Showing 33001 words to 36000 words out of 54699 words

Chapter 12 - Mukaddari Ne Daga Allah Complete Hausa Novels By Suhaima Abubakar Shehu.txt

furar ni ne aciki, gabaki daya gurin yayi ma Khalil kyau sosai,


Muryan wannan mutumin sukaji yana ce musu kushiga shine zai hayar daku wannan kogin, duk da jikin su yana bari amma kuma sai da suka shiga cikin jirgin,



Still muryan mutumi nan suka sake ji "kurufe idanuwar ku, ae kuwa suka rufe kam, tare da kamkamme junan su,


Haka jirgi nan ta rufe su gam, kai tsaye jirgin tayi sama da su kogi nan tayi kai tsaye tana zuwa tadawo kasa, kuma still idanuwan su arufe take basu yarda sun bude ba duku da yadda aketa wena su amma kuma basu bude ba, jirgin ne tayi kasan ruwa da su, ai kuwa ruwa ya lulube su, basu sanda suka bude idanuwan suba, ganin su sukayi cikin ruwa, ga kuma kifaye masu hadiye mutum, ga kuma kada masu cin mutum abubuwan ruwa wanda suke cutar da mutum babu wanda babu cikin wannan kogin, Alili harda fitsari a wandon sa, yayin da Khalil duk addu'ar da tazo bakin sa shiyakeyi,


Kwan nan su daya cikin ruwan nan sunga, tashin hankali har sun fida rai da rayuwa, har sun sadakar mutuwa zasuyi dayake kwa nan, su yana gaba da taima kon Allah sai gashi sunfito amma gabaki dayan su basu cikin haiyacin su, abakin kogin jirgin takifar da su, tajuya abunta,

Sam basu masan sufito daga cikin kogin ba, gawani uban yunwa adadde su,

Muryan wannan mutumin sukaji yana musu magana, "lokaci yana kure muku fa akwai sauran k'alubali agaban ku fa"

Kamar a mafarki suke jin maganan nan ai kuwa da sauri suka tashi sai ganin su sukayi abakin kogin, gaggara mekewa sukayi hancin cikin su sai murda musu yake tsabar yunwa, abinci suka gani agaban su, magana suka sake ji kuci abincin nan lokaci yana kure muku, ai kuwa suka faracin abincin nan sai da suka ci suka sha ruwa, mekewa sukayi suna jiran abasu umarni dan basu san ta ina zasubi ba,

Muryan mutumin nan sukaji yana magama saura tsallake ta biyu kuma nasan kunsani dan Kaka yafada muku dan haka ni taima kon da zan muku shine kawai nunamuku hanyar, ai kuwa haka yayi kawai ganin su sukayi agaban wata hanya, ai kuwa sukashiga kallon junan su wannan yaga wannan haka

Wata kofa suka gani tana mutsi, ai kuwa suka kam-kame jikin su, gabaki dayan su atsorace suke kowa da abunda yake rayawa acikin zuciyar sa,


Ai basuka tashin hankali ba sai da sukaga kofar nan ta bude ai asannan maganar Kaka ta dawomu su hanya uku ce na farko kogi ne ta biyu kuma Aljannu masu kaga dasu, ai gabaki dayan su suka rake junan su,

Basu gama tunani ba sukaga Aljannu nan masu kagama dasu sak sunfito ta wannan kofar, wayyo Allah na zo kaga yadda Khalil Alili suka shiga cikin rudani, ai ruwan zam-zam din da Kaka yabasu agani ba ai kuwa Ajannu nan suna tukaran su, sukuma suna ja da baya, gabaki dayan su arude suke basuka ruwan zam-zam din nan ba ga kuma suna daf dasu, sun sadakar shikenan taso takare, ai bazato ba tsammani sai ganin ruwan zam-zam dinan sukayi agaban su alokacin Aljannu nan suna daf dasu, ai Khalil yana ganin ruwan zam-zam dinan akasa, yayi kasa yadauka yawatsa musu, lokaci guda suka bace, Alili duk bai san abunda yake faruwa ba sai da Khalil ya tabashi ai kuwa atsorace ya bada kai duk atunanin sa wannan Aljnun ne sukayi nasaran kamashi, amma shurum da yaji ne yabashi daman bude idanuwan sa, babu su babu alaman su, ai sauke ajiyar zuciya yashigayi, gabaki dayan su suka zube akasa suna mai da numfashi,


