Showing 27001 words to 30000 words out of 54699 words

Chapter 10 - Mukaddari Ne Daga Allah Complete Hausa Novels By Suhaima Abubakar Shehu.txt

gama taro afada kowa ya kama gaban sa, Alili da sauri yazo wajan Khalil ya fara masa fada cikin bacin rai "Khalil kana cikin hankalin ka kuwa kasan waye Bushar kasan mai yake takama dashi da zakace ka aminta da batun sa, gabaki daya shifa babu Allah acikin zuciyar sa amma kana cewa wai kai ka aminta, tabbas idan bai kashe kaba too zaimaka ila da bazaka iya komai ba, arayuwar ka, " Khalil rike hannun Bintu yayi gam yana kuka yana cewa kasan me Alili bakasan yadda nake jin Mimi cikin rai na kuwa hmm yadan numfasa kana yadaura dacewa Alili ina son Mimi zan iya bada rai na fansa akan ta dan haka koda Bushar zai kashini ne yau daya kam saina gwada jarumta na akan Mimi, kasan yadda tasha wahala akai na kuwa acikin daji nan ya karisa maganan sa cikin kuka,

Sosai jikim Alili yayi sanyi kana ya fara girgiza kan sa yana cewa addu'a itace kawai abunda zan taya ka tashi, Baffahn Bintu ne ya cafke zancen da cewa insha Allahu zamu taya ka da addu'a baki dayan mu, haka ma Kaka ya fada, sosai Khalil yaji dadi daganin dukan su sona son shi kuma suna masa fatan alkhairi cikin rayuwar sa, da haka kowa ya nufi gidan sa, yayin da Bintu tabi Baffahn ta kana Kaka Alili sai kuma Khalil suma sukayi gidan,


WASHI GARI

Bushar a kofar gidan su Bintu yana jiran fito wan ta, babu bata lokaci sai ga Bintu ta fito, fuskan ta ahade kamar wanda aka mata mutuwa, Bushar ya fara magana "ae dama nasan basona kikeyi ba, Bintu nikum ko ina sona ko baki sona sai na aure ki babu wanda yafi karfina awannan garin dan haka kima sani dole sai nadawo miji agare ki, Bintu da tagama sauraron sa tace " Allah yafika Bushar ayanzu bana jin tsoron ka kuma kasani Allah baya barci kuma yace murokesa zai amsa mana, ni Allah ne gatana kuma dashi na dogora kuma washi zankai wa kukana, kuma ina da yakinin zai amsa mun da yardan sa, "


Bushar yafashe da dariya kana yadaura dacewa, kinga wannan abun shi zai nuna muku karfin ikona akan ku keda ragon mutumin da kike son sa Bintu zan nuna miki nafi karfin kowa awannan duniyan, Bintu tace ae idan kafi karfin mu bakafi karfin Allah ba kuma Allah daya ne abun bautan mu kuma baya barcci, tayi tsaki tabangaje shi tashege cikin gidan kai tsaye dakin da take kwana tayi, kuka take sosai barci ba rawo ne kawai yasace Bintu,


Bintu 3:am dai-dai Bintu tashi futa adakin tayi kai tsaye bayi tayi tayi fitsari bayan tagama tayi alola, takoma d'aki wani kodaddan sallaya tashin fita ta da kafbara sallah tafara bayan ta idar hannayen ta sama tad'aga tafara zuba addu'a Bintu tace "ya Allah ya ubangiji na babu abin bautawa dagaskia sai kai Allah ya Allah dan wanda kayi duniya kayi lahira domin sa ya Allah dan wanda kace idan mun bisa za mushiga aljanna nan ka, dan Amina da Abdullahi Annabi Muhammad (saw) Allah nagawo kukana zuwa gare ka Allah ina rokon ka kazaba mun abunda yafi zama alkhairi awaje na,"


Tabbas Allah Allah ne kuma maji rokon bayin sa Bintu magana take da ubangijin ta kya kace tana ganinsa, tabbas shi yana ganin ta amma zuciyar ta yana hasko shi buwayi gagara misali, Bintu ta daura dacewa ya ubangiji kai ka halice ni bani da kowa bani komai
sai kai kuma da kai kadai na dogara, kai ne kace muroke ka zaka amsa mana, Allah katsaya mun da kanka, kada kabarni da iyawa ta dai-dai da kiftawan ido na bazan iyaba, Allah idan har wannan bawan naka alkhairi ne agari ne ina rokan ka da katabbar mun dashi amatsayin mijina, Allah idan har shi ba alkhairi baine kazabamun mafi alkhairi agarini, Allah zabin ka nake so, Allah kazabamun miji nagari wanda zai kula da rayuwata, sosai Bintu take addu'a tana kuka tana rokon Allah,"


