Showing 39001 words to 42000 words out of 54699 words

Chapter 14 - Mukaddari Ne Daga Allah Complete Hausa Novels By Suhaima Abubakar Shehu.txt

sun fida rai da sake ganin nasu Alili kuka yake yana furta wayyo Allah na Kaka shikenan bazan kara ganin kaba wayyo rayuwa ta shikenan na banu na lalace sosai suke kuka a haka har barci ya dauke su, iskar asubahi ne ya tashe su daga barcin da sukayi mai cike da munanan mafarkai ganin yadda suke ne yasake basu da man kuka sosai, suna cikin kukan ne suka ji murya a saman kan su, muryan mutumin da yake musu magana ne kuma yanuna musu hanya har takai sun samu bulalan, wannan karon kam ya fito musu amma basu iya ganin fuskan sa, magana yafara musu a tsaye yace "tabbas lokaci ya kure muku kuma dama wannan hanyar ba'a fita idan anshigo ta dan haka zan nuna muku hanyar fita to amma kuma akwai bakin Aljani Kahu agun tabbas bazan iya dashi ba amma kuma zan nuna muku idan kunyi nasaran wuce hanyar to tabbas wannan gasar kai ne zakayi nasara akan ta, amma kuma wani sa'in idan ya kwanta barcci baya sanin akwai mutani a gurin da yake domin bai cika barcci sosai ba, idan kunci sa'a yayi barcci to shikenan zaku waje dan haka kutashi nanuna muku hanyar lokaci yana kuraiwa, haka kuwa sukayi gabaki dayan su suka tashi, hanyar da ya nuna musu suka bi, sunsha wahala sosai domin hanyar tsiririya ce Allah ne kawai ya taimake su suka yi nasaran fita a hanyar kuma sukaci sa'a Aljani Kahu barcci ya dauke sa, numfasawa Kaka yayi da ya gama jin labarin yace Allah ya taimake ku yanzu kutashi kushirya kar lokaci ya kure, haka kuwa suka mike suka dau haraman shiyawa domin daurin auran Khalil da Bintu,


BUSHAR

Bushar kai tsaye wajan Bokan sa yayi domin a wannan lokacin da niyar kashe sa yaje gun, yana isa kokon Bokon ya hau dukan Bokan nan sai da yamasa jina-jina kafun yarabu dashi kuma yabashi umarni yabar garin baki daya idan kuma ba haka ba zai kashe sa, haka kuwa Bokan nan yabar garin badan ran sa yaso ba sai dan yana tsoran Bushar idan yace zai aikata abu to tabbas zai aikata, Bushar ihu yasaka mai cin zuciya yana furta bazan barka ba nine nan zan kashe ka kazo gari na kuma karabani da abar sona kuma kayi nasara akai na kowa a garin nan yana jin tsoro na amma kuma yau kasa kowa ya rabu da tsoro na sai na kashe ka nine zan kashe ka ya kuma ihuu yana magana cikin fitar haiyaci,



BINTU

Yau take sallah agun Bintu daga gurin gasar kai tsaye gida tayi domin yau tana cikin farin ciki zata aura zabin ran ta, tana shiga cikin gida ta tarar da Inna Jummai a tsaye a kofar gida tare da muciya a hanun ta, Bintu tana ganin Inna Jummai da muciya ahanun ta taja da baya dan bata son yau ataba lapiyar jikin ta yau auran ta guda, Mero ne tazo tarike hannun Inna Jummai tafara magana cikin sanyi murya "haba Inna ke baki jindadi idan baki dauki hannu ki kinduki Bintu ba haba haba Inna wallahi abunda kikeyi baki kyau tawa Inna Jummai tace Mero ki matsamun yau na kashe yarinyar nan bazata taba aure ina da rai ba, yarana biyu dukan su babu wanda yayi aure sai ke yar tsutuwa wallahi Allah bazakiyi auran nam ba matsamun Mero!! Mero tace "wallahi Inna bazaki duke taba idan kuma kin matsa sai kin duketa to tabbas saidai kifara dukana dan Allah bazan bari kiduke taba, zainab tace Inna meye abun duka anan dan zatayi aure bayan dan tsutuwa ne zai aura yar tsutuwa dan haka Inna ta karki wani damu kanki, ajiye muciyar Inna Jummai tayi dai-dai lokacin da Baffah yashigo gidan, harara Inna Jummai ta gallamasa tare da tsaki ta wuce d'aki abun ta Mero ne tayi masa barka da dawowa yawwa kawai yace kana yafito da kudi ya mikawa Mero yace "ayiwa Bintu lalle yau auranta, sosai Mero tajidadin hakan , lalle akafarayiwa Bintu da kitso tafito sak Amaryan ta Bintu kyakyawace sosai akamata kwalliya irin ta Amaryan kauye sosai Bintu tayi kyau abunta,


