Showing 18001 words to 21000 words out of 54699 words
Chapter 7 - Mukaddari Ne Daga Allah Complete Hausa Novels By Suhaima Abubakar Shehu.txt
saboda ku nake zaune ku kan ku kunsan gabaki dayan mu babu wanda yake kula da mu amma ku kullum cikin fada, shiyasa akullum nake yawaita muku addu'a,
Sosai jikin su yayi sanyi kama hannaye ta sukayi suka zaunar da ita akan kujera suka fara mata magana, mom mun tufa bazamu karaba insha Allahu wallahi mom bama son ganin bacin ranki dan Allah mom kidai na fushi da mu, sosai suka fadawa mom Razia magana maidadi suka sata farin ciki sosai
Arana nan ma daki daya suka kwana dukan su pillow daya suka kwana cikin farin ciki, washigari da safe mom tace yau zakuje siyayya ae murna ba a magana sosai sukaji dadi suna ta godewa mom din su, gabaki dayan su kaya iri daya suka sa ka shigan riga da wando jaa sun baza gashin kansu abayan su sunyi kyau sosai,
Mom ne tace wow twins dina kyawawa ne sosai Allah yatsare mun ku Allah yakai mu lapiya yadawo mun da ku lapiya sosai tamusu addu'a
BARI MUKOMA BANGARAN SIDDARTH
Siddarth ne zaune shida abokin sa Raj, Raj yace masa wai nikam baka sha'awa ne ko kallon mata bakayi balatana kace kana son ta, Siddarth ya dubi abokin sa yace ina har yanzu ban samu kalan mace danke soba, Raj yace ko zan iya sanin kalal mace dakake so, gyada kae yayi amun ehh zaka sani,
Siddarth yace ina son mace wace take da ra'ayi kalan nawa wace tasan zamantakewar aure wace tasan darajan aure, kasan wasu mutane suna, aure abune na har abadah wasu na kankata girman wanan kalma da har abada wasu da alama ma basu masan mai take nufi ba, bayan ma'anan ta kalman soyayya gurin cewa ina son ki har abadah kafin kayi aure kafara duba wannan kalma ta har abadah zamane da ake so mutuwa ce kadai zata iya shiga tsakani, shin zama ka iya rayuwa ko da dabba ne na har abadah? bare kuma mutum irin ka mai tunani irin naka mai ra'ayi daban da naka mai kalan tsarin rayuwa da ban da nakanaka kuma na tsawon har abadah? Shin zaka iya kafun kafada rijiya mai zurfi kafara tunanin daya fi rijiya zurfi sosai, airin zaman takewa na har abada mai yakamata mufi bukata agurin abokiyar yinta kyawu ne? Ko kyawun hali? Kuma dai soyayya ce ? A irin wannan dogowar tafiyan mai dogon zango mainene abu nafarko da yaka mata mufara kalla agurin abokiyar tafiya nan, ara'ayi na hausawa suna cewa tun za'a ake shiri basai andawoba, ma'ana ba afara niman guziri bayan anfafa tafiya , kafun kafafa tafiya yakamata mutanadi duk wani abun bukata wanda kasan baza ayisamun saba acikin tafiyar, Siddarth yakala abokin sa Raj da ya nutsu yana jin sa yace kana fahimta na ko, girgiza kai yayi amun ehh ina fahimtar ka,
Yadaura dacewa ka aureta dan tana da kyawun hali bawai dan tana da kyawu ko iya kwaliya ba, haka zalika ma ita macen, bawai dan yana da kudi ba, ko kyawun ba, domin kyawu baya rike aure haka ma kudi, haka ma soyayya bata rike aure amma kyawun haleya zasu iya babu kyawu na har abadah haka ma kuma babu soyayya ta har abadah amma kuma anasamun kyawun halaya na har abadah, idan kana son mace sauki zairika azuzuta maka kyawun ta karin ga ganin kamar tafi kowa komai nata zai ringa maka dadi muryan ta, murmushin ta, dariyan ta, dama komai da yashafi ta, karinga jin kamar ita daya ce ta iya