Showing 36001 words to 39000 words out of 54699 words
Chapter 13 - Mukaddari Ne Daga Allah Complete Hausa Novels By Suhaima Abubakar Shehu.txt
tazo ta amsa bag din ta, abunda ake ta mai-maitawa kenan Aripot dinan
Juyawa Suha tayi dagudu tana bingefe-gefen mutani tana wuce su dan tagama mantawa da bag din ta sai yanzu dataji ana niman ta tukuna ta tuna,
Arjun sakowan sa kenan daga jirgi ya manna waya akun nan sa da alama waya yake, waya yake da Aaraw, Aaraw yace bro yakaji garin yama kuwa, Arjun ya lumshe idanuwan sa kana yadaura dacewa "wallahi tunda nasaka kafana akasan nan nakejin bugun zuciya, bugun zuciyar danake ji cikin mafarki na wallah kara tsanan take ye,
Aaraw yace gaskia Allahu ya nuna maka wannan yarinyar idan ba Aljanna bane kabar kasan kama bazata narka ka huta ba, Allah har nafara tsanan ta,
Arjun baice masa komai ba sai tsakin tayai, tsaki yatayi akai-kai, Aaraw ne ya tambaya sa lapiya kake tsaki ko dan nace natsana wannan yarinyar datake damun mun d'an uwa,
Arjun yace wallah wata yarinya ce wai Suhaima Abdulkadir tamanta bag din ta shine ake ta cika kun nan mutani wajan niman ta, inbanda rashin kamun kai taya mutun yazo tun daga wata kasa kuma ace yamanta bag dinsa daga gani zatayi rawan kai,
Aaraw murmushi yayi baice komai ba suka canza firah,
Suha gudu take gashin kanta yana bin bayan ta, dai-dai lokacin da Arjun yasha kwana yana cigaba da waya da Aaraw, bugun zuciyar sa sai karuwa take, sosai Suha bangaje Arjun tayi batarai da tasani ba yayin da wayan tafadi kasa shi , Arjun dago kansa yayi dan ganin wata yarinya ce tamasa ta'asa haka,
Suha hartayi gaba, idanuwan sa yazubawa gashin kanta, juyowa Suha tayi ta dan hada hannayen ta biyu tace kayi hkr, 🙏
Sumewa Arjun yayi atsaye yarinyar da yake gani mafarkin sa, yau itace agaban sa, kafun yayi wani yunkuri yani maita yarasa,
INDIA
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
_________________________________________
____Arjun tsayawa yayi cak yarasa abunda zaiyi, yunkura yayi zaibi bayan ta amma kafun ya isa gare ta har tabace wa ganin sa, gabaki daya gurin babu yadda Arjun bai duba ba dan kawai yagan ta amma babu ita babu alaman ta,
Arjun yashiga tashin hankali sosai, wani ciwon kai ne mai zafi yakama sa, lokaci guda, adaddafe ya isaka gurin da akaturo masa, direba yashiga cikin moton,
Kai tsaye aka kaisa gidan daddyn sa dake mumbai gidane madai-daici dan uncle din sa yaso ya sauka gidan sa dan susaba da Sima amma kuma Arjun yanuna kin abincewar sa akan hakan,
Kai tsaye d'akin da ako dayau shi idan yazo India yake sauka, yashiga kai tsaye toitel yashiya ruwa yasakar wakan sa sai da yayi awa guda ruwa yana sauka akan sa kafun yayi wanka ya daura alola yafito, jallabiya yasaka ajikin sa tauzauna kamar dama ajikin sa akayi, kyau sosai tamasa masha Allahu kai tsaye masallaci yanufa, bayan ya idar da sallahn sa ya koma gida kai tsaye jikin windon d'akin sa yaje yatsaya,
Zubawa furani idanuwa yayi ga iskar datake kadawa, duniyar tunani yafada, yanzu kam zuciyar sa tagama yarda masa cewa wannan yarinyar Aljana ce,
Yanzu magana nan da Aaraw yafada gaskia ne, tabbas koda ita Aljana ce tabbas zan zauna da ita,
___Arjun duniyar tunani yafada, wayar sa dake kan bed ne tafara ringtone ne ya katsai masa tunanin sa, komawa yayi kan bed din ya dauki wayar ganin sunan Aarawn ne yasashi daukawa,
Aaraw jin Arjun ya dauka sai da yasauke numfashi wanda sai da Arjun ya jisa, Aaraw yace "ina kashiga ne tundazo damuke waya ta ktsaye, kuma inata kiran ka baka dau waya taba fatan kana lapiya ko? mai yafaru naji wayarka ta katsaye?
