Showing 1 words to 3000 words out of 54699 words

Chapter 1 - Mukaddari Ne Daga Allah Complete Hausa Novels By Suhaima Abubakar Shehu.txt

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

MUƘADDARI NE DAGA ALLAH
By
Suhaima Abubakar Shehu
(Sallamar D. A. W. A)

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

DASHEN🌲ALLAH
WRITER'S📚ASSOCIATION

TEAM
_*ZAFAFAN🔥DASHEN🌲ALLAH*_

_*بسم الله الر حمن الر حيم*_

_* Yanayin Damuna ne yayiwa Garin rumfa, ga gajimare da har wannan lokacin ya hana rana fitowa. Sakamakon ruwan da aka kwana ana zubawa a daran jiya, hakan ne ya samar da iska mai daɗin shaƙa dake tafaman kaɗawa a tsakanin Bishiyoyin da suka yiwa Dajin ƙawanya, ko'ina kaduba furanni ne shar sun fiffito, wasu sunyi tsayi sosai yayin da wasu ƙananu ne sosai. Ko ina yayi lif-lif gwanin sha'awa da ƙawata kallon mazauna Garin.

Babu abun da kake iyan
juyowa a kaf dajin face kukan Tsutsayen daya ƙarawa yanayin matukar daɗi kasancewar a cikin Dajin babu motsi mai tada hankali, shiyasa dukkan mazauna wajen basa san rabo dashi, musamman ma wanda basa san hayaniya bazasu taɓa so su rabu da wajen ba.
"Sautin Sarewar da wani matashin Saurayi dake zaune akan wani falalin dutse wanda kallo ɗaya zaka masa zaka fahimci matuƙar nishaɗi da wannan busar take bashi, yakuwa haɗa ƙafa ɗaya kan ɗaya yana fuskanta kata faran Dajin da iyakar hangen ka babu abinda zaka iya hange wanda ba kyawawan furanni da bishiyoyi masu matuƙar kyaun kallo da kuma daɗin shaƙa dan ƙanshin su akwai kwantar da hankali, gashi sun ƙawata Dajin fiye da tunanin mai tunani.

Cikin wata yar ƙaramar Rigar saƙi yake data amshi fatar jikinsa sosai ruwan ƙasa ce wadda bata ciza ba sosai ga wani ɗan walki da tsawon sa bai wuce iyakar gwiwarsa ba.
Fari ne sosai duk da irin tarin dattin dake damfare a fatar jikin sa, hakan kuwa bai ɓoye zallar baiwar farin fatar da Allah yayi masa ba. Gashi ko kallo ɗaya kai masa zaka fahimci irin kyawu da kuma sheƙi da sulɓin da fatar take dashi.
Busa Sarewar sa yake har wannan lokacin yana wani rausayar da kai da alama ba kaɗan yake jin daɗin hakan ba.

Ɗif ya tsaya da busar saka makon a bunda idon sa ya hango masa da kuma ƙwa-ƙwalwarsa ke ƙoƙarin gazgata gaskiyar hakan wani sashen ƙwa-ƙwalwar tasa kuma yana kokawar ƙaryata masa mutum ya gani yashe a can ƙasa cikin wani mawuyacin hali domin duda ta zarar dake tsakaninsa da mutumin hakan bai hana ya iya fahimtar halin buƙatar taimakon da mutumin yake ciki ba, sanin cewa lafiya ba zata sa mutum yayi kwance a irin wanan dajin da hakukuwa suka cika ba ko dan tsoron abunda ka iya cutar da lafiyar sa ya saka yake kuma mamaki da kuma tabbatarwa da zuciyar wannan ba lafiya ba.

Dakatawa yayi da tunani da kuma lissafin da kansa ke masa ya kuma kallon Mutumin.
Bai sai lokacin daya furta “Mutum ne nake gani anan fa“ ya faɗa cikin yanayin tabbatarwa da kansa da kuma hasashen da zuciyar sa ke ƙoƙarin karyata masa.
Na dakika ɗaya bai tsaya kara sauraren halin da zuciyar sa ke masa ba ya riƙa kiciniyar saukowa daga dutsen dayake akai bayan ya maƙale sarewar tasa a jikin zaren da yake ɗaure a walkin sa,

Kamar wani ɗan ƙaramin matashin Biri ya riƙa sassarfa cikin ƙwarewa da sabo, yana kamo nan da can har ya dira ƙasa, nan fa ya zura a guje, ya nufi gurin dayaga mutumin nan a kwance.