komai, rayuwa karigajin bazaka iya hakura da itaba karinga jin zaka iya aura ta kobaka da ko sisi, ae Allah na nan zai hore maka karinga jin zaka iyayi wakowa rashin kunya in yace bazaka aure taba, koda iyaye ne dama sauran su, amma shi tasirin sa yana raguwa ne daga sanda kasame ta dama abunda yake burgemu dan yana nesa ne damu daga sanda muka samai sa to hankalin mu zaidawo dai-dai sauran abubuwa kafu nan kuma sai darajansa zai ringa yin kasa har mukai lokacin da zaman zabi ne kawai mukeyi,
Siddarth ya numfasa yadaura dacewa
Wayan hanka yanzu haka zaman hakuri muke da ita amma kuma idan zaka tuna kafun ka siye ta har wani jindadi kakey
i ayanzu ma idan kasamu kudi nasan akwai wace kake so kacanza ko? to mukala abun haka yadda zamu fi fahimtar sa da kyau zakaji kana son wayan hanun ka kaji ko saurin shiga internt kodai wani abu to mace ma haka ne saidai idan tana da kyawun hali kawai zakaji kana son zama da ita namiji ma saidai idan yana da wannan ne zataji tana son hakurin mace zataji tana son zama dashi,
Siddarth dubi Raj da yakafeahi da idanuwa yadaura dacewa, kada kabanbanta so da kwaya daya ne aduniya shine son mace da muke kira soyayya kuma dai shi so wani abune arayuwar mu m, ina tsoron aure da mace da badan Allah zata aure niba saidan wani abu nawa,
Yanzu kafahimce ba soyayya ake bukata azaman takewar aure ba ba kuma kyawu ake bukata ba asahun farko ba domin kyawu bai rike aure Raj ina son nasamu mace wace zata soni dan Allah
Sosai Raj yake girgiza kai yabude naki zaiyi magana...........
Raj yace wannan gaskiya ne Allah yabamu mata wanda zasu so dan shi,
Yakuma kallon Siddarth yace kamata zamu fita shofing, no banmata ba bari nashirya, mekewa Siddarth yayi toilet yayi wanda bayan yafito, tsayawa yayi cak yana tunanin yau wani shiga zaiyi shi mutum ne me son kasan sa, yau ta kasance friday dan haka shigan manya kaya yayi, yafito sak ba hausa fulani, Siddarth kyakyawa ne ajin farko, yayi kyau sosai, kai tsaye parlo ya nufo wajan Raj, Raj kafesa da idanuwan sa yayi yace masha Allahu amma fa abokina kayi kyau sosai, gaskiya bazaka barni nayi budurwa ba idan ina tare dakai irin wannan kyau haka,
Hararan sa yayi tare da lumshe idanuwan sa woow woow woow Siddarth yakashee ni da idanuwan sa mai rikitar da mata, yace plz bana son surutu mutafi kona fasa yakari sa magana kamar wanda akace dole yayi magana, a'a bazamu fasa ba mutafi cewar Raj,
Suha da Sana sai siyaya suke yi, su dauki wannan sudauki wancan haka suka ringa jabga kayya, masu kyau da tsada, Suha ne ta dubi Sana tace mata too tunda mungama muje can muyi wasa, ae kuwa Sana sarkin wasa tace haka ne fa muje, ajeye kayan acikin moto sukayi, suka nufi wajan wasan kamar wasu kananun yara,
Sana ne tacewa Suha wani kallan wasa zamuyi, tunani Suha tashiga can kuma tace natuna, fuskan ki zan daure, kinga wancan benan zamu haura inkin kamani kinyi nasara, inbaki kamani ba nine nayi nasara kin yarda, Sana tace ehh nayarda,
Daure fuskan Sana Suha tayi suka fara wasa kan benan Suha tayi Sana tana bin bayan ta, Suha dawowa tayi ahankali batare da Sana ta ankara ba ta sauko kasa, ita kuma Sana cigaba da haurawa sama takeyi har ta iso karshen benan,
