Showing 12001 words to 15000 words out of 54699 words
Chapter 5 - Mukaddari Ne Daga Allah Complete Hausa Novels By Suhaima Abubakar Shehu.txt
Allah sai na miki abunda baki taba tsammani ba, ya kauce da dariya yace kema kinsa abunda zan iya komai zaki mata daga yanzu zuwa gobe zan gani atafin hanuna yafada yana nuna mata hanun sa, batsa na wuce ko saina bangaje ki ae kuwa babu shiri ta matsa, harya kai kofar gida yaga Baffah dawowa yayi ya tsuguna ya gaishe sa yayi ficewar sa, duk gari Bushar wa Baffah ne kawai yake bashi girma,
"Haka inna jummai tana gani tabar Bintu taci tsiran ta ta kwanta Baffah sai godewa Allah yakeyi, dama akace gaba da gaban ta,
Khalil
"Mutsu-mutsu yafara da alaman dai yafarka, rike kansa yayi yana juyawa akan katafar, hawaye sai zuba sukeyi acikin idanuwan sa, baki daya baya cikin haiyacin sa kuka yake sosai kamar karamin yaro ahaka Alili yashigo yasame sa abirkice Alili ya farama masa magana cikin yaran sa, kafarka ne? Yakake jin jikin ka? yamasa tambaya lokaci guda, dagudu Alili ya juya yanufi kakan sa yana fadama masa, bai karasa maganan ba kakan Alili yatashi suka koma dakin yadda Alili yabar sa haka suka shigo suka samai sa rike da kai hawaye sai fita yake acikin idanuwan sa,
"Rayuwa kenan baka sanin yadda kaddara zata samai ka yau Khalil ne wance akan wata katifar da baitaba ganin irin taba, baima san yadda kansa yake ba"
Da taima kon Allah dana kakan Alili suka samu yabar murkusuwa akan katifa nan,
"Kakan Alili yaduba Alili yace gaskiya jinyan wanan mutumin na asibiti ne kagafa rike kayin sa yake gaskiya yana bukatar likita ya duba sa, Alili yaduba kakan sa yace hakane amma kuma ina zamuga likita har mukai sa ya duba sa mubar sa kawai anan tunda ya farka insha Allahu zai tashi cikin aminci yakarasa magana yana duban mutumin da ya tsuto cikin matukar tausayin sa,
Kakan Alili yace too Allah yasa, " gyra masa kwanciya sukayi kakan Alili yace shi yatafi dayake Alili ad'akin yake kwana"sai da safe Alili ya masa,
"Cikin dare karfe 2:46 daidai Khalil yafara bude idanuwan sa da suka masa nauyi, cikin sauri Alili yatashi yana masa magana kafarka? Ina yake maka ciwo? duk yajera masa tambaya lokaci guda,
!kallon sa kawai Khalil yakeyi baya fahimtar abun da Alili yake fada masa, Alili kuma shi damuwan sa mutumi nan ya masa magana ko zai ji sanyi cikin zuciyar sa .........