Yanayin gudun da yake yi cikin matuƙar hanzari yasa bai ɗauki wani dagon lokaci ba saiga shi ya karaso gurin da mutumin yake a yashe kamar wanda rai yayi halin sa mamaki ne fal a zuciyar sa ganin abunda Idanuwan sa ke gane masa, matashi ne yake gani da shekarun sa ba zasu iya haurawa ashirin da uku ba, yanada duhun fatan amma ba za'a ce masa baki ba. Dogo ne amman kuma ba sosai ba sai kuma a yanayin ƙirar jikin sa da ba za'a iya kiranta ta masu ƙarfi ba, ga wata suma himili data karawa kan nasa girma, Da wani maɗaukakin mamaki yake kallon sa ganin suturar dake jikin matashin ko kusa ba irin tasu bace, tsaya yake akan dan matashin har wanan lokacin yana ƙare masa kallon ta'ajibi.

Cikin zuciyar sa kuma bayaga gargadi babu amon dake amsawa, ko ba'a faɗa masa ba yasan wannan mutumin ba irin su bane, domin idan aka cire yanayin halittar sa dake tabbatar masa cewa mutum kalan sa babu wani sauran kamanceceniya da zata karyata gaskiyar cewa ba daga wata duniyar ce yazo ba, ko kuma ma watakila Aljani ne.
Kallonsa ya cigaba dayi yana jin tausayinsa na yaƙar hanin da zuciyar sa ke sake jaddada masa game da taimakowa baƙon halittar da bai sani ba.

Jim yayi kafin nan kamar wanda aka tsikara ya fincikar da duk wani zancen zuci yakai hannayen sa kan matashin yana girgiza sa alamar ya tashi magana ya rika yi masa da yaren su amma ko gezau bai ji matashin yayi ba bare ya farfaɗo

Ganin bazai iya ba shi kaɗai, kuma ga numfashin da matashin yake yi sama-sama cikin matuƙar galabaita dake nuna har wannan lokacin yana raye ne ya bashi tabbacin za'a iya ceto rayuwar sa idan dai yakai sa gurin kakan sa daya kasance babban likitan dake duba mutunen garin nasu da sauri ko ya saɓesa kamar wani kayan wanki ya ɗorasa akafadar sa yabar gurin.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
_*ASIBITIN MTH SPECIALIST*_

Cikin sassarfa Likitan yake takawa da irin saurin da ba za'a iya kiran sa gudu ba, a bayan sa wasu Nuses ne guda biyu Mata biye dashi har suna dan haɗawa da gudu dan ganin yana ƙoƙarin yi musu nisa, ɗayar Matashiyar Nurse ɗince riƙe da na'urar auna hawan jini sai kuma ɗayar dake rataye da yar na'urar sauraron bugun zuciya a hannayenta ko wani ɗan ƙaramin akwatin allura ne da take ɗauke dashi, dukkansu suna sanye ne cikin fararen kaya irin waƴanda malaman Asibiti suke sanyawa idan ka cire Likitan da sauit ce ajikin sa Amma yar cikin ce kawai da alama ya baro coat ɗin a Ofishin sa.

Wata babbar Mace ce daga ganin yanayin ta kaɗai zai iya fassara maka zallan tashin hankalin dake ɗawainiya da ita, sai faman baza babban Hijabinta kawai take tana gudu kamar wacce aka biyo, da alama dai ita tai kiran Likitan dan a gabansu take kamar itace zata nuna musu ɗakin da yakamata su shiga.

" Intensive care unit (ICU) shine dakin data nufa likitan da sauran nurses ɗin biyu suna take mata baya.

Cikin hanzari ta tura ƙofar ɗakin baki ɗaya bata cikin hayyacin ta, tana nunawa Likitan da sai bayan shigar ta da Ƴan daƙiƙu ne suka ƙara so cikin ɗakin, ko ba'a faɗa ba ganin gado ɗaya tal a katafaren ɗaki irin wannan ya isa bayyana gatan wacce take kwance akan sa.