Sai da suka gama sauke numfashi kafun Alili ya tambaye Khalil maiya faru ne meyasa wannan Aljanun suka rabu dash, gabaki daya abunda yafaru Khalil ya fadawa Alili, Alhmdullh kawai Alili ya iya furtawa,

Gabaki dayan su sunmanta aikwai, wani aiki agaban su barci mai dadi ne ya dauke su, sai daf yamma suka tashi ganin duhu sukashi ga tashin hankali baki dayan su,

Suna tunanin da ina zasubi kuma yanzu, ae basuka gama tunanin suba suka ji muryan mutumin dazo nan yana musu magana,


Tabbas lokaci ya kure muku dan saura kwana daya shadin ka amma kuna zaune anan kuna bacci kuma kunsan akwai wani tafiyan agaban ku ko to tabbas kutashi tsaye zan nuna muku hanyar ta karshe sai ku kula dan nasan Kaka yafada muku akwai namumin daji wanda tabbas a yunwace suke musaman idan dare yayi kuma dole kutafi da daran nan saboda gobe ne wannan gasar, taku,

Ganin su sukayi awani katafaran daji mai duhu sosai, gabaki daya kukan namomin daji suke ji ya kewaye dajin ku ina suka bi kukan sukeji, tsayawa sukayi cak suna tunanin ta ina zasuyi kuma ta ina zasu ga wannan bulalan,

Bazato batsamani kawai ganin zaki sukayi tayi kansu, ai kuwa gabaki dayan su, suka rasa yadda zasu nufa Alili fisari yafara Khalil kama hannun sa yayi suka fara gudu, suna gudu zakin nan yana bin su, ai kuwa sauran abubuwan cikin dajin sukaji ai gabaki dayan su suka nufe su suka hau bin su,


Tashin hankali da ba'a saka masa rana kenan Khalil tuntube yayi yazobe akasa gashi wannan namomin dajin suna daf dasu wayyo Allah Alili kokarin sa yataimaki Khalil amma kuma yakasa dan gabaki daya a tsorace yake shima,

Da taimakon Allah Khalil ya mike yayi gaba gudu suka cigaba dayi, gudu gabaki dayan su sunfita haiyacin su,


Gudu suke sosai da sosai duk yadda kafan su tanufa dasu haka suke bin gun,


Wani babban kofa ne mai kiran zinare gabaki daya guri jajayen furani ne komai nagun launin jaane, Khalil Alili tunkaran kofar sukayi suna tunkaran ta kofar tana buduwa, suna kariso bakin gun kofar ta budu gabaki daya, ai kuwa suka shiga da gudu, kirif kofar ta rufu,


Sauke numfashi suka shigayi, gabaki daya dakin launin jaa ne acikin d'akin komai na d'akin launin jaane,

Tsayawa sukayi ta ina ne zasuka bulalan, Alili yace "taya zamuga wannan bulalan kuma jina yana bani anan ne bulalan take",


Khalil yace " Kamar yadda Kaka yafada mana cewa bulalan tana cikin wani kwanu ne, mai murfin roba, dan haka buduba duk kwanu mai murfin roba na cikin d'akin nan",

Ai kuwa haka sukayi duk kwanu mai murfin roba sukashiga dubawa,


Wani kwanu mai launin jaa kiranta kiran maciji ne murfin roba, Khalil nufan gun yayi ai kuwa yana zuwa yana addu'a, hannun sa yakai kan murfi da bismila ya bude murfin wata zufgegiyar bulala ne aciki, dauko bulalan yayi kana ya daura idanuwan sa agan ta bulalan babba ne sai sheki takeyi sosai irin sosai dinan,

Alhmdullahi Khalil yace ya duba Alili dashima yake tafaman furta Alhmdullh haka kuwa suka ta murna sosai,


Kofar ce tafara rufewa ai kuwa murna ta koma ciki sukayi kofar da gudu dan karta rufe dasu aciki,



YAU RANAR SHADI
_________________________________________

__fada yacika makir kowa ya halata a fada dan ganin yadda wannan gasar zata kasance yau tsakanin Garkuwa da Bushar,

Bushar yace yasamu Bokan sa yabasa wani magani yace masa yashafa ajikin sa, dan idan yashafa ajikin sa to tabbas bazaisan ana dukan saba,

