Showing 6001 words to 9000 words out of 54699 words

Chapter 3 - Mukaddari Ne Daga Allah Complete Hausa Novels By Suhaima Abubakar Shehu.txt

nufin a bude saboda baya jin akwai sauran saboda baya jin akwai sauran kalmomin da suka rage a bakin sa daga cikin motar kuwa tunda abun ya faru take rike da kunneyen ta cikin matukar tsoro ita kanta sautin bugawar motar ta tsorata ta sosai tasani ko iya wannan sautin kad'ai abun tashin hankali ne balle kuma illar da zata iya biye bayan sa,

Bawai tana jin tsoron fitowa bane daga motar saidai tsawon wannan lokacin tana tariyo yanda abun ne ya faru daki-daki kokarin take ta gano daga inda aka samu matsalar.


Kwarai tasan laifinta ne amma kuma ta yaya? tambayar da tasa komar da tunanin ta tun daga farkon fitowa daga gida bayan tayi wanka ta shirya tsaf fuskar ta tamkar farin wata a daren goma sha hudu


Daga shiga toilet har zuwa kammala shiryawa babu wani kuskure ta fada cikin ranta tana mai kara baza tunaninta a faifai dan samun wata marikar da zata iya alakan ta sanadin da wannan hatsarin


" Bayan na hattama shiryawa Ammi ta kwalo min kira dan yin breakfast na fita da sauri bayan na amsa ina mai nufar dining area inda Ammi da Abi Suhaima Hanan Iman da Imran suka kusan kammalawa na gaishe da su daban-daban sannan na janyo kujera na zauna zan iya tuna tambayar da Abi ya fara min daga zaunawa ta mai sunan mama ya kike jin yau din a matsayin ranar ki ta farko a jami'a?


Murmushi nayi har sai bayan dana hadiye abincin dayake bakin na cikin damuwa sosai nace Abi tsoro nake ji

Haba dai karamar zakanya ta nikam me zai iya tsoratar min dake nifa ba matsoraci bane bansani ba dai ko a gurin Amminki kika dauko tsoro ya fada cikin sigar tsokana

Ammi ko da taga alamar hira na kokarin kacemewa tsakanina da Abi wata maganar ta kawo dan ture wannan


Nace kinyi magana Dan ladi direba kuwa? Ammin ta tambaya


Haba Ammi ba mun riga da mun kai karshen wannan maganar ba ni gaskiya bana so Dan ladi yakai ni ni zan tuka motar zan fashe da kuka
Wanda yasa Abi ya karba zancen da cewa wane irin Dan ladi kuma?

To meye amfanin koyon motar da tayi kenan idan kullum. Dan ladi ne zai rika kai ta makaranta har zuwa yaushe zata jaraba koyan da tayi?



Dama ai kai kullum kana bayanta nifa tsorona kda taje ta bugawa wani motar sa kawai ina laifin suna. zuwa da Dan ladi kafin nan sai. ta rika tukawa da kanta

a'a ban yarda da Dan ladi ya rika kai mamana makaranta Abi ya fada yana mikewa daga gurin alamar ya gama

To ya fada cikin mamakin inda ya jefar da wayar sa sai lulubar jikin sa yake mamana kira min wayata naji da sauri kuwa na laluba number sa nakira

Wayar ce a hannun kujerar tsakiyar falo inda ya fara zaunawa kafin ya karaso gurin dinning din ban katse kiran ba har yaje gurin ya dauka ganin har wannan lokacin ban katse ba yadaga kiran yace ki fadawa maman ki kwalliya ta burge ni kit ya kashe

Babu bukatar sanar da ita domin already na saka a soeaker ne wani kallon zaka sani rayi masa yayin da daga mu har shi muka kwashe da dariyar ta


Ku kuma zaku yi ku kare ne kowa ya wuce makaranta ko kuma sai kun tsaya batawa masu kaiku makaranta lokaci


π”»π”Έπ•‚π•π”Έπ•Œ ayanzu nagano inda matsalar ta faro Ammi ce silar wannan matsalar kina tsoron na bugawa wani mota kuma ga hakan ya faru ta fada a fili,