Nufasawa Arjun yayi cikin cool voice Arjun ya furta " nagan ta Aarraw"
Kaganta wakagani kardai yarinyar mafarkin ka? Arjun yace "ita" kana yadaura dacewa "Aaraw wannan yarinyar ba mutum bane Aljana ce Aarae zuciya ta tana mun zafi shin dagaske idan ita Aljana ce bazan kara ganin taba,
Zuciyata tana mun d'aci kaima kasan yadda nake son ta da kaunar ta ina son ta sosai Aaraw kataima kamun dan Allah, Arjun yakarisa magana nan cikin dashashiyar murya wanda yake daf da fashewa da kuka,
Aaraw yafurta " kuka zakayi Arjun?
tabbas nisheda ne akan son ta amma meyasa tazabi kai bayan tasan kai dan Adam ne babu aure a tsakanin ku nidai shawar da zan baka itace kullum nake fada maka, itace addu'a kacigaba da addu'a insha Allahu komai zai wuce addu'a tana maganin komai brother na dan haka zantaya ka kaji,
Sosai Aaraw ya kwantar wa d'an uwan sa rai kuma yamasa alkawarin zai cigaba da tayasa da addu'a har sanda aljna nan zatafi ta daga rayuwar sa, dan a yanzu Arjun ya yarda da itadin Aljana ce, amma kuma yasaka aran sa cewa fa koda ita Aljna nace sai ya aure ta yayi rayuwa da ita, dan yadda yake jinta nan bayacin zai iya hakura da ita,
Bayan sun gama wayar ne yakira ummin sa, amma bai sanar da ita abunda yake faruwa ba, bayan gaisawa kawai ta masa fatan nasara cikin rayuwar sa,
Daddyn sa yakira bayan kammala waya da ummin sa sun jima suna fira, kana sukayi sallama,
Babban yayan sa Siddarth yakira awaya, Siddarth yana daukan wayar Arjun ya gaishe sa kana yafurta "nayi kewar ka yayana kullum cikin kewar ka nake, Siddarth daga bangaran sa yafurta" nima nayi kewar ka sosai ya India fatan kaji dadin zuwa gun ko? girgiza kai Arjun yayi kamar yana ganim sa, yafurta ehh sosai, lumshe idanuwan sa Siddarth yayi kana yadaura dacewa "Alhmdullahi naji dadin hakan" Kana yadaura dacewa Arjun katayani da addu'a akwai abunda nasa gaba fatan Allah yaban nasara akai, Arjun yace insha Allahu yayana Allahu yashiga cikin lamarin ka, bayan sun kammala wayar ce Arjun ya koma kan bed din ya kwanta, yacigaba da tunanin da yazamo masa dole a rayuwar sa, ehh dole mana tun yana ganin ta a mafarkin sa gashi yanzu tana masa gizo,
Suha tana karban bag dinta tazzi tashiga ta nufi gidan da mom dinta tace ta sauka agun, a parlou ta sauka gabaki daya kayan ta agun tabari ta kwanta agun, tayi barccin ta suhaima kenan
Karfe 10pm ta tashi da wani yunwa da ya murde mata cikin ta, gashi babu komai a gidan dama itace zatayi siyayar komai idan tazo tunda babu wanda yake zama cikin gidan,
A parlou tabar bag dinta wanka tayi tasaka doguwar riga yamata kyau sosai kai tsaye gurin cin abinci tayi dan bazata iya barcci bataci abinci ba,
Arjun mekewa yayi ya nufi gun cin amincin dake kusa dashi dan shan coffi da shima babu wani abunci agidan sa,
____Suha bayan tashiga gun cin abinci tazauna akan kujera, list din abinci waiteres takawo mata tafara dubawa zaban abincin da zata iyaci tayi, bayan ankawo mata, faraci tayi ahankali tanaci tana lumshe idanuwan ta da alama dai bakad'an abinci yamata dadi ba,
Bayan tagama cin abincin tabiya kudin tamike ta nufi gidan ta dan gabaki daya agajiye take sosai, fita tayi tafara tafiya akasa dan babu wani nisa tsakanin gidan ta da gun cin abin cin,