Dan haka gabaki daya Bushar yashafa maganin nan ajikin sa, da wuri yazo fada dan yana cike da farin ciki ya kosa dan ganin yau anyi wannan gasar, dan yacanza wata gasar daza'ayi,


Kaka gabaki daya acikin rudani yake yarasa yadda zaisa kansa dan babu alamun su Alili gashi kowa yazo dan ganin gasar nan

Bintu tashiga rudani , kai tsaye tayi gun Kaka dan tambayan sa ina su Khalil suke,

Bintu tasamu Kaka tace "Kaka ina su Alili har yanzu basu dawo bane Kaka, "

Kaka yace "har yanzu basu dawoba ina jin tsoro kardai wani abu yafarau dasu ne shiyasa basu dawo ba, sosai suka shiga cikin damuwa, Bintu kuka take sosai,

Idanuwan Kaka yayi jaa sosai sam baya cikin haiyacin sa,



Fada kowa yazo mai gaba tarwa ne yafara magana " Kowa yazo ina Garkuwa, ina Garkuwa, ina Garkuwa, ina yaje tabbas idan Garkuwa baizo ba yabata wasan sa, kuma tabbas Bintu zata aura Bushar,

Zan kiraka sau uku idan bakazo ba to tabbas, gasa takare daga nan tunda kai kayi wasa da gasar.

Ina Garkuwa daya, ina Garkuaa biyu, ina garkuwa uku kafun yarufe bakin sa sai ji sukayi ganin,


BARIMU KOMA BANGARAN MANGA FAMILY

________________________________________

Arjun kwace a bedroom dinsa jikin sa ya dau zafi zazzabi ne yayi mungun kamashi, kwance yake a kan bed din sa,

Aaraw ne yashigo bedroom din sa, zama yayi akusa dashi kama hannayen sa yayi yafara masa magana cikin sanyin muryan sa wanda yanzu tunani ya gama gauraye rayuwar sa akan brother sa yana matukar tausayin d'an uwan sa,

Magana yafara masa "haba dan uwa na karege damuwa cikin zuciyar ka katashi muje muyi breakfast, ummi da daddy suna jiran mu a parlau,

Arjun yadubi Aaraw yafara magana " Aaraw ina cikin damuwa sosai narasa yadda zanyi kaina ya dau zafi sosai narasa ina zansaka kaina,

Kullum idan na kwanta barcci sai nayi mafarkin ta, zuciya ta tana matukar son ta, ina son ta sosai irin sosai dinan,

Aaraw yace nasani Arjun amma yanzu muje parlau muyi breakfast kaji, haka suka fito parlou,

Ummi da Daddy duk suna jiran fitowar su, bayan sunfito kai tsaye dining area suka nufa bayan sun zauna, Arawa yace "morning ummi na"

Morning haw are u autana, cewar ummi turabaki Aaraw yayi, ummi kina mai dani Auta fa, haba my son idan ban mai dakai Auta ba towa zai zamo auta na,

Turabaki yayi kamar zaiyi kuka, Daddy yace ni kuma bazaka gaishe niba ko, turabaki yayi yace ai ina jiran nagama da ummi na ne sai nadawo kan daddy na gabaki dayan su sukayi murmushi,

Arjun yace barka da safiya uwa tagari fatan kin tashi lapiya, ummi tace "lapiya kalau d'an albarka, Alhmdullh" masha Allahu Arjun yace kana yadaura idanuwan sa akan daddyn sa, abun alfahari na fatan katashi lapiya,

Daddy yace Alhmdullh natashi ina kaunar ku Allahu yacika rayuwar ku da farin ciki, sosai sukaji dadi kuma suka amsa da Amin,

Daddy yace "yawwa dama ina son magana daku baki dayan ku, fuskan sa yadaura akan Arjun kana yasoma magana Arjun zakatafi india,

Arjun yace " daddy India kuma meyafaru wani abu yafaru ne?