" Adai-dai wannan lokacin ne taga tsaya a kan gashin motar ta wanda ko ba'a fada mata ta san wanda tayiwa barna ne saidai hango yanayin masifar datake tattare dashi ya tsorata ta, tana cikin shwarar sauka gashin ko a'a taga ya kara dukan gilashin cikin matukar fusata, aiko ba shiri ta zuga lokaci guda zuwa kasa wanda yabawa Khalil din damar kai hannu dan falla ma ko uba waye wannan lafiyayyen mari kafin kuma ya fito dashi cikin motar yaci masa kaniya,

Cak hannun ya taya kamar wanda aka tsayar da remote, ya kasa karasawa a kyakkyawar fuskar da i danuwan sa sukai masa tozali dasu, wannan fuskar ko ba'a fadawa mutum iya kallonta kadai ya isa shaidar cewa iskar wucewar mari bai taba gigin wucewa ta gefen fuskarta ba,


Sauran daliban da suka yi dafifi dan jiyo sautin kukan wanda ke cikin motar nan ganin irin zafin da Khalil din ya kwaso, ai bazai yuyu bama wanda yayi wannan b'arnan ya sha, dole ayi wacce za'a yi ganin yanda dramar zata kai karshe ne yasa daliban tsayawa dan more kallo bawai dan ba'a fara lectures ba,

Jin shuru har yanzu ba'a alamun kwalla kara ba yasa wasu suka fara lekowa dan ganin abunda ke faruwa musamman wayanda ke daya dashen motar da basa iya hango komai da wani madaukakin mamaki suka kallon sa ya wani saki ido, hanci da baki ga kuma hannun da har wannan lokacin yake sakale a isaka, shi baiyi abunda ya kamata ba kuma ya wani yi tsaye a gurin kamar an dasa shi,

Nan fa kowa ya fara watsewa yana nufar aji, kowa da abunda da yake fada aikin banza kunga yanda ya wani zo kamar jikan iliya dan mai karfi kai kace wata tsiyar zai tsinana amma ji yanda ya kare a tsinkar fure sauran daliban baki daya suka kwashe da dariya,


"A cikin motar kuwa tun bayan data sauka gilashin taga tahowar hannu kan fuskar ta a tsorace ce ta kai hannayen ta ta dafe kumatun ta dan kare su daga saukar wannan azababben farmaki,
Seconds daya, biyu, uku, saida ta kirga seconds har goma ta hanyar amfani da bugawar da zuciyarta keyi cikin da mamaki ta bude i danuwan ta da har wannan lokacin suka a rufe dan tagama sadakarwa fa sai jikinta ya karbi bakon al'amarin da a tarihin rayuwar ta ba'a taba ba,

A hankali ta d'ago i danuwan ta dan ganin abunda ya tare fadowar wannan farmaki, daram kirjin ta ya buga matashi ne kyakkyawa a fuska kamar bazai yi masifa ba, kallon sa tayi sannan tayi kasa da idon ta, saboda kwarjinin da yayi mata, Khalil akwai kwarjini gashi ba daukan rai ni amma yau kamar ba Khalil nima bayi mamakin Khalil wanda mata basa gaban sa, amma bari nayi ahuruπŸ™ƒ

Cikin muryarta dake fita kamar yaro na gangar fashewa da kuka tace kayi hakuri dan Allah, πŸ™

Sai a sannan ne yaji ya dawo hayyacin sa cikin second biyu kwakwalwar sa ta rika tariyo masa abun kunyar dayi,

Tofa masu karatu yau Khalil har yasan yayi abun kunya duniya kenan


Nan take haushin kansa ya kamashi, ko arzikin amasata bata ci ba da sauri yabar gurin motar yanufa tasa, bumper sa dake tashe a kasa ya dauka ya saka a boot din motar sa yarufe ya nufi department din su.