Wata farar mace ce wadda a ƙiyasi bazata haura shekaru arba'in ba sakama kon rawar ganin da hutu ya taka a fagen shekarun ta, domin dai a zahirin gaskiya tana layin Ƴan shekaru hamsin ne, rashin lafiyar nan ce ma da tsananin tashin hankalin da ya yi wa ahalin su dirar mikiya da rana tsaka ne ya janyo bayyanar tsufan ta kaɗan, ga wanda ya ko ya tsere ta da kallon kurulla ma zai ga tafi hakan.

Yau kwanan ta biyu kenan tun a lokacin da mummunan labarin da ko a mafarki taga faruwar sa saita ƙaryata shi, wannan shine mummunan labarin dake jaddada ikon ubangiji akan bayin sa mummu nan labarin dake tabbatarwa da kowa cewa lallai kaddara makauniya ce, bata duba gurin da ya kamata ta sauka, ko'ina Allah ya ce ta kasance saita kasance dan shine kaɗai mai iko da kuma kum-fayakum akan dukkannin bayinsa.

★★★
Tun yanke jikin da tai a wancan lokacin ta faɗi duk da irin yunkurin da Abba yayi dan hanata kaiwa kasa amma ina saida ta kifo kanta ya daku da centre table din dake tsakiyar falon.

Ga baki ɗaya ahalin ne sukayo kanta dan bata taimakon gaggawa inda ganin irin halin da take ya shallake iyawar su ɓata lokaci Abba ya umarci Aliyu da ya tada moto su wuce Asibiti kawai.

Haka tun bayan zuwa Asibitin da Likitoci sukai kanta Abba, Umma, salim, Aliyu da sauran yaran gida da Umma ta kira ta sanar musu halin da momy take ciki, duk sukai cirko-cirko

Shima ta ɓangaren Abba sosai dangin sa suka zozzo wayar da ya yi dasu ne ɗazun bayan faruwar abun yake shaida musu.

Aiko kafin kace kwabo dangi sun kusan cika Asibiti kowa zazzau ne a kujerarun da aka tanada banda Abba da har wannan lokacin yake rike da hannaye abaya yanata kai kawo.

Ba'a rufa awa ɗaya ba Dr. Harun yafito daga ɗakin, ai kuwa kamar wanda yaci bashin su suka yi kansa da tambayoyi Abba kam har kafaɗar Dr. Harun ɗin ya riƙe yana jero masa tambayoyi.

"Likita tana raye? Wane hali take a yanzu? Zamu iya ganinta?"

Dr. Hurun da har wannan lokacin bai samu damar cewa komai ba sai faman kallon su yake da murmushin daya zamowa fuskar sa Al'ada, cikin kwantar da murya ya ce "Alh ku kwantar da hankalin ku yanzu bata cikin hatsari, sai-dai kuyi haƙuri bazaku iya ganin ta ba yanzu, tana buƙatar hutu"
Dr. Hurun ɗin ne yake faɗawa Abba hakan bayan ya gama sauraren tambayoyin da bazai yuyu ya amsa su duka ba.

Ajiyar zuciya Abba ya sauke tare da furta Alhamdulillahi yanayin Addu'a a cikin ransa.

Dr. Harun ne ya katse musu shurun da cewa
"Alh zanso nayi magana dakai a office"

"To to ai ba damuwa zamu iya tafiya ko" Abba ya faɗa cikin hanzari kafin Dr. Hurun ya wuce gaba Abban ya biyo sa a baya.

Tun bayan tattaunawar Abba da Dr. Haurun inda ya sanar masa ba'a buƙatar duk wayan nan mutanen da saboda irin halin da take ciki da kuma sauran Marasa Lafiya da suke a Asibitin. Dan saboda ba'asan hayaniyar su zata iya ƙara jefa mara lafiyar ne a damuwa.
Saboda haka Abba ya sallame kowa, daga bangaren dangin sa, da kuma ɓangaren su Baba Saminu, sai kuma akabar Umma dan ta kula da ita.