Ummi ma tace wani abu yafaru da su hajjo ko? gabaki dayan su sun rude, daddy yace babu abunda yafaru sai Alkhairi, kana ya daura dacewa Arjun zaije ganin yar uwa jan yayan ki ne Sima,

Arjun Aaraw suka mai-mai ta sunan abakin su Sima yarinyar da bata da kunya ko kadan,

Daddy yadaura dacewa tajima tanason Arjun, mahaifin ta yajima da mun magana amma kuma nace mubari bayan zuba sai nan gaba, yadan numfasa kana yadaura dacewa jiya kuma nagano matsalan da take damun Arjun naciwon mara tabbas yana bukatar mata, shiyasa nayanke hukunci tunkafin abun yafi karfin mu,

Mai da idanuwan sa yayi kan Arjun yace nasan zakaji dadin Sima saboda tana son ka sosai dan haka kafara shiri zakatafi India,


Ummi gabaki daya tashiga cikin rudani dan tasan yaron ta yana son wata yarinya amafarkin sa,

Aaraw har yabude baki zaiyi magana, Arjun ya katsae sa, ya kalla daddyn sa yace "yaushe kake son natafi,"

Daddy yace "duk sanda kashirya,

Bayan kamala breafst kowa yabar daning din yayin da daddy yayi office,

Ummi ta dubi yaran ta tasoma magana cikin tausayin Arjun din tace " Arjun mai yasa baka fadawa daddyn ka kana da wanda kake soba? bayan nasan bazai maka auran dole ba,

Arjun yace ummi na har yaushe zanta dakon soyayyar da babu ita, ummi bantaba ganin ta azahiri ba, sai amafar ki na kawai, ummi zanyiwa daddy biyayya, zan aura Sima insha Allahu duk da atsarin rayuwa ta bana da ra'ayin auran mace sama da daya amma kuma duk abunda Allah yatsara dai-dai ne,

Ummi tace Allahu yanuna maka wannan yarinya gabaki dayan su suka amsa da Amin,


Sun tausayawa Arjun sosai, Arjun sai shirye-shryen tafiya yake,

AMERICA
_________________________________________

Mom Razia zaune a parlou, gabaki dayan su, suna cikin damuwa sosai, Sana tace "mom yanzu yazamuyi",

Mom kallon su tayi tasoma magana cikin tausayin yaran ta, " ina son ku sani duk wata matsala da tasame ku, kada kuyi kokarin guje mata kutun karai ta kusa aran ku ko ina nan ko bana nan zaku magance matsalan ku y'a y'a na tabbas kowata matsala akwai maganin ta, ina ji ajiki na duk wannan abunda yake faruwa damu watarana zai zamo labari, "


Dan haka kujigaba da addu'a tabbas addu'a tana canza kaddara, kuma kusani duk abunda yasamu bawa to fah tabbas MUKADDARI NE DAGA ALLAH,


Sosai mom Razia tayi nasihawa yaran ta, cigaba da tattaunawa sukayi akan yadda zasu fuskan ta matsalan su,


Mom Ninah ne zaune a parlou ta waya take da kawan ta Maro, tattaunawa suke akan wata magana, mom Ninah tace "nafadamiki nagaba da Sana dan zan hadata aure ne da wani mutum talaka ne sosai, Suha ne bansan yadda zanyi da itaba tana da taurin kai,

Dayan bangaran Maro tace ita kasheta zamuyi dan haka zamu nimo mutani da zasu gama da ita, Mom Ninah tace wannam gaskiya ne dan haka zuwa gobe ita zamu gama da ita Sana kuma bayan rasuwa Suha sai na aura mata wanna talakan, sosai Mom Ninah tayi na'am da shawaran da kawan ta tabata,

Gabaki daya wayan da Mom Ninah tayi akunna nan Sultan ne, bai bari Mom din sa tagan saba yabar parlon kai tsaye part din su Mom Razia yayi,


Suna cikin tattaunawa saiga Sultan yashigo abujajan kamar wanda aka biyosa, sai haki yakeyi, Mom Razia ne tameke ta nufi gun sa, kama hannun sa tayi tazaunar dashi akujera tadauko ruwa mai sanyi tabashi sai da yasha kafun nutsuwa tafara dawo jikin sa bayan, nutsuwa tagama gauraye jikin sa,

Ya fuskan ta Mom Razia yasoma magana "Mom yakamata Suha tabar gari nan tabbas idan bata bar gari nan ba komai zai iya faruwa da ita, "

Mom Razia tace ban fahimta ba ka nutsu kamun bayani yadda zan fahimce ka, Sultan gabaki daya abunda kunuwan sa sukaji masa agun Mom dinsa yafadawa Mom Razia, ai gabaki dayan su suka shiga cikin rudani sosai,