Yana mamakin kansa anya shine kuwa maiyake faruwa dashi ne haka,

*******************
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

MHT HOSPITAL


Tsawon mako guda kenan an kasa shawo kan matsalar maganar momy babu irin kokarin da Dr. Harun baiyi ba wanda takai har consultants aka rika kira suna zuwa na musamman domin matsalar momy amma har wannan lokacin abun saidai ma ace cigaba yake wucewar rana zuwa take da wani sabon salon sauyawar rashin lafiyar izuwa wani abun daban domin kan yau dai iya matsalar magana ce kawai take fama dashi, amma a yau cigaban lamarin yakai har ciwon sashe mata fara kamata ada tana iya komai da hannayen ta gurin yin nuni ko yin bayanin abunda take bukata amma a yanzu damar haka ma bata da,

Yanzu momy idan kaga irin halin azabar ciwon da take ciki saika tausaya mata,
Masu zuwa dubiya kuma wasu da hawaye suke barin d'akin Abba kan sa baya iya mallakar kan sa a duk lokacin daya zo dubata sai yayi mata hawaye dan haka ne ma yayi magana da Dr. Harun akan yayi musu duk wani shirye-shirye daya kamata na fitar da ita izuwa manya Asibitocin duniya,


Akwai wata asibiti a Mumbai ta kasa Indiya suna da k'warewa akan matsololi irin wannan ina ganin acan yakamata ku kaita, shawarar da Dr. Harun din yabawa Abba sosai kuma yayi na'am da shawarar domin dama ya yarda kwarewar India a fannin kiwon lafiya,

Yau ya rage saura kwana biyu su cika zuwa India yazo asibitin Umma ce sai su Khairat da Kausar wayanda tun safe da Bala direba ya kawo suke nan har yanzu da agogo ya buga biyar saura kwata suka kawowa su umma tunda momy bata iya cin komai sai duren sa a wani dogon tube ganin Abba ya shigo duka suka gaishe dashi cike da girmamawa shima cikin nuna kulawa da y'anyan sa ya amsa yana jin wani tausayin su na kara danne zuciyar sa musamman ma daya kara kai idon sa yaga halin da momyn su take ciki,

Kausar ne taje gaban gadon tarike hanun momyn ta momy har yanzu baki tashiba momy kinsan saidake nake iya barci akirjin ki yau momy kinki tashi kullum ina nan momy dan Allah kitashi kince komai nake so zakimun momy ina son jin muryan ki najima banji muryan kiba babu yaya Khalil kema baki nan

Kuka takeyi sosai gabaki daya d'akin hawaye ne afuskan su kuka suke sosai,

Khairat ce tazo tarike hannun kausar tana fadin haba autan momy kidai na kuka in momy taji bazata jidadi ba momy in sha Allahu zata samu lafiya oooo auti khairat kullum kice mun momy zata samu lpa amma har yanzu ko magana batayi,

Kuka take sosai gurin Abba ta nufa Abba kowa yaki tashe mun momy na Abba kai katashe ta nasan zata tashi intaji kana magana nasan momy tana jin maganan ka ko yau she kamata magana tanjin maganan ka kuma kullum tanace mana muji maganan ka

Hannayen Abba tarike tana rokon sa akan yatashe masa momyn ta,

Khalisat ma tazo gurin Abba katashe mana momyn mu muna bukatar ta ,


Khairat Khalisat Kulthum Kausar kuka suke sosai

Abba yadube su yace in sha Allahu momyn ku zata samu sauki kucigaba damata Addu'a gobe zamu tafi Indiya insha Allahu momyn ku da kafaffun ta zata dawo gida

Kulthum tace Abba ance duk wanda yabar kasan sa baya dawowa kasan sa darai mu kalm kar afitar mana da momyn mu abarmana ita zamuta mata Addu'a

Abba yace addu'anku take bukata kawai yanzu Bala yana ciran ku awaje kuje kuka Kausar tasa ita agun momyn ta zata zauna da lallashi Abba yabita ta tafi

Bayan tafiyan su Abba ya gadon da momyn ke kwance kamar mai bacci ya wuce kai tsaye ya riko hannunta da irin salon da Abban ne kadai keyi mata yasa ta bude idanuwan ta a hankali cikin nasa daya kafeta dasu ko k'iftawa ba yayi saida suka jima ahaka kowa da abunda yake sakawa aran sa kallon da Abban ke yi mata kallone na cikakken so da kauna wanda tausayin yake kara hura wutar ruruwar su a zuciyar sa.

🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
KAUYE GUMA

Yanayin garin yana matukar dadi wa mazauna garin babu wata hayaniya mai tada hankalin mazauna garin babu wata damuwa acikin zuciyar su farin ciki ne yake tahanikin acikin arayuwar su kowa kagani harkan gaban sayake cikin matukar farin ciki da annashuwa,


"Wata yarinya ce zaune agaban wata bishiya tayi tagumi farace sol bata da kiba sosai kyakyawace sosai ajin farko al-k'alamina bazai musultamuku yadda kyawun ta yake ba duk tayi wani iri gabaki daya babu kwanciyan hankali atattare da ita babu nutsuwa tafada duniyar tunani,

Magana takeyi cikin zuciyar ta shin dagaske ni ba y'ace kamar kowa ba tsinto ni akayi mai yasa inna jummai bata sona kamar su Hauwa da maryam mai yasa kullum nake zama abun musgunawa agun inna jummai bana jindadi agidan sai Baffah yana nan Baffah ne kawai yake sona sai kuma Maryam komai Baffah yayi masu Hauwa yana mun shin dagaske maganan da ake fada bani da kowa ni y'ar tsuntuwace wacce bata san kowa nataba mai yasa ako da yauahe inna sai ta duke ni mai yasa bana samun farin ciki agidan mu sai Baffah yana nan, tunuwa da maganan Baffah tayi alokacin da yashigo gida yasamu Inna jummai tana dukan ta,

Bintu kowa da kika gani akwai tasa kaddaran dan Allah yayi ki yar tsutuwa bashi sai zaki zargir kaddaran kiba ko kuma iyayan ki Bintu ina ji ajiki na iyayan ki suna son ki kuma nasan har yanzu basu fitar da ranganin kiba inkina raye Bintu ina son ki rayu cikin farin ciki, tabbas ina fatan wata rana kiga naki iyayen ki Bintu dukan abunda Jummai zatamiki kiyi hakuri wata rana sai labari in sha Allahu Allah ubangiji zaikawo miki miji nagari wanda zai kula da rayuwar ki,

Bintu ina son kisani aduk inda kike kisani Allah yana tare dake kuma Addu'a ta tana tare dake Bintu

Bintu ina son kisani kimai da al'amuran ki zuwa ga Allah kiyi dogoro na gaskiya gare shi kiyi aiki da bin shar'an sa sababi ki aminta dacewa lallai wanda yake gudanar da al'amura daga sama zuwa kasa masani da abin dayake iyakance dukkan al'amuran ta kowace fusaka ma'abocin cikin abin da yaso yana kewaye dake da ludufi irin na illimin sa da kyautatawa da dudanarwa wanda ba wanda zai iya cikin halitu ko wani haziki ya fahimce karki shgaltu da sha'anin ki kibe dan bautawa ubangijin ki kiyi yakinin cewa dukan wanda yadogara gareshi to fah ya isar masa kuma zai kasance amintattan ce daga hudura kuma yasamu cikekken nutsuwa da kwanciyan hankali kinji Bintu na

Bintu tabbas zakiyi farin ciki arayuwar ki Allah zai kawomi ki miji nagari wanda zai kula dake da rayuwar ki, ubangiji Allah yana sane dake zai kawo miki mafita arayuwar ki kuma in sha Allahu iyayen ki Allah zai hadaku da yarddan sa Allah yamiki Albarka diyar albarka, dukan abun da jummai zatamiki kikasance mai hakuri nasan kina hakuri kikara wata rana sai labari in sha Allahu

Bintu tace nagode Baffah kuma in sha Allahu zankasance mai hakuri aduk indanake ai nika kaine komai na Baffah bani da tamkar ka aduniya nan

Tunani take sosai

Alili tafe yake babu nutsuwa atare da shi a yanzu burin sa shi ne wannan bakon halitan yatashi yau kimanin wata guda kenan amma bai san yadda kan sa yake ba tafiya yake yana magana har yazo zai wuce sai yaci karo da Bintu zaune itama cikin duniyar tunanin da kowa yasan Bintu afagen tunani ako ina kaga Bintu indai batare da maryam ba to cikin tunani take,