Yauma tun safe yazo duba momyn amma har wannan lokacin dai babu wani sauyi, bayan ƴar jimawa ne ya yi sallama da Umma ya wuce office bayan shaida mata zuwan su Hajia Zuwaira wacce take Ƙanwa ga momy'n

Fitar Abba da kamar awa ɗaya, Umma daketa faman kwashen flask da kofukan da tayi breakfast ne taji kamar motsi a bayanta ta waigo da sauri, itama Mommy cikin sauri ta farfaɗo har tana iya motsa ƴan yatsun ta aikuwa da saurin ta Umma ta ƙaraso gurin tana tambayar ta "Umman Sadauki kin farka, kina iya jina, yatsu nawa ne nan" ta kai hannuta gaban fuskar Momyn tana tambayar ta.

Ito ko Momy'n sai kallon ta kawai take da lumsassun Idanuwanta da suka ƙara bayyana rashin karfin jikin ta ganin Umma tafice da sauri dan kiran Doctor, yasata tabi ƙofar da kallo, aikuwa tana shiga officer ɗinsa tana cikin gaya masa ko rufe baki batai ba aiko ya tafi yana fitowa kamar labarin da yake zaman jira kenan, ita ce ma ta biyo bayansa dan ya rigata fita ma, suna fita Nurses biyu da suke tare alokacin suka rufa masa baya, dan dama yana musu bayani ne akan suje wajen ta.

Kusa da Mommy ya ƙara so da ɗan saurin sa yana nazartar ta kafin ya ce.

"Hajiya ya jikin naki? Ya kike ji a yanzu?"

Bata iya ce masa komai ba sai ido data bisa dashi.

"Hajiya kina iya jina?"

Awanan karon ma dai kallon sa take kafin ta ɗauke idon ta daga kansa ta maida kan Umma wacce ke magana da wani a waya
"Idan kina iya jina kiyi mun wata alama dan na sani, kamar ko idonki ma zaki iya yi mun alama dashi tayadda zamu san abun yi!"

Haka kuwa tayi domin dama can tana iya jin kome, magana ce kawai ta rasa meyasa ta kasa yi.

Idanuwanta ta lumshe sannan ta bude alamar eh ina jinka ƙaramar ajiyar zuciya ya sauke kafin nan ya karɓi ma'aunin gwada hawan jini ya soma daura mata dan auna hawan jini da dai-daiton bugun zuciyar ta.

Haka ya cigaba da yan aune aunen su na likitoci yana wani rubutu a file ɗin daya shigo dashi nata, sallmar da suka jiyo ce ta katse rubutun da yake ya dago domin amsa sallamar.

Abba ne ya shigo kamar wanda aka jefo, Umma ta kirasa take ta shida masa Mommy ta farka, nan take ya tabbatar mata yana kan hanya komai na office ya ajiye a gefe, yakira Habu sakatare ya shaida masa zai tafi wani uzuri bai tsaya jin amsawar Habu bama yayi ficewar sa ko minti shida bai cika ba kuwa sai gashi a MTH HOSPITAL, sakamokon gudun da ya rika yi kamar wani matashin dan tsere.


Kai tsaye Mommy'n yanufa baima lura da gaisuwar da Ummar keyi masa ba, Ummun Khalil yafaɗa yana kai hannusa ya riƙo nata da wani tausayi daya kewaye fuskar sa.

Jin ya ambaci khalil kuwa kamar ya dawo mata da kome sabo ne, Khalil dai ɗanta Namiji ɗaya tilo data mallaka a Duniya, Khalil dai wanda tafi so kaf sama da sauran Ƴaƴan ta, Khalil wannan dai Khalil ɗin da mutuwa ta karbe mata a sanda take cike da so da ƙaunar sa.

Hawaye kaɗai ne abunda tambayoyin Abban ke ƙara bankaɗo mata, ta kasa tsaida Idanuwan ta a fuskar Abban kamar yadda taga abunda yake nema kenan.

So yake ta kalle sa ta faɗa masa ta samu lafiya, sai faman rarraba ido kawai yake a fuskar ta da a yanzu ta soma. Canja launi izuwa ja abun ka da farar fata.

Kuka take son yi mai fitar da duk wata damuwa anan take, amma kamar wacce ana zarewa murya ta kasa fitar da sauti da ko na kusa da ita zai iyi jiyowa bare kuma na ciki dakin.

