Showing 54001 words to 54699 words out of 54699 words
Chapter 19 - Mukaddari Ne Daga Allah Complete Hausa Novels By Suhaima Abubakar Shehu.txt
yakamata tabbas wannan mutumin yana gani jarabawa saida kaka yama sa duk abunda yakamata bayan gabaki daya mutanin sunwatse kawai sai wannan mutumin da ya kama hanun Alili gabaki daya abunda yafaru ya fadawa Kaka suma sun gan sane kawai akwance babu numfashi ajikin sa, sosai Kaka ya masa godiya shi kuma ya musu sallama ya tafi abun sa
Kaka kama hanun Alili yayi ya fara masa nasiha sosai kuma nasihar tashiga jikin sa, haka ya umar ce sa akan yaje yasanarwa Bintu kuma suzo tare bayan Alili yazo wajan Bintu sai da yafara mata nasiha da tunatar da ita akan duk wani abun da yasa mu bawan sa tabbas MUKADDARI NE DAGA ALLAH yamata nasiha sosai kafin yafaɗa mata abunda yafaru da Khalil abun mamaki Bintu cewa tayi Allahu yabashi lapiya haka tafi Alili
Rayuwa kenan yau Khalil watan sa guda bai san yadda kan sa yake ba sosai cikin Bintu yayi girma sosai kuma hakan bai hanata kula da mijin taba
Yau garin antashi da wani tashin hankali na mayu masu cinye naman mutani wanda suka shiga kauyen kunkar kusa da kauyen guma kuma gabaki daya sun gama da kauyen Kunkar sun tunkari kauyen Guma, yau tun safe Kaka yatafi daji dan nimowa Khalil magani Alili kuma ya ɗan fita kauye ya har gitse dan mayu nan sun shigo kauyen Guma sun fara daga farkon garin
Dai-dai lokacin da Khalil ya fara bude idanuwan sa a hankali ware idanuwan sa yayi gabaki ɗaya a cikin ɗakin zubawa ɗakin idanuwan sa yayi yana kallon gun, bude bakin sa yayi yana furta MIMI MIMI MIMI kar ki mutu kibar ni a'a dan Allah kubar ta kar kuka she ta tashi yayi a firgice dai-dai lokacin kuma Bintu tashigo ɗakin da sauri tazo waja sa ta kama hannun sa tana masa magana "SADAUKI katashi? zuba mata idanuwan sa yayi yana kallon ta yana magana cikin zuciyar sa wannan kuma daga inaa haka sake kama hannun sa tayi tana kai hanun ta akan cikin ta tana cewa kaji yaron mu shima yana murna katashi dama kullum sai yayi kukan rashin ka,
Wacece ke? nan ina ne ? mai nakeyi anan? gaban ƙirjin tane yabuga tashi ga cikin ruɗani amma hakan bai sa tayi shuru ba tace "matar kace Mimin ka kaga har da cikin ka ajiki na, mekewa Khalil yayi yace mata na ɗaya ce a duniya ita ce INJILA MIMINA bayan ita babu kowa banga je Bintu yayi ya fita a ɗakin ai da gudun ta Bintu tabi bayan sa ta rugume sa ta baya tana fadin dan Allah kar kabar ni wallahi ni matar kace kuma sahibar kace, bai bari ta karisa magana nan ba yawani ture ta ajikin sa yasa kafa yataka yatsan ta na hanu yana murzawa yana magana WALLAHI WALLAHI WALLAHI ko a hanya kika ganni kikace ni mijin ki ne kuma har da ciki jikin ki kuma wai nawa sai na kashe ki mtss yaja doguwar tsaki yabar gun baki daya, yabar Bintu tana furta "kar katafi kabar ni wallahi ina son ka, tana kuka sosai tana sumbatu,
A haka Alili yazo ya same ta afirgice yashigo gidan yana haki yana furta Bintu kitashi mu gudu mayu masu cin naman mutani suna daf dashi gowa gidan nan kitashi ni zanyi kokarin na dauki Garkuwa mugudu, Bintu tace yatashi kuma yatafi, Alili yace wani irin yatashi kuma ya tafi ina yaje? gabaki daya abunda yafaru Bintu ta sanar masa, Alili zama yayi a gun zaman dishin ya fashe da kuka ya manta da mayu nan gabaki dayan su kuka suke,
MAYYUN nan masu cin naman mutani ne suka shiga gidan ganin Bintu da Alili a wani hali yasa su suka kauce da dariya sukaye sukace mata da miji kukan baza mukashe kuba sai matar ka tahaifu zamu tsaka yaron agaban ku gafin mukashe ku............
_________________________________________
ALHMDULLAH
ALHMDULLAH
ALHMDULLLAH
ANAN NAKAWO KARSHEN MUKADDARI NE DAGA ALLAH TAKUN FARKO SAI KUBIYON A TAKU NA BIYU
TABBAS YANZU ZA'A SHIGA SARƘAƘIYA DA KUMA RUDIN KAUNA
ZAKUJI YADDA KHALIL YA NUFA DA KUMA YADDA BINTU DA ALILI ZASUYI DA MAYYUN NAN DA KUMA WAYE INJILA A GUN KHALIL KUDAI KUBIYO NI DAN JIN LABARIN WANNAN YARINYAR DA TABUGAWA KHALIL MOTO
SAI KUN BIYONI ZAKUJI
BY
SUHAIMA ABUBAKAR SHEHU +2349168176464