Alili bayan yashirya yafito yasamu Kaka da kuma Khalil yace nizan fita Khalil yace ina zuwa haka Alili yace jarumin garin mune fa zaiyi aure dole naje nayi sanarwa kowa yasani dan namu ai ba irin nasuba ne, murmushi kawai Khalil yayi Kaka kuma yace kadawo da wuri fa insha Allahu Kaka cewar Alili, haka Alili yace yakarba abun magana sifika yana tafiya a cikin gari yana sanar da auran Khalil da Bintu,


Alili yace "aure kofar shiga duniyar so da kaunar juna damba kuma foundation naginin shakuwa mai daurewa Aure masamar dukan wata alkhari wannan ne yasa Garkuwar mu jarumin mu da Amaryan sa Gimbiya Fatima Bintu daurin auran su da za'a daura a yau dinan sakamakon yin nasara akan Bushar dan haka kowa da kowa ana bukatar sa wajan daurin auran nan, fatan azo lapiya, gabaki daya mutani sunata jin-jinawa Khalil yayin da Alili yadaura dacewa kuma akwai shagalin dazamuyi da dare bayan ankawo amarya gidan ta Allahu yabawa kowa ikon zuwa,

Gabaki daya magana nan Alili akunan bushar ne sosai Alili yasake fusata Bushar,


Khalil yasha jamfan sa da hulan sa faran yadi masha Allahu yafito sak angon kauye hmmm yau auran Khalil da Bintu abun mamaki nace Allahu yabasu zaman lapiya, Kaka Khalil Alili suka tafi wajan daurin aure kuzo koga farin ciki da annashuwa atattare da Khalil kyc,


Dubin al-uman mutani ne suka sheda auran Bintu da Khalil bayan kammala daurin auran ne kowa yazo yana taya Khalil murna, da fatan zaman lapiya auran Khalil ya dauru yayin da kuma Bushar yake can da bakin cikin a cikin zuciyaar sa da kuma sake-saken abunda zaiyiwa Khalil


Bintu sosai take kuka agaban Baffahn ta nasiha yashigayi mata, "Bintu yau kinzama mace wanda ko wata mace wannan ranan take jira Bintu kinta so cikin wahala a cikin gida nan amma yanzu zakitafi gidan y'anci amma hakan baya nufin iyi abunda ranki yakeso saboda kinga gidan kiba Bintu tabbas nasan duk wanda ya aure ki yayi sa'a a cikin rayuwar sa wajan samun mata tagari dan haka kibi mijin ki sauda kafa duk abunda yace miki kimasa dan Aljanna nan ki tana gare sane kisani yardan Allah yana tare dake tunda har kika samu yarda na Bintu duk abunda kikayi azaman auran ki dayan biyu sakamako zai bayar inma dai jinjjinawa tarbiyar ki da kuma wanda suka tarbiyar dake ko kuma akasim haka Baffah ya numfasa kana ya daura dacewa kiyi kokarin karai martaba na kamar yadda nakarai martabar naki Bintu duk dana sancewa banyi wani abunda zo agani a cikin rayuwar kiba
hakika babu wanda zai miki alkawarin farin ciki mai daurewa amma kuma tabbas hakur, da kuma juriya, da kuma addu'a zasu baki Bintu ki martaba auren ki kamar yadda zaki so a martaba auran y'ay'an ki Bintu, Aure ibada ne dukan ibadah kuma tana zuwa da kalubale daga shed'an Bintu karki bari shed'an yayi galaba akan ki Aure gida ne mai zaman kansa wanda daga shi kuma ake zarcewa gidan Aljanna mata tagari dole sai tayi hakuri kafin tazamo tagari Bintu, kisaka gskiya cikin al'amuran ki Bintu kije Allahu yashiga cikin lamuran auran ki, addu'a zatabaki sa'ar yiwa shed'an bara'a