"Alili yana ta masa magana damuwan sa wannan mutumin ya masa magana, khalil kallon sa yake kwai baya fahimtar sa, " Alili fita
ad'akin yayi ya nufi d'akin kakan sa dan yasanar masa cewa fah wannan mutumin yafar ka,
"Kaka katashi yafarka fah amma baya magana kaka kana jina kuwa yakarasa maganan kamar zaiyi kuka"
Kaka yace Alili ina jinka fah gani futowa ya karasa magana nan yana mikewa, fitowa yayi suka nufi dakin dan ganin halin da mutum nan yake ciki, shiga cikin daki sukayi yadda Alili ya barsa haka suka zo suka same sa,
"Kaka ya dubi mutumin da har yanzu basu san sunan sa ba magana ya fara masa da yaran su, yawwa bawan Allah ka farka yau kima nin wata guda kenan kana kwance a nan baka san yadda kanka yake ba sai yanzu Allah yayi zaka tashi, yanzu dai katashi kasha koda koko ne dan rabon ka da abinci kajima yakarasa magana nan ya kara kai duban sa ga mutun nan,
"Khalil kallon kaka kawai yakeyi baya fahimtar abunda kaka yake fada masa, idanuwa ya zuba masa sai bin sa da kallo yakeyi, Alili yace kaka anya kuwa yana cikin hankalin sa kuwa sai magana muke yi amma yayi shuru baya ko magana, kamar zai yi kuka ya karasa magana nan,
Kaka yace in sha Allahu zai dawo dai-dai Allah yasa Alili yafada yana kara duba mutun nan
"A haka suka kwana ajikin sa dan kar su tafi kuma yazo yana bukatar wani abu"
Bayan gari ya waye ne kaka yasa Alili yakai masa abun karyawa, kuku da kosai Alili ya kaiwa Khalil
Hmmm rayuwa kenan yau khalil ne aka kai masa kuko da kosai mutumin da shi abinci ma saiya zaba Allah kama maikyau,
"Shiga d'akin Alili yayi ajiye kokon da kosain yayi agefe ya koma wajan khalil, taima ka masa yayi ya dakasa, bayan yadaga sa, ya koma ya dauko kokon nan da kosai dawowa yayi kurin khalil ya mika masa kokon nan, khalil bin hanun yayi da kallo, Alili yace kasha nasan kana jin yanwa dan rabon ka da abinci kaji ma, kallon sa kawai khalil yake yi, Alili ya fahimce wannan mutumin baya jin magana nan sa fah dan haka yakai kokon bakin sa ya nuna masa yadda zaiyi, ae kuwa shima khalil yayi haka, sosai Alili yaji dadi yacigaba da bashi dakan sa,
Bayan ya gama bashi ne sai yameke alaman zai tafi, juyawa yayi da niyan tafiya yaji ancefke hanun sa, ae kuwa da sauri Alili ya juya yana kallon sa, still Khalil baiyi magana ba, girgiza masa kai Khalil yake masa hawaye fal cikin idanuwan sa.........
"Idanuwan sa fal da hawaye, Alili yace mai ya faru kana bukatar wani abu ne? still khalil baiyi masa magana ba sai kallon sa yake, hawaye ne suka zubo daga idanuwan sa, kuka yake sosai kamar karamin yaro, hankalin Alili ya tashi matuka ya rude mai ya faru dashi yakeke kuka kashi ya k'i sake sa bare ya kira kakan sa,
" Kuka sosai Khalil yake kamar kara min yaro duk wanda yaga Khalil a wannan hali sai ya tausaya masa, Alili magana yake ta masa kana bukatar wani abune kodai na maka wani abu ne? bansani ba, shima kuka yasa yana kiran kaka, kaka, kazo kazo yana kuka yana kiran kaka, duk wanda ya gan su sai tausaya musu,
"hawaye ne suka suba acikin idanuwan suhaima tana rubutu tana kuka abun yabata tausayi,
" Bintu zaune ka kasuwa zuba idanuwan ta tayi tana ganin ta yadda Alili zai bulo ako wata safiya sai Alili yazo gun Bintu inta fita talle, yazo sun gai sa amma yau shuru, hankalin Bintu ya fara tashi Alili bai taba mata haka ba kodai ba lapiya yake ba, girgiza kai tayi tace in Allah yadda yaa Alili yana cikin koshin lapiya, bari ko zuwa anjima ne, nasan wani abu ne yari kesa nasan zai zo,