Tafiya tayi mai d'an nisaka, sosai wata moto ce tasha kwana fitilan moton ce ta haska fuskan ta gabaki daya hasks moton yakashe mata idanuwar ta gashi bata ganin wanda yamata haka,
Magana tafara cikin masifa da nuna fa duk wanda yamata haka to tabbas kar yabari idanuwan sa suyi tozali da nata dan tabbas wallah Allah daya ne bazata barshiba,
Shikuma Arjun da yake cikin moton gabaki daya ya fita cikin haiyacin sa idanuwan sa kawai yazuba mata kallon ta yake sosai babu ko iftawa,
Suha kaucewa tayi daga hasken moton kai tsaye wajan mazaunin direban ta nufa, kwan-kwasa kofar tayi, zuge gilashin moton yayi zuwa kasa, kafe ta da idanuwan sa yayi yana kallon ta,
Suha tana hada ido dashi ya mata kwarjini amma hakan bai hanata magama ba tana magana zuciyar ta yana bugawa sosai, nunashi tayi da yatsa tafara magana cikin tsawa da nuna abunda kamun ya batamun rai "kai makaho ne ko baka gani ne kodai kai kurma ne kodai babu hankali ajikin ka ne, da zaka haska mun cikin idanuwa ta kuma nasan kasani amma kuma kacigaba da haska mun fuskata tabbas magana nan dake fada gaskiya ne akan ku, ku y'an India kuna da giraman kai da wulakanci danuna kuna da kyau, okayy dan ga ganka mai kyau ko, to karkayi tunanin haka nake to ba haka nake ba, taja tsaki tawuce abun ta tabar sa agun zaune kamar gunki,
Saida tabace wa ganin sa kafin yadawo cikin hai yacin sa, dukan kansa yakeyi kamar wani mahaukaci yana tambayan kan sa shin maike faruwa dani ne naganta kuma ta kubuce mun, mai take nufi da karnayi tunin haka take ita ba haka take ba, tunani yakeyi sosai, fasa shan coffi din yayi ya koma gida da fatan sake ganin ta koma yaya ne.
Arjun shigan sauie yayi yama sa kyau sosai, fita yayi a parlou yayi kai tsaye waje yayi sai gashi sa masu aikin gidan sukeyi yana amsa musu babu yabo babu fallasa, motar sa ya nufa ya kunna ta yabar gidan baki daya,
SIMA
___Sima wata rigace ajikin ta duguwa jaa sosai ya mata kyau futowa tayi tace Ammi na yayi mun kyau kuwa?
Wanda ta kira da Ammi ta numfasa kana ta daura dacewa haba Auta saunawa zaki sauya kayya ajikin ki tabbas karki sauya wannan rigan dan tamiki matukar kyau sosai Autana,
Sima tace Ammin ina son nayiwa sweet Arjun dina ne kyau sosai, Ammi tace ai kinyi kyau sosai,
WAYE SIMA
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
Mahaifin Sima DR Sulaim yana da mata Azara DR sulaim yaya ne agun Hajia Sarah wato mahaifiyar Arjun haifuwan Dr. Sulaim uku amma dukan su basa zuwa da rai, Sima ce kawai Allah yabasu tazauna sun dauki son duniyar nan sun daurawa Sima suna son farin cikin ta, sunsar garta ta komai tace suna mata,
Suna kaunarta shiyasa duk abunda take so suna kokarinyi mata,
CIGABAN LABARIN
_________________________________________
Abu ne yafito daga d'aki yana magana daughter na gaskia ke yarinya ce kyakyawa ai dole ma Arjun ya rikece miki yana ganin ki, murmushi Sima tayi tace "Allah ko Abuna" sosaima kuwa daughter na,