"Am Alhaji kayi haƙuri ka bata lokaci, bata iya magana har yanzu" Dr. Harun ne yatari numfashin Abba dayake ƙoƙarin ganin momyn ta amsa mishi.

"Bata iya magana kamar ya kenan me yake faruwa da ita ne? Abba ya tambaya cikin alamun ɗaure war kai"


"Abunda muke ƙoƙarin ganowa kenan Alhaji, yanzu dai ga wannan alluran"
Da sauri, ya faɗa yana miƙa masa fallen takardar daya kammala rubutun maganin a ciki, cikin rashin ƙwarin jiki Abban ya karɓa yana jujjuya ta a hunnun sa.


KAUYEN GUMO
Har wanan lokacin khalil baiko motsa ba barema asa ran zai farfaɗo tun bayan da Alili wannan saurayin daya tsinto sa daga cikin daji, sunan sa Aliyu ne amma kowa a garin Alili yake ce masa, sunan da a yanzu ya goge ainihin sunan sa a harsunan mutanen garin kenan.


"Kaka ina so ka taimaki wanan mutumin" Alili ne ya faɗa a sanda ya ƙarasa gidan Kakan nasa cikin tashin hankali, sai maida numfashi yake kamar wanda kuɓuto daga hannun mutuwa.


Kaka kuwa da har a lokacin ya sandare ne a tsaye yana musu kallon rashin fahimta, kalma ɗaya bata yi sa'ar fitowa daga bakin sa ba.

"Kaka zai mutu wlh idan baka taimaka masa ba, jifa irin halin da yake ciki na roƙeka Kaka" Ya ƙarashe maganar kamar zai saka kuka

Kaka kuwa da tsoron abunda kaje ne kadawo ya cika masa ciki sai a sannan ne ya iya ce wa "Ɗannan kana cikin hankalin ka kuwa ka tattalo sa kazo min dashi ashe har yanzu baka da hankali, wanan karon ya ƙarashe zancen ne cikin faɗa-faɗa

"Kenan kada na taimaka masa? Nabarsa acan ya mutu ko Kaka? Hakan kake so nayi iye? Shi kenan Kaka zan koma dashi, zan bar shi a can ya mutun tunda haka kake so. Amma ka sani yanda ba zai ƙara dawowa gida nan ba Kaka, to haka nima da idanuwanka ba zaka ƙara ganina ba" Yana gama faɗar hakan ya juya a fusace.

Ganin dai da gaske Alili zai tafi yasa Kaka yin sauri ya taro jikan sa da wayancewa ya ce "Haba dai Ɗannan, ba nufina ba kenan ina nufin kada mu taimaka masa a ƙarshe hakan ya zama matsala a gare mu."

Alili kuwa da riƙon rigar sa ta baya da k/Kaka ya yi, yasa ya dakata daga tafiyar da ya yi niyya, batare da ya juya ba yake amsa Kakan "Dama taimako na iya janyo wani abun daba Alkhairi ba a rayuwar mutum Kaka" Dariya yake ƙasa-ƙasa a wannan karon, sarai ya gama sanin lagon Kakan nasa, ko abu ya nema a bashi idan ya hana masa to sai ya yi masa barazanar barin gari, shi kuma Kaka ganin bayada kowa a duniya sai Ɗan jikansa a kullum baya shanye rada, duk sanda Alili ya yi barazanar barin Gida atake hankalin Kaka yake tashi ya yi masa abunda ya nema.


"To ka shigo dashi na duba sa ko?" kakan ya faɗa cikin sanyi murya aiko Alili saida ya ƙara turɓune fuska kafin ya juya a fusace yana bin bayan Kakan da ke ƙoƙarin shiga wani ƙaramin ɗaki

Babu ɓata lokaci ya shiga yi masa abubuwan da suka dace dan ceto rayuwar sa.

Abunda babu Alili yake turawa daji ya nemo, ya nemo masa saiwar bishiyu takai biyar, kwana d'aya kenan a ana abun d'aya kullum sai anyi masa turare da shafe jikin sa kaf da magungu nan gargajiya, dan kaka yasa Alili ya rasaba sa da wayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login