musamman,nan take suka fara tunanin wannan itace wadda ta sace zuciyar Anwar, a hankali yake takawa dan ya qarasa gaban ta, Eamaan kuwa  da sauri ta juya baya ta na sauri ta bar wajen, tini hawaye sun wanke fuskar ta saboda rashin halin da ta tsinci kanta a ciki da tayi,Eamaan ta rasa me ya Kamata ta ji game da sake had'uwar ta da Anwar ,shin farin cikin ganin Anwar zata ji ko baqin cikin sake ganin shi a wannan lokacin? Shin Kunyar shi take ji ko Kuma kunyar Kan ta a matsayin ta na  bazawara a yanzu? Me ya sa take Jin kamar ta koma wajen shi ta dena gudun da take yi? Anwar kuwa bai b'ata lokaci ba wajen rufa mata baya.

Hafsat ce ta tafi da sauri wajen Kamal d'in ta ta fad'a masa me ke faruwa, a tare suka bi bayan Eamaan da Anwar.

Da qafa Eamaan ke sauri har ta Isa qofar gidan su, tana zuwa qofar gidan  nasu dole ta tsaya dan a kulle yake kuma babu key a wajen ta,Anwar na haki ya isa inda take tsaye tana share hawayen ta wasu na zuba, duqawa ya d'anyi yace,

" Yanzu meye na bamu wannan gwale-gwalen dan Allah, kullum sai fa na tafi gudu da asuba inna gama sallah, abin biyan bashi ya zama dan yau ban je ba ki sani gudu haka,"

Bata tab'a zaton ta yi kewar muryar shi haka ba sai da sautin muryar shi ya sauka a dodon kunnen ta, Wani irin kuka ne ya kub'uce mata mai nauyi a qirjin ta, ba makawa tsohuwar soyayyar Anwar ke neman yi mata dabaibayi a cikin lokaci ƙanƙani,tabbas tsohuwar soyayyar shi ke son d'aure mata jiki da ruhin ta, ba zata Iya jure wannan feelings d'in ba, abun ya mata nauyi sosai, ba ta San ta ya zata Iya fassara abun ba.

Kamal ne ya iso, dauke da Fatee a hannun shi cikin haki ya ce,

" Malam kai waye ka ke bin qanwata haka? Meye tsakanin ka da ita da zaka matsa mata, har kasa ta gudu haka a titi," Dan jimmm Kamal ya yi sannan ya ce

"Ahhh Anwar dama Kai ne ke bin qanwa ta da sauri haka? Me ya faru?"

Murmushi Anwar ya yi ya je gaban shi ya miqa masa hannu suka gaisa, Kamal na bin shi da kallon ina jiran amsar ka,

" A zato na Hafsat ta Sanar da Kai ko ni wane ne a wajen Eamaan,koda yake bahaushe ya ce waqa a bakin mai ita ta fi dad'i ni ne zuciyar ta, kuma ita ce zuciya ta, shekarun da suka shud'e ne ta tafi da tawa zuciyar na zama ba zuciya a jikina,tinda da ace akwai zuciya a ƙirji na dana aje son ta na fuskanci rayuwa na samu kowacce kalar mace ce na aura wataqila nima Allah ya bani kamar wannan kyakkyawar yarinyar na haifa na aje na sa mata suna Eamaan in dinga kallo ina jin dad'i, amma ban samu dama ba, shine yanzu dana gan ta na biyo ta in ji dalilin tafiya da ta yi da zuciya ta, ta dawo Kuma bata neme ni dan ta dawo min da abata ba"

Mamakin yanda Anwar ya zama me surutu haka ne ya cika Eamaan, Kalaman shi sun Sanya Kamal sassautowa, be tab'a zaton abokin shi Anwar ne Anwar d'in da Hafsat ke bashi labari ba, sake gaisawa suka yi, sannan Anwar ya ce,

"Ka na magana da Anwar d'in Eamaan da yardar Allah"

" Na ji dad'in cewar Kai ne Anwar d'in Eamaan, amma ni labarin Anwar d'in Eamaan  da aka bani bashi da magana Sam-Sam kamar ka"

Dariya suka yi suka tafa,Eamaan kuwa ta gaji da tsayuwa, ta samu gefe ta rakub'e Allah-Allah take a bud'e gidan ta shige abunta dan bata da ta cewa a yanzu, bata jin ma ko ta buɗe baki akwai kalmar da zata iya fita mai ma'ana a bakin nata, Hafsat ta kula da hakan dan haka sai ta ce,

"My dear Ina ga a bud'e gidan mu shiga mu zauna, dan kuwa yau mu na da babban baqo ko?"