Yayin da Bintu take addu'a haka ma Baffan ta shima yake addu'an wa yarin yar sa Allah yabata miji nagari wanda zai kula da rayuwar ta, haka ma Kaka da Alili ba abar so abaya ba,


Fada ya cika makil kowa soyake yaga wannan gasar da za'ayi da Bushar, wasu sunyi Allah wadai da wannan mutumin da yace zaiyi gasa da Bushar shin shi bai da hankali ne, wasu sunyi Allah wadai da Kaka, da kuma Alili, fada tacika kowa wanda yakasance dan kauyen guma ne yazo fada dan bawa idanuwam sa abinci da maza da mata, kowa yasa aran sa cewa fa wannan mutum da zasuyi gasa da Bushar shine zai fadi,


Angama cika y'an gasa kawai akejira domin fara wasa, Bushar yafito filin gasar yayin da Khalil yake gifen fili yana taraba idanuwan sawa Bintu dan gabaki daya atsorace yake, kama hannun sa, tafara masa magana cikin ruwan sanyin ta, Sadauki na kaman ta alkawarin da kamun nacewa yau zaka zamo jarumi wanda hawaye bazai taba fita daga cikin idanuwan saba? girgiza kai Khalil yashigayi kamar karamin yaron dayake daf da fashewa da kuka, yancewa ban manta ba ina sane Mimi, ya daura dacewa Mimi tsoro nakeji kigani fa bulalan da take hanun sa kuma dashi zai duke ni har guda dari jikina bazai iya dauka ba idanuwa na bazasu iya jure rashin fitar hawaye ba idan har aka zuba mun wannan bulalan ajikina, wallahi Mimi tsoro nake ji, yakarisa magana yana mai fashewa da kuka maicin rai wanda duk wanda yagan sa agun sai ya tausaya masa,


Bintu kama hannuwan sa tayi tace nasan Sadauki na jarumi ne wanda zai iya jure komai akaina idan nace komai ina nufin komai, numfasawa tayi kana ta daura dacewa ehh tabbas jikin ka bazai dauka ba amma zuciyar kafa, nuna kirjin sa tayi da yatsan ta tana cewa tabbas nayarda da matsayin da nake ciki ciki awannan zuciyar taka nasan zatayi komai akaina daga ciki harda hana idanuwar ka zubar da kwala, Sadauki kasan yadda nake jin ka acikin zuciya ta kuwa? Hmmm to inbaka sani ba yanzu zan fada maka, kana da matukar shiga rai, kana da komai, komai da yake dauke hankalin mai kallon ka Sadauki na, babu wani yanayin da za'ariske ka face sai anga wannan yanayin yada d'an kara maka fito da kyawun ka, Sadauki , numfasawa Bintu tayi yayin da hawaye ke zuba daga cikin idanuwan ta tadaura dacewa
Murmushi, damuwa, kunci, ko kuka duka afuskan ka ababen murmushi ne amma kuma yau bana bukatar hawayan ka, nasan kowa yana son ganin ka dan ganin wannan gasar bakai ne zakaci wannnan gasar, haka kowa yake fada, amma nikuma nasan wannan jarumin mazan shine zaici kasani fa idan har hawaye yazubo daga cikin idanuwan ka tabbas karasa ni dan haka dan Allah karkabari hawaye sufito daga cikin idanuwar ka.