Sosai Bintu take kuka babu abunda ta iya furtawa haka aka dauketa akaita gidan ta saidai mu musu fatan zaman lapiya tare da samun zuriya masu Albarka,


Dandali auran Khalil da Bintu wakokin soyaya aketa sakawa mc ne yabukaci amarya da Ango afilin dandaki dan sununa farin cikin wannan ranar, ai kuwa sunfi to wakar soyaya akasaka musu masu sanyaya zuciya wakar Sadiq Sale Khalil kama hanun Bintu yayi suka fara juyawa, mutani kauyan suka fara magana kasa-kasa wakar Sadiq Sale wanda yakecewa

Natafi kuma nai nadawowa kuma ban komaba indai zakimun soyayyar gaskiya tare dake muyi zaunawa zama mai daurewa masu fada su fada mudai muyi dauriya narasaki zanyi shekewa karyi musawa nafi bukatar mu haka kai muzama tsitsya kanki bana iya jurewa wasu sukushe ki zan ma tubin daka dan daka makiya nidai kece, nanace maitsace ke natattance kyayawace bazaku gane dalilina ba,

Macen matace "sona gare ni zalama ne alkhari ne inna gujeka za'akirani tsinaniya shima masoyin ka abun sone makiyin ka abun kine idan naganka da wata y'a zamuyi yar watattiya koda sonka jaraftace na toshe kunne zan gada kai har nayi dariya zana tsaya inkakame inbibbine kai nagani acikin taro zanafada dole nafada kaine zabina

Kosufada kokarsu fada dai nidai sai kai sake ko sunki kaine kaine koda sunki gabaki daya taro bikin Khalil da Bintu yani shadantar da mutani kuma anyi farin ciki sosai daga karahe akai amarya dakin ta,



Bayan ankai amarya d'akin ta agefen gaton ta Khalil yazauna ya furta "Alhmddullahi yau dai burina yacika wajan zauran mace tagari farin cikin rai na Khalil yace Bintu mamaki yakama Bintu dan tasan a iya zamantakewar su baitaba kiran ta da Bintu ba amma kuma yau Khalil da Bintu ya kirata, gani tazuba mishi idanuwan tane yashi daga mata gira yace muje muyi alola muyi sallah godewa Allah haka kuma sukayi bayan sun kammala sallah ne Khalil yacirai rigan sa a lokacin Bintu tana karshen gado, kusa da ita Khalil yayi babu komai ajikin sa sai gajeran wando Bintu makuraiwa tayi ajikin gadon shi kuma Khalil sosai ya matseta ajikin sa ta yadda tanajin dumin jikin sa sosai magana yafara mata cikin kunnuwan sa, Bintu na wannan kyakyawan suna ne da yasamu daman radawa kyakyawar yarinya, darajan ki takai yanda babu wanda wani abun da za'a ya cewa kinyi sa'ar samu sa sai dai ace yayi sa'ar samun ki dan haka nine nayi sa'ar samun ki cikin rayuwa ta tun daga hijabi riga gyale wando da dankwali babu abunda zaki saka ace yayi miki kyau face kika masu kyau da kara hasken su Bintu ke ko acikin mata ke tamusaman ce ko a cikin kyawawa ta daban ne hakama ko acikin abubuwa masu daraja ke mafi darajan cikin su ne nikaina ba daga nan ba yanzu dana sameki Bintu, komai nawa yadawo kan saiti ina matukar son ki Bintu, ina burin kasancewa dake a cikin rayuwa ta Bintu ina son ki Bintu irin sosai dinan fatana Allahu yabamu zaman lapiya mai daurewa


Sosai Bintu tashiga cikin tsananin murna da kuma fargaban kar wata rana tarasa shi tabbas arana nan zata iya mutuwa domin tana matukar son sa