Cikin sauri Eamaan ta ce,

"Da wa za a shiga gidan? Me zai je yi mana a cikin gidan?  ni gaskiya ka sallame shi anan kawai,ya tafi sai da safe"

Kamal ne ya ce,

"Eamaan kin manta na tab'a ce maki zan sama maki aiki a Wani asibiti? To ba asibin kowa bane face wannan bawan Allah'n, kin ga kenan na riga da na San shi ko ba dan ke ba ma ai zai Iya shiga gidan nan ko? Ballantana yanzu da na san cewar shine Anwar ɗin ki dole ne na ƙara ƙarfafa abotar mu."

Tura baki ta yi gaba ta kauda kai gefe,sam ba za su gane halin da take ciki ba, ita kad'ai ta San ya take ji game da sake had'uwar ta da Anwar a halin bata da aure a yanzu.

Hafsat na bud'e gate d'in  ta sa kai ta shige ciki ba tare da ta ce wa kowa komai ba, qasan zuciyar ta kuwa ba qaramin dad'i ta ji ba da Hafsat ta ce ya shiga, ko ba komai ta na Jin dad'in sake Jin muryar shi.

Amma daga ganin shigar shi da yanda Anwar d'in ya koma, sai ta ke Jin Wani fad'uwar gaba, Anya Anwar zai sake kula ta da sunan soyayya kuwa? Ita d'in fa bazawara ce a yanzu,daga Kalaman shi na d'azu ta fahimci cewar be yi aure ba, anya Anwar zai aure ta a yanzu kuwa? Farin cikin me ta fara yi ne tin kafin taga ya rayuwa zata maida ita a yanzu bayan haɗuwar ta da masoyin ta na farko? Dole ta tsawatar wa zuciyar ta kar ta saka tsammanin samun abinda ba lallai ne ya zama nata ba, ko Anwar ya yarda zai aure ta bata jin Hajiyar shi zata yarda, duba da cewa a baya ma ba Wani son ta take da Anwar d'in ba sosai balle yanzu da ta zama bazawara.

Daki ta shige ta rufe tana jin su suna ta hira,amo da sautin muryar shi na ratsa kunne da jikin ta, Hafsat ce ta shiga kitchen ta dakko masu kazar da Eamaan ta gasa kan su fita siyo pizza,sai kawai ta aje masu da plates da komai da zasu buqata,Juice din farar shinkafa da pineApple da Eamaan din ta hada nan ma ta dakko masu da cups ta aje ta koma d'akin Eamaan, kwankwasawa take tayi tana jin ta taqi budewa, daga qarshe komawa ta yi wajen su ta zauna,cikin murmushi Anwar yace,

" Hafsy kar ki damu ai naga waje, zan ta zuwa yad'a manufata ina fatan ba zaku damu ba da yawan gani na da za ku na yi akai-akai ?tinda da can ba mu Maida hankali mun yi zumunci ba ai kunga yanzu se a fara"

Dariya suka yi sannan suka tabbatar masa da  suna maraba da zuwan shi a kowanne lokaci, ya ji dad'in hakan nan take ya d'aga Fatee sama yana mata wasa yana murna yace,

" ki ce ma Mum din ki ta tausayawa bawan Allah kin ji,"

Dariya take kamar ta san me yake nufi da hakan,shi ma biye mata ya yi suka dinga wasa su na dariya sauke ta ya yi bayan ya zaro kud'i ya baiwa Hafsat yace asai mata sweet,godiya suka yi mishi har Fatee d'in daga nan ya masu sallama da saqon a gaida mai zuciyar shi, ya fara taka wa zuwa waje, Hafsat kuwa ta ce,

"Ai gashi zaka tafi baka ganta ba, inni ce kai tin da ban gan ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login