"Har Bintu tagama sai da kokon ta Alili bai zo ba hankalin ta yatashi sosai, addu'a tafara cikin zuciyar ta Allah yasa kar Bushar yazo yau dan ko yaushe sai yazo yarakata gida idan tagama sai da kokon ta "
"Yaso ya hanata amma Bintu tace kar yafara ita tace zatayi badan tana son talle ba a'a saboda tana tausayin Baffah ta saboda aduk lokacin da Bushar yayi ma inna jummai fada akan karya sake ganin Bintu tayi wani abu to fah kan Baffah ta zata koma shiyasa tace ita tace zatayi saboda tasan kullum idan garin Allah yawaye sai tayiwa Baffah fada idan ta tuna Bushar ya hana Bintu talle shiya tace tana so ne, kuma Bushar najin magana nan Bintu sosai,
"Ae kuwa addu'an Bintu ya karbo dan yau Bushar baizo ba, taji dadi sosai,
" Gidan su Alili ta nufa dan ganin ko yana lapiya dan har addu'a takeyi cikin zuciyar ta Allah yasa yayan ta Alili yana lapiya, bayan ta iso kofar gidan tsayawa tayi ta fara tunanin tashiga ne ko kar tashiga, sai kuma tace ae gidan su ya Alili kamar gidan su ne kakan Alili yadauke ni tamkar jikan sa ne, kawai nashiga, bayan tagama yanke shawaran shiga cikin gidan, kafafuwan ta tasaka cikin gidan da sallama acikin bakin ta, ta kusa kai cikin gidan, sallama takeyi atsakar gidan amma shuru babu kowa,
Alili zama yayi kusa da Khalil yana masa magana yana kuka yana cewa kafada mun mai yasa maika kake kuka wani abu ya faru dakai ne, kuka sosai Khalil yakeyi harda shasheka, Alili shima haka kuka yake sosai, kuka sosai sukeyi kamar wanda aka musu mutuwa,
"Bintu tana ta sallama shuru saboda kaka baya gidan tun lokacin da Alili yake kiran kaka akan Khalil na kuka baya gidan yatafi daji dan nimowa wannan mutumin maganin da zaisake samun karfin jikin sa,
Har Bintu tayanke shawaran komawa, " Kawai taji shashekan kuka ad'akin ae kuwa hankalin ta yatashi sosao ita atunanin ta wani abu ya faru da yayanta Alili shiyasa bai zo yau wajan taba ae kuwa bata sanda tashiga cikin dakin ba babu ko sallama gabaki daya bata ma cikin haiya cinta, ya Alili kawai take fada sam bata cikin haiyacin ta Ya Alili mai yasa maika, sam bata lura da abunda ke faruwa acikin dakin ba,
"Alili rike hanun Khalil yayi yana kuka yana masa magiya ya fada masa mai yasa shi kuka haka,
Khalil daugo kan sa yayi ya daura idanuwan sa akan Bintu ae babu shiri yafisge hannun sa daga rukon da Alili yamasa kai tsaye gurin Bintu yayi , yana isa wajan ta yaron gumota ajikin sa sai bari yakeyi yana fadin..........
"Cikin barin jiki Khalil ya rumgume Bintu yana cewa ki boye ni zasu kamani suka she ni, " Kuka yake sosai karamin yaro abu daya yake tafadi, "kiboye ni zasu kamani sukashe ni" Sake rumgumo ta yayi akirjin sa gabaki daya yamata rumfa, k'ankame ta yayi ajikin sa, Bintu tsaban tashi cikin rudani takasa kwace kanta ajikin sa, tashiga bakon yanayi, wanda tunda take acikin rayuwar ta bata taba shiga cikin sa ba, tunda take arayuwar ta namiji bai taba mana haka, tsaban ta rude takasa tabuka komai, shi kuma khalil sai kara cusa kansa yake akirjin ta yana fadin zasu kamani su kashe ni, "
"Alili idanuwa yazuba musu yadae na kuka amma kuma abun yana ta bashi mamaki me hakan ke nufi da wannan bawan Allah kansa kalau kuwa kodai mahaukaci nakawo gidan mu, duniyar tunani yashiga, sai sake-sake yakeyi cikin zuciyar sa, "
"Sumewa Khalil yayi dukan su suka zube akasa anan ne Bintu ta dawo haiyacin ta tunda ga farkon shigo wanta gidan harda shigan ta dakin sai ta tsaya tayi tunani ae kuwa nan, Bintu ta meke tana zare zazzaran idanuwan ta hawaye fal cikin su, sam bata lura da Alili ba tayi da tasanin shigan ta daki baki daya gidan ma tayi da tasani, kokarin ta bar dakin, har tazura kafan ta awaje, taji Alili ya kira sunan ta, Bintu " tsayawa tayi cak ita bata karisa fita ba, ita bata koma ciki ba, "
"Tun lokacin da Khalil yafadi Alili ya dawo daga duniyar da ta aura tunanin sa, yadawo cikin haiyacin sa, "yace Bintu idawo kar kitafi wannan shine mutumin danake fada miki na tsuto sa adaji, tun jiya yafar ka amma baice mana komai ba, sai kuka yake sai da yaganki naga ya fiske hanuna daga rukon da na masa, yaje wajan ki, karki tafi kitsaya dan Allah suma yasake yi nasan dole zai bukace anan gun tanan ne kawai zamu gane mai yafaru dashi, "
"Bintu bazata iya musu wa Alili ba dan haka takoma ciki, mikewa Alili yayi ya fita adakin, randan kasa naga yanufa, yacika kofi da ruwa mai sanyi, komawa dakin yayi kusa da Khalil yanufa, ruwan ya watsa masa akan fuskan sa, doguwar numfashi Khalil ya sauke tare da tashi araza ne yana baza manyan idanuwan sa da suka numshe, sai mutsa bakin sa, yake yi da alama magana yake son yi yana ta baza manya-manya idanuwan sa, daura idanuwan sa yayi akan Bintu ae da sauri yanufa wajan ta, "
"Bintu tana ganin ya nufa wajan ta tafara jada baya tana kokarin boyewa abayan Alili, dan gaskiya bazata bari yanzu yataba taba, "
"Ganin tana kokarin guduwa yasa Khalil tsayawa cak ya fara magana, kema gudu na zakiyi kowa baya sona babu wanda yake kulane sai ke amma kema yanzu guduna kike yi yana magana hawaye suna zuba cikin idanuwan sa,
" Cikin rudani Bintu da Alili suka shiga kamanya daman yasan Bintu ne dama kodai yasamu tabun kwakwalwa ne, "
"Khalil yace inna miki laifi ne na yarda kizane ni amma dan Allah karki kuje ni MiMi, Mimi suka hada baki wajan furtawa baki dayan su da Bintu da Alili,
" Kaka ne yashigo gidan da ganyan maganin da yasamowa wannan mutumin da suke jinyan sa, kai tsaye dakin da yake kwance yanufa, ae yana shiga ya tsinkaya muryan mutumin nan yana magana, tsayawa yayi cak sai da yagama sauraro ya kusa kan sa cikin dakin, "
"Alili kaka ya kalla yace ae nace maka jinyan nan wannan mutumin na asibiti ne, dan haka ya kamata mukai sa asibiti gobe in allah yakai mu
Alili yace.............
Alili yace Allah yakai mu goben insha Allahu zamu kai sa,
"Khalil durku sawa yayi akasa yana kuka yana cewa Mimi dan Allah karki gujeni kamar sauran mutanin, yana kuka yana mata magiya akan karta barshi, daga Kaka har Bintu sunshiga tashin hankali sosai yasan Bintu ne
" Alili ne yanu fah wajan Bintu kama hannun ta yayi ya fara mata magana cikin sanyin jiki, Bintu nasan baki sanwan bawan Allah kamar mu bamu san ko ma haukaci bane amma gashi yana magana ne cikin hankali dan Allah Bintu ina son kimun taimako ki taimaka ki isa wajan wanan bawan Allah kece kawai mafitan mu musa mu kan sa, shifa masoyi abun so ne, makiyan ka kuma abun, kine Bintu tunda yanuna yana bukatar ki kitai maka karyasa ke shiga wani hali dan Allah Bintu Alili yahada hannuwan sa duka biyu alaman yana rokon ta,
"Girkiza kai Bintu tashiga yi tace haba yaa Alili basai ka roke niba insha Allahu idan nice sanadin warakan sa zanyi bakin kokari na ganin yasamu lapiya, takarisa magana nan tana nufar wajan sa,
" Magana tafara masa cikin sanyin muryan ta mai dadin sauraro, tace haba yazan tafi nabar garkuwa na kaima kasan bazan tafi nabar Sadauki na ba kasan ina ji dakai Sadauki, kaine fah abun alfahari na awannan duniya nan kadai na kuka kar kasani nayi nima inkana wannan kukan kana karya mun zuciya ta, kadaina karka sani kuka nima, "
"Kallon ta Khalil yakeyi cikin wani karamin muryan sa mai dadin saurara yace bazaki barki ba ko Mimi, ehh bazan barka ba Sadauki na, sosai Khalil yareke hanunu wanta kamar wani zai kwace masa ita "
*******
"Abba sai shirye-shiryen tafi india sukeyi, gobe ne tafiyan su, Abba ne ya kalla umma yace Rahama gobe ne tafiyan mu insha Allahu sai ki kula da gida, kinga halin da Hafsatu take ciki magana ma batayi babu abun da takeyi saidai adaka akwantar bamu san sanda zamu dawo ba nasan kina da kokari to dan Allah kikara, umma tace insha Allahu zan iya bakin kokari na, kuma samu tamata addu'a Allah yasa atafi asa'a Allah yabata lafiya, amin amin Abba yace yaji dadi sosai da addu'an umma yasanta da kokari sosai, mikewa yayi yace bari nadan je gida nadawo, adawo lafiya umma tace masa,
"Abba yana shiga cikin gida yaji hayani acikin gidan sa, da sauri yashiga cikin parlo amma babu kowa kuma still yana jin hayaniya, kai tsaye sama yayi dan daga gun yake jin hayaniya, ae kuwa yana isa gun yaga su Khairat, da Khalisat, da kuma kulthme, zaune abakin kofan d'akin Kulthme sai kuka suke suna magiya akan Kausar tabude musu kofar dakin tunda zo takulle kanta adakin tana kuka tana cewa ita akaita gun momyn ta babu idan za akai mata momyn ta ae dan sunga babu yaya KYC, ne dama shine mai son ta bayan momyn ta kuka take sosai , Khalisat tace haba autan momy wayace miki muba muson ki ae duk gida nan babu wanda yakai ni son ki, momy fah saboda bata da lapiya ne za aje nima mata magani, addu'an mutake bukata, ba kuka ba haba haba yar autan momy da Abba da umma, ooo nikam ban yarda dake ba to naji momy magani za'a nima mata to yaaa KYC fah kufada mun inda yake kullum kuce mun yayi tafiya kuma haryan zu bai dawo, takari sa magana nan tana kuka mai karya zuciya, Khalisat ce tace babu inda yaa KYC yaje mutuwa yayi kuma idan. bata kari sa magana ba Khairat ta rufe mata baki, ae kuwa Kausar taji komai, sumewa tayi akan gadon, magana Khairat take mata amma shuru ko numfashin tama basuji, "
"Khairat ta dubi Khalisat tace haba mai haka kikayi ita dayace fa adakin kika fada mata wannan magana nan duk tsananin yaa Khalil yana matukar shagwaba Kausar itace kawai take ganin dariyan sa amma zaki fada mata wannan magana nan, "Khalisat tace to kullum zamu ringa boye mata ne bayan idan an mutu ba adawowa, " Khairat tace za afada mata mana amma ba ta hakaba, to acikin haka ne Abba yazo yasame su, "
"Abba ya tambaya abunda yake faruwa Khairat ce ta faiyace masa komai, kai tsaye kufar dakin yayi bugu yakai masa ae kuwa sai ga kofa ta bude, baki dayan su suka shiga cikin dakin kai tsaye gadon da kausar tak kwance akai suka nufa,
" Asume suka same ta babu numfashi atattare da ita gabaki dayan su sunshiga cikin tashin hankali dukan su sun rude sun rasa mai zasuyi, Khalisat kuwa tayi da tasanin fada mata da bata fada mata ba da duk haka bata faru ba, kuka Khalisat da Kulthme suka fashe dashi, "
"Abba ne yayi azancin tura Khairat ta dauko ruwa , ruwa mai sanyi ta dauko akazoba mata, doguwar numfashi ta sauke, idanuwan ta taware akan Abban ta Abba...! tafada arede Abba dagaske yaa KYC ya mutu? Abba yadobe ta yace haba autan momy kina son momy tayi fushi dake ne ko yayan ki Ibrahim ae in sungan ki ahaka baza su jidadi ba haba yar autan yayan ta KYC, ki kwantar da hankalin, kitayiwa yayan ki addu'a shine kawai zai gane kina son sa dan ayanzu yafi bukatar addu an ki, kinji yar auta na,
"Girgiza kai takeyi kafada mun ya mutu ko yana raye kafada mun Abba, Abba yace yanzu nasan kingaji ki kwanta kiyi barci gobe da safe zamuyi magana,
" Dalalabi Abba yasamu yashawo kan Kausar, bayan tayi barcci baki daya Abba ya kira su,
"Ya dubi Khairat yace Khairat