Wata sanyayiyar shakuwace tasake shiga azaman auran Bintu da kuma Khalil sosai suke bawa junan su kulawa musamman ma Khalil baya kaunar Bintu tayiwani abu idan ba yazama dole ba akoda yaushe suna manne da junan su Khalil shiyake taya Bintu komai, babu idan da Khalil yake zuwa sai da yayi kusan sati biyu kafun Alili da Kaka suka zauna sukayi magana akan yakamata fah Khalil yaringa wani abunda kodan saboda rikon gida, haka Kaka da Alili suka hadawa Khalil kudi domin yafara wani kasuwanci dan yafi zaman dayakeyi agida, haka kuwa Alili yasamu Khalil har gida yadan kamasa kudin sosai Khalil yajidadin kudin kuma yayi musu godiya,

Khalil ya nima shawara agun Alili akan abunda yakamata yafara siyarwa, Alili yace idan har babu wata damuwa kafara saida kayan miya kamar su ataruhu da albasa da kuma tumatur, Khalil yace babu wata damuwa hakan ma yayi, Alili yamike yace to ni zan tafi sai idan Allah yakai mu gobe zan shigo da wuri domin zuwa sarin kayyan miya dan haka kashirya da wuri, insha Allahu zan shirya cewar Khalil haka sukayi sallama Alili yatafi Khalili yashige cikin gida,

Bintu tana zaune abakin murhu tana aza wuta dan tana sauri taga tagama abinci dan kar Alili yatafi baici abinci ba Khalil yashigo gidan, Bintu batama san Khalil yashigo gidan ba,

A hankali sadaf-sadaf Khalil yake zuwa gare ta batare da Bintu ta lura dashi ba ai kuwa adai-dai lokacin Bintu ta mike tsaye tana cewa "yawwa yanzu abinci na zaiyi yaa Alili yaci afin yatafi" batakai da karisa magana nan ba kawai taji anyi sama da ita kamar yar babyn roba, saura kadan Bintu tasaka ihu taji muryan Khalil yanacewa matsoraciya nine nan sahibin ki,

Sauke ajiyar zuciya Bintu tayi a dai-dai lokacin da kuma Khalil yana sauke ta kasa, ai kuwa yana sauke ta kasa ta juya ta fuskan cesa ta kama wuyan sa da dukan hannayen ta tatusa kanta a faffadan kirjin sa tana tace wallahi Allah katsoratar dani dan haka karar rasheni tafada tana mai dako kanta daga kirjin sa, tana tura masa baki , Khalil kama bakin yayi yajaa yace ai kuwa sai na ciza wannan bakin naki,

Kukan shagwaba Bintu tafara ai kuwa da sauri Khalil yakama kunnuwan sa yanacewa agafarce ni ayi hkr dan Allah bazan karaba nine ko to mijin ki ya tufa, ya kuma hada hunnuwan sa alamun yana niman afuwa a gare ta, sosai Bintu tashagala da kallon sa tana jin wani soyayyar sa da kaunar sa yana sake shigan ta, bude baki Bintu tayi tace to shikenan na hakura, sosai suka shiga kallon soyayya sun manta ma da abinci akan wuta, zaida yafara konewa tukuna suka ankara da abinci ai da sauri Bintu ta katsai kallon ta koma kan abincin,

Sai da tasauke abincin akafi, tajuyo ta kalli Khalil tace ina yaa Alili? d'aga mata gira Khalil yayi yace "sai yanzu ne zaki tuno da yayan naki ko to yatafi, tura baki Bintu tayi tace " mai yasa zaka barshi yatafi bayan kasan na kusa gama abinci, Khalil yace sauri yakeyi dama yazo mutattuna ne akan abunda yakamata nafara siyarwa, gabaki daya Khalil ya kwashe duk abunda sukayi da Alili yafadawa Bintu sosai Bintu taji dadin hakan kuma takuma jin jina-jinawa Alili da kuma Kaka akan kokarin dasukeyiwa Khalil, tabbas samun mutani kamar su Alili a wannan zamanin akwai wahala,

Abincin Bintu ta zuba musu sukaci tare bayan san kammalaci ne Khalil yashiga wanka da yau suna son zuwa ziyara gidan Kaka da kuma Baffah,


Gabaki dayan su sangama shiri suka fito sunyi kyau sosai masha Allahu Khalil da Bintu badai kyau ba, dama Bintu farace sol sosai yayin da kuma Khalil baki ne ba sosai ba,

Gidan Kaka suka fara zuwa suka gaishe sa sosai sukayi fira Khalil yayi godiyawa Kaka harda dan hawayen sa, Kaka yace "haba babu komai dan nayiwa jikana abu basai yamun godiya ba, sosai sukayi fira daga bisani kuma sukayi sallama da su Kaka da Alili, suka nufi gidab Baffah,


Sallama sukayi suka shiga cikin gidan Baffah suka tarar a tsakar gidan shikadai yana wankin kayyan Inna Jummai, da sauri Khalil yaje gare sa ya fara masa magana " haba Baffah wanki da kanka kuma ai da ka aika anki rawoni ni sai nayi wanki amma ace kana damu kai kuma kana wanki!