Sosai Khalil yashiga cikin da muwa da yaji labarin idan har hawaye suka fita acikin idanuwan sa zairasa Bintu dan haka yace Mimi tabbas yau zaki kasance mai alfahari dani, tabbas hawaye bazasu fito daga cikin idanuwa taba haka Khalil yana ta, zan saka juriya acikin zuciya ta, sosai, bazanyi kuka ba addu'a kawai nake bukata,


Mekira ne ya fara magana dayan bangaran yazo saura dayan bangaran shuru har yanzu kodai yaji tsoro ne ya gudu, ae kuwa mutanin wajan suka fashe da dariya har anfara surutu ana cewa ae dama bazai iyaba matsoraci ne dama wazai iya da Bushar fili yaciki da surutun mutani, shikuma Bushar saiwani wage baki yake dajin anyaba masa, Bushar duk atunanin sa yazata gargadin da yayiwa Khalil ne yasashi guduwa, kawai bazatao ba tsammani sai ganin Khalil sukayi atsakiyar fili babu riga ajikin sa kamar dai Bushar, ae kuwa fili yasake fashewa da surutu.


Saida me magana yafara magana asaurara yanzu gasa zata soma dan haka kowa yazauna shuru yayi kallon gasa zamuga atsakanin Bushar da Garkuwa wazaiyi nasara, sosai mutani sukayi shuru suka nutsu danganin wannan gasar yadda zata kayya,


Kaka Alili Baffah gabaki dayan su basa cikin haiyacin su atsorace suke sungama sadaukarwa cewa Khalil yafadi sbd kafun sufito gidama kuka yake duk jikin su yayi sanyi,


Za'a fara cewar mai gabatarwa Bushar matso ae kuwa Bushar ya matso dawani uban bulala ahanun sa yana jujuyawa idanwan Khalil nae yadawo kan mutani ae tuni jikin sa yadau rawa, yayin da mutani sukaga wannan bulalan suka fara magana kasa-kasa suna nuna bulala ae wannan bulalan ko daya aka maka sai kayi kuka bare kuma dari haka mutani suke ta magana,


Mai gabatarwa yace wannan gasar takunsa abu biyu, dafarko Bushar zaiyi bulalawa Garkuwa har guda dari, idan har Garkuwa idan yayi hawaye kuma shikenan yarasa Bintu, idan kuma baiyi hawaye ba to nan da sati guda mako kenan za'asake dawowa domin gasar amma kuma akan Bushar shima za'a masa bulala dari, idan shima baiyi hawaye ba tofa tabbas za'acigaba da wannan gasar har sanda daya daga cikin su zaiyi kuka, dan haka mai gabatarwa ya kirawo Bushar yace zan kirga uku kacal, ina kamawa sai afara gasar,

Bushar tunkar Khalil yake da wata uban bulala ahannun sa, ae kuwa Khalil ganin wannan bulalan hanun Bushar yashiga cikin dimuwa harta kai ga yana kokarin barin filin baki daya, kamar akun nuwar sa yaji magana nan Bintu"koda jikin ka bazai dauka ba amma nasan zuciyar ka zata dauka nasan matsayin da nake dashi acikin wannan zuciyar taka, " ae kuwa Khalil yatsaya cak dumin yanajin maganar Bintu kamar yanzu take masa,

Mai gabatarwa kuma yafara kirgan sa, daya, biyu, uku, afara aekuwa, ae kuwa Bushar yadago bulalan nan yazubawa Khalil bawan Allah, adai-dai lokacin da Bushar yazubawa Khalili adai-dai lokacin Kaka, Alilil, Baffah suka runtsa idanuwan su dan ganin kar idanuwan su ganin halin da Khalil zaishiga, awannan lokacin kuma Bintu addu'a kawai takeyi yayin da Khalil addu'a yake tayi cikin zuciyar sa, tabbas Khalil yaji bulalan nan amma idanuwan sa sunyi jaa runtsa su yayi, babu alamun kuka attare dashi, saida Bushar yayiwa Khalil bulala biyar kamun ya tsaya dan duba idanuwar Khalil ko yayi hawaye amma kuma abun mamaki aduba idanuwar Khalil babu ko alaman hawaye aciki,


Ae kuwa mai gabatarwa yace aradu idanuwar Garkuwa babu ko d'igon hawaye ciki dan haka acigaba, ae kuwa Bushar yashiga cikin damuwa meyasa Khalil baiyi hawaye ba, amma kuma ae da saura da yawa, Bushar yacigaba da bulalawa Khalil har yana hadawa da mugun ta, saida yayi bulala ashirin kafin Bushar yatsaya dan duba idanuwar Khalil, dasuke aruntse mai gabatarwa ya zakayo wajan fuskan Khalil dan ganin ko Khalil yayi hawaye amma kuma har yanzu Khalil babu ko hawaye cikin idanuwar sa, ae kuwa, ae kuwa mai gabatarwa yace "aradu idanuwar sa ko ruwa babu, " ae mutani suka fara magana gaskiya yaburge ni jarumin gaske ne, a fuska kamar bazaiyi jarumta ba, mutani da yawa suka fara yabon sa suna zagin Bushar, dama tun can bason sa suke ba tsoron sa sukeji, amma kuma yau sunga wanda yafishi jarumta, kuma babu wata sihiri ajikin sa hakan ya matukar burge su,