Alili ya ambaci sunan ta Bintu Bintu Bintu kamar yana magana da dutse babu alaman taji sa har ta amsa masa tabbas Bintu abun atausaya mata ne duba da yadda rayuwar ta ke tafiya kowa yasan Bintu agarin tun tana yarinya aka tsunto ta akoda yaushe inna Jummai sai tayi mata gori harda duka badun Baffah ba da rayuwar Bintu yajima da tarwatsaiwa duk da rashin gatan da Bintu bata dashi amma Allah yamata farin jini ga sanyi hali uwa uba kyawun ta tabbas Bintu batayi kama da y'an garin ba duk da suma Allah yazuba musu kyau ubangiji Allah yamata ruwan kyau,

Alili yatabata yace Bintu tunanin mai kikeyi haka tun dazo ina magana amma shuru kamar ina magana da dutse

Babu komai ya Alili haba Bintu yazakice babu komai bayan nagan cikin tunani cewar Alili babu komai ya Alili kawai kaina ke mun ciwo bana jin dadi ne

Taya zakiji dadi bayan babu wata nutsuwa atare dake Bintu kaf gari nan kowa yasan babu farin ciki da kike samu a gidan ku Bintu rayuwar ki abun tausayi ne amma kisani kowa da kallan tasa jarabawa da Allah yake daurawa bawan sa arayuwa kici rai damuwa aran ki wata rana sai labari dama ubangiji Allah yana jaraftar bawan sa akan abubuwa da yawa dan ya gwanda imanin ka

Kiduba fa kigani yau wata guda kenan wannan mutumun dana tsunto sa bai san yadda kan sa yake ba Allah yana jarafta bawan sa aduk sanda yaso wani baya gani wani baya ji wani mahaukaci ne wani yana kwance bashi da lafiya to Bintu duk abunda yasame ki kimika lamuran ki zuwa ga mahalincin ki kiroki Allah yashiga cikin lamuran ki kefa kina da lafiyan ki kuma kina cikin haiyacin ki amma kinga shi wannan mutumin dana tsunto bai san yadda kan sa yake ba Bintu rayuwar nan abun tsoro ne amma Allah ne maganin komai arayuwa

Nasani ke mai hakuri ne Bintu tabbas in Allah yasa kinada rabon ganin iyayen ki zaki gan su

Nasiha sosai yamata yace taje gida anjima in sha Allahu zaizo

Maiyasa kowa yace nayi hakuri wata rana sai labari magana Bintu takeyi cikin zuciyar ta

Tabbas Alili tana girmama Alili a rayuwar ta dan bayan Baffah Alili yabata gudumawa sosai arayuwar ta kuma kullum cikin nasiha yake mata akoda yaushe in suka hadu da Alili har bata son su rabu saboda yana ibemata kewa

*Godiya sosai tamasa kuma tamasa alkawarin in sha Allahu zata cire damuwa aran ta kuma zata tayasa da Addu'a mutumin da Alili ya tsunto sa Allah yabashi lafiya


🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
KAUYEN GUMA


"Kauye ne babba wanda kowa harkan gaban sa yake kauye ne wanda kan su ahade yake


" BUSHAR wani matashi ne wanda kafgarin kowa tsoron sa yake babban mutum ne mai jiki sosai amma kyakyawa ne afuska Bushar matashi ne wanda matasan garin tsoran sa yake yagama adaban garin duk abunda yace shi akeyi Bushar atsarin sa baya magana biyu matashi magidanci duk suna tsoron sa saboda yana amfani da sihiri ajikin sa,

Bushar yana matu kar son Bintu, Bintu kyakyawace kuma yarinyace dan shekarun ta bazasu wuce shekara shataraba ko ashirin

Bintu yarinya ce mai farin jini amma babu wanda ya isa yace yana son ta saboda Bushar

Duk abunda inna Jummai takeyi mata bata yarda tayi agunda Bushar zaiji saboda akwai wani rana da yamata rashin mutumci akan tanunawa Bintu yatsa

Alili yakasance yana son Bintu amma tsoron Bushar yahana sa fada mata cewa yana son ta

*******
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

BABBAN BIRNIN TARAYA ABUJA


Anguwar Area one manya-manyan gidaje nagani wanda tsaru wansu bazasu musultuba ina cikin kallon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login