Daga cikin d'akin Inna Jummai tayi magana tace idan bai yi awanki ba uban wakake so ya masa, Baffah yace Garkuwa kar ka tamka mata karabu da ita tun ran da Bintu ta tafi nina dawo nake komai a gida nan, garama wani sa in Mero tana fakan idanuwar Jummai tana tayani amma kar ku damu kan ku komai mai wucewa ne,

Bintu tun sanda suka shigo cikin gidan ta tarar da Baffah ta yana wanki tazube agun ta fashe da kuka mai cin rai, sosai take kuka Baffah ne ya shiga rarrashin ta da k'ar yasamu tayi shuru, Khalil ne ya karisa wanki bayan yagama ne kuma suka koma d'aki suka fara fira sun tattauna sosai kana sukayi sallamawa Kaka suka koma gidan su,


Tun da suka dawo gida Bintu batawani farin ciki Khalil ya lura da hakan amma kuma baice mata komai ba sai da yadawo daga masallaci, kafin yasaka Bintu a gaba dan ko abinci takici, "Mimi nasan meke damun ki tun damuka dawo daga gurin Baffah kika shiga cikin damuwa kuma nasan sanadiyan ganin Baffah cikin wannan yanayin da muka ganshi ne, tabbas Baffah yana cikin da muwa amma kuma Baffah addu'an mu yake bukata dan ya hadu da mata maral imani amma kuma kisani addu'a itace take sauya komai dan haka kicirai damuwa aran ki kuma insha Allahu zan kawo karshe abun da yardan mai duka,

Bintu kwanciya tayi ajikin Khalil ta kuma fashewa da kuka tana sake tusa kanta a kirjin sa tana magana, "Baffah na shi ne komai na shine gata na ina matukar kaunar Baffah na tabbas Inna Jummai bata da imani amma kuma kamar yadda kace mijina addu'a itace gaba da komai to zanci gaba Allahu ya wace mana gabaa, Allah nagode maka da yaban kai amatsayin mijina tabbas kai alkhairi ne a cikin rayuwata kuma zanci gaba da maka biyayya Allahu yaba mu zaman lpa,

Khalil sosai yaji dadin maganganun Bintun sa kuma yakara godewa Allah da yabashi mata kamar Bintu, kara kwanta da ita yayi ajikin sa, sunfi awa guda a haka suna jin dumin jikin su, kana daga karshe Khalil ya dauki Bintu yayi d'aki da ita, kan gado ya nufa da ita kwantar da ita yayi shima ya haukan gadon sukayi barci rumgume da junan su,


Karfe uku na dare dai-dai Khalil ya farka daga barccin sa fita yayi a d'akin mand'aki ya shiga daura alola bayan ya kammala ya koma cikin d'akin Bintu ya tarar tayi ruf da ciki, yasha ganin Bintu tayi irin wannan barccin sai dai ya gyra mata amma kuma har yanzu tanayi dan haka yayan ke shawarar tashin ta daga barccin dan yafada mata ilar ruf da ciki,

Mimi kitashi a barcci nan akwai magana nan da zan fada miki, idanuwar Bintu a lumshe tace "haba Sahibi na kabari mana sai gari yawaye" a'a Mimi ki tashi kawai babu yadda ta iya ta tashi daga kwanciyar tazauna,

Khalil jawota yayi kirjin sa yasaka tsakakanin kafafafuwan sa ya kwanta da ita a kan kirjin sa yafara mata magana cikin sanyin muryan sa wanda zatayi saurin fahimtar sa,

Mimi na zan fadamiki illar kwanciyar bacci akan ciki (Rub da ciki)!!!

Mutane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login