Sana tace "mom yanzu maiyi abunyi ina Suha zataje ",

Shuru Mom Razia tayi tana tunanin, gabaki dayan su zubawa Mom idanuwa sukayi, yayin da Suha take fara rayawa cikin zuciyar ta babu inda zataje ai yanzu Mom dinta tagama fada mata duk matsalan da tashafi kai karkace zaka guje mata ka fuskance ta, to tabbas zan fuskance wannan matar, kuma lokaci yayi da yakamata ta nuna mata ita ba tsoron ta take jiba,


Mom Razia ta numfasa kana ta daura dacewa "Suha zata tafi India akwai gida na acan kuma tabbas Suha zata ji dadin zaman gun dan gidan agefen kankara ne wanda yake sakowa daga sama kuma ga abubuwan more rayuwa agun,

Sulatn Sana, Alhmdullah suka fada baki dayan su, yayin da Suha ta tashi tsaye tana magana ina bazai yayyu ba intafi nabar ku cikin hatsar ni babu inda zanje wallahi, mom yanzu kika gama fada mana duk matsalan da ta tukaro ka karkayi kokarin guje mata amma kuma yanzu zakije natafi wani waje, Mom kibarni kawai na tunkara matsala ta,

Mom Razia mekewa tayi takama hanun Suha kana tasoma magana cikin sanyi murya wanda kana jin muryan ta zaka gane yanzu Mom Razia an kure ta sosai, magana take hawaye yana zuba cikin idanuwan ta "tabbas yarinya ta duk matsalan da ta tukaroka karkayi kokarin guje mata ka tunkare ta amma wannan ba yanzu ba maiyasa bance Sana zata bar guna ba sabda ita ba kashe ta za'ayi ba ina son ki sani magana nan kisa tayi dan haka yazama dole kitafi dan Allah ina son rayuwar ku sosai kunake gani naji dadi dan Allah Suha kitafi ai zaki dawo yayin da komai ya lafah,

Suha da hawaye yagama wanke mata fuska tace "zantafi mom insha Allahu zantafi, " Sosai Mom taji dadi kana ta daura dacewa, "Suha zaki ji dadin tafiyan nan sosai,

Addu'a sosai Mom tamusu kuma tagodwa Sultan,


Mom Razia da Sana sai shirye-shiryen tafiyan Suha India suke gabaki daya sun hada mata kayan ta, saboda suna son tafiyan ta yakasance yau ne,

Suha ne tasamu Mom din ta da kuma Sana a parlou tafara musu magana " Mom Sana zan tafi yau kuma zan barku gaskiya zanyi kewar ku sasai da sosai,

Sana da hawaye yagama bin fuskan ta tace ni kuma gaskia bazanyi kewar kiba, Suha tana hawaye tana murmushi ai dama nasan bazakiyi kewata ba gabaki dayan su suka fashi da kuka mai cin rai, Mom Razia ma kuka tafashi dashi yayin da taje ta rumgume su tabayan ta, kuka suke sosai basu masan lokaci ya kure ba,

Sultan ne yashigo d'akin ya soma magana yakamata kutashi kubarta tashirya lokaci na kure mana haka kuwa sukayi gaba ki dayan su, suka rabu da ita yayin da hawaye nazuba daga cikin idanuwan su, shima kan sa Sultan din hawaye ne cikin idanuwan sa yayi Allah wadai da halin mahaifiyar sa,


Suha tafito sak India dan shigar India tayi gashin kanta bazashi tayi abayan ta yayin da ta dauko rigan sanyi babba tasaka ajikin ta,

Tana fitowa parlou taje da gudu ta rumgume Mom din ta hawaye sai zuba suke cikin idanuwan ta yayin da Sana kuka take kamar ranta zai fita daga gaggan jikin ta zuwa tayi ta rumgume su tabaya tana fadin bazanyi kewar kiba Suha, ita kuma Suha tana cewa zanyu kewar ku kullum zan kasance cikin kewar ki sosai suke kuka kamar wanda akace musu rabuwan su kenan yayin da Sultan hawaye sai fita suke daga cikin idanuwan sa,

Gyran murya yayu ya furta lokaci yana kure mana fah, haka kuwa suka rabu badan suna suba shi kuma ya raka Suha har filin jirgi,


INDIA
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
_________________________________________

Suha saka kafar ta tayi akasa yayin ta ta lumshe idanuwan ta tana shakar iskan kasan India wanda gabaki daya garin ya matukar burge ta wannan ne zuwan ta nafarko,

Idan Suhaima Abdulkadir tana kusa bata bar nan wajan ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login