Tuntube tayi tayi kasa ae kuwa batasan sanda tafuncike abun fuskan taba ganin ta akarshen benan aekuwa tashiga cikin tsoro, da rudani, jada baya take, bata ankaraba kawai jinta tayi tayi kasa, ae kuwa da sauri tarike wani dogon wani abu kamar fanka, wannan abun she kawai yahana ta saukowa kasa gashi benan dogone kuma nakarahe take,
Suha Suha Suha ta kwalla mata kira Suha shikenan karshe na yazo mutuwa zanyi nasan bazan rayuba, Allah sarki mom dina shikenan daga yau bazan kara ganin kiba kuka take sosai tana niman agaji, da farko Suha tazata iskancin Sana ne amma da tadago akan ta zuwa saman benan ae kuwa tashiga rudani, tana ihu tana kiran Sana Sana kire da kyau gani zuwa taimakon ki, saikace zata iya, dan Allah kutaima keta yar uwata ce dan Allah karku bari tafado, ita kadaice yar uwata kuka take sosai, mutani suncika agun sosai ankewaye gun baki daya, Suha ganin babu wanda zai taimaka ma yar uwan ta, gashi kuma Sana sai kuka take hannayen ta da tarike wannan abun da shine kawai maka manta yayi jaa ida nuwanta duk sunyi jaa gashin kanta duk yabazu afuskan ta, Suha yanke shawara tayi tace tacice yar uwan ta, ae kuwa nufanta tayi tana kuka kamar mahaukaciya, mutani suka ankara da ita ae kuwa suka rireke ta, kusake ni kusakeni yar uwatace fa kubarini intaima keta idan ma mutu zamuyi babu ruwan ku, haka kawai Suha take fada, Allah sarki abun tausayi, mutani kuma sai kallon Sana da gabaki daya ta
tafita cikin haiyacin ta,
Adai-dai wannan lokacin kuma moton Siddarth da Raj ta kunno kai, Raj yace maiyake faruwa nan ciki dan mamaki yafo daga cikin moton dan ganin abunda yake faruwa, kallon abunda yake faru cikin mamaki, Siddarth ya daura idanuwan sa akan Sana da gaba ki daya numfashin ta yana dafda daukewa, numshe idanuwan sa yayi yakadaura idanuwan sa akan ta, Sana tana ta sumbatu, Suha kice mom tayafeni nikam nawa yakare, zufa duk ya rufeta ko ina zufa ajikin ta gabaki daya tafita cikin haiyacin ta, murmushin gefen baki yayi, yana numshe idanuwan sa azuciyaya tace sarki numshe idanuwa, Raj yace Allah sarki ina mazan iya ceton ki danayi, Siddarth kafafun sa yasa awaje yafoto daga cikin moton kai tsaye bai tsaya sauraran magana da Raj yake masaba yanufa wannan benan domin ceton wannan yarinya da baisan taba,
Gudu sosai yake kamar ya ara kafa kamar wanda ya ara kafa, gashi manya kayane ajikin sa, yana isa benan yafara kokarin hawa yadda Sana take ae kuwa idanuwan mutane suka dawo kan sa dan babu wanda ya ankara dashi sai ganin sa sukayi asaman benan kawai,
Yana isa gare ta, yana kama wannan abunda yake kama da fankan wanda shine yasa Sana bata fadi ba ita kuma Sana tana sakewa sbd hannaye ta sunyi jaa kuma sunyi tsami tayi kokarma harta kai wannan lokacin,
Ae kuwa yarike ta da dayan hanun sa yayin da dayan ahanun yana rike da wannan abun mai kama da fanka, alokacin da Sana tasake wannan abun ae kuwa Suha tasaka ihu dan tagama sadakarwa yar uwan ta tarasa ta baki daya dan idan mutum yafado dakan wannan benan tabbas bazai yi raiba idan yayi rai to bazai iya tabuka komai ba,
Siddarth rike Sana da hanu daya yayi yayinda wannan hanun sa yana kan wannan abun, sosai yarike ta , soyake yadawo da ita kirjin sa ae kuwa yadawo da ita hannayen ta yasaka abayan wuyan sa, ita kuma alokacin ta sumee sosai ya rike wannan abun da hanu daya dayan hanun kuma yarumgumo ta dashi,.........