Bushar kuma yashiga cikin tashin hankali sosai haka yacigaba da bulalawa Khalil har akagama bulalan batare da digon hawaye yazuba acikin idanuwar saba, ae kuwa fili yakafce da surutu da hayaniya sosai, anata yabon Khalil kai tsaye akanufa Khalil akayi sama dashi sai gidan Kaka jikin sa sai futar da jini yakeyi, yayin da mai gabarwa yana cewa tabbas Garkuwa ya gwada jarumta anan shima wata sati za'ayi nashi, Bushar bai tsaya sauraran duk wata magana nan da'akeyiba kai tsaye ya nufa wajan Bokan sa,


Khalil gabaki daya asume yake baima san yadda kansa yake ba, Bintu sujjad tayi tagodewa ubagijin ta, saida Kaka yayi maganawa mutani akan suyi hkr zasuyi maganiwa Khalil dan ayanzu yana bukatar maganin ae kuwa suka tsaya akofar gidan Kaka damuwar su Khalil ya farka dan yanzu cewa suke sunsamu jarumi agarin su wanda bashida sihiri ajikin sa, magani sosai agashigayiwa Khalil


Bushar zaune agaban Boka sai masifa yakeyiwa Boka, kace haba haba Boka kaifa da kanka kafadamun cewa tabbas sai yayi kuka idan har nazane sa da wannan bulalan amma kuma yau munyi gasar amma kuma ko kuka baiyi ba, Boka yadobi Bushar yace "tabbas shima wannan mutumin da kukayi shadi dashi naga abubuwa da yawa ajikin sa amma kuma ka kwantar da hankalin ka karka damu ba wata sati nakaba kabari idan har akayi naga akagama too zan fadamaka wata gasar daza ka sauya da wannan shadin dan haka ka kwantar da hankalin ka sosai Boka yake ta maganawa Bushar dan kwantar masa da hankali ae kuwa yayi nasara akan sa,


Alhmdullah jikin Khalil yad'an samu sauki har yana iya fita kofar gida, Alili yadubi Kaka yace Kaka bamusamu daman fadama cewa fa ran da mukaje daukan bulalan nan munga Bushar dashi da wani mutumin da gabaki daya ba'a iya kallon fuskan sa, munji tattaunawar su suna jayya da Bushar akan dole sai yayi amfani da bulalan da mukaje daukawa amma shi Bushar yace sam bazaiyi amfani da wannan bulalan ba, Kaka tsayawa yayi cak yana tunanin wanene wannan mutumin haka, gabaki daya kaka yafada duniyar tunani damuwan sa yagano wannan mutum, can kuma ya numfasa kana yadaura dacewa bakuga fuskan saba? Alili yace ehh kaka ae kuwa Kaka yace nifa ina ji ajiki na Kakan Bushar ne indai kuma takasance haka to tabbas akwai babban kad'ubali agaban mu dan Kakan Bushar babban matsafi ne, tabbas kuyi kokari kuma kudage danganin kunsamu wannan bulalan, dan wannan bulala tabbas zata taimaka muku,


Kaka yanumfasa kana yadaura dacewa kunsa masifar dake tattare da wannan mutumin Kakan Bushar, Shehu to tabbas akwai babban aeki agaban mu damuni muyi shadi dashi amma Allah yabani narasa akan sa, Alili yace insha Allahu Allah zaibamu nasara akan sa, yanzu haka zamusharya domin dauko bulalan nan kuma zamu dauko ta da yardan Allah, yau saura kwana uku gasar dan haka yau da dare zamuje, fatan alkhairi Kaka yamusu dafatan nasara,


SIDDARTH
_________________________________________
Siddarth wata daya yayi a Negeria yakoma Amireca domin kamala karatun sa abubuwa sunyiwa Siddarth yawa ga nauyin da Alh. Kaka ya daura masa ga kuma Zoey a wannan lokacin tana addaban rayuwar sa akan dole sai ya aure ta shikuma baiga abun so ajikin Zoey ba,