Komai da Arjun zai bukata agama hada masa jiran sa kawai akeyi,
Kafe 9:30Am dai-dai Arjun ya isa gidan tun daga ged Sima tazo da gudun ta tana masa oyoyo nufoshi tayi zata rumgume sa, yayi sauki kaucewa yafurta "hayanzu baki sauya ba ko" kama hannun sa tayi tana murmushi tana cewa "har yanzu bazaka gane yadda nake son kaba ko" Bai ce mata komai ba,
Bayan sunshiga parlou ne suka za zauna akan kujera ya gaishe da uncle din sa tare da Ammi bayan sun gai-gai sa suka fara cin abince, sosai Arjun yaci dama akwai yunwa atattare dashi, sai da suka gama cin abinci aka dawo parlou suka cigaba da tattaunawa,
Suna cikin tattaunawa Sima ta mike gabaki dayan su suka mai da kallon su kanta, Ammi tace ya ana cikin tattaunawa kuma naga kin mike, Sima tace "wallahi Ammina so nake mufita shan iska da swwet Arjun dina,
Abu yace " hakan ma yana da kyau sosai"dan haka sai kundawo,
Magana nan gaskia Arjun bai jidadin wannan fitan ba shiyasa bai so shiyasa bai son zuwa India saboda abunda su uncle din sa sukeyiwa Sima komai tace tana so suna mata, babu yadda zaiyi haka ya tashi yabita suka tafi,
Suha sai karfe goma tayi wanka tashirya cikin rika da wando, tayi kyau sosai kamar ka dauke ta ka gudu da ita, gashin kanta kuma zubashi tayi abayan ta farin gele ta dauka ta rataya akan ta tafito sak baturiyan ta, Suha badai kyau ba bag dinta ta dauka tafita daga cikin gidan baki daya,
Tsayawa tayi cak a kofar gidan tana tunanin ta ina zata je tafara siyayyar, acikin zuciyar ta kuma tunani take anya bazataje cin abinci ba, yanke shawaran fara zuwa cin abinci tayi, ai kuwa tana zuwa taga gun cin abincin arufe, tambaya tayi ko mai yasa masu gurin cin abinci nan basu fito ba? wanda ta tambaya yace mata ae basa fitowa ranan sunday, bata jidadin hakan ba ga kuma yunwa da yake damun ta sosai haka ta juya ta nufi gurin da zata je,
Arjun zaune cikin motar sa gabaki daya gurin da sukazo da Sima gurin yarane sai wasan furere sukeyi na omo ga wata iska tana kadawa mai dadin shaka, lumshe idanuwan sa yayi yana kara tunano yarinyar nan da take a daddaban tunanin sa, wanda duk sanda zai kwanta tofah tabbas sai yagan ta a mafarkin sa,
Suha ne ta yanko gun da Arjun yake shi da Sima, Arjun yana cikin moton yayin da kuma Sima tana waje tana siyan sweet,
Idanuwar Arjun a lumshi zuciyar sa tana bugawa a dai-dai lokacin da kuma Suha takusa daf dashi, kamar anjewa Arjun ya bude idanuwar sa, kawai ya fara bude su a hankali-hankali ganin kamar gizon ta yakeyi, ai bai san sanda yakara kwangale suba, domin tabbatar da ita yagani, ai kuwa ita yagani tana tunkaran sa, gefen sa ta wuce gilashin motan sa ya saukar dan ganin kara ganin ta, ai kuwa itadin ce ya furta haka cikin zuciyar sa,
Wasu yara ne kananu suka kewaye Suha suna watsa mata fure, ita kuma tana saka hannun ta tana bebegewa tana murmushi, wayyo kuzo kuga yadda Arjun ya rude sosai, bai masan da ya fito daga cikin moton ba yazuba mata idanuwan sa mai riketa mata.