Sosai ya rumgumo ta akirjin sa yana rike da wannan abun dashine yarike so dukan su sosai yarike abun kuma yana rumgume da Sana
Raj idanuwa yazubawa Siddarth sbd wannan yana rayawa azuciyar sa shin Siddarth ne da gaske ko a'a Siddarth din da baya son yarike hanun mace bare kuma ya rumgumo ta akirjin sa Siddarth din da adini yagama bin jikin sa Siddarth da babu ruwan sa da ko wata mace wannan dai Siddarth din shine dai wannan yau rumgume da mace,
Cigaba da kallon sa yake Raj din abun yanata bashi mamaki, shi kuma Siddarth kokari yake yaga yabar kan benan,
Mutani da yawwa suna yabon Siddarth sbd ya gwada jarumta anan gun gaskiya wannan jarumi ne sosai mutani suke yabon sa, shi kuma Siddarth haka yata bin katangan benan har Allah yabashi sa'a saukowa kai tsaye yanufo gurin motar sa da ita shiga da ita cikin moton yayi ya dauko ruwa mai sanyi yazuba mata akan fuskan ta, doguwar ajiyar zuciya ta sauke tana mai numfashi sama-sama kallon ta Siddarth yakeyi cikin sanyi muryan sa yace fita mun amoto na, idanuwa tabishi dashi tana sake numshewa ina miki magana nace kifita amoto na idanuwa kawai takafa masa bata ko kiftawa, numshe idanuwan sa Siddarth yayi yana kallon ta aran sa yana cewa wannan yarinya akwai raini atattare da ita ok dan taga nataima kamata ko shikadai yake magana cikin zuciyar sa,
Suha ne take bubuga moton tana kiran sunan yar uwan ta Sana Sana kina jina kifito mutafi gida, Siddarth fuciko hannu Sana yayi fito da ita daga cikin moton sa ya koma ciki, Raj yashiga yaja motar yabar gurin baki daya, kuka Sana tasaka sosai kuka mai jin rai taji zafi azuciyar ta taji radadi aran ta taso tayi masa magana ko da godiya ce kukan ya hadu kashi biyu shin ina zata sake ganin sa har tamasa magana itafa lokaci guda yatafi da zuciyar ta kuka take sosai irin sosai dinan, Suha ne taje tazauna kusa da ita tafara mata magana haba Sana kitashi mutafi gida tundazu ina miki magana kina kuka kima gode Allah wannan mutumin yazo yacece ki da yanzu ba wannan labarin akeyi ba
Sana riko hannayen Suha tayi cikin dacin zuciya tafara magana ina zan gan sa ina zan sake ganin sa lokaci guda naji yashiga raina wallahi ina son sa Suha itai maka mun karna rasa sa idan narasa sa mutuwa zanyi, sosai Suha take kallon ta tana mamakin Sana Sana nan da aduniya idan kana son ganin bacin ranta too kamata magana nan namiji kokace mata wani yace kana son ta too fa anan ne zaku samu matsala da ita
Bazata taba mantawa ba wani lokaci da suka samu matsala da ita akan takawo mata magana nan wani matashin saurayi yagan ta a school nasu yace yana son ta shine fah yasamu Suha yafada mata akan dan Allah ta taimaka tafadawa yar uwan ta yana son ta kuma tashawo mata kan ta
Suha ne tashiga dakin Sana alokacin Sana tana chatting da kawayan ta tana cikin nishadi sosai Suha tashiga dakin kusa da Sana tasamu guri ta zauna tana kallon ta ita kuwa Sana ko kallon yadda take batayi bare tasa ran zata mata magana Suha ne tace ina son magana dake dan Allah kiban aron lokacin ki, kallon ta Sana tayi tace ina jinki wayan hanunta ta ajiye agefen ta tace ina sauraron ki,
Magana Suha tafara da farko dai sako akaban nabaki, Sana tace sako dagawa, Suha tace sako daga masoyin ki aman, Sana ta anbata suna abakin ta Aman ehh Suha tace mata tace yace infada miki dan Allah ki saurare sa kuma yaban sako nikuma zan isar da ita zuwa garki yace mun infada miki abun farin ciki nazuwa ne yayin da yasamu abokiyar rayuwar sa yace mun yar uwan ki akwai shiga rai kina da komai da yake dauke hankalin mutum dan Allah kikarba soyayyan sa dan Allah
Bata karisa rufe bakin taba taji saukan fari akan fuskan ta hakan yasaka Suha ware manya-manya idanuwan ta akan Sana tana mai mamakin marin ta tamata ae kuwa fada yakauce tsakanin su wanda yakai dambe ne yashiga tsakanin su sosai har takai sai da mom taraba su, saida sukayi kwana kusan goma basa magana akan wannan amma wai yau Sana take cewa wai tana son wani mutum kodai dan yataima keta ne amma kuma ae gayen Allah yazuba masa ruwan kyau sosai take kuka akan ita ina zata sake ganin sa lallabata Suha tayi ta tace mufara zuwa gida sai mufadawa mom itace zata san abunyi da haka Suha tashawo kan Sana har suka nufi gida,
Siddarth gabaki daya ran sa abace yake yanajin zuciyar sa na masa zafi sosai ganin halin da Siddarth yashiga ne yasa Raj bai ko masa wata magana ba, wayan Siddarth ne tafara ruru ae kuwa yaga daddyn sa ne ke kiran sa ae kuwa da sauri ya dauka da sauri yakai kun nan sa yace Assalamaalaikum daga bangaran daddy amasa wa'alaika musalam my son fatan kana lapiya, lpya kalau daddy ya ummi da Arjun da Aawa suna lapia kalau, dady yafara magana cikin sanyi murya yace masa jikin Alhaji kaka yatashi sosai yanzu haka muna asibiti kuma yace yana son ganin kowa gobe dan haka yau kabi jirgin dare kadawo
Siddarth yace insha Allahu daddy Allahu yabashi lapiya
************
KAUYEN GUMA
Washigari da safe Alili da kaka suka shirya domin tafiya asibiti kaka yadobi Alili yace wani asibiti yaka mata muje ne Alili yace kaka muje asibitin haske haka kuwa sukaje,
HASKE HOSPITAL
Doctor ne ya dumi su Kaka da Alili yace duk kwaje-kwajen da yakamata mumasa mun masa kuma mun gano brain din sane yasamu matsala kodai yasamu accedet din da yabuga kan sa kodae wani abu yasame sa akai dumin iya binciken mu mungano komai na brain din sa yamanta wato komai tunanin sa da kwakwalwan sa yamanta shi bazai iya tuno komai ba amma kuma zai iya tunuwa idan ana tuno masa da rayuwar sa na baya, yanzu zaina abu kamar karamin yaro kuma mungano wani abu game dashi akwai firgici da tsoro atattare dashi abu kadan zai zai sashi zubar da hawaye, zai kasan ce kamar yaro dan goye wanda yanzu zai sabada mutani kamar uwa da tahaifi dan ta ae yaro da uwan sa yake fara sabawa kafun baba da sauran su to haka wannan majinyacin zai kasance yanxu zamu daurasa akan magani insha Allahu zai samu lapiya kuma kuna yawwan tuno masa da rayuwar sa ta baya hakan ma zai taimaka sosai, sosai likita yabasu shawarwari mai amfani,
Amma kaka Alili sunshiga cikin damuwa sosai taya zasuna tuno masa rayuwar sa na baya bayan basu sansaba basu taba ganin saba basu san daga ina yakeba bare har suna tuno masa da rayuwar sa nabaya kuma shine abunda zai taimaka masa har yadawo cikin haiyacin sa, wannan abun yasa su arudani kuma sosai, saida likita ya dan taba tebur gin gaban sa tukun na suka dawo cikin duniyar da ta aura tunanin su insha Allahu zamuyi abunda kace likita,
Bayan sunsiya magunguna da akarubuta musu ne suka nufo kauye guma Khalil da ayanzu suka sakama sa sauna da garkuwa shine atsakiyan su, haka suka dawo gida suka daura sa kan maganin sa akoda yaushe yana manne da Bintu,
Bushar ne yasaka Bintu agaba duk wannan abun da yake faruwa bai san labarin ba sakama kon tafiyar da yataso masa kai tsaye, duban Bintu yayi yace tafiya takamani zuwa birni