Zoey zaune ita da kawan ta mecol suna magana akan Siddarth mecol tace "Zoey ai tun farko nabaki wannan shawara amma kince ke bazakibi shawaran ba to yanzu yakike so nayi miki, " Zoeya tace mecol bazan wajan ki dan jan magana ba kuma banzo dan nabi shawaran kiba kawai nazo gunki, nazo gunki ne dan kisake bani wata shawara, nafuskan ta Siddarth shi mutum ne wanda kyalekyale bashi gaban sa kuma naga shi mutum ne wanda yakeson taimako, shine nazo kiban shawara akan abun da zan jawo hankalin sa gare ni, dan jam kadan mecol tayi kana tace kin san wani abu kawo kunnan ki infada miki,


Sana ce tafio daga loyala beach sanye cikin wando palazzo black colour da shirt riavy blue tayi rowling wani veil navy blue akan ta, tana rataye da wata yar bag black colour dayan hannun ta kuma na dama cup ne na coffe rike a hannun tafiya take tana shan wannan coffen tana lumshe idanuwan ta da sukayi jaa saboda kukan rashin wannan mutumin da yataemake ta yauma tagaji da kukan ne tacewa mom dinta zata fita shan iska ita dayan ta tafito babu Suha sai direba dake jiran ta a moto,


Siddarth ne yau gabaki daya baya cikin haiyacin sa tafiya yake cikin moton sa gawanu uban yunwa dayake ji dan rabon sa da abinci tun jiya parking yayi dai-dai loyola beach domin yana bukatar sha iska, fitowa yayi daga moton cikin shigar jamfa amma babu hula akan sa suman kan sa duk yabaje masa agadon bayan sa kai kace mace ne tafiya yake kamar wanda bai son taka kasa,


Sana tana shan coffen ta tana lumshe idanuwan ta gashi kuma tafada duniyar tunanin da ayanzu ya aure ta tuninin wannan mutum takeyi bata ankara ba da wani babban tudu dayake gaban taba tudun da idan tafada ciki to tabbas sai dai muce Allah yajikan ta gangara take kawai bata kula da gaban taba, mutani sai magana suke mata amma ina, bata jinsu dumin bata cikin haiyacin ta dai-dai lokacin da Siddarth yakai idanuwan sa gunda aketayin surutun mutani daura idanuwan sa yayi akan ta datake dafda fadi ai kuwa da sauri da gudu Siddarth ya nufo wajan ta rumgumata yayi sukayi kasa turmusu suka farayi akasa, wannan ya haukan wannan hakama wannan har suka isa bakin wannan tudun kuma Sana ne tayi kasa, rike hannun ta daya Saddarth yayi yana mata magana cikin zazzakar muryan sa mai dadin sauraro "karki sakeni kirike ni sosai tarike hannun sa yayin da dayan hannun yana lilo akasa da dukan jikin ta rikon da Siddarth yamata ne kawai ya hanata faduwa, kasa da tuni ta fada kasa magana yake mata cikin muryan sa karki sake hunnuna insha Allahu bazaki fadi ba, idanuwan ta tazuba masa babu ko kiftawa sosai take kallon sa kamar tasamu tv bataki su tabbata a haka ba miko dayan hunnu yayi akan tarike sa ai kuwa da tema kon Allah sai ga Sana tamiko janta yake har ya fito da ita daga ciki zubewa sukayi akasa yayin dashi yafadi dabaya ita kuma da ruf da ciki gashin kanta duk yarufe musu fuskan su sai da su sai da sukayi minti kusan goma kafun Siddarth yacilla ta gefe kana yadawo kusa da ita hunnun sa ya daga ya zafga mata mari kana yaja laben bakin ta ya kuma jaa yafara magana cikin sanyi muryan sa, "meyasa kike son kashe kanki, " abunda yafada mata kenan yabar gun,


Kallon sa take har yabar gun sai da tadaina kallon sa kafun tadawo haiyacin ta, bin bayan sa tayi amma kuma har yabar gun, kuka take tana surutu da sumbatu gabaki daya tafita haiyacin ta, direban ta haka yazo yasame ta, "madam lapiya wani abu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login