___Arjun tsayawa yayi yazubawa Suha idanuwan sa masu rikitar da mata, yayin da Suha sai murmushi take cikin yaran tana bibbige hannun ta, sosai ta kashe Arjun da wannan murmushin ta,
Sima ce tazo gurin Arjun kanta ta kwantar a kirjin Arjun tace "swwet Arjun mutafi nagama siyan sweet din Arjun baima san Sima tana masa magana ba, sai da Sima tadan buga kirjin sa tana tura baki tukuna Arjun ya dawo cikin haiyacin sa yafara magana cikin yake " kingama mutafi ko" ehh nagama cewar Sima,
Haka Arjun yana ji yana gani yabar gun bai samu yayiwa Suha magana ba datake tafaman wasa cikin kananun yaran nan,
KAUYE GUMA
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
_______________________________________
__Khalil yace gani nan ai kuwa kallo yadawo kansa baki daya mutanin wajan suka fara sauke numfashi, Bintu wani wawan juyi tayi jin muryan sahibin ta Alhamdullahi ta furta yayin da Kaka kuma fuskan sa ta sauya da murmushi, gabaki daya gurin kowa furta Alhmdullah yakeyi,
Mai gabatarwa kuma yace "kazo amakararan lokaci amma yanzu ma bai baciba zamu iya fara gasar,
Kamar yadda Bushar yayiwa Khalil wancen lokacin haka mai gabatarwa ma yafara yayi bayani, Bushar hankalin sa kwance damuwar sa wannan gasar a fara kuma agama ta dan ya sauya wata gasar wanda yana da tabbacin zaici wannan gasar,
Bushar rigan sa yaci rai kamar dai yadda Khalil yayi wancan lokacin, mai gabatarwa ya fara magana yace zan fara da daya, zuwa uku sai a fara haka kuwa akayi, mai gabatarwa kuma ya fara "daya, biyu, uku, a farah haka kuwa Khalil ya fara gasar,
Bulalan da su Khalil suka dauka ne a hannun Khalil ya tunkara Bushar dashi, Bushar sai sake murmushi yakeyi, dan shi so yake agama wannan shadin ga maganin da yashafe jikin sa dashi sai sheki yakeyi
Bulalan Khalil ya daga ya zubawa Bushar runtsa idanuwan sa Bushar yayi tabbas yaji zafin bulalan nan amma kuma ya sake murmushi gai kana ganin murmushi nan kasan na karfin haline, sai da akayi guda biyar kafun Khalil ya tsaya da bulalan dan aduba fuskan Bushar aga ko yayi hawaye, amma kuma fuskan Bushar babu hawaye, mai gabatarwa yace acigaba fuskan Bushar babu alamun hawaye, budan bakin Bushar yace kar abar bulalan sai angama, mai gabatarwa kuma yace ai ba haka tsarin gasar yake ba, idan kayi kuka fah, Bushar yace koda nayi kuka kar kubari kucigaba dan nasan bazanyi kukan ba, haka kuwa aka cigaba da bulalan, guda 50 akayiwa Bushar sai ga hawaye ya cika idanuwan sa, Khalil cigaba yayi da bulalan Bushar kuma yana kuka kamar karamin yaro daga karshe ma fita yayi afilin da gudun sa dan bazai iya juran bulalan nan ba mai shegen zafi sosai ba, ai kuwa mutani suka fara dariya wasu harda rike ciki wasu kuma harda kwanciya, sama mutani sukayi da Khalil sunata juya sa suna fadin munsamu jarumi a kauye mu, Bintu tsabar farin ciki rasa yadda zatayi tayi, sujada tayi kamar dai wancan lokacin, Kaka kuma farin ciki har yakasa rufe bakin sa,
Bayan kowa ya nutsu mai gari ya fara magana cikin jin dadi dan gabaki daya garin sun ji dadin nasaran da Khalil yasamu dan dama Bushar ya gundiri kowa agarin, mai gari ya fara da "Alhmdullh Allah shine abun godiya tabbas komai tsanani yana tare da sauki yanzu kam Allah yakawo mana saukin annoban wannan mutumin Bushar dan haka Allah zamu gode da yakawo mana wannan mutumin cikin kauye nan, mai gari ya mai da kallon sa kan Baffah Bintu yace kamar yadda muka tsara duk wanda yaci wannan gasar shine zai aura Bintu to yanzu nan za'a aurawa Bintu da Garkuwa fatan gabaki dayan ku kun amince Baffah yace na'amince Allahu yabasu zaman lapiya gabaki daya gurin ya kauce da Amin Amin
Mai gari ya dubi Khalil yace kaje kashirya karfe 3:30pm za adaura maka aure da Bintun ka, Khalil tsaban murna rasa yadda zaisaka kansa yayi shi da Alili suka mike har da Kaka, yayin da Baffah ma ya mike zaije yashirya dan zuwa daurin auran yarinyar sa, farin ciki cikin zuciyar Baffah ba'a magana
Bayan Kaka yadawo gida ya saka Khalil da Alili su fada masa mai yasa basu dawo da wuriba,
BARI MUJI YADDA SU KHALIL SUKA FITA A DAKIN NAN
Khalil suna ta murnan samun bulalan nan suna tsaka da ganin bulalan kofar ta fara rufuwa ai sukayi kofar da gudun su dan karta rufe dasu amma kuma ina kofar ta rufe dasu, sun shiga cikin tashin hankali sosai da sosai gashi sunyi nasaran samun bulalan amma kuma babu da man fita daga cikin d'akin dur kusawa sukayi a kasa agun Alili kuka yake harda hawaye Khalil ma haka kuka suke